Showing 36001 words to 39000 words out of 141223 words

Chapter 13 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

shiyasa sukeson ziyarar sa, balle wannan ziyarar ta bazata.




Sai shigowa ma'aikatan suke Suna kwasar gaisuwa gurin Alhaji tallafy, tun bayan sannu da zuwan da sukai Masa, shida iyalansa suka tafi WANI gini can daga gefe, Wanda dama anan Alhaji tallafy yake yada zanzo DUK sanda yazo,bayan DUK angama hada_hadar da ake ta murnar zuwan Mai gayya Mai aiki abun cikin sha'awa kana ganin wannan kasan tabbas Alhaji tallafy yaci Sunansa yana tallafawa al umar da suke 'karkashinsa, yadda yake mu'amala da body guard da ma'aikan foundation d'insa babu wanda zaice shine sama da su sai kayi duba zuwa gareshi kayi duba zuwa garesu, Amma wasa da dariya abun Ba'a magana.




An samu sabbin d'iba acikin TALLAFY CHARITY FOUNDATION, dan haka Alhaji tallafy Saida Duk ya gana da yaran kowanne yasan tarihin rayuwarsu da musabbabin shigowarsu, kowanne baya rasa nasaba da maraici ko kuma had'uwa da shaidanun abokai,su koyawa yaro shaye_shaye da sace_sace da kallon fina_finan banza ta yadda zasu dinga kallon iyayensu a banza da 'kokarin lalata Yara Mata 'kanana, Duk da yaran suma basa gaza 17_20 Duk haka suke, sai fatan ALLAH ya shirya.






Duk wannan Abubuwan da suka faru a gaban AKEEL da AQEEL da kuma AKEELA ne, kuma da alamu suna sauraron matsalar kowanne yaro ne, musamman masu halin maraici ne sila, Basu da cin yau balle na gobe Wannan tasa suka Fara sata,da kuma masu mahaifiyarsu ce ta fita kishiyar uwarsu ce me gallaza musu, akwai kuma uwar tasu ba fita tayi ba, aikin asiri ne yake dawainiya da mahaifinsu bai san cin su
Da shan su ba, su AQEEL fa sunji halayen Rayuwa kala_kala ga yaran Kuma sun tausaya musu, Amma fa har yanzu sukam Basu samu irin tasu rayuwar da sukayi tun daga lokacin kuruciya zuwa tasawar su ba, su fa yayar mahaifiyarsu ce tai musu Duk wani muzgunawa da zalunci, kuma ta hana mahaifinsu yasan halin da suke ciki, kullum cikin kyautatawa yake tunani take musu, ta yaya zaiyi zaton zata cuci y'ay'anta kanwarta, kowannen su irin tunanikan da sukeyi a ransu kenan.






"Bayan Alhaji tallafy ya KAMMALA saurarar kowanne Bangare na sababbun zubi da akayi na foundation d'insa, yai wa Mai kula dasu magana Akan yanason azo Masa da Yassir Ammar bn Yassir (Alhaji) shikam yaronnan ya tsaya Masa a ransa, yanason yazo ya kuma bada tarihin rayuwarsa a gaban su AQEEL ne, yanason ganin y'an uwansa d'innan gaba d'aya.tun baisan lokacin su Hadiyyah sunzo visiting D'IN Alhaji ba.




Kamar yadda Alhaji yaso hakan, akayi ma'aikaci yazo ya kirawo Alhaji Akan Yallabai yazo kuma yanason ganinsa, Alhaji kam yace to dan shima yanasan yakuma ganin Alhaji tallafy mutum Mai mutunci Mai karamci,


'lokacin da yake shigowa wajen, daga AKEEL da AQEEL da kuma AKEELA da uwa uba Hajiya Aisha sunyi mamaki sosai da akace musu. Wannan yaron Wanda babu alamun wahala a jikinsa,daga gani yaron d'an gata ne, Amma 'kaddara ta kawoshi Wannan cibiya, alamun shaye_shaye dai sun Fara bayyana a gareshi, ta yadda le'ben sa yad'anyi ba'ki da kuma idonsa yad'anyi ja, Duk da YANZU Duk yadaina Wannan al adar Amma komawa daidai sai a hankali kam.




