Showing 12001 words to 15000 words out of 141223 words
Chapter 5 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
ga shaye_shaye yanayi, basa ganin kowa da gashi...) Duk su yaran suna kallon abunda Alhaji yayi, Zahar da Hadiyyah sunsha kuka, Wai yau Alhaji ne take shaye_shaye, saboda Rashin mahaifi, me Abbynsu ya ragesu, Alhaji yaro Mai hankali, da nutsuwa ko fita waje bayayi, Amma shine yanzu Abby Yana Masa duk abunda yakeso, Amma yazama hakan, lallai sunyi rashin Abby rashinsa yasa Alhaji yazama Mara kunya Kuma d'an shaye_shaye rayuwa kenan.....
Zuciyar kawu Isma'il kamar zata fashe saboda ba'kin cikin abunda Alhaji yakeyi Kuma yai Masa,yanke hukunci yayi zai kaishi makarantar kangararrun Yara........
********************
"Bangaren Hidayah mutanen Kaduna state Kuma , suna waya dasu Hadiyyah anan taji labarin cewa Hunaif Yana wajensu, Hidayah tanason Hunaif tun asali dama, Dan hakan tagayawa Baaba cewa idan sukaje Kano kawai su d'auko Hunaif yadawo wajenta da Zama, tunda can sunada yawa,ita Kuma ita kad'aice, Hadiyyah tana gayawa Hidayah duk irin wahalar da sukesha, wajen Sa'adatu, Hidayah har kuka take tana Basu haquri, tace idan sukazo Kano da Hunaif zasu dawo kaduna, itama Nan zamanta yanada amfani wajen Baaba Domin tana tayata jinyar Mahaifiyarta wajen y'an wanki wanke_wanke da sauransu, itama zaman nata yanada amfani da saita dawo gida kawai su zauna tare cewar Hidayah, Koda tagayawa Baaba yadda sukayi dasu Hadiyyah....
itakam Baaba batayi mamakin Sa'adatu ba Dan tanayiwa su Zahra mugunta, la'akari da yadda akasha fama da ita farkon Aurenta da Alhaji Ammar d'in, makirci kala_kala tadinga yiwa Ummu Ruman y'arta, badon Allah yayi Ummu Ruman zatayiwa Alhaji Ammar takaba ba Aida tuni Aurensu yaqare tuni, yadda aka Fara sakinta bayan auren Sa'adatu da Alhaji Ammar d'in, Amma dayake Allah yafi qarfinta Kuma makircinta baiyi tasiriva, haka dai sukaci gaba da Zama har mutuwa ta rabasu da juna, daga baya itama Ummu Ruman d'in tabishi...
Baaba kullum tanawa su Hadiyyah da Zahra nasiha akan suyi haquri da Sa'adatu komai mai wucewa ne, sukayi haquri da *RASHIN IYAYE* biyu ma, balle wani muguntarta da makircinta suda suke Mata duk ranar da lokacin aurensu yayi suka tafi suka bar mata gidan shikenan, wannan nasihar da Baaba take musu tana kwantar musu da hankali a Koda yaushe......
********************
"Zahra wani d'an saurayi Mai hankali da nutsuwa, ya nuna yanasonta, Kuma Yana tausaya Mata da halin maraicin da suke ciki, anan gaba da unguwarsu yake, d'an masu kud'ine sosai, sunansa IBRAHIM Yana zuwa xance wajenta, Shirin kawo kud'i akeyi ma, jira yake Zahra suyi exam tukunna....
IBRAHIM marayane shima mahaifinsa Alhaji bala ya rasu shekara d'aya da tawuce, sai mahaifiyar sa, Hajiya maimuna, yayyensa duk matane sunyi aure, Hajiya maimuna macece Mai tsaninin kishi, ga kishiyoyinta tun Alhaji baka Yana raye, Amma bayan Wannan batada wani mugun Hali, Koda IBRAHIM yace Mata yasamo wacce yakeso Bata nuna wani abuba tace Allah ya Sanya albarka yakaimu lokacin lfy.........
