Showing 54001 words to 57000 words out of 141223 words

Chapter 19 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

Rashin kuɗi a hannu ne yai ma sa cikas, sai kuma ya koma ƴan buga_buga kafin ALLAH yai Masa luɗufi Yasamu aiki a tallafy foundation,shi kuma Alhaji tallafy da ya ga yaron yana da Hankali da ƙokari sosai,In Alhaji ya kawo ziyara cibiyarsa yazo cikin girmamawa ya gaishe shi, shine fa ya ɗauke shi ya mayar da shi can gidan sa inda yake rayuwa, yake kula da shige da ficen gidan, anan Alhaji ya gane yaron yana da basira, Shirin da yayi Akan Kawu isma'il idan yasa jibo akai zai aikata abunda akeso, sai kuwa ga shi cikin ƙanƙanin lokaci komai ya yi daidai, nan sukayi sallama a waya da Alhajin (Alhaji tallafy ya na Abuja ne)






Bayan gimtse wayar ne Alhaji tallafy ya shiga mama ki da al ajabi Akan halin Kawu isma'il "lalläi ma isma'il besan yasan halinsa ba, yasan wanene shi tun bai kai hakaba, tun Alhaji Ammar yana ra ye, kawai dai kallon sa yakeyi,da ma barinsa yayi ya ga iya gudun ruwansa ne,Tun asali bayan rasuwar Alhaji Ammar niyya ya yi ya karɓi dukiyar yaran yaci ga ba da kula musu da ita, Amma kuma sai ya ga ai bai kyautu ya karɓa ba, tun da ga ɗan uwansa na jini, kuma shima yana irin harkar da Alhaji Ammar ɗin yakeyi, kuma shine a haƙƙu da abawa, ƴaƴan Duk matane kuma ba wasu manya ba,
Lallai kam fans Alhaji tallafy yasan Alhaji Ammar kenan?Har da Kawu isma'il ma,Duk yadda akayi Kawu isma'il bai gane Alhaji tallafy ba, ko da yake shi da bai ma ganshi ba, kawai dai sunan ya sani,ko lokacin cuki_cukun Zuwan Alhaji, tallafy foundation da yayi ai ba a hannun Alhaji tallafy yai Masa komai ba,maybe shiyasa bai gane kowa nene ba,ita kuma Sa'adatu kar ku manta Basu taɓa haɗuwa da Alhaji tallafy ba balle ko zata ga ne Shi... Lallai kam akwai lauje cikin naɗi🤔😳


Duk yadda sukayi da jibo Alhaji tallafy ha ka ya kwashe ya gayawa Hajiya Aisha(mommah) da nasarar da aka samu cikin sauƙi, ta yi murna sosai ta Taya mijinta murna Akan nasarar da ya yi ta amsarwa marayu haƙkinsu,Ranar Alhaji tallafy ya yi barci cikin murna da farin ciki, ita ma Mommah haka, Duk da dai batasani meyasa Hakan ba, Ba yau Alhaji ya taɓa wannan aiki na taimakon marayu ba, Amma kuma farin cikin wannan daban yake, kuma ba ya wani damuwa da Duk irin marayun da y haɗu da su, Amma waɗannan marayun ya shiga damuwa lokacin da suka haɗu hakama yanzu da aka ƙwatar musu haƙkinsu da kuma taimaka musu da yake yi yafi koyaushe murna da farin ciki. Lallai kam bake ba Mommah mu ma kanmu muna da ayar tambaya Akan Hakan ko ba hakaba fans


Tun daga sannan wani tunani da Rashin barci da Alhaji tallafy yakeyi Duk ya daina, walwalar sa ta dawo, Duk Mommah ta shaida Hakan,su ma su AKEEL da AQEEL sun ga yanzu Abbu yadawo walwala kamar da kafin ya tawo da ga NEW DELHI(india) lokacin da yakai musu ziyara can,
Tun bayan dawowar su suka san akwai abunda yake da mun Abbu ɗin,ko na ce AKEEL yasani, dan shikma AQEEL bai wani da mu da Hakan ba, mutumin da ba lura yake da Yanayin kowa ba, shi kullum ya na waje ɗaya ba bu uhum hare um'um ta ya zai gane wani ya na matsala ne, shima matsalar sa ta isheshi, Amma yanzu kam ma Sha ALLAH AQEEL da sauƙi shariya da shiru_shiru tun da AKEEL yake masa nasiha ɗinnan.