Sun tausaya Masa tun basuji ainahin cikakken labarinsa ba, daya qaraso gurinsu cikin girmamawa ya gaisar da Alhaji tallafy dasu AKEEL, sun yaba hankalinsa sosai,




Nan Alhaji tallafy ya dinga jansa da Hira tun bai saki JIKI ba har yasaka, Saida Alhaji TALLAFY ya gabatar Masa dasu AKEEL sannan yace wad'annan yayyyenka ne, gasunan, suma irin abunda ya faru da y'an uwanka ne ya faru dasu, to yaro na kullum cikin damuwa suke sunqi walwala musamman Wannan da kake ganinsa, ya nuna Masa AQEEL wanda ya kafe Alhaji da idanu yana kallonsa shidai, Saida Alhaji tallafy ya nuna shi sannan ya sauke idonsa daga gareshi had'e da murmushi,shima Alhaji murmushi yayi, Yana tausaya musu najin suma a da sun shige irin halin dasu Hadiyyah suke shiga, har yaji yana 'kwadayin jin labarin su, ta yaya su da suke da kud'i da mahaifi su shiga Wannan halin?




Yawwa Yassir kabawa y'an uwanka labarin ku tun mahaifinku Yana raye.




"Tiryan_tiryan Alhaji yafara bada tarihin rayuwarsa gaba d'aya shida y'an uwansa, ai kafin yakai karshe idon AQEEL yayi jajawur alamun kam gaskia wannan ahali sun shiga cikin bala'i kan bala'i musamman y'an uwansa su Hidayatullah su kam sunga rayuwar maraici RASHIN IYAYE a cikin wata shida, fuskarsa tayi jajawur abunka da fari alamu sun nuna Lallai wannan labarin ya shigeshi alamun tausayi ya bayyana a fuskar sa, hakama AKEEL da AKEELA Duk sunyi zukud'in, ita kam AKEELA har da su Kuka, shima AKEEL Saida ya share wayayen tausayin wad'annan marayun Allah din, sannan Kuma sun tsinewa kawu isma'il yafi cikin carbi, Lallai kam wannan bashida i mani, y'ay'an d'an uwanka zakaci amana, ko da yake su ma fa anci amanarsu Amma ba irin hakaba,mahaifiyar Alhaji itama tayi nata sharafin sosai kuma ita ma batada imanin, Amma Kuma sunyi addua ALLAH yasa kawu isma'il ya cuceta ya kar'be mata komai na dukiyarta.....ai kusan hakan ya faru harda tago mashin saki ma , Amma Kuma dukiyar kam bai ci ba sai wacce aka bashi da amana Akan ya juya musu ita yake Shirin cinyewa, Duk bada'kalar da akayi tsakanin kawu isma'il da sa'adatu Alhaji bai sani ba idan baku mantaba ankawoshi tallafy foundation lokacin kawu isma'il da sa'adatu Suna jone kamar tip da taya....




'Shima kansa Alhaji sai da yayi kukan tunowa da mahaifinsa da mahaifiyarsu Hadiyyah, Alhaji tallafy Saida ya rarrasheshi, sannan yajita ga oga AQEEL da, sannan sai ajiyar xuciya kawai yakeyi, kaji labarin wannan marayan ko da halin da y'an uwansa mata suke ciki ko? To inaso dan ALLAH kacirewa kanka damuwa Akan abunda ya faru shekarun Baya, kema AKEELA kinji dai ko? Yakai duba gareta ita kam Kuka take sosai Akan rayuwar da su Hadiyyatur_rahman suke ciki,.... Lallai kam AKEELA bakisan rayuwar da suke ciki bane bayan tawowar Alhaji, tallafy foundation bane ina ga da sai kinyi kukan jini,


