Showing 72001 words to 75000 words out of 141223 words

Chapter 25 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

Advertisement

ba, balle Ummu Ruman kuma da tun bayan rasuwar Abby ɗin itama ta haɗu da lalurar ajali, tana ta lafiyarta ba ta faɗawa kowa ba, kuma bataga alamun ansan da zancen Auren ba dan da cikin zaman jana 'izar Abby ɗin za'ayi zancen,har Hajiya Sakinah ita ma ta rasu bataga alamun kowa ya sani ba, ita ma ku ma bata faɗawa kowa ba, ko Auren ta da Kawu isma'il batai Masa zancen Auren ba, hakama ƴaƴan bata taɓa gaya musu ba, abunda yasa Hakan ga Sa'adatu shine, ita fa tasan wane Ɗalhat yana da kuɗi daidai misali, iyayensa ma suna da dukiya, shi yasa ma bata gayawa kowa ba, bata fatan su Hadiyyah su Auri mai kuɗi su huta,sai ku ma gashi ku ma Zahra ta Auri mai kuɗi ɗan gata,ta yi baƙin ciki sosai da Hakan, sai saidai ba yadda zata iya' sai kuma wata masifar da ta sameta shine samun su Mahmud da Mus'ab a matsayin Samari, tasan ƴaƴan ma su kuɗi ne,ta yi baƙin ciki sosai da Hakan, sai ta yi shiru da zancen cewa fa su Hadiyyah su na da Aure, su Mus'ab da Mahmud har wajenta suka zo suka gaisheta, ita ma kuma bata ce ai da Aure Akan waɗanda kuke ne ma ba..Anan Sa'adatu tunanin ta ya tsaya saboda murɗawar da marar ta tayi na lokaci barkatai.
Ita Hidayah mai tambaya ta yi shiru tana kallon Auntyn da take jiran ta bata amsa Amma shiru,dan haka ta kuma je fa MATA tambaya? Aunty bakiyi magana ba dan ALLAH ki fitar da mu daga cikin duhu! Da ma kinsan Alhaji tallafy? Saboda shine ai Ɗalhat ɗin Abokin Abby!
Kamar saukar aradu haka Sa'adatu taji wannan zancen! Alhaji tallafy shine da ma Ɗalhat dukiya ta fi ta da kenan! Ko shi yasa yake kulawa da su ne? Wayyo da ma ta tsaya Ranar da sukaje visiting ɗin Alhaji kaicona!
Ƙara Sa'adatu tasaka jin mararta kamar zata ɓalle masu Kuka a hanzarce su ka ɗago jin Aunty ta saki ƙara mai rikitarwa da tsananin ƙara, ai tozali sukayi da Aunty ya she a ƙasa jini kam kamar an yanka karamar dabb a ya na biyo ƙafafaunta abun tsoro!
Hidayah ce ta farga! Ta ƙwalawa Hydar Kira wanda yake tsakar gida, Yaje ya faɗawa maman Annour ta zo!
Da gudu Hydar ya fice zuwa maƙotan inda suna mutunci da Sa'adatu ya kirawo maman Annour ɗin,domin ta ga halin da Aunty ta ke ciki! Hankalin su Hadiyyah fa yakuma ta shi, da ma ga damuwar da suke ciki, da kuma wannan ta shin Hankali na Aunty, sun san dai Aunty ciki ne da ita, gashi kuma ta na bleeding sun san Hakan matsala ce ga mai ciki.
Suna ta aikin Sannu ga Sa'adatu, wacce takeshan wahala sosai, lokacin da Maman Annour ta zo gidan tuni Sa'adatu ta yi ɓarin cikin jikinta(ƙarshen tika tika tik fans) sai da maman Annour ta taimaka Sa'adatu ta gyara jikinta, su Hadiyyah suka wanke kayan,har lokacin cikin damuwa suke, Akan wannan al amari na cewa Aure ne da su kuma waɗannan, ƴaƴan Alhaji tallafy ɗin, marasa sanin darajar ɗan Adam musamman wannan ɗayan (AQEEL) ko ya nuna akwai mutane a wajen lokacin visiting ɗin Alhaji da sukaje, Kowacce cikinsu irin tunanin da takeyi kenan a zuciyarta!
Ita dai Sa'adatu zuciyarta ba bu daɗi, na ɓarin cikin da tayi, shikenan yanzu tata ta ƙare, kenan duk wani makirci da take ƙullawa su Hajiya ikilima Akan cikinta ku ma ya ƙare, Amma ku ma ai ALLAH zai bani wani cikin ba da jimawa ba,dan haka ba bu damuwa ai! Sa'adatu ta faɗa a zuciyarta, tana daga kwance saboda gaskia ta Sha wahala fa, sai kuma tunanin Su Hadiyyah ya dawo MATA, ai nan da nan annurin fuskarta ya ɗauke, wata tsana mai zafi ta su ta shige MATA rai.
A haka Alhaji gambo ya shigo gidan, Hankali a tashe, dan khadija ce ta ɗau wayar Auntyn ta kirawo shi ta ke faɗa ma sa,shiyasa hankalin sa a tashe ya dawo gidan, har Kuka Alhaji gambo yayi na asarar cikin nan, daya ƙwallafa rai akansa, gwanin tausayi (yanzu iskanci gasu Hajiya ikilima kuma Akan ciki ai ya ƙare ko? Inkuma zaka rabu da su a Hakan shikenan)Duk baƙin cikin da Sa'adatu ta ke ciki sai ta shanye bata ta dinga lallashin Alhaji gambo ɗin, da kalamai na kissa da kisisina Akan cewa " indai cikine ai kwana nawane ALLAH zai bata wani kar ya da mu! Shi kam Alhaji gambo kawai dai ya na jinta ne Amma hankalinsa a tashe yake, ga shi da hawan jini, kafin kace kwabo ya tashi sai da aka kirawo likita yai Masa taimakon gaggawa da allura sannan ya samu barci.


