Showing 105001 words to 108000 words out of 141223 words

Chapter 36 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

da Zakiyya ta fice MATA a rai,Amma tun da yadawo da yadda tayi Hankali sai komai a Hankali ya dinga fita daga zuciyar Maama najin haushin Zakiyyah da takeyi,na ɗiban albarkar da tai MATA lokacin barowarta gidan mukhtar🤗
A Hakan gidan nasu Kullum da mutane masu zuwa ganin sabon gida da kuma barkar baby, ABIE yafi kowa murna da wannan, yaita jagula babyn, Bilkisu bata cewa komai Amma da zarar ya taɓa ta Zakiyyah tana wajen lallai nan zakiga yadda ake ƙuli_ƙuli da ABIE🤣, dan haka indai Zakiyyah tana wajen Baya kula babyn,saboda yasan Hali maganin kar ayi kar a Fara.
Bilkisu tana jin daɗin Zama da Zakiyyah, wacce dama ita ma tun farko bada Wani abun ta shigo gidanba, halin Zakiyyah ne kawai ada Yanzu kam sai sam barka.
Mukhtar yabawa Bilkisu zaɓin sunan da za'a sanyawa baby, ko ɗar Babu Bilkisu tace ita kam sunan babyn ta *ZAKIYYAH* mukhtar baiyi musu ba yai MATA kutuba da Hakan, kuma yaji daɗi sosai ganin matansa suna zaman amana Irin Hakan, Zakiyyah tafi kowa murna da wannan abu da Bilkisu tai MATA na kara, ta kuma sanin lallai Bilkisu Mutuniyar kirki ce, taji daɗi sosai!
ABIE sai murna take yafara kiran babyn da little Mammah, kuji me wayi fa fur ya hana a canza MATA suna, sai sunan da Yake kiran mammahn tashi ta asali da shi, ya su Bilkisu suka iya haka suke kiranta dashi Suma ko suce Mammah ko little ɗin ki su haɗe kamar yadda ABIE yake faɗa🤩.


Hajiya Jameela tana jin sunan baby tasan Lallai Zama yayi Dadi da Zakiyyah da Bilkisu wanda shine burinta ,ko dan kwanciyar Hankalin ɗan ta, wanda abaya bai samu ba.
rainon mammah a wajen Zakiyyah yake indai ma mama zata Sha ba takaiwa Bilkisu ita, Hakan baiwa ABIE daɗi ba domin Baya sakewa ya taɓa Little in tana wajen Zakiyyah.
Tuni aka saks ABIE a school dayake yaro ne mai wayo, nan danan da anyi karatu ya ɗauke.








_______AKEEL da AQEEL____


Ƙaramar magana ta Zama Babba, Duk su biyun burinsu su mallaki wannan vedios ɗin, su sake kalla shine burinsu, shi AQEEL yana da dauriya dama kun sani, ba lallai a gane meke damunsa ba, Amma shi ma AKEEL Ba bu bai iya ɓoye ɓoye ba, yaga abun kullum gaba yakeyi dan haka, yace 'nidai bro kafini taurin zuciya da ɓoye damuwa, Nikam bazan iyaba yau zan wa Abbu maganar ya mallakamun flash ɗin nan inason ƙara gani, saboda ai dama namune mu yayi wa, kaga ya AJIYE a gurisa ai Babu amfani" tun da AKEEL yake magana AQEEL ya kafeshi da idanuwa, daga ƙarshe yace " tab Nikam bazan iyaba, Vedios ɗin me wannan shirmen ni fa har na manta da shi ma(kuji ƙarya fans,mutumin da kullum tunanin su yakeyi) ALLAH yabaka Sa'a sai kai ta karɓa, Nikam bazan iya ɓata lokaci na ba! Kamar gaske ya ƙarasa maganar yana haɗe Rai, " ai shikenan Nikam sai na kalli abuna mi kaɗai, kaishi zanyi ma Amayar mun dashi a turan ta waya ta kawai,cewar AKEEL ya zata da gaske AQEEL yake, nan kuwa baisan gwamma shi da shi ba ma Akan zaƙuwar samun vedios ɗin.


