Showing 108001 words to 111000 words out of 141223 words
Chapter 37 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
kuma Abunda yasamu Shukrah yai ajalinsa Usman yaci Kuka,bai bai samu Umma a gidan ba saboda bata nan,Gidan ɗan yayanta daya ɗauketa nan yaiwa tsinke, aikuwa sai ga umma tana Kuka! Ganin yadda Usman Ɗan ƙwalisa ya koma yafita daga hayyacinsa,(Fans batasan bala'in daya sameshi ba, (Umma Usman ai shi Yanzu zan iya cewa dashi gwamma Babu yasin🤣dan kuwa Fanko ne)
Suna hirar Yake gaya MATA cewa ai cuta yayi,bai faɗi ainahin abunda ya sameshi ba,nan dai Umma tai Masa tatas tace "Usman cuta tasa kadawo garemu ai dama duniya ba gida bane,haka naita gayawa Babanka,Amma yasa abun a Ransa ga ɓacin ran abinda ya samu Shukrah,sai ga Usman yana kuka da neman gafafar ta, sannan ya nemi Alfarmar yanason ta rakashi wajen Mama dan yasan Yanzu fushi take dashi, yagano Shukrah da Daddy batayi Musu ba ta shirya direban gidan ya haɗa daga ita har Usman sai gidan Jimmai ikon ALLAH.
______GIDAN JIMMAI______
Shukrah yau tana scholl exam suke za'a kammala Secondry,Daddy ma yana school, dan haka Saida tayi abunda tasan zatayi ta tanadarwa da Jimmai komai a kusa da ita,dan Yanzu hannunta yana motsi tana iya daukan abu dashi,tana Hawa fo tayi tsarki, saidai tabarshi wajen dan kuwa babu kafafun tafiya Babu bakin magana kuma,ta kammala Fitsari kenan umma tayi Sallama Duk da ba amsawa zatayi ba! Innah sai a slow
Usman ne ya biyo bayanta,Hakan ne Yasa Jimmai shiga shock wanda yasa bakinta karkarwa kamar wasa sai ji sukayi tace"k..a..i.. k..a...i..k..a..i.n..e!cikin mamaki Umma tace "Jimmai kece yau kike magana Alhamdulillahi ea tabbas Usman ne ALLAH ya amsa du'a'in mu gashi yadawo Kuka ya ƙare (kowa yana tunanin kukan da Jimmai take na Rashin Usman ne,nan kuwa basusan.....)
Umma Hannun Usman ta riƙe sannan ta jashi har in da Jimmai ke zaune tana sunkuyar dashi alamun ya nemi gafarar ta!
Jimmai dai Kuka takeyi,shima Usman ɗin yafara kukansa yana kallon mahaifiyarsa wanda yasan kowanne Hali ta shiga shine sila,cikin kukan yake magana "Mama ki yafemun nasan Haƙƙinki kine ke bibiyata tunda na tafi........ Nan ya kwashe komai ya faɗa har cutar da yayi da cewa bazai Haihu a duniya ba!
Saiga umma tana salati garin Yaya wannan wace Irin cuta ce Usman haka,cikin in ina ya fayyace musu ai an yanke Masa ball's ɗin sa ne,Amma bai faɗi meyasa ba,sai ga Umma tana Kuka, ita dai Jimmai idanu ta zubawa Usman kukanta ya tsaya, tabbas tasan Alhakin AKEELA marainiyar ALLAH ne,dan bazatace na Shukrah ba dan kuwa wannan SAKAYYAH ce ALLAH nuna MATA,nacin Amanar zumuncin da tayi...