**************




A haka dai mukhtar ya na driving fuskarsa ba bu walwala, Bilkisu dai ta na lura da yanayinsa, zaman kuramen ne ya isheta,
"zaujin saleh Dan ALLAH ka yi haƙuri Akan Duk abunda ya faru, tsakanin ka da maman ABIE,komai ya wuce kamar yadda kace ka yafe MATA ɗin, Duk Abubuwan da suka fa ru,kadaina tunawa kamance da su kawai, ka tuna ALLAH ma munai ma sa laifi mu roƙeshi kuma ya yafe Mana, balle mu ƴan Adam, Haba Abban ABIE!kai da nasanka mai haƙuri da yafiya, me yakeson ya ruɗe kane? Kayi haƙuri yanzu ka saki fuskarsa kaji?
Bilkisu ta ƙarasa maganar tana ƙasa_kasa da murya alamun rarrashi!
Kaifa miji na gari ne abun Alfari,
Hakanan Bilkisu ta dinga gayawa mukhtar maganganu cikin hikima da kwantar da murya,Har ALLAH yasa mukhtar ya saki ransa ɗin,kuma ya yi murmushi!
Sannan yace"shiyasa nake ƙara ƙaunarki a koda yaushe Mar atussaliha! In dai Kika ganni cikin damuwa kema damuwar kikeyi,kuma ta kowanne Hali sai kinsan ta yadda kikayi Kika fitar dani,kin mayen gurbinsa da farin ciki ALLAH yau miki albarka! Ku ma in Sha ALLAH bazan kuma tu na abunda Zakiyyah tai nun ba balle raina ya ɓaci, suna a haka suka ƙaraso asibitin,fuskarsa a sake cike da annuri, mar atussaliha tayi aikinta.


"Anya kuwa Aunty Yaya mukhtar zaizo kuwa? Hidayah ta faɗa ta na mai nuna alamun karaya zatayi kuka!
Sa'adatu ta nisa ta ce "Nima ina tunanin hakan Hidayah, ko wayar Zaki ba ni nayi Masa magana dakaina, kar muje ta farka, dan Kinga ta na da ƙarfin jini allaurar da wuri ta ke sakinta!
Hadiyyah ta ce "To Aunty ga wayar" muryar ta cike da karaya da lamarin.


A dai dai lokacin kuma Bilkisu da Mukhtar suka ƙaraso bakin su cike da sallama wajen da suke a tsaye, sunyi cirko_cirko, hakan ne ya sa Sa'adatu fasa kiran da tayi niyya, ta miƙawa Hadiyyah wayar, Hadiyyah da Hidayah tare sukai ajiyar zuciya da amsa sallamar ta su,
Sannu da zuwa Sa'adatu tai musu.


Bilkisu gaisawa ta yi da Sa'adatu ta na mata ya mai jiki! Su ma su Hadiyyah suka gaisar da ita murya a sanyaye da alamun an Sha kuka,


Mukhtar shima gaisawa da Sa'adatu yayi yanai mata ya mai jiki,


Tun bayan da likita yace a nemo mukhtar wa Zakiyyah, ya ba su umarnin su fito da ga ɗakin, su ba ta iska, bata son hayaniya idan ba hakaba akwai matsala, shiyasa ma suka samu wajen da aka tanada na masu zaman jinya suka zauna, Amma kuma daga ƙarshe suka dawo bakin ƙofar Ɗakin da Zakiyyah ɗin ta ke su na jiran ikon ALLAH.