" Cikin Kuka tace "Abbu naji halin da suke ciki in Sha Allah zan cirewa kaina damuwar dake raina, Duk da har yanxu inajin ciwonnan Abbu"


Ta 'karasa cikin Kuka


Yawwa AKEELA da naji dad'i, wannan kuma ciwon da sannu zai warke kinji daughter cikin lallashi ya 'karasa zancen


" In Sha ALLAH Abbu nai alqawari"




Shikam AKEEL dama damuwar tasa da sauqi ba kamar y'an uwan sa ba, shima Abbu d'in sai da yai masa magana cikin share hawaye yace


" in Sha Allah Abbu zaka samemu masu cirewa kanmu damuwa kaji abbuna cikin"


Yawwa d'an albarka




"Yakai duba ga AQEEL yace " AQEEL nawa kaima inason Dan ALLAH ka cirewa kanka damuwa Duk da abun daya faru dakai akwai ciwo, Amma ai yanzu komai ya wuce kaji, sakawa rai damuwar na iya sa ciwon ka ya tashi, kasan kuma abunda likitanka yace"


Alhaji tallafy ya 'karasa maganar yana kai duban sa ga AQEEL d'in.


Wanda har sannan ajiyar zuciya yakeyi, Kuma in Yana Wannan yanayin Baya iya magana saidai yayi shiru idonsa da fuskar sa suyi jajawur yai ta ajiyar zuciya, yafi shiga wannan yanayin in aka tuno masa da rayuwarsa ta Baya.




Lallai Wannan ahali sun bani tausayi matu'ka gaya, inason jin tarihin rayuwarsu yadda Alhaji yakeson ji.




"Ruwa Mai sanyi body guard ya tsiyayo a dispenser dake flourn Mai sanyi ya miqawa AQEEL da ke ta ajiyar zuciya, bai iya kar'ba ba sai AKEEL ne ya kar'ba ya kai Masa saitin bakinsa bashi sannan yasha, bayan ya gama sha ya lumshe ido, alamun yasamu relief, haka ake Masa In ya shiga irin wannan yanayin,




Ajiyar zuciya Alhaji tallafy da Hajiya Aisha sukayi ganin AQEEL ya lumshe idanunsa alamun an samu nasara Kenan, shima AKEEL da AKEELA hankalinsu ya kwanta ganin abun baiyi nisa ba ga d'an uwansu,Duk da itama AKEELA d'in tana da cutar Amma batayi tsamari ba kamar ta AQEEL d'in.




Alhaji ya tausaya Wannan ahali su da suke da uwa da uba a raye Kenan Suna da damuwa ina ga su Hadiyyah da shi kansa ma, da irin yadda kawu isma'il yasanya rayuwarsu cikin wani yanayi da uwa uba Aunty(saadatu) mahaifiyarsa ita ma ta bada kamasho dan idan bata auri kawu isma'il ba ai Duk wani abun bazaiyi tsamari ba.




" To Yassir yaushe y'an uwanka zasu kawo maka ziyara ne, inason ganinsu baki d'aya, ALLAH yasa dai lokacin da Mutan kaduna za'a zo dan inason ganin wad'annan y'an biyun naku,




Alhaji tallafy ya 'karasa maganar yana murmushi,alamu dai ya nuna yanason y'an y'an biyu, dai gashi su Hadiyyah har sun shiga ransa.


"Yallabai ai yau suka zo Masa visiting d'in gaba d'ayansu abun gwanin sha'awa, har da wasu masu kama d'aya sak, kamar dai wad'annan y'an biyun naka ya nuna AQEEL da AKEEL,




"Amma Tanko baka gaya mun ba,ai da dasu za'azo Ayi wannan zaman, lallai kam fad'uwa tazo dai_dai da zaka cewar Alhaji tallafy yana shafa gemun fuskarsa, jeka zo Mana da wannan a Hali masu albarka,


"To Yallabai cewar Tanko yana yana fita cikin sauri domin tawo wa dasu Hadiyyah.......