*******************
Halin Zakiyyah yananan Babu abunda tacanxa, na yawonta, da Tara Mata a gidanta, sai Mukhtar yayi tunanin kodan batada yaro ne yasa take hakan? Har wajen Hajiya sakinah yaje yace yanson abashi zeenah qanwar Zakiyyah d'in xai riqeta, Hajiya tabashi kuwa zeenah , yakawowa Zakiyyah ita Wai ko kula da yarinya xaisa Zakiyyah tadaina fita yawo an samarwa xeenah makaranta pravet school Mai tsada, tun safe sai magrib, ake dawowa, Mukhtar Yana son yarinyar sosai, yasiyo Mata kayan Wasa, kayan ciye_ciye......
Zuwan Zeenah Bai canzawa Zakiyyah hali ba, Domin da safe idan ta shirya Zakiyyah Isma'il ne yake tafiya da ita yakaita makaranta, suna fita itama zata saka qafa tafice, yawan bin makota, d har lokacin tashin su Zeenah sannan take ta d'aukota su dawo gida, mukhtar Bai San da wannan ba, Shi zai bayan sallar isha'i yake dawowa, yayi tunanin Zakiyyah tadaina fita d'in, tunda inya dawo Yana damunta a gida.....
IDan Zakiyyah taji zance yayi zance, a makota anata Hira wataran mancewa takeyi da zeenah tana makaranta fa, har atashi bataje ta d'auko taba, yarinya tagaji da jiran Aunty Zakiyyah, saidai takamo hanya tadawo gida, ta ra'be a bakin gate, Kota shiga wasu maqotan, sai Zakiyyah tadawo sannan ta nemota su koma gida, haka halin Zakiyyah yake, ko tausayawa qanwarta batayi, shikuma mukhtar Bai saniba......
Yau, Zakiyyah Hira tayi Hira, tanacan makota, har Zeenah tadawo daga makaranta Bata dawoba, gidan da zeenah ta shiga shine matar ta aiki zeenah d'in bakin titi ta siyo Mata abu a kanti, a wannan lokacinne Kuma Allah da ikonsa zeenah......
Muje next page kuji mexai faru da zeenah marainiyar Allah, Wanda Allah yahad'ata da sha_shashar Yaya Zakiyyah, gwanda ma abarta a gidansu cikin Yan uwanta masu hankali ba rikon kaaka ba Kuma ga'buwa marar hankali
*✍️©️ Rabiat Amin Oum Arqam 👩🍼 ce*
Domin sharhi ko shawara
*08128131163*
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M°W°A)*
*RASHIN IYAYE* (babbar musiba)
*✍️daga Al'kalamin Rabiat Aminu (Oum Arqam 👩🍼)*
Marubiciyar✍️
Komai nisan jifa📚
Hakan ba kuskure bane📚
*PAGE THIRTEEN 13*
"Hajiya sakinah takirawo kawu isma'il tace maza_maza yad'auki Hunaif ya kaishi kaduna, rana tsaka su baaba da Hidayah, sukaga ankawo musu shi, to dama dai baaba tayi niyya ko ba'a kawo Shiba zataje ta d'auko shi, koda aka kawoshi Babu tantama ta kar'beshi, su Hidayah anata murna Hunaif yadawo wajensu, ga Kuma wahala ta ragewa su Hadiyyah,,,,,
Haka baaba yau da dad'i gobe Babu dad'i take riqon su, domin kuwa dai sai kawu isma'il yayi ra'ayi yake musu Aiken sabulu da man shafawa, da y'an kud'i, acikin ribar da ake samu nasu, Amma lissafin dayakeyi duk wata kowanne ake bashi hardasu Hunaif da Hidayah d'in...
Amma banda Zeenah domin mukhtar mijin Zakiyyah yace abunda zaiwa y'ay'an daya Haifa in Allah yabashi itama xai matane..........