Ganin zuwan mukhtar da sauri Hidayah
Ta tafi office ɗin doctor domin ta sanar da shi ga Mukhtar fa yazo, ba ta jima da dawowa ba doctor ya zo ya not mukhtar zuwa office ɗin sa.


Anan doctor yai ma sa bayanin Abubuwan da suke damun Zakiyyah ɗin, da kuma cewa tabbas cutar sa ta na da alaƙa da Shi, dan Haka yanzu dai zai zauna a nan ne har zuwa farfaɗowar Zakiyyah ɗin aga kuma mene mataki na gaba, nan dai doctor yai masa cikakken bayani, ta yadda komai zaizo da sauƙi.


Fitowa da ga office ɗin suka yi mukhtar na biye da shi zuwa ɗakin da Zakiyyah ta ke kwance, su Hadiyyah sai su ma suka biyosu, doctor yace baya buƙatar su shi dai kawai yake so ya shigo ɗakin,a sanyaye suka juya zuwa wajen da Sa'adatu da Bilkisu suke zaune, su na ɗan tattaunawa.


Sai da Mukhtar ya girgiza! Da ganin yadda Zakiyyah ta koma, ta ga za lokacin bikin zahra da ya ganta, nan wani tausayinta ya kamashi lokaci guda, da rayuwar da sukayi a baya, yadda ta ke mai jiki da ƙibarta irin Giant nan komai ta sa kyau ya ke mata, Amma ji yadda ta koma kamar ba wannan ƴar hutun ba, tayi baƙiƙirin ta rame, Duk wannan wasi wasin mukhtar yana yin sa je ne, a daidai kan Zakiyyah da yake tsaye,Ga ƙarin ruwa ajikinta, ga kuma Robar ƙara numfashi (Dan kuwa sai da aka mayar ma ta da ita komai yayi normal)
Likita dai ya ga jikin mukhtar ya yi Sanyi,kuma ya hango nasara a tartare da shi, ko ma dai me wannan baiwar ALLAH tai Masa zai yafe matan,tun da dai ya shi yazo.


Nuni yai Masa da kujera alamar ya zauna(dama kuma sun tattauna cewa zai zauna a wajen ne har ALLAH ya sa ta farfaɗowa aga me ALLAH zai yi,in ta farfaɗo kuma ya ƙarasa wajenta yai MATA magana yagani, sannan sai ya yi masa flashing a waya shi kuma zaizo)dan haka ya na Zama doctor ya fice abinsa.


Doctor Yaje ya sanarwa da su Sa'adatu yadda abun zai kasance, yanzu haka mukhtar ya na can in Sha ALLAH kuma ta na farkawa zata dawo normal, da zarar ta ji muryar sa, in ya so in ma magana ce zasu yine.


Hamdala su Hadiyyah sukayi, yayin da Bilkisu ta tuna alamun tausayi a fuskarta kuma tana adduar ALLAH yasa ta farfaɗo yadda suke tsammani, da Ameen suka sa, zuciyar su cike da begen halayen Bilkisu ma su kyau, ba kowacce ma ce zatayi haka ba,Kishiyarki ba bu lafiya, ki tawo tare dashi wajenta,kuma harki zauna jiran tsammani ga shi dare ya yi wajen 10:00pm, tsakanin Hadiyyah da Hidayah sai tattauna kirkin Bilkisu suke yi.
ALLAH sarki Bilkisu bayanin da su Hadiyyah sukai mata Akan cutar Zakiyyah itace ta sa ta ƙara tausaya MATA matuƙa,lallai Bilkisu sai Kinga yadda Zakiyyah ta koma ma, danke rabonki da ita tun tana kan ganiyarta kafin aurenki da Mukhtar ɗin.