Hakan ce tafaru da AKEEL bayan sun gama breakfast Duk Suna dining ɗin, Akeel yace"Abbu inason kabani flash ɗin nan nakai Amayar Mana dashi na waya inason ƙara kalla yana sani nishaɗi,Me AKEELA zatayi in ba dariya ba,haka ma Mommah jin abunda ɗan ta yafaɗa iya gaskiyar sa, dan dama shi Baya ɓoye ɓoye, gogan naku wato AQEEL ko motsi " kai yanzu Akeel sai kace kanason ƙara ganin wannan vedion,wanda naga baku kalla da muhimmanci ba, inji Abbu cikin muryar barkwanci yana kallon Akeel ɗin, Amma reaction ɗinsa yana ga AQEEL yaji ko shima zai ce yanaso amma sai yaji shiru". Ea gaskia Abbu inason ƙara gani sa yai mun kyau! To Shikenan ka kwantar da hankinka zan sa a mayar dashi Vedios na waya sai na sa atura maka,tun da kai kadaine me buƙata, shi Dan uwanka bayaso, " ea gaskiya Abbu mene abun ƙara kalla a Wannan vedios ɗin, shi ma AKEEL ne da bashi da aikin yi, AQEEL yai wannan maganar yana tashi yana barin dining ɗin, alamun ko ajikinsa, kuma bai damu da vedios ɗin ba, Amma cikin Ransa yafi kowa son ƙara gani😄,daga Abbu har Mommah bakinsu a sake take jin furucin AQEEL ɗin, haka na AKEELA me dariya sai ta ƙunshe kayarta, shi kam AKEEL sakato yayi yana bin bayan AQEEL da kallo!
Shikenan AKEEL je ka zan baka kai kaɗai, ka rabu da ɗan uwanka mai bauɗaɗɗen Hali,shima yana so ne na Sani,kawai halinsa na miskilanci zai hanashi tambaya, haka suka watse a dining ɗin.
AKEEL sai da yaiwa AQEEL magana Akan abun da ɗa zu yayi, aikuwa sai yace "bro ƙarya zanyi to bana buƙatar vedios ɗin ai!
To Shikenan ai ni inason ganin abuna yana sani nishaɗi.


Aikuwa a Ranar Abbu yacika alƙawari aka yiwa AKEEL editing nasa, yana zaune yana kalla yana kwasar dariya, Amma su AQEEL ya basar kamar besan me yake kalla ba,idan anzo wajen AQEEL da HIDAYAH sai yace "bro kallu show ya wuceka,Amma ina sai AQEEL yace 'kaine baka da aikin yi ai,Amma a zuciyarsa yana son gani, da zarar AKEEL ya ajiye wayar ko shigo bayi ko da daddare zai buɗe wayar AKEEL ɗin,yasan password nasa,me zasu ɓoyewa junansu, komai nasu tare sukeyi, ya kalli vedios ɗin yana nishaɗi, " nafika wayo ai dama bro tun muna Yara, yanzu gashi a Ruwan Sanyi ina kallan Vedios ɗin batare da na zubar da ajina ba😄,kai kuwa fa,haka kullum suke kasancewa, ALLAH ya tona maka asiri AQEEL, AKEEL ya kamaka kana kallon Vedios ɗin da kace baka damu dashi ba.