USMAN yaci gaba da magana Umma ki yafemun abunda zan faɗa ita Mama tasan abinda ya faru bakin magana ne bata dashi balle ta gaya muku... Ni..ne nai.wa.shukrah.faɗe ba ko.wa ba kuma Daddy ɗa na ne shi kaɗai ya ragemun a duniya ƙwaina in bayan shi Babu ni Babu Haihuwa,sai ga Umma tana salati "Amma Usman ka cuci kanka ni Hajara,kanwarka uwa ɗaya ina Hankalin ka da tunaninka sai tasa kuka! Yaci gaba da magana " kiyi haƙuri Umma abun da Yasa Hakan......nan ya gaya MATA lokacin zaman Asibitin Baba anan ya samu dama, ALLAH ya taimaki AKEELA bai faɗi nata ba,Kunga my Fans Asiri ya rufu ruf
Umma sai Kuka take gwanin tausayi,data tuna tsinuwa da ALLAH wadai da sukaitawa wanda yaiwa Shukrah wannan aikin,sai da Usman ya fallasa sannan ma tunanin Umma yakai wajen to inba har gida akawa Shukra fyaɗe ba to Wanene? Ko a school aka MATA sai sharar hawaye da majina takeyi gwanin tausayi,daga sama Jimmai tafara magana Sosai " Usman ai dama nasan Duk inda kaje zaka dawo ne kuma ALLAH bazai baka ikon Zama lafiya ba,tunda ni dana gatataka ni kaiwa haka, ka tasa wacce zaka Lalata sai kanwarka uwa ɗaya uba ɗaya, ai abun ya ƙazanta kaɗan ma kafara Gani...... Sai tasa Kuka
Umma ganin kukan Jimmai ya ƙara volume ne yasa ta Fara lallashin da cewa " haba Jimmai baki Masa baki bama yayi haka Inaga kinmasa wannan abu dai ya faru sai dai Haƙuri ALLAH ya kyauta gaba, Yanzu addu'a zamu Masa ta samuwar cikakkiyar lafiya gareshi fushi dashi ba namu bane,Ai yayi nadama sai dai Haƙuri mai faruwa ya faru yanzu yaron nan Abun tausayi wlh jimmai,, Umma tana zancen tana sharewa Jimmai idanu da baki wanda yahu yake zuba, Alamun anjima ba'ayi magana ba!
Jimmai dai sai Kuka da maganganu marasa daɗi take ga Usman,shima sai Kuka yake yana Mama ki yafemun ki tausaya min.....
Tun farkon Fara maganar Shukrah tashigo gidan da sallana Suna Cikin Hatsaniya shiyasa Basuji ba, dan haka jin kamar muryar Yah USMAN da Umma kuma Suna Kuka da maganganu n da Suke ne Yasa ta ɗan tsaya ai sai taji wata magana banbara kawai wai Yah USMAN ne yai MATA Cikin Daddy! Amma har dashi a masu neman wanda yai mata Lallai Yah USMAN ai MATA adalci ba, ya cuceta ya lalata MATA rayuwa ya zasuyi da wannan Abun kunyar! Daddy ɗan Yah USMAN ne kuma ɗan ya uwarsu ɗaya ubansu ɗaya! Wannan wace irin cakwakiya ce sai Kika ya ɓallewa Shukhra gwanin tausayi! Kafin daga bisani Numfashinta ya ɗauke gaba ɗaya, daga waje su Umma sukaji jiiiiiif! Alamun abu ya faɗi Usman ne ya leƙa sai yayi tozali da Shukhra ƙanwar sa, wacce ya zalunta a Rayuwarsa, Haƙƙinta dana AKEELA yake bibiyarsa da kuma saɓawa ALLAH wato neman maza da yadingayi da neman MATA Duk shi kaɗai ga Shan giya! Kai shifa Abubuwan sun Masa yawa!
Salati yasa wanda Umma tayyo wajen itama aka bar jimmai na zubar da Hawayen nadama da baƙin Cikin!
Sungumar Shukrah Usman yayi zai waje da ita Umma ta daka Masa tsawa "ina zak kaita ne ko so kake Ragowar asirin da yake rufe ya tone, shigo da ita ɗaki shock ɗin maganganun da nake tunanin tajine ne yasa ta Hakan,ana shafa MATA ruwa Shikenan!
Jiki a sanyaye Usman ya juya da Shukrah ɗaki.