*************
"Bangaren Sa'adatu da Hauwa kishiyarta kuwa, abundai Babu yabo Babu fallasa, Hauwa ta takurawa Sa'adatu da habaici da cin mutunci kala_kala, Babu damar ta fito tsakar gida ta zauna, acikin d'akinta ma Bata tsira ba, ikon Allah kenan ai dama duk abunda kayi sai an maka kad'an tafara gani, Allah sarki Ummu Ruman kuduba irin xaman da sukayi da ita gallazawa iya gallazawa ga makirci iya makirci da kisisina Babu Wanda Sa'adatu batayiwa Marigayiya Ummu Ruman, a wajen marigayi Alhaji Ammar (bn yassir)to yanzu dai Kashi tasamu dai_dai da ita, shukam su Zahra da Hadiyyah Babu ruwansu abunsu, suna gefe suna ganin ikon Allah, suna tuna xaman Aunty(Kamar yadda suke Kiran Sa'adatu dashi) dama akwai Wanda Sa'adatu zataji tsoro? Akwai Wanda yafita dama rashin mutunci? Lallai kam hakkin ummyn sune, ta qarkashin qasa Hauwa ta fara bi tana yaqar Sa'adatu tasa yanzu kawu isma'il kwata_kwata baya wani kulata, ya mayar da ita Kamar banza a gidan, duk abunda Hauwa take na rashin mutunci agabansa takeyi baya magana, idone nasa, idan Kuma ta rama yayo kanta da masifa, yace batason xama lafiya,halin da Sa'adatu take ciki kenan tsakaninta da Kawu isma'il da matarsa Hauwa.......
Hajiya sakinah kuwa, tun bayan rasuwar Abby ta samu kud'ad'e acikin kud'in daya bari, duniyarta takeci da tsinke, gidan datake ciki, an qawatashi da kayan qawa Kai bakace gidan tsohuwa kamarta bane, ko wata yarinyar mace d'in albarka, kowa sai mamakinta yakeyi ace d'an ka Wanda yakeji dakai, ya fad'e ya mutu Amma kamance, duk da lokacin mutuwarsa tajita Amma yanzu ta girgije, tana kallon y'ay'an daya mutu yabari an rasa me d'aukar nauyinsu, da dukiyar da ake juya musu ribar da ita ake musu wahalhalun yau da gobe, Kuma tasan kawu isma'il Yana almundahana da dukiyar Amma takasa magana.......
Gidan da ake ginawa Ummu Ruman, zasu tare Allah be yiba, an kammala ginashi Masha Allah yayi kyau, wannan gida bai kamata da haya ba, saboda tsaruwarsa,Amma hakadai aka saka haya d'in, sama da qasa mutum biyune suka kamashi, wa da qanine xasuyi Aure, shine suka kama, Masha Allah Saida akayi jere aka tsara gidan yayi kyau, kud'in haya kawu isma'il ne Wai xai dinga kar'ba duk shekara, Wai xai bud'e banki ya dinga zuba kud'in idan Allah yakaimi Auren y'ay'an Ummu Ruman su Zahra Hadiyyah da Hidayah da Khadija sai ayi musu wahala dasu,to FANS Allah Yasa hakan......
*************
"Allah da ikonsa zeenah zata tsallaka titi saura qiris wata mota ta kad'eta tabi takanta, Allah ya kiyaye tad'an bigeta Amma,Kuma ta wad'i qasa, mutumin dayake tuki ya fito Yana sallallami, Abba ne (wato mukhtar) cewar zeenah, mukhtar Yana zuwa wajen zeenah ya d'auketa daga qasan da take tana kuka, mukhtar karkad'e mata jiki yayi, zuciyarsa kamar ta 'billo daga qirjinsa saboda masifar da take cinsa, cikin murya wadda take nuna 'bacin Rai tambayar zeenah yayi wane ya aikeki Zeenah? Cikin shashsheqar kuka Zeenah Babu wayo ta kashe komai ta gayawa Mukhtar cewa ai ita ta dawo daga makaranta Kuma tana gidan Maman Waleed yau bataga Yaya zakiyyah ba, shine ta aikota tasiyo mata Pampers, zuciyar mukhtar yau takai karshe, rike hannun Zeenah yayi yasata a mota, bayan ya duban yaga bataji ciwo ba, razana ce tasa ta fad'i a qasa, sai kujewa kad'an datayi a gwiwa,koda sukaje gida har sannan zakiyyah Bata dawoba, sauka yayi yaje ya bud'e gidan ya bud'e gate ya shiga da motarsa ciki, cirewa Zeenah Kaya yayi Yasa tayi alwala Shima yayi sannan sukayi sallah agida,sai Kai kawo yakeyi yaga ta Ina zakiyyah zata shigo.........