Ganin Haka ne yasa Sa'adatu ta ce ba ri ta Kira Alhaji ta gaya Masa yadda akayi in yaso sai su tafi gida,tun da ga Bilkisu nan ga kuma mukhtar.


lallai Sa'adatu ƴar daɗi miji, Zakiyyah ba bu lafiya Amma saikin koma gida ai shikenan da uwarta mahaifiya ce ai da bata tafi ba,
Alhaji gambo yazo kuwa a motarsa suka tafi gida abunsu,da barin in ALLAH yakaimu da asba zasu dawo suji ya ake ciki, nan sukayi sallama sai gida suka bar Hadiyyah da Hidayah da kuma Bilkisu( ba kowacce mace zata iya hakaba) a asibitin


Wajen 11:00 Zakiyyah ta motsa, bakinta ya na motsi alamun ta na son magana, mukhtar kama har sannan ya na zaune ya zubawa Zakiyyah idanu, ya na tunani, ai kuwa Mukhtar yana ganin haka, Kiran likita yayi kamar yadda suka tsara, minti 3 ba'ayi ba sai ga likita, ya cire MATA Robar ƙara numfashi, aikuwa magana ta Fara "mukhtar ka yafemun, Akan Abubuwan dana maka" bazan sake ba" sam batun da Zakiyyah keyi kenan, alamu likita yaiwa mukhtar da yayi MATA magana!
"Zakiyyah na yafe miki Duk abunda Kika mun, buɗe idonki ki kalleni" mukhtar ya faɗa ya na kai hannu kan hannun Zakiyyah wanda ba ƙarin ruwa ajiki,alamun rarrashi!


Kamar a mafarki Zakiyyah ta daina fusge_fusgen da take,Amma kuma ba ta buɗe idonta ba, sai numfar fashi takeyi, alamun numfashinta yanason daidai ta,


"Ki buɗe idonki nace Zakiyyah! Ki kalleni nine mukhtar mijinki" wani ku ka ne ya kwancewa Zakiyyah da kuma tari mai ƙarfi wanda ya sa Jini fita da ga bakinta, yi ta ke ba bu ƙaƙƙautawa!


Mukhtar ya girgiza da ganin halin da Zakiyyah take ciki, tausayinta ya tsirga Masa!


Shikam likita ya san wannan kukan da Tarin da zubar jinin da Zakiyyah zatayi a daidai wannan lokacin shine sauƙin abunda takeji, a game da matsalar ta da Mukhtar ɗin,sai da tayi mai yawa kafin ya lafa mata, ta buɗe idonta da sauri mukhtar yaje ya ɗago da ita zaune a Hankali! Ya sa tissue ya na goge mata jinin bakinta,
Sai mayar da numfashi dai Zakiyyah takeyi, ta kafe mukhtar da idanuwa, shikam sai kallon ta yake cike da tausayi a fuskarsa, Zakiyyah kam wani irin k...........




Muje zuwa dai ƴan Amana akwai sauran tafiya




Nasan akwai tarin tambayoyi a bakunan ku, to ku adana su amsoshinsu suna gaba




✍️ OUM ARQAM ce ontop🥰
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*


*PAGE THIRTY SEVEN 37*


wannan karon kam Bilkisu Tasamu yabawa daga team ɗin Zakiyyah, yanzu kam kun faɗi gaskiyar lamari akan komai, da Amma soyayya ta rufe muku idanu😄






"Zakiyyah kam wani irin kallo na tausayawa gareta takewa mukhtar, shima fuskar ta sa kallon tausaya ne a tare da tasa fuskar wanda yake kallon Zakiyyah da ita,
"Kayi haƙuri kaji Abban ABIE! Akan Abubuwan da na dinga mak......


Katseta mukhtar yayi da cewa
"Na yafe miki Duk abinda kikamun Zakiyyah, yanzu ki kwantar da hankalin ki, kinga bakida lafiya, kinason zuciya da ƙwaƙwalwar ki ta samu salama,kar na kumajin zancen Abubuwan da kikamun ki tura komai baya, abunda yake yanzu shine a gabanmu!