____HAUWA DA KAWU ISMA'IL___


Tun bata kulashi a Asibitin har tazo tana kulashi, Ganin tabbas yayi nadama ta gaskia,gana ɗaya kullum sai yayi Kuka, da neman gafafar ita kanta Hauwa ɗin, hakane ya sanyaya Maya zuciya take bashi kulawa, kuma ta na Kwantar Masa da Hankali, Ganin jininsa yayi sama sosai, saboda yasan yanzu dai yanajin sauƙi sai prison saboda shi banki Baya lamuni balle afuwa, karaya saura kaɗan dan har ya na takawa shi kaɗai, sallamar su za'ayi ma, Yanzu ina suka kama ne Babu gidan komawa, su Meenal sai gidansu Hauwa suka koma anan suke kwana, Kawu isma'il fa yau jikinsa da ɗan da ma, dan haka taje can gidansu domin gyara musu ɗakin da zasu zauna, malam babanta ya Basu, kafin Kawu isma'il ɗin ya samu mafita, jibi Za'a sallamesu, dan haka Shi kaɗaine a ɗakin jinyar ya na ta tunanin duniya! Yasan dai muddin aka sallameshi shikenan sai prison" wai shi isma'il ne a Wannan yanayin, mai juya nera kai ALLAH ya karemun da cin dukiyar maraya da cin amanar zumunci,dan kuwa shine ya janyo Masa komai, dan shima Kawu isma'il ɗin daidai gwargwado yana da rufin asirin sa tunda san zuciya kawai yakaishi taɓa dukiyar Amana,gashi yadda yanzu tazame Masa!
Kawai sallama yaji akansa"ƙirjinsa yai mummunar bugawa! Dan kuwa bazai manta da muryar Ƴan fashin nan ba! Wato su snake da awale da roci...........






Lalläi ne fans Muje zuwa






✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰
6/20/24, 10:19 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba)



Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM}
08128131163


Marubuciyar
Komai nisan jifa
Hakan ba kuskure bane


____________________
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A*
____________________


*PAGE FIFTY EIGHT 58*


*My fans I'm back Again🥰 , Happy Eid Al Adha*


Nadawo daga esolation na wajen 3month and above, idan kunci gaba da ƙarancin comment ko late comment zan kuma tafiya esolation ɗin ko na haƙura da typing ɗin kwayi imagination da kanku ku ku karasa🤣
ILove you All my Fans
Seerat
Haseena
Mummy Waleed
Aisha Sulaiman
Zeetopha..........✍️kuna da yawa 🥹 Zakiyyah tana miƙo gaisuwa sosai🙏






_______USMAN_____


Daya Fara Shan maganin da Doctor ya bashi shikam baiji sani sauƙi ba,abu ma sai gaba Yakeyi, idan gabansa yafara Masa ciwo Kamar zai mutu,ga kumburi abun gwanin tausayi ga kwailewa da yakeyi, yana Ruwa,musamman wajen ball's ɗin sa kamar lalacewa yakeson yayi,tuni clara tabarshi,daga shi sai halinsa ta kwashe Masa ƴan kadarorin daya mallaka ta ƙara gaba,to dama abunda takeso a gareshi shine sex kuma yanzu Babu abunyi.


Abokan shashancinsa ƴan Homosexual kuwa tunda suka ga yanzu Babu mammora gareshi suka kaleshi,ina Abun yake,ƙyanƙyamin sa sukeji ma,Duniya fa tajuyawa Usman Ɗan jimmai😀 Baya,ciwo idan yatashi kamar ya mutu,idan ya lafa kuna kamar bashi ba,akwai WANI Abokin Harkallarsa Bature me suna Alex yayi tafiya ya jima bai haɗu da Usman ba in zasuyi masha'arsu Baya WANI kiransa takanas yake Zuwa gidansa yau ma Hakan ce ta faru,yana Zuwa ya tarar da Usman a halin da yake ciki, kunsan turawa akwai tausayi,ya kwashi Usman sai Asibiti cikin gaggawa!
Doctor ya dubashi, yace Ball's ɗin sa sun lalace sai dai a yanke,Amma shi da Haihuwa har abada,in Anyi Aikin andace ma Kenan,Amma yawanci ana mutuwa amma wasu kuna ana samun nasara!
Cikin gaggawa Alex yabada maƙudan ƙudi aka shiga da Usman emergency surgery,
Ba'ayi cikakken Awa biyar ba aka gurguro da Usman cikin gadon marasa lafiya gwanin tausayi! A Ranar ake farfaɗowa,Amma shikam sai da yayi Kwana da wuni ya farfaɗo,Anyi aiki a Sa'a sai dai shi da ƴaƴa sai dai yagansu a wajen wasu Amma shikam Babu,satinsa hudu a Asibiti yafara jin sauƙi,dan Kullum safe da yamma sai Anyi dressing ɗin wajen kuma sai ya fita daga hayyacinsa! Yanzu Alhamdulillahi.
Alex yai tafiyarsa nan,
Tun da Usman yaji sauƙi kuma sai tsoron ALLAH ya shigeshi Akan Abubuwan daya aikata a Rayuwarsa musamman cutar da yaiwa Shukrah yakuma tuna da Daddy Dole yakoma gida kam ya nemi gafarar ta ga Akeela ma da Mama wacce Yasan shine musabbabin cutarta datake fama da ita har yanzu,haka yafara shirin durowa 9ja.........