Ita dama zakiyyah tasan Zeenah tana gidan Maman Waleed, takanas gidan taje tun daga bakin qofa ta qallowa Maman Waleed Kira tace Ina Zeenah ne? Ta tawo mutafi gida, shiru taji, sai sannan takula da qofar Maman Waleed a rufe take.turus zakiyyah tayi tana mamakin Ina Maman Waleed tayi haka? Kaqewa tunaninta yayi lokacin da Maman Waleed tace wa zakiyyah, Kinga Aiken Zeenah nayi bakin titi ta siyomun Pampers naga shiru_shiru Bata dawoba,nabita kantin batanan, jimamin Ina taje nake, sororo zakiyyah tayi, saboda ta qware a harkar qarya saita d'auko waya ta Kira mukhtar Wai zata Gaya masa cewa, Zeenah bayan tasowa daga makaranta Bata ganta ba, taje d'aukota, Mai gadin makarantar yace yaganta ta tafi gida, tana Kiran wayar mukhtar ya d'aga kamar Babu abunda ya faru, zakiyyah Saida tagama Yi masa qarya sannan ya qatseta, cikin fad'a to maqaryaciya gani da Zeenah acikin gida idan kingama barbad'a da yawon naki ki dawo gida banza ballagaza marar hankali, wacce batasan inda yake mata ciwo ba, Saida zakiyyah tagama jin cin mutincin da mukhtar yai mata sannan ta kashe wayar, sai Kuma tabasar tacewa Maman Waleed ai mukhtar ne yadawo ya had'u da ita ya tafi da ita gida, da safe na Aiko Miki da Pampers d'in,kuji FANS lallai Zakiyyah babu hankali, Bata gano rashin hankalin abunda tayiba,ta 'batawa mijinta hankaki Amma ko ajikinta,,,,
Lokacin da Zakiyyah ta dawo cikin gidanta, sunyi bala'i itada mukhtar, ya gaggaya mata magana Mai ciwo, yace da ita "shashasha ballagaza Y'ar iska jaka mahaukaciya wacce batasan meyake damunta ba, sannan ya d'auketa da maruka lafiyayyu, itama cikin ga'bunta da rashin iya magana da rashin hankali Zakiyyah tace " Wai akan Zeenah kake gayamun wad'annan maganganun? To Ina ruwanka da Zeenah Y'ar uwarka ko Y'ar uwata, mene had'inka da ita? Uwartace Kai ko ubanta? Acikin banza aikin wofi,taja tsaqi tayi wucewarta cikin d'akinta,da makamantan wad'annan maganganu, Zakiyyah tagayawa mukhtar. Lallai fans Zakiyyah batada Hankali.....
Aikuwa mukhtar cikin d'akin ya bita yace ki fitarmun daga gidana, bana buqatar ganinki a wajena, Zeenah tafiyemun ke sau dubu, ita yarinyace Amma tafiki Hankali, zo ki ficemun daga gidana,.....
Zakiyyah kuwa Babu wani tsoro tace " saime Dan nabar gidanka, irin cin mutuncin da kakemun da zagin iyayena, da kakeyi ya isheni, ta d'auko Zeenah daga d'akinta har tafara barci "zo mu tafi gidan ubanmu Zeenah, aikuwa mukhtar ya riqe hannun Zeenah yace ai bakece kika bani itaba Dan haka baki Isa ki kar'beta daga hannuna ba, kedai kije ki gama haukanki acan.......
Haka Zakiyyah ta fice daga gidan a wannan Daren, ta nufi gidan Hajiya sakinah, koda taje qarya da gaskia ta gayawa Hajiya sakinah, Hajiya sakinah tace " nasan halinki Zakiyyah bakida dama bakida hankali da tunani,sai mukhtar yazo naji ta bakinsa......
Mukhtar Kiran mahaifiyarsa yayi Hajiya Jamila yagaya mata, yadda sukayi da Zakiyyah d'in, Amma maman mukhtar rufe idonta tayi taciwa mukhtar mutunci, tace meyasa bakada Haquri Mukhtar kadinga haquri da Zakiyyah yarinyace Kuma gata marainiya, sai haquri wata rana sai labari, kadaina kulata akan abunda takeyi, zanzo nai mata magana akan halinta,in Sha Allah zata daina, wuyarta Allah yabaku Haihuwa wata macen haka take saita haihu take hankali, hakadai Mama tayiwa Mukhtar tatas, yace Kuma gobe kaje ka d'aukota ka dawo da ita gidan karshe ta kashe wayar......