Mukhtar ya ƙarasa maganar da tausasa murya alamun rarrashi da tausayawa,yana kai hannu kan nata hannun!


Ita kuma Zakiyyah tana mai sunkiyar da kanta da jin zuciyarta tai MATA wasai, ciwon.da ƙirjinta yake mata ta ji ya ɗan ragu, sannan ta ji kamar ta haɗiye wani abu wanda a ƴan kwanakin nan ya tokareta!


"Abban ABIE inason ka mayarni ɗakina kaji!


Zakiyyah kenan ai kece Kika ƙi ɗakin naki, Amma ba ni mukhtar na hanaki ba,dokin zuciya ki ka hau shiyasa na baki sarari, Amma tun da yanzu kinason komawa ai shikenan daga kinji sauƙi sai komawa gidanki!


Ya ƙarasa zancen da murmushi da alamun tausayi gareta!


Zata kuma magana yace ya Isa hakanan bakida lafiya.


Tun Fara maganar su likita ya ba su waje, domin wannan zancen na su sirrin sune, ya na fita kuma ya je yake sanarwa da su Bilkisu ɗin Zakiyyah ta farka kuma Alhamdullillahi da sauƙi, dan har ta yi magana ma,


Cike da zumuɗi suka ta shi da niyyar ɗunguma zuwa ɗakin, sai likita ya katse su da cewa ku bari ta ɗan samu nutsuwa,su ga ma zantawa sai kuje, jiki a sanyaye suka koma su ka zauna.


Acan ɗaki kuwa bayan Zakiyyah ta yi shiru, a zuciyarta sai tunanin wa ya gayawa mukhtar batada lafiya ne? Shin waima wa ya kawota asibitin kodai shine? Da makamantan zantukan da take a zuciyarta sai dai kuma batada amsoshinsu.


Bari na kirawo su Aunty da Hadiyyah ɗin ta re da Bilkisu nake ma, itadai Zakiyyah batayi magana ba mukhtar ya fice domin kiransu.


Ko da yaje bai ga Aunty ba anan suke ce masa ai ta tafi gida tun ɗazu, shikam mukhtar yayi mamakin Hakan amma bai ce komai ba,
Sun ɗunguma zuwa ɗakin gaba ɗaya Hadiyyah da Hidayah sai rige rige akeyi, ita kuma Bilkisu tare da Mukhtar suka jera.
Anan take tambayar mukhtar ɗin jikin nata da sauƙi Amma ko? Da ea ya amsa MATA suka ƙarasawa ɗakin.


Su Hadiyyah sai Sannu suke jerawa Zakiyyah ita kuma tana ɗaga kai alamun yawwa.


Sai Bilkisu ta razana dataga Zakiyyah yadda ta koma, gaskia kam abar tausayice, wannan ra ma haka,Duk yadda akayi batajin daɗin zaman gidan nasu,zata yiwa zaujin saleh magana Akan yai MATA izinin komawa ɗakin ta ko Dan ABIE ma daya Fara kuka akan haka, saboda tana son yaron tanaso yai rayuwa da mahaifiyarsa,zancen zucin da Bilkisu takeyi kenan harta ƙarasa wajen Zakiyyah tai MATA ya jiki,ita kuma ta amsa a Hankali.


Zakiyyah ta yi mamakin zuwan Bilkisu gurinta fa,kuma ta ji Duk wani haushi nata da takeji ta daina,saima burgeta da tayi, haka ai dama abun ALLAH yake Zakiyyah kam kinyi Hankali kinyi ta ƙawayenki.


Haka dai suka zauna wajen Zakiyyah Babu mai alamun barci, mukhtar da Bilkisu su na kan kujera kusa da juna, su ma su Hadiyyah Hakan.