___KAWU ISMA'IL___




Kafin yadawo hayyacinsa har su snake da roci da awale har sun ƙaraso gaban gadonsa,sai ga kawu isma'il jikinsa na kakkarwa!
Dan yasan zuwansu ba alkhair bane garesa, yatuna irin sharrin daya musu a Tv da Radio,yasan sunji Zuwa sukayi ɗaukar fansa!
Isma'il Zuwa wajenka mukayi!dan kuwa munji irin sharrin da kai Mana a Media, lokacin munzo wuya mun ɗau Alwashin sai mun yanke maka ƙafa ɗaya shine fansar sharrin daka Mana nacewa mune Duk wata dukiya daka mallaka data marayun ALLAH mu muka ƙwace ta......Kawu Isma'il jin Abunda Awale yace ai iwu ya kurma kafin yafara magiya garesu Akan suyi haƙuri,ai ya janye furucinsa a inda yayi......
Dakatar dashi Roci yayi da cewa kai ka Mana shiru ai da ace bamu watsar da kudurin mu ba ai da tuni yanzu maganar nan da ake baka da ƙafa, ALLAH ya shirye ka ai kaga aya bayyana na yanzu,nasan ko kuɗi ka gani a ƙasa na marayu bazaka ci ba balle a baka ka Handame sai anjima cewar snake yana ficewa muƙarrabansa na bin bayansa!Kawu Isma'il kuwa wata ajiyar zuciya yayi haɗe da idanuwansa Suna ƙafewa gaba ɗaya alamun ruɗu yasa ya Suma!


Su yaran snake wasu daban fashi sukaje Wani Gida to gidan soja ne me gadi aikuwa ya tumfarosu shine fa sukasa gudun wuce Sa'a a motar su! Aikuwa sukayi hadari Wani mummuna daga masu karaya sai masu mutuwa!Wani mai suna gwanki take kansa ya fashe sai ga ƙwakwalwa a ƙasa,shine fa aka kawo su Asibitin,dan shi sojan zuwaya gida yayi,bai bisu ba, dan kuwa yagansu da gangan makamai a hannunsa shikam ko Allura Babu yasan a banza zasu kasheshi,shine fa dama su Roci suna daga can gaba to daidai wajensu abun yafaru,sai sukayi dabarar kwashe makaman a motar su,A sa'annan suka Kira ƴan sanda , Kafin suzo fa suka bar gurin! Koda Ƴan sanda sukazo basusan Ƴan fashi bane! shine fa aka kawo jikkatattun Asibitin da kawu Ismail yake,
Kuma tun Hatsarin da Ƴan uwansu sukayi jikinsu yayi Sanyi, tsoron ALLAH ya shigesu, Yanzu Haka Shirin miƙa kansu da Hukuma suke!
sunzo shigewa zuwa dubiya kamar mutanen arziƙi shinefa suna hangi Kawu Isma'il ta window.....


Doctor yazo yaga halin da Kawu Isma'il Yake nan ya ɗaura Masa ruwa, sai yamma Hauwa ta dawo sannan Kawu Isma'il ya farfaɗo yabata labarin yadda sukayi dasu roci, Addu'ar shiriya tai musu.
Kwana biyu tsakani aka sallami Kawu Isma'il dan kuwa karaya ta warke, haka suka koma gidansu Hauwa da zama gwanin tausayi, Yanzu dai kawu Isma'il tsoron sammacin kotu yakeyi...........