Wayyo hannuna y'an amana, wannan ma dai nayi muku ne Amma har yanxu ina cikin alhini ne.






ALLAH ya gafartawa Zainab da y'ay'anta guda hud'u yakai haske kabarinsu ya kar'bi shahadarsu baki d'aya Yas aljannah makomarsu, ya bawa mijinta Ado haquri da sauran y'an uwanta, please FANS kusakata a cikin adduar ku, gobara suka samune cikin dare, daga ita har yaranta suka mutu ranar da akayi gobarar yarinyar data ke goyo ta rasu, washe gari gari kuma Yara biyu suka mutu, kwana biyu tsakani ita maman ta rasu itama kwana Daya tsakani itama guda dayab data rage ta bisu, munga masifa da bala'i y'an uwa mijinta ma abun tausayi 😭😭😭😭😭😭






✍️Oum ARQAM ce
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*




*PAGE TWENTY EIGHT 28*




ALLAH ya kai haske kabarinsu gaba d'aya iyalan Zainab da ita ma kanta,ya kar'bi Shahadarsu baki d'aya yabawa mijinta haquri da dangana da sauran y'an uwa baki d'aya








"Lokacin da Tanko ya qaraso cikin Hall d'in dasu Hadiyyah suke ciki, sukam har sun 'kosa da Rashin dawowar Alhaji, Yara duk sai wasa sukeyi,manya kuma anata Hira, da murnar ganin Alhaji ya nutsu yadawo kamar yadda yake da , sai abunda ba'a rasaba, sai addu'a Alhaji tallafy yakesha daga bakunan wad'annan ahali masu albarka.




"Ya isar musu da sa'kon Alhaji tallafy yana son ganawa dasu ne, ai sai aka shiga mamakin HAKAN, to Alhaji WANI ganawa zaiyi dasu su kam, koda yake yadda sukejin labarin sa ai Dan yace zai gana dasu ba abune na mamaki ba.


"Tanko yace ina Zuwa Amma,






Fita yayi yaje ya gayawa Alhaji tallafy cewa ai Basu kad'ai bane, mutane da yawa ne,


Anan Alhaji yake cewa "ai dama ba y'an gidanmu bane kad'ai, harda matar kawu Isma'il da y'ay'an sa,


"Ok to shikenan Tanko kirawo su gaba d'aya,ai ba WANI Abu bane,kawaii gaisawa zamuyi, sai Kuma muga y'an uwan nasa




"To shikenan Yallabai bari nakirawo su, Tanko yafad'a yana ficewa


"Gaba d'aya suka Antayo dan amsa Kiran Alhaji tallafy harda su Hajiya Baaba, dasu Hauwa matar kawu Isma'il,sai dai dana kai du bana Banga 'bur'bushin Sa'adatu ba ko ina tayi?






"Tun bayan zuwan Hauwa matar kawu Isma'il fa sudai su Hadiyyah meya faru tsakaninsu da ita? sai alkhair da ta ke musu, lokacin zaman ta a gidansu baza su mance ba, yadda ta dinga kula musu da Hunaif in zasu makaranta da yadda ta dinga wankin kashin sa, ko bama haka ba, tun kafin tazo gidansu akwai girmamawa tsakaninsu da ita, saboda matar kawun suce, tun da tazo suketa murna aketa hirar yaushe rabo, hakama y'ay'anta, itama Baaba sun gaisa da ita da hirar bayan rabuwa, to wannan hirar da ake tsakanin su ita ta hassala Sa'adatu Akan dan me zasu Kula Hauwa tun da bata mata magana ai suma bai kamata suyi mata magana ba, shine taji haushi tayi tafiyarta gida,'karya tai musu wai zata dubiya asibiti ne, sun tawo sukam Suna takan Hira, da to suka bita babu WANI kulawa, shiyasa yanzu babu ita a tawagar zuwa wajen Alhaji tallafy d'in.