Kamar yadda Umma ta faɗa Hakan ce ta faru ana shafawa Shukhra ruw takawo numfashi haɗe da ihun Kuka " mama nashiga uku na kice abunda nakeji ba gaskia bane! Yah USMAN bashine ya lalatan Rayuwa ba,ba kuma shine Mahaifin Daddy ba sai fisge fisge take gwanin tausayi! "Sai dai kiyi haƙuri Shukrah abunda kunnenki yaji miki hakane Babu batun ɓoye ɓoye! Wayyo nashiga uku nah ALLAH kaɗau raina da ganin wannan rana!
Ganin halin da Shukhra take Ciki ne yasa jikin Usman kara Wani sanyin da share hawayen baƙin cikin biyewa Sharrin zuciya, ƴar ƙanwar sa wacce takewa son so ,shima yake MATA Hakan wai yai shine silar sata a Wannan yanayin shikam ina zaisa kansa A duniya!
Da sassarfa Yaje gareta ya saka gwiwoyinsa a ƙasa ya Fara roƙar ta Akan ta yafe masa , sharrin SHAIƊAN da biyewa zuciya dan kuwa kallon BF ne Yasa shi a kowanne Hali (yakamata matasanmu samari da Ƴan MATA ku kiyaye kallon Blue film yana haifar da matsaloli da yawa a rayuwar duniya Harda irin halin da Usman ya shiga, ga matsalar idanu, awajen ALLAH kuma akwai babbn zunubi, ALLAH Yasa mufi ƙarfin zuciyarmu akoda yaushe,Kunga dai haƙurin da AQEEL yayi Akan irin tasa matsalar ya tsaya wajen Azumi da roƙon ALLAH samartakarsa tai Masa Amfani dan kuwa har yanzu gashinan nutsatstsene ALLAH Yasa mufi ƙarfin zuciyarmu akoda yaushe)
Ita dai Shukrah Duk ban baki na Usman da magiyar da neman gafafar ta bata saurareshi ba sai sharar ƙwalla take, haka har yamma tayi Lokacin ɗauko Daddy daga school yayi, 3years yake Amma akwai wayo da surutun shiyasa aka kaishi school ɗin da wuri, idanun Shukhra kamar famke tsabar kumburi Amma haka tasa niƙaf ta fice domin ɗauko Daddy, bin bayanta Usman yayi ko kulashi batayiba, ta ɗauko shi ta riƙe hannunsa,Abun gwanin tausayi, shikam Usman yana zuwa ɗaukar Daddy yayi ya rungumeshi a ƙirjinsa yanajin nadamar Hanyar da yabi wajen Samar da yaron, gadai shi kaɗai ne ƙwansa a duniya Amma kuma Babu daɗin jin yadda aka Samar dashi, Daddy ya manta Usman Amma kuma tunda namiji ne sai gashi ya yarda dashi,ganin Usman ya ɗauki Daddy sai Shukhra tayi wuf tai gaba ta barsu Abaya.
Koda suka koma gidan Jimmai da Umma sai zancen Bala'in da ya samesu sukeyi, kamar ba ita bace wacce ta shafe shekaru bata magana ba, tanajin sallamar Usman ta haɗe Rai tajuya fuska,sai Bayan magriba sannan Umma tabar gidan Shukhra itakam tace binta zatayi, Umma yace wazai kula da Jimmai ɗin? Dan haka ta haƙura da tafiyar Umma tai tafiyarta zuciyarta ba daɗi.
Fin sati da dawowar Usman daga Jimmai har Shukhra basa kula shi, sai dai yaiwa Daddy wasa,haka Yake Zaune a cikin gidan zuciyarsa Babu daɗi,yana dan sanin abunda yayi, Yanzu ma so yake yake wajen Abbu dasu AQEEL da AKEELA na nemi gafararsu Akan Abubuwan da ya aikata musu......