Ita Hadiyyah Kiran mus'ab ta yi a waya Akan yaudarar ta da yayi, aikuwa kunsan ba ki abun magana sai da tai Masa tatas, shi kuma sai haƙuri ya ke ba ta Akan, Abbun su AKEEL ne ya aiko su daga shi har Mahmud wajensu,saboda su kula da su, kar su dinga kula wasu samarin, ya na son suyi karatu ƴaƴan Abokin san, sai yanzu kuma suke jin ai su ɗin matan su AKEEL ne, nan dai Mus'ab ya dinga bawa Hadiyyah haƙuri, daga ƙarshe yace MATA sai haƙuri, ai kema kina mun ƙorafi Akan mai Yasa bana ba ki kulawa kamar yadda kowanne masoyi yake bakwa masoyinsa kulawa, to hakanne ya sa ai saboda kar kusa rai da mu alhalin ba soyayyar gaskia Muke muku ba plan ne! Nan dai Hadiyyah ta kashe wayar zuciyarta kamar zata fito waje tsabar baƙin ciki!
Itama. Hidayah haka sukayi da Mahmud gwanar ta ku bata iya magana ba,har ya ga ma zancen sa, kiyi haƙuri Hidayah abunda yasa da ma kenan Babu wata kulawa a soyayyar kenan, Muke kawai nu na kishin mu Akan kar ku kula Samari kenan, Abby ne ya wakiltamu Akan ku, saboda mu kula da ku Akan karatu kawai zakuyi Babu kula Samari, mu Duk ba mu kawo komai ba ashe ku ɗin matan su AQEEL ne! Cikin muryar dariya ya ƙarasa maganar, Hakan ya sa ba bu shiri Hidayah ta ka she wayar, ta na ci ga ba da kukan ta itama Hadiyyah Hakan,suka tattauna tsakaninsu. Hadiyyah "tace lallai su Mus'ab sun yaudare mu, ALLAH ya saka Mana" ita kuma Hidayah tace" Amma Nikam gaskiya waɗannan ƴaƴan Alhaji tallafy ɗin bana son su dukkan su ......