Likita ya dawo yace zai kuma sakawa Zakiyyah ruwa da jinin da yayi saura dan taji ƙarfin jikinta kafin safe, acikin Ruwan yasa MATA allurar barci wanda zata kuma samun hutu sosai.








*************




Bayan su Sa'adatu sun koma gida, anan maƙota sukejin labarin jikin Zakiyyah da sauƙi, ta farfaɗo ma kafin tawowarta,Amma ta kuma komawa, tana kiran mijinta, kuma yanzu haka yazo, su ma yaran su Khadija da Farouk da hydar sai sannan zuciyarsu tai Sanyi jin Yaya Zakiyyah bata mutu ba.


An Sha ƙauna kam Sa'adatu da Alhaji gambo, sai asubar kamar yadda tace sannan ta komo asibitin,ita da shi Alhaji gambo ɗin, Hadiyyah tace ta tawowa da Zakiyyah kayan sawa, lokacin kuma Zakiyyah ta farka ma Sha ALLAH har tayi wanka ma da taimakon su Hadiyyah, da abun karyawa Sa'adatu ta tawo(Alhaji Gambo ya ajiye, albarka in Auren Sa'adatu da yayi)


Sai sannan kuma Sa'adatu tacewa Mukhtar da Bilkisu suje gida, tun da ga ta tadawo,basuyi musu ba saboda sumbar Husna da ABIE a gida ba da zummar kwana ba,nan sukayi sallama suka fice sai gida.


Nan Zakiyyah ta gayawa Sa'adatu cewa mukhtar yace idan taji sauƙi ta dawo ɗakinta, cikin murna tai maganar, Hadiyyah da Hidayah sunfi kowa murna da wannan zancen,Duk sun ƙarya, anata Hira jikin Zakiyyah kam ma Sha ALLAH,likita ya shigo ya bata magani, ya kuma jona MATA ruwa da jini danta samu ƙarfin jiki.


Kafin safiya tuni zancen cutar Zakiyyah ta je kunnen Baaba Hadiyyah ta kirata, jin Abubuwan da Hadiyyah ta zayyana yana damun Zakiyyah ya tadawa Baaba Hankali,dan haka tace in anjima tananan zuwa day kaduna ɗin,kuma ta gaisa da Zakiyyah ɗin, har Baaba take MATA tsiya "in mijinki kike son komawa ai ba sai kins kanki a uku ba, sauƙi kirashi kubashi haƙuri, koda yake ai akwai kunya,sannan yunwa kuma bansan me ya sa ta sameki ba(Baaba batasan anawa Zakiyyah horon yunwa ba)
Itadai Zakiyyah ba bu bakin magana sukayi sallama da Baaba.


_____
Can gurin mukhtar ma haka da suka koma gida, sun samu har ABIE ya tashi yana rigima, Husna tai Masa wanka itama tayi, ta na mamakin daɗewar su, su da sukace MATA siyayyah zasuyi, barcin ma rabi_rabi tayishi, sai kuma sallamar su yanzu, a sanyaye ta amsa da tambayar su ina sukaje suka kwana?ta kwana cikin tsoro da fargaba, kwashe komai sukayi suka gaya MATA kuma ta tausayawa Zakiyyah ɗin tun da da ma tasanta.


Saida sukayi wanka da karyawa, sannan Mukhtar ya Kira Hajiya jamila yake gaya mata,itama ta tausaya Zakiyyah ɗin dama kuma tana ƙaunarta tun asali,itace dai take haukanta a da,ku ma ta ji daɗi da yace MATA yace ta dawo ɗakinta in taji sauƙi, tai Masa addu'a.


Mukhtar yacewa Bilkisu Zakiyyah zata dawo gidanta da taji sauƙi, Alhamdullillahi zaujin saleh da ma haka nake burin gaya maka kayi, ta bani tausayi sosai, ALLAH ya haɗe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login