Duk irin xaman da mukhtar yakeyi na haquri da Zakiyyah, da laifukan da take masa, muddin zai gayawa Mamansa Bata goyuwa da bayansa, Haka take goyuwa da bayan Zakiyyah, ita tausaya mata takeyi, saboda halin maraicin da take ciki.lallai FANS Anya xa'a samu irin Hajiya Jamila, batasan halin Zakiyyah bane Allah Yasa kar takaita qarshe..........
Muje zuwa next page yanzu aka fara wasan, har yanzu bamu shiga cikin labarin tagwaye masu kama d'aya ba wato Hadiyyah da Hidayah........
*✍️©️Rabiat Amin oum Arqam ce 🤱*
Domin shawara ko sharhi *08128131163*
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba)
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M°W°A)
*✍️Daga Al 'kalamin ©️Rabiat Amin (oum Arqam🤱)*
*PAGE FOURTEEN 14*
"Washe garin Ranar kuwa mukhtar yatashi da safe ya shirya Zeenah yakaita makaranta,yatafi kasuwa, sai yamma yaje gidan Hajiya sakinah,fuskarsa Babu walwala suka gaisa da Hajiya sakinah d'in, bayan sun Gama gaisawa Hajiya ta tambayeshi meya had'ashi da Zakiyyah? Tiryan_tiryan ya kwashe labarin duk halin da suke ciki da irin halin zakiyyah yagayawa Hajiya sakinah,duk da Daman dai ta sani, Zakiyyah tana cikin d'aki Hajiya ta qwala Mata Kira, bayan ta fito, Hajiya tace "duk kinaji abunda yafad'a kinayi, kije kici gaba dayi, bazan hanaki ba, Zakiyyah bansan halin wa kika d'auko ba, mahaifiyarki ba Haka takeba,nima Dana riqeki hakan, ke kikasan a inda kika kwaso, Zakiyyah tana ganin Hajiya sakinah tana Mata fad'a,(wannan ai ba fad'a bane FANS anawa ganin fa,mutuniyar da take wannan Rashin wannan xa'a yiwa irin wannan fad'an?) Kumbure_kumbure ta fara, to itama Hajiya sakinah itace dama ta 'batata da sai abunda takeso, sai tace kiyi haquri kinji Zakiyyah ta ki qara haquri nasan ke Yarinyace me hankali, shidai mukhtar yana zaune Yana kallon ikon Allah, duk da baiyi mamaki ba bayau yata'ba ganin wannan halin na Hajiya sakinah da Zakiyyah ba Amma abunda tai masa be kamata a wani lalla'bataba, ai shikenan muje zuwa ni daku,tunda Haqurin danake da ita bakya gani ko Hajiya? Mukhtar yafad'a a zuciyarsa,
Saida Zakiyyah tagama iskancinta tagama Hulaqanci sannan ta tashi ta d'auko mayafi ta taiwa Hajiya sallama, suka tafi, ko a mota Zakiyyah Bata kula mukhtar ba,Shima Kuma bai kulata ba har sukaje gida.......
Haka Xaman Zakiyyah da mukhtar yaci gaba, kunsan tsakanin Mata da miji sai Allah, a halinta Babu abunda ya sauya, in tayi yayi Mata fad'a, in yagayawa Hajiya Jamila Kuma ta goyi bayan Zakiyyah tace shine bashida Haquri, Zeenah tana zuwa makarantar ta yau da dad'i gobe Babu dad'i, harta Saba da halin Zakiyyah,yanzu dakanta take dawowa daga makaranta, inta sameta a gida ta shiga idan batanan ta zauna a qofar gida ta jirata, don yanxu Zakiyyah Bata kaiwa sallar magrib a maqota,
Zakiyyah yanzu cikine da ita, ga cikin Mai sa laulayi da kasala, Bata aikata komai, fita maqota tadaina yinta,Inna tashi Bata iya ta'bukawa kanta komai, aikin gida mukhtar kafin yafita yakeyi Mata, kullum tana gida, samun cikin sai yayiwa mukhtar dad'i, gwanda yayi aikin gidan, ita Kuma ta zauna a gida dadai tayi aikin gidan kullum tana maqota, ko ta Tara masa Mata a gida, itama Zeenah taji dad'i kullum Aunty tana gida, har wata qiba tayi,yanzu Babu zaman bakin gate,tun daga laulayin Zakiyyah kuma saita rage fita har cikin ya tsufa........