____KAWU ISMA'IL___
_kamar yadda likita ya faɗa a yau ya sallame shi sai gidan su Hauwa, su Minal anata murna Abba yadawoe, Kawu Isma'il sai sussunne kai yake yanajin kunyar su innar Hauwa,sai suka bagarar dashi kamar basusan ABunda yakeyi ba,shi tausayi ma yake Basu,mutumin daya saba riƙe kuɗi shine yau yake wannan Hali Duk da shine ya jawa kansa, Amma ai akwai Tausayi, ko sisin kwabo Bashi bashi dashi,sai a gidansu Hauwa and ci dashi da matarsa da ita kanta,idan ya zauna yaita tunani kenan, na tsoron haɗuwarsu da banki ,yasan Yanzu sunajin an sallameshi daga Asibiti zasu makashi kotu, ƙarshen sa ma gidan yari ne! Wannan abu yana ɗaga Masa Hankali shiyasa tunda aka sallameshi yake ɗar ɗar zuciyarsa Babu daɗi!haka innar Hauwa da Hauwa kanta tai tai Masa nasiha.
Haka kwanaki sukaita tafiya shiru_shiru banki Basu nemi Kawu Isma'il ba kuma har sannan zuciyarsa bata kwanta ba,ga hawan jinin daya sameshi kusan kullum Babu lafiya yau shuni gobe Dauɗa, a haka harya Fara fita yana tattakawa Duk indai yabi sai kallo ake binsa dashi shikam wannan abu yana Bashi kunya Duk da yasan halinsa ne yajawo Masa, kullum sai yawo da carbi da istigfari da Hailala yakeyi akan ALLAH ya yafe masa zunubansa,Duk sanda zaiga su Hadiyyah da Hidayah da sauran ƴan uwansu sai yayi Kuka da neman gafararsu sukam Abun yana damunsu sukace "dan ALLAH Kawu komai ya wuce adaina sawa kansa tension kana kallon halin da kake ciki.......
_____GIDAN MUKHTAR_____
_Zaman lafiya kamar a gidan aka same shi tsakanin Zakiyyah da Bilkisu zamansu sai san barka, kamar ba kishiyoyin juna ba,Kowacce burinta ta faranatawa mijinta rai, Hakan yana faranatawa mijinsu mukhtar Ransa yayi fresh sai wata ƙiba yakeyi ga kuɗi ya zauna da kwanciyar Hankali,Tuni ABIE an ƙara tasawa anyi Hankali sosai yanzu, waɗannan ƙiriniyar ya rage ta saura kaɗan, yana primary 3 yanzu,ka ƙoƙari sosai da Yake dashi ga wayo wanda yafi ƙarfin shekaraunsa,Har sannan a wajen Bilkisu yake komai nasa a bangarenta yake Babu wanda zai tunanin ba ɗan ta bane.
Itama Zakiyyah haka ta riƙe takwararta kai kace itace ta haife ta, Little Mammah angirma sosai yanzu haka rarrafe take inta kama abu ma tana miƙewa gwanin sha'awa, tayo wayon ABIE dama Suna kama dashi Sosai kuma shi ABIE ɗin yana yanayi da mamansa shi yasa har wata kama ake Tsakanin Zakiyyah da little Mammah,tuni aka yayeta dan kuwa a wajen Zakiyyah take kwana kuma Babu abunda bataci, Zaman little Hannun Zakiyyah ko ƙarzane bai sameta ba ba kamar lokacin goyon ABIE ba lokacin Zakiyyah anakan hauka Yanzu kam anyi hankali.
Naga itama ALLAH yakawo ciki ne da ita gashinan ya fito ba sosai ba, sai nace ALLAH ya Raba lafiya, su seerat da Aisha Sulaiman da MamaGee da oum Nawwar zeetopha,mummy Waleed a shirya zuwa Suna fa ƙawarku an kusa sauka , nasan za'asha shagali....