**************


Tun ranar da wannan zancen ya fallasa na cewa ƴan biyun Alhaji Ammar BN Yasir matan su ne shikenan fa, AQEEL ya koma ƴar gidan jiya,a halinsa yanzu yadaina walwala, shi ma AKEEL da sauƙi kam Duk wannan barkwancin ya rage.
Duk Alhaji tallafy ya na sane da su, haka ma Mommah ta na lura da Hakan, dan haka suka tattauna Akan batun!
Ya kake ganin Abu AQEEL tun da yarannan suka san cewa ƴan biyu matan sune shikenan su ke wani cika suke batsewa,anya ba akwai matsala ba kowa, baza su na mu matsala ba? Cewar Mommah ga Alhaji tallafy wanda suke zaune a kan sofa su na tattaunawa Akan zancen Kawu isma'il da kuma Auren su AKEEL ɗin, shi ne ta soko wannan tambayar gareshi?
Bana jin hakan oum AKEEL in Sha ALLAH abun zaizo da sauƙi, kinsan ƴaƴan na ki sai a Hankali musamman wannan miskilin, kinsan a kwanannan aka samu kansa ai, Amma ni kam inada abun da zaisa kowanne ya so matarsa ai, kin manta ƴaƴan naki akwai tausayi da jin ƙai ga iyayen su,kar ki da mu kinji matar so, soyayyar yarinta ta na da tasiri sosai a zuciya, Hakan ne ma yasaka nida Aminina cika wannan soyayya ɗin da aura musu junan su, tun suna ƙananan,Kowacce wacce yake nunawa kulawa ita muka Aura Masa, ba don makircin Hajiya jimmai gareni ba, ai da tuni su AKEEL su na tare da matansu war haka tuni ai, ko dan lalurar shi AQEEL din ma,dan kuwa ba mune ma zamu faɗi cewa mun Aura musu juna ba, sune zasuce suna son juna, mu kuma muce da ama ai munmuku aure tun ku na yara, dan yadda tun a shekarun yarinta suke kulawa da juna da nunawa juna soyayya, abun gwanin dariya fa Oum AKEEL! Alhaji tallafy ya ƙarasa zancen da dariya, alamun ya tuna budurin da akasha dasu AKEEL ɗin itama murmushin ta yi, sannan yace MATA kamar ni nasan Hajiya jimmai zata rabamu ni da abokina, Duk kulawar da AKEEL da AQEEL suka nunawa su Hadiyyah muna ɗauka a waya mu Adana, da ga ƙarshe kuma muka kai aka fito Mana da a vedios ɗin flash, photon suma aka fitar,Duk muka ra ba ni dashi kamar shi ma yasan mutuwa zaiyi,ku ma isma'il zaici amanar sa ne, Amma shi dai bansan nasa photon da vedios ɗin waya bawa na saba? ALLAH ya gafartawa Ammar BN Yasir
Allahumma Ameen inji mommah ta faɗa tana nuna alamun tausayi ga mijin nata da Abokin sa.
Ni na wa suna nan a killace! Zan ɗauko na nuna miki su duka, shikenan Abu AQEEL ALLAH yakaimu lokacin lafiya.
Nan suka ƙarasa tattaunawa tsakaninsu kafin su dangana ga ɗakin barcin su...
Su kam su AKEEL da AQEEL suna can su ma kowanne da abunda ya ke saƙawa a zuciyar sa, dangane ga wannan auren da Abbu ya ce sun ƙulla shekarun da suka shuɗe!
Shi AQEEL ya na tunanin ta yaya ma za'a ce wannan yaran ne wani matansu! Aina za'ayi Hakan? Lallai akwai sake Abbu! Haka yake faɗa a ransa.


Shi kuma AKEEL mamakin Hakan yakeyi shima! Ta yaya Hakan ma zata faru wai wani su na da Aure,Auren ma waɗannan ƴan biyun!gaskia akwai sake an bai mai kaza Kai.....






Lallai fans akwai cakwakiya fa😳


Ga dai cikin da Sa'adatu take taƙama dashi ta ƙwallafa rai akansa ya zube🙆‍♀️


Ya su Hajiya ikilima zasu riski wannan labarin🤧


Me su AKEEL da AQEEL suke nufi da Hakan😢


Su ma dai su Hadiyyah ta na alamun bara'a zasuyi Akan wannan auren🙆‍♀️


Ku biyo oum ARQAM dan jin Duk amsoshin ku da waɗansu ma
Amma in Sha ALLAH next page zakuji aininhin tarihin Alhaji tallafy ɗin wanda da yawa nasan kun jima da matsuwa da ji irinsu Haseena kenan to Musha kurimin ku👌 page 44 na Alhaji tallafy


✍️oum ARQAM ce ontop 🥰
2/7/24, 4:31 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*


*PAGE FOURTY FOUR 44*




Ina miƙa ɗimbin godiya ga RASHIN IYAYE fans group da adduoinku gareni🙏 jikina da sauƙi sosai ga wannan Page ɗin na kune😍




Waiwaye.........
Alhaji Abdul'rahman da Hajiya Binta sune mahaifan Ɗalhat (Tallafy) asalinsu ƴan jihar kano ne, tun iyaye da kakanni,sai dai zaman nasu bai daɗe ba, Tana haihuwar Ɗalhat ko ganinsa batayiba ALLAH yai MATA rasuwa,dan haka akwai ƙanwar Mamansa mai suna Rabia ita Aka mayar ɗakin yayarta, saboda ta kula da wannan jariri da yayarta ta Haifa, da yake lokacin ita Rabia batada saurayi kuma yarinya ce mai biyayya haka ta yadda ranar sadakar bakwai aka Ɗaura Aure da Abdul'rahman,wanda mutuwar Binta ta jigatashi sosai saboda wannan jaririn ne ma ya yadda zai auri Rabia ɗin, dan yana matuƙar tausayawa ɗan jariririnsa,yana kyautata Zaton Rabia zata kula dashi,kuma da ma suna kama sosai da Binta yanayin halin su ɗaya ma, akwai Sanyin Hali ga fari'a.