Cikin ikon Allah Zakiyyah ta sauka lafiya Namiji ta Haifa, mukhtar yasaka masa suna *Ammar* Sunan babansu Zakiyyah suna kiransa da *ABIE* ko taron suna ba'ayiba, sai Wanda Allah yayi shine yazo yayiwa Zakiyyah barka, duk rashin hankali na Zakiyyah Ranar Saida tayi kukan Rashin iyayenta data tuna Haihuwarta ta fari Babu Rai tayita, lokacin Abby da ummy suna Raye Babu Wanda zaice Babu d'a irin yadda akayi cikowa zuwa Yi Mata barka da Kuma Allah ya jiqan Rai, Amma yanzu darai ta haifi yaro y'an uwansu ba kowane yazo ba, sai wa'yanda baza'a rasaba, sai Kuma maqotan da suke mutunci dasu.....
Baaba da Hidayah da Hunaif sunzo Kano Sunan Zakiyyah, Masha Allah Hunaif yaro yayi girma Yana samun kulawa ke bakyace shine Wanda yasha cutar Kashi ba, ya murmure abunsa, Kuma sun xagaya dangi, sai mamakin d'an maraya akeyi ya gagije,ai suna zuwa Hidayah da Hadiyyah rungume juna sukayi sunata murna, sun fara zama y'an Mata abunsu,kamarsu taqara fitowa Babu banbanci kam,ansha hirar zumunci Hidayah tadinga bawa y'ar uwarta labarin kaduna, Ranar ansha hira ai Zahra da Khadeeja sunyi murnar zuwan Baaba.........
Hadiyyah ce taje yiwa Zakiyyah zaman wanka, tunda lokacin anyi hutun makaranta, sai Hidayah ta bita can kafin su koma kaduna, Ranar Sunan da Zakiyyah take kuka Baaba tadinga Mata fad'a kuwa "ai inajin duk halin da kike ciki keda mijinki, duk abunda yake faruwa dake baxaisa kiyi hankali ba Zakiyyah, yaronan Mukhtar meya raga Miki? Yazake Miki mijin marainiya, komai baki rasaba ga Y'ar uwarki Zeenah Yana riqonta kamar shine ya haifeta, sauran y'an uwanki sunanan an rasa Mai kula dasu saboda Allah, kinadai kallo abinci sabulun wanka Dana wanki da sauran abubuwan buqata Babu Wanda yad'auke musu acikin kud'in da ake juya muku ribar da ita ake musu amfani,Amma hakan be zame Miki izina ba, yakamata kiyi hankali dai yanxu gakinan da d'anki a hannu, ki gyara Halinki karki Kai mukhtar bango ya sakeki, ko ya qara aure bakisan wacce iri zai auroba me halin kirki ko akasin hakan, inkinji mgana ta ke kika sani idan kin watsar kece aciki, y'an uwanki y'an Mata ma a gidanku xaman wahala da haquri sukeyi balle ke, nikuma danake Rikon Hidayah da Hunaif sai haquri ba sana'a nake ba sai rufin asirin Allah kawai da Rikon marayu kuma. Nan dai baaba taiwa Zakiyyah fad'a tayi shiru kamar taji, Hadiyyah Saida tasa baki, (kuji FANS yarinya ta fita hankai..) nima baaba abunda nake gayawa Aunty Zakiyyah kenan, muma cikin halin matsin rayuwa muke ta riqe Yaya mukhtar hannu bibbiyu Babu abunda ya raga Mata Amma,saita dinga cewa Wai Zan mata rashin kunya daga nafad'a Mata gaskia, shiyasa nadaina nikam, ai shikenan Hadiyyah qaleta