"Su AKEEL kam Ashe Basu ga komai a kyau ba Saida suka ga twin's Hadiyyah da Hidayah sannan, da kuma Su Zahra da Zeenah ga Hunaif, dan kuwa su kyawun su daban yake da sauran y'ay'an Sa'adatu, DUK da suma d'in Basu da makusa, AKEEL ya ganesu Hadiyyah ne saboda Kamar da suke da JUNA, babu shakka sune twin's d'in su Alhajin, Wanda Halin maraci ya rabasu da JUNA, Amma shikam ai Baya ganin abunda xai rabashi da d'an uwansa AQEEL abune Mai sauqi.




sai da suka shigo gaba d'aya sannan CIKIN girmamawa suka gaisa da Alhaji tallafy d'in, baaba sai godiya take Masa Akan tallafawa rayuwar marayu da marasa 'karfi da yake, da adduar ALLAH yasa yafi haka,




Shi dai Alhaji tallafy sai "Ameen Ameen yake cewa, saboda matar ta kwanta masa a rai,




Bayan an gama gaishe_gaishe ne, Alhaji tallafy yace" wad'annan sune twins d'in da Alhaji yabamu labarinsu, Lallai kam ALLAH yai muku albarka baki d'ayanku,


Da Ameen suke amsawa




Lallai sunga karamcin Alhaji tallafy yadda yake jansu da Hira, baza ka ta'ba yarda cewa shine Alhaji tallafy d'in ba, yadda ya tamfatsa Wannan foundation d'in da kadarorin daya mallaka, amma YANZU gashi CIKIN su sai Hira yake jansu da ita, DUK da dai ba wani ahi suke cewa ba daga "ea sai a'a"


"Idon AKEEL ya'ki d'aukewa daga kan wad'annan twins d'in,dama akwai twins masu kama irin haka? Bayan su? Yana kallon motsin kowa tsakanin Hadiyyah da Hidayah, yaga dai d'aya tana wa d'aya surutu ita kuma d'ayar Bata magana sai dai kallon d'aya, shi kam shin burgeshi fa.




"Ita ma AKEELA sun burgeta DUK da dai, ta girmesu, Amma Zahra zasu iya sa'a da ita, dan sun burgeta gaba d'aya y'an uwan Alhaji d'in.




DUK Wannan Hirar da akeyi, babu AQEEL a wajen, tun bayan shan ruwansa barci ya kamashi, Dan uwansa ya kamashi ya shige dashi bedroom d'in da yake cikin flourn domin ya samu nutsuwa ko zai dawo dai_dai idan ya farka.




"Tun bayan shigowar su Hadiyyah ya farka, duk surutun dasu keyi yana jin su, Amma kam bazai iya fitowa ba, shi yasa yaci gaba da kwanciyarsa.




Bayan gaishe_gaishe da sauran abubuwan da akayi, su Hadiyyah sukayi haramar tafiya gida, nan Alhaji tallafy yake tambayar shin wacce school suke Zuwa ne? Sukace ai sunyi candy Amma Basu ci gaba ba, ya tausaya musu, dan kuwa yadda mahaifinsu yake da burin y'ay'ansa suyi karatu, bai kamata kawu isma'il ya dakatar dasu, ko da bai bar musu gado ba, tun da dai dai gwargwado yana da rufin asiri ai zai tsaya musu suyi karatun,nan dai aka tsayar da magana,cewa zaizo har gida ya duba lamarin karatun nasu zai tsaya musu, har kawo ALLAH ya kawo musu miji na gari, kar kuso kuga murna gurin su Hadiyyah,sai godiya sukewa Alhaji tallafy d'in,




Nan Baaba take cewa ai cikin satin ga suke Shirin komawa Kaduna kuma har da Zeenah zata tafi,Alhaji tallafy yace idan babu damuwa ta d'an jira zuwan sa kafin su koma, zai san abunyi, ALLAH sarki Alhaji tallafy yadda kake tallafawa al uma kaima ALLAH ya tallafa maka.