______AQEEL DA AKEEL______
Tun daga lokacin da asirin AQEEL ya tonu kuma aka samu abun tsokana gareshi tun yana kumburi har ya daina,sai ya Fara murmushi ganin kumburin yana ƙara sawa ayi tsokanar, aikuwa sai ya fuske,Amma Duk xa Hakan fa shi AKEEL bai daina Masa ba, idan yaga Abun ya isheshi sai kawai yabarwa AKEEL ɗin wajen, shi kuma sai ya bishi ɗaki ya ɗauko waya like yadda AQEEL yai daya ɗauki wayarsa yana kallon Vedios ɗin su Hadiyyah,kawai sai ya daina kallon AKEEL ɗin in yana iskanci gareshi ko kuma ya cire glass ɗin idanunsa yadda bazai ganshi da kyau ba😀
ABBU burinsa Yaga Ƴan biyunsa kowanne ya danƙa Masa matarsa, ya cika wa Abokinsa masoyinsa burinsa,na haɗa ƴaƴansu Aure,
Sai kuma Wata sabuwa, yanzu fa AQEEL kwanciyar Hankinsa yadawo kaso 70%cikin 100%,dan haka ciwonsa yai Masa Sallama, abu ma yaso yafi nada Yanzu ciwon Ciki da mararsa idan ya Yunƙuro kamar zai mutu,Jiya abun ya Fara dawowa,kuma yana dawowa sai da suka dangana ga Asibiti, aka rubuto wasu sababbin magungunan da suka fi nada ƙarfi, Doctor yaiwa ABBU gargaɗi Akan Hakan dan kuwa Maganin yanada nasa illar idan yayi yawa a jiki,mafita kawaii Amasa Aure in Sha ALLAH zai warke ne! nan ABBU yace wa doctor sh wannan yaron ɗan baiwa ne kamar munsan yanayinsa tun yana ƙarami muka Masa Aure, badan wasu Abubuwan da suka faru ba aida tuni yanzu Suna tare da iyalinsa, sai da yasha ruwa sannan suka dawo gida! Abun Tausayi AQEEL yini guda ya rame gashi baya miƙewa dakyau saboda ciwon marar,sai zuwa dubiya akeyi.
ABBU yaso barin bikin nan da wata takwas masu zuwa a haɗa dana AKEELA wacce sannan tayi candy,
To ga kuma yadda abu Yake tafiya,
Dan haka Abbu ya yanke shawarar danƙawa kowanne number matarsa su Fara daidaitawa a waya in yaso dakansu zasu saka Ranar Zuwa wajen juna,sai matsalar AQEEL ta taso shiyasa Basu Kira ba Hankali bai kwanta ba,to Yanzu yafara jin sauƙi Alhamdulillahi sai shirin kiransu Hadiyyah......
______ GIDANSU HADIYYAH_____
Shirye shiryen tafiyar ALHAJI china akeyi,kamar yadda Alhaji tallafy ya faɗa,Duk ABunda zai buƙata Saida Abbu yai Masa kwana biyu tsakani ya cilla china cike da kewar gidansu da Ƴan uwansa.
Gida yakoma shiru dama zuwan Alhaji ne Yasa gidan aketa walwala da dariya, Kwana Biyu da tafiyar Alhaji sai ga Baabah mutanen Kaduna anwa gidan tsinke sai murna tadawo sabuwa!kar kuso kuga yadda Hunaif ɗan maraya ya girma ba,kamar ba shiba, sai da naduba naga Zeenah kai nayi mamaki fa Yarinya anzama budurwa kamar ba ƴar rainon Zakiyyah ba Lallai Kaduna ta karɓeta, kunsan dama irin jikin Zakiyyah gareta ga tsayi ga ƙiba ma Sha ALLAH,sai naga da kaɗan ma Khadija tafi ta.
_Duk Abubuwan da suka faru su Hadiyyah sub zayyanawa Baabah,sai gashi tana kukan farin Cikin jin jikokinta kyautar da ALLAH yai musu na samun mazajen nunawa Sa'a kamar ƴaƴan Alhaji tallafy,da kuma samun siriki kamarsa aikuwa tayi murna sosai,
Zahra tuni ta Haihu ƴan Biyu mace da namiji, Khadija ce taje ta zauna Mata,ƴaƴanta ma Sha ALLAH gwanin burgewa, ƙauna tsakaninta da mijinta sai Abunda yayi gaba hakana uwar mijinta Maimuna kowa son Zahra yakeyi, twin's sunci sunan Ammar da Ummu Rumana ana kiransu da Ummu da Abbiy,sun yi ɓul_ɓul kamar na kwacesu yakawowa seerat yasin🤗
Tunanin da Hadiyyah da Hidayah suke Akan su AQEEL sai Abunda yai gaba, Yasin Basu da tunani sai nasu, Yanzu burgesu sukeyi Basu da burin komai sai na Ganin su AQEEL,Kusha kuruminku su Hadiyyah saura ƙiris su AQEEL da AKEEL su Zama naku Yanzu zasuzo gareku....