Kamar yadda akayi tunani kuwa hakanne ta kasance dan Rabia ta riƙe Amanar da aka danƙa MATA, ta kyautata cikin rainon ɗan yayarta,ba bu wanda zaice ba ɗan ta bane,a haka shekaru suka ja, Rabia ta Haifa wa Ɗalhat ƙanne, kuma Abdul'rahman yana jin daɗin Zama da ita, fiye da yayarta ma, ko da yake zaman da sukayi da Binta guda nawane Akan wanda yanzu suke da Rabia.
Sai da Ɗalhat ya girma sannan yasan ba Rabia ce ta haife shi ba, kunsan halin mutane,an dinga ga ɗan maraya nan da sauran waɗannan zantukan to anan yasan cewa ba itace mahaifiyarsa ba.
Tuni ya kammala karatun sa na secondary ya ɗora da university kuma anan su ka haɗu da Ammar BN Yasir shima,sai dai karatun na Ammar BN Yasir baiyi nida ba ya koma kasuwanci, shi kuma Ɗalhat ya cigaba da karatun sa, ɗan kuwa shi mahaifin sa yana son Hakan, shi kuma Ammar BN Yasir shi ne ma ya tsayawa kansa da karatun, ƴan uwansa Duk kasuwanci sukeyi,.
Har sannan kuma suna tare abunsu,
Haka shekaru suka ja Ɗalhat yana karatunsa har ALLAH ya haɗashi da Ummul khair, Basu ji ma ba kuwa sukayi aure, Duk da yana karatunsa sannan,kuma ba wani girma yayi ba, lokacin shekarunsa basufi Ashirin da biyar zuwa da shida ba,irin mutanen nan ne ƙarfin sha'awa, to tun da yace yanason Auren mahafinsa bai tambayi ba'a si akai ba ko ai karatu kakeyi, yai Masa aurensa, kuma Auren bai tauye Masa karatun sa ba, abokansa kuwa sun Sha Masa tsiya shikam bai ji suba sai karatunsa yakeyi,shi ma Ammar BN Yasir sai da yayi mamakin Auren Ɗalhat ɗin, Duk da dai yasan yanayin Abokin nasa, Amma kuma ya ga karatu yakeyi, Ɗalhat yace "dan ina karatu kuma shine bazanyi aure ba, ai karatu baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu, matuƙar akwai halin yi ɗin, Ammar yace "Hakane abokina, iyaye ne ai basa ganewa idan ɗan su yana karatu sai su hanashi Aure, ko shi da kansa ya hana kansa Auren, alhali yanason Auren, daga nan kuma sai ya bi wata hanya daban wacce zai dinga biyawa kansa buƙata ta hanyar saɓawa ALLAH Zina, ko kuma biyawa kai buƙata da hannu da sauran hanyoyi Marasa kyau" ALLAH yasa mudace ƴan uwa.
Ummul khair yarinya ce mai Hankali da nustuwa, kuma itace ƙarama a wajen iyayenta sai yayye,Suma Duk sunyi aure, haka suke zaune itada Ɗalhat cikin soyayya da ƙaunar junansu, tana tsananin son mijinta shima kuma mijin yanason matarsa,
Sun jima ALLAH bai ba su Haihuwa ba, dan haka mutane suke tunanin ko dan Ɗalhat yana karatu ne shiyasa ya ɗauki matakin hakan, nan kuwa ba haka bane, ALLAH ne dai bai kawo ba.
Cikin ikon ALLAH kuma sai ga ciki ajikin Ummul khair kar kuso kuga murna a wajen Ɗalhat da sauran ƴan uwa anata addu'a ALLAH ya raba lafiya,cikin ikon ALLAH kuwa ALLAH ya bata ƴan biyu Duk maza,ranar suna suka ci Hassan AQEEL da Hussain AKEEL, zo kuga murna kamar ba gobe, Ammar BN Yasir yanason waɗannan ƴaƴa na abokinsa ƴan biyu, haka komai ya kawo yace na ƴan biyu ne,har lokacin ya na kasuwancinsa , shi ma ya haɗu da Ummu Ruman sannan, suna soyayya, itama ALLAH yayita da son ƴan biyu, to da ma kuma Ummul khair da Ummu Ruman tuni sun zama ƙawaye sanadiyyar Ɗalhat da Ammar ɗin,bine kaɗan ta Kira wayar Ummul khair ina ƴan biyu, nice zan raine su ai, bar Mana za'ayi idan mukayi Aure da Ammar wannan alƙawarine maganar kullum kenan.
Ba'a jima sosai ba kuwa Ammar BN Yasir ya auri Ummu Ruman,zumunci ya daɗa ƙarfi tsakanin su, ƴan biyu basa rigima dan haka koda yaushe suna wajen Ummu Ruman tana rainon su,ko da aka yaye su sai rainon su ya koma gurinta gaba ɗaya, lokacin itama ALLAH ya bata Zakiyyah, ga rainon Zakiyyah gana ƴan biyu, dan ma su sunyi wayo sannan.
Ita kuma Ummul khair ALLAH yabata wani cikin mai wahala tun farkon sa, itace ba bu lafiya yau ace ba bu jini yau ba bu ruwa, kullum suna yawon asibiti, bata sati biyu sai ta kwanta, ana tausayawa Ummul khair sosai, tuni An ya ye Zakiyyah kuma Hajiya Sakinah ta ɗauke ta, Ammar BN Yasir da Ummu Ruman ba su da mu da Hakan ba, tun da ga ƴan biyu a wajensu har sun ta sa ma, sannan ALLAH yabawa Ummul khair ɗin wani cikin mai wahalar da itan,kwanci tashi ba wuya a wajen ALLAH gashi har ALLAH yakawo lokacin haihuwar Ummul khair, ta Haifi yarinyarta mace sai dai ko ganin fuskarta batayi ba ALLAH ya karɓi abarta,tashin Hankali wanda ba'a saka ma sa rana kar kuzo kuga yadda Ɗalhat ya shige tashin Hankali,da Duk wasu ƴan uwa ma, sai ma an kalli jaririyar da Ummul khair ɗin ta Bari,haka aka dinga cewa Ɗalhat ɗin shima haka mahaifiyarsa ta rasu ta barshi, shima ga shi an bar Masa,Ummu Ruman tayi Kuka kamar ba bu gobe na rasuwar Ummul khair ƙawarta Aminiyarta, sai haƙuri, haka aka share makoki.
Ummu Ruman ta na da ciki lokacin,har sannan kuma ƴan biyu suna wajen ta.
Ɗalhat ya Zama shiru_shiru duniya tai Masa zafi ga jaririya an bar Masa kuma ya ce shi zai raini ƴar sa ba bu wanda zai bawa.