___AKEEL DA AQEEL___




misalin 2:00am na dare. AKEEL ya Tashi ya shiga bayi,bargon da Yake jikinsa ya cire ya ajiye a gadonsa,sai yayi like yana kwance,to Dai Dai lokacin da AQEEL yasa alarm a wayarsa ,na Tashi kallon Vedios ɗin su HADIYYAH, yana tashi kuwa,Dama Glass ɗinsa yana wurin da Yaje ajiyewa saboda tashin dare,bayan yasa Glass ɗin ya dumfari wayar AKEEL kai tsaye ya shiga ya Fara kalla ya juya baya,yana kalla yanashan murmushi Abunsa,basaiwa junansu gate da wayarsu shiyasa bai turawa wayarsa ba,gwamma ya kalla a ta AKEEL ɗin, A daidai lokacin AKEEL ya kammala abunda zaiyi a bayi ya fito shi AQEEL ya tafi shauƙi beji ƙarar ruwa a bayi ba, da kuma ƙarar rufe ƙofa, mamaki yakama AKEEL Ganin bro yana kallo daidai wannan Lokacin,mutumin da bashi da lafiyar idanu da sassarfa ya tawo domin yaga ne yake kallo,Amma ina!!!! Har yazo gareshi yaga abunda yake kallo Amma ina AQEEL anyi nisa cikin nishaɗi baiji bro ba,sai da bro ya kwa che wayarsa sannan bro yadawo hayyacinsa sai kuma kunya! Ya haɗe Rai zai juya ya kwanta aikuwa bro yakewa bro " dakata Mana bro kwanciyar me zakayi aina kamaka,dole Abbu yaji wannan magana! Ya ƙarasa zancen da sheƙewa da dariyar shakiyanci! Shikam AQEEL ya shaƙa,kuna yaji kunyar kamashi da bro yayi,Amma kunsan gogan naku akwai shanye abu.


Sai da Asba da suka Tashi,sai Wani kumbure kumbure AQEEL yakeyi,shikam AKEEL yana kallonsa ya basar, yasan koya kulashi bazai sauko ba,tabarmar kunya Kenan!


A Masallaci bayan idar da Sallah sun shigo gida AQEEL yai wuf ya komo gida Babu jira,shi kuwa AKEEL yana wajen Abbu yana Bashi labarin yadda ya faru tsakaninsu aikuwa Abbu yasha dariya, yace wa AKEEL nasan hakan zata faru,ka ƙyale ɗan uwanka kasan halinsa ma ai Muje zuwa dai.


A wajen breakfast ma haka AQEEL yake a kumbure, sai da Abbu yaga abun babu ƙarewa sannan yace ' mommahn AQEEL Ɗanki fa kumburin ankamashi dumu_dumu yana kallon Vedios ɗin ƴaƴana shine Yake wannan kumburin,Ai kinsan da kunya mutum yagama cika baki kuma akamashi!!!!!!!! Gaba ɗaya aka kwashe da dariya har AKEELA ma!
Mommah tace "Abbu Dan ALLAH ku rabarmun da ɗa na Hakan ai shine daidai ba wai ya dinga zaƙewa ba, ai shine namijin! Bawaninan mommahn AQEEL kare Ɗanki kike kawai! Amma kowa yaji Hakan yasan....Abbun AKEEL ba fa haka bane....... To mene itama ta katseshi haka sukaita barkwanci a wajen breakfast ɗin nan like ahalin da suke cikin farin ciki kamar abaya Basu kasance cikin baƙin ciki ba! Daga ƙarshe AQEEL ya karɓi lefinsa da cewa "nifa kawai fa kallo nakeyi, shine fa ya ƙare Vedios ɗin ya shigo shine nifa nake kalla, kama faɗi gaskiya bro kallo talatainin dare sai aka kuma dariya.........








______HADIYYAH DA HIDAYAH_______




Tun daga kallon Vedios kuma sai Basu da Abun so su Gani Kamar AQEEL da AKEEL abu kamar tsafi fa kuma su biyun,sai suka Fara tunanin bro da bro ganinsu da sukayi a Asibiti da a Tallafy foundation ya dinga dawo musu,sarkin soyayya HADIYYAH sai taga tunanin AQEEL (wanda batasan wanene daga ciki ba me surutun ko miskilin) yana neman mantar da ita Mus'ab da yaudarar da take ganin yaimata Alhalin yai MATA bayanin komai fa.