"Haka dai su Hadiyyah suka bar tallafy foundation cikin farin ciki da murna, shima Alhaji yakoma cikin y'an uwansa Hostel.






"AKEEL ya shiga gurin d'an uwansa AQEEL yaga har ya farka ma, babu wata matsala tare dashi, damuwar ta ragu ba kamar da ba, dan kuwa idon sa ya washe da fuskarsa Jan ya ragu, haka ma Ajiyar zuciyar da yakeyi ta ragu, nan AKEEL ya dinga Jan sa da Hira, yana bashi labarin su Hadiyyah yaga twins masu kama d'aya kamar yadda suken nan, babu banbanci, sannan Abbu ya d'au nauyin karatunsu, zasu ci gaba da zuwa school,sun bashi tausayi sosai da ua gansu, da irin halin maraicin da suke dashi na babu uwa Babu uba a 'karancin shekarun su, shi dai AQEEL Duk yana saurarar dan uwansa har sannan bai yi magana ba, a haka Alhaji tallafy dasu Hajiya Aisha suka shigo suna Masa sannu yana d'aga kai, har lokacin da suka tattara yana su yana su suka bar tallafy foundation suka d'un Guma zuwa gida, maaikatan ta d'aga wa motar Alhaji tallafy hannu har suka fice,




"Tun daga sannan, abokan karatun Alhaji suke ganin girman shi sun d'auka ko d'an uwan Alhaji tallafy d'in ne ganin sa y'an uwansa su kazo visiting har 'bangaren Alhaji suka shiga, ALLAH sarki basusan kauna ce kawai ALLAH ya had'a tsakanin zuri'ar Alhaji Ammar bn Yassir da Alhaji tallafy ba, da kuma alkhair d'in da Alhaji Ammar d'in yayi lokacin Yana raye ne yake bibiyar y'ay'ansa ba.








**************




Sun koma gida lafiya su Hadiyyah, Zakiyyah Babu Wanda taiwa kallon arzi'ki a cikin su, Suma basu bi takanta ba.




Sa'adatu gidan abokin marigayi Alhaji Ammar bn Yassir taje, uwar gidan sa aminiyar ce , Babu WANI uban nisa da tallafy foundation shi yasa ta wad'a gidan, ita kad'ai ta tawo su haidar da su Hafsat ta barsu wajen su Hidayah,


Su nata hira da Hajiya ikilima sai ga Alhaji gambo ya dawo, nan aka gaisa da sa'adatu da tambayar ta Yara, tace DUK Suna lfy qlau, ya tambayeta ina Mai gidan Isma'il, nan take gaya masa "Yaushe rabona da Auren Isma'il ai da jimawa muka Rabu, duk ta bashi labarin komai yadda ya faru.




Sai naga Alhaji gambo yana WANI kallon Sa'adatu ta kasaj ido ko HAKAN me yake nufi oho?




Alhaji gambo dai abokin Alhaji Ammar bn Yassir ne tare suke Sana'ar su ta safarar shanu, Kuma shima ALLAH ya sa Masa albarka yanada kud'i, Amma saboda babu zumunci tun bayan rasuwar Alhaji Ammar d'in bai waiwayi iyalansa ba yaji me suke buqata me suka rasa.


Matan sa uku Hajiya ikilima qawar Sa'adatu, sai Hajiya suwaiba da Amarya Hajiya sahura, kowanne daga cikin su asiri suke junan su naganin Alhaji gambo ita kad'ai ce y'ar gaban goshi a gareshi, shiyasa Alhaji gambo yake kamar Baya cikin nutsuwar sa,to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login