Jimmai yayar Ummul khair mijinta ya mutu, ta na da ƴaƴa Biyu mace Shukra da namiji Usman, ya ɗan girmi su AKEEL da AQEEL, kuma Duk su na dangin ubansu, daga jimmai dai Ummul khair dan haka ba wata babba bace, ganin halin da Ɗalhat yake ciki ga jimmai a gida kawai sai iyayen su suka haɗa Auren tsakanin jimmai da Ɗalhat ɗin ko dan jaririyar nan(Ummul khair) wadda ake Kira da AKEELA, baiyi gaddama ba, aka Ɗaura musu aure,jimmai irin matan nan ne marasa tausayi da cikakkiyar tarbiyyah, Duk da iyayenta sun mata tarbiyyah ɗin, Amma tun da tayi aure ta watsar ta kama wani halin da tarbiyyah wacce ba iyayenta ne suka ɗora ta akai ba,mijinta ma haƙuri yakeyi da ita, asiri kala_kala take Masa Duk ta mallakeshi sai abunda tace Masa, iyayensa ba su iya komai a kai ba,sai a bunda ta ce,ana haka kuma ALLAH yai Masa rasuwa, aikuwa tana gama takaba a gidan ƴan uwan mijin suka amshe yaransu, ta dawo gidansu, shine fa yanzu kuma aka ƙallafawa Ɗalhat ita..
Ammar BN Yasir baiso wannan haɗin da akayiwa abokinsa ba, mijin jimmai yasanshi farin sani, Duk halin da Yake ciki game d it ya sani, shi yasa yaso ya nusashshe da Ɗalhat illar Auren ta zaiyi, amma ALLAH ya Riga ya ƙulla, jimmai ta na kallon take_taken Ammar BN Yasir na ƙin Auren ta da Ɗalhat da yaso ya rusa,shiyasa ta ƙudire wani abu a ranta game da shi ɗin wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login