Mara soyayyar ma wato HIDAYAH wacce bata damu da Mahmoud bama sai gashi Yanzu tunanin AKEEL (itama batasan wanene daga ciki ba) ya zame MATA kamar me data zauna sai tunanin sa, su kam har mamaki Hakan yake Basu,sai suyita yiwa junansu tambaya Amma sis da sis sai suka ce kyautatawar da Abbunsu yai Musu ne,shiyasa suke tunanin ƴaƴansa kuji fa Fans wai hakane Fans?
Yanzu dai burin HADIYYAH DA HIDAYAH suyi tozali da twins bro and bro na Alhaji tallafy........










_____SA'ADATU_____




Alhaji Gambo fa yakasa gane kanta, hulaƙancin yai daban na gobe daban! Shikam Baya ta tata,tsakani da ALLAH Yake Zaune da sauran matansa wato Hajiya ikilima da Hajiya suwaiba da kuma Hajiya sahura,Suma kuma yanzu sunyi Hankali tun Akan abunda Sa'adatu dashi Alhajin yai musu abaya ganin cikin da tasukewa iyayi zance ya ƙare. Sun haɗe kansu sun duƙufa da addu'a ALLAH yabawa mijinsu Haihuwa ko a wa cece kuwa!cikin ikon ALLAH kuwa sai ga Suwaiba Babu lafiya har dasu Amai,dan haka Sahura ta ɗau mota domin kai ta asibiti, Suna shiga asibiti itama taji warin asibiti itama tafara jin babu daɗi kanta yafara ciwo,Dan haka bayan duba Suwaiba akace ciki ne da ita ɗan Wata huɗu ma,sunyi murna sosai kamar Babu gobe sunwa ALLAH godiya, ciwon kan da Sahura take ne yasa itama aka MATA gwaje gwaje aka gano itama ashe cikin gareta wata Biyu ita kuma! Wannan wane irin farin ciki ne yasamu Alhaji Gambo Fans?
Dan haka jikin Hajiya suwaiba babu ƙwari,na Sahura kuma kanta na sarawa harda jiri,dan haka takira Hajiya ikilima a waya suka mata albishir, aikuwa tai murna kan kace mene sai gata a Asibitin a da driver ya juya da motar ita kuma ta shiga wacce Hajiya Sahura suka shigo sai murna sukewa junansu kamar ba kishiyoyin da suka tafka masifa da bala'i a Baya ba.


Tun daga sannan Hajiya ikilima take Basu kulawa ta musamman abun gwanin burgewa!


Alhaji Gambo yayi murna da wannan kyauta ta ALLAH daya bashi Amma bai zaƙe kamar na Sa'adatu ba daga ne cikin har Mara cikin kulawa ɗaya yake Basu,sai Addu'ar ingantawa take wa matan sa fatan ALLAH yabawa ikilima itama da Sa'adatu wacce Yanzu yakasa gane kanta, har yau bai gaya mata cewa Sahura da suwaiba Suna da ciki ba.......topha ko me Sa'adatu zatayi intaji bayyanar cikin su Hajiya suwaiba da Hajiya Sahura




✍️Oum ARQAM
6/22/24, 9:47 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba)



Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM}
08128131163


Marubuciyar
Komai nisan jifa
Hakan ba kuskure bane


____________________
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A*
____________________


*PAGE FIFTY NINE 59*


*My fans I'm back Again🥰 , in Sha ALLAH Har End,indai ba Halin Kuka kuma ba 🌝*






_______USMAN_____


_Cikin ikon ALLAH da jikin ya kuma warwarewa dan Yanzu andaina dressing guri ya warke tatas, Doctor yayi mamakin Hakan saboda irin wannan aikin majority rasa rai akeyi.
Ya sauka lafiya a 9ja ƙasarmu ta gado.
Gidansu inda yabar Baba da Umma nan yanufa saidai yasamu labarin bakin cikin barinsa gida da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login