_____TALLAFY'S ____
TALLAFY foundation.....Sai ABunda yayi gaba fa bayan yaye su Alhaji an kuma zuba Wasu daban, acikin su Alhaji ba shi kaɗai aka ɗauki nauyin karatunsa ba ,yara da yawa sun samu, Babu adadi yaran da suka shiryu sanadin TALLAFY foundation, Yanzu ba iya Kano ba wajen jahohi kaɗan ne Babu TALLAFY foundation, sai addu'oi yake samu ta ko ina,shiyasa Abbu Kullum yake ƙara gaba, lokacin cutar AQEEL Ƴan Dubiya kamar me da sassan nigeria daban daban,ga addu'oin alkhair da take samunsa.
TALLAFY group of company yayi gaba ya kera Sa'a jahohin nigeria yanada rassa ba kaɗan ba, indai harkar idar kayan abinci ne ga sauƙi manyan shaguna dayawa a wajen suke sarin kayan masarufi Babu abinda Babu wanda ake sarrafawa aci Ayi amfani dashi, sai son barka.
TALLAFY Holdings company ma Hakan take Duk WANI Abun amfani na zamani da wuta da karatuna akwai shi a Wannan waje shima akwai rassansa sosai a nigeria kayansa daga ƙasar japan Yaje oda Babu gara Babu zago, Abbu ya ya wuce yadda kuje sauraro kuma ba komai ne Yasa Hakan ba illah taimakon da yakewa marayu da Marasa ƙarfi........
✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰
6/25/24, 12:05 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba)
Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM}
08128131163
Marubuciyar
Komai nisan jifa
Hakan ba kuskure bane
____________________
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A*
____________________
*PAGE SIXTY 60*
*I LOVE YOU ALL MY FANS🥰*
"Nifa bro bansan yadda za'ayi na Kira wannan Yarinyar ba fa Duk da bansan wacce acikiba! ALLAH yasa dai ba wannan dunkum ɗin bace dan bazan ɗau wannan Al amarin ba,Mutum ya zauna kamar Wani kurma!
AQEEL ne ke wannan maganar a daidai lokacin da Suke tattaunawa Akan kiransu Hidayah a waya!
Duk maganar da AQEEL yakeyi shi dai AKEEL shiru yayi kawai yana kallon bro ɗin sai da yakai Aya sannan shima ya tofa Tashi!
"Banda abunka bro kaima ɗin menene?kaima da ita ai duk Babu banbanci,idan itace ai kaga ka huta sai kuyi zamanku Babu hayaniya!Babu takura Dan duk lokacin da zamu zauna tare dakai sai kace na fiye surutu na dameka!kaga kuwa idan wannan mai surutun aka haɗa ka da ita sai ta dameka ko? Ya ƙarasa maganar da duban bro ɗin sa!
"Kai bro ya isa haka fa zaka tsaya wannan tsarin,kai ai surutunka yayi yawa ne, Yaushe zaka haɗa kanka da wannan yarinyar! Kawai dai ni na sare da wannan lamarin,idan dunkum ce ALLAH sai na daidai ta mata zamanta,bazai ɗauka ba, dole ta buɗe baki ta dinga mun Hira! Lalläi bro to wazai koya ma...... AQEEL Ɗagawa AKEEL hannu yayi alamun ya isheshi da surutu! Dan haka ya rufe bakinsa ya barshi yasan idan jarabarsa ta tashi ya dinga kumbure kumbure Kenan da ciccin maganin Babu gaira Babu Dalili dama gashi bashida lafiya cikakkiya. A haka yirar ta watse Haka bro da bro ɗinsa in ana Hira Rimi Rimi sai an gama ta baram_baram.
Sai Bayan isha'i sannan AQEEL yasamu ikon Kiran waya,saboda mutanen da suke ta zuwa dubiya har yanzu Basu daina zuwa ba,guri guda ya keɓe saboda baison bro yasa Masa idanu,sai kuma gashi ma tun bayan