Showing 66001 words to 69000 words out of 141223 words

Chapter 23 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

bu kowa a gidan da ma,ya ra suna Asibiti abunsu, zuciyarta sai suya take MATA, dan kuwa tanaji a kafafen yaɗa labarai yadda Alhaji tallafy yake tallafawa marasa shi yabasu jari da marayu, ita ma Akan kanta ba gashinan su Hadiyyah da Hidayah sunacin gajiyar arzikin sa ba, yanzu karatu ya yi nisa, kuma a Hakan kuɗin makaranta da komai da komai shine yake musu, hakanan Alhajin ta shima ga shi yanacan foundation ɗin sa ya samu kulawa,yazama nutsatstsen yaro kamar da, Duk wasu Abubuwa ya daina, yai Hankali yanzu ha kama shirin saukar al ƙur'ani yakeyi da wasu littattafan ba bu ko sisi sai abunda ba'a rasaba,yaronta ya Zama Zakaran gwajin dafi, itakam ba bu abunda zata cewa Alhaji tallafy sai godiya, kenan ya zo fuska da fuska ya tallafawa Isma'il kenan kamar yadda ya Saba,ai kuwa da sake an baiwa mai kaza kai, in yasan wata bai san wata ba, zata ɓullo ma sa ta bayan fage, ai yasan wacece ita! I yunwar cikinsa, a tafin hannunta yake komai, zata ɓullo Masa a Sa'adatun daya santa can baya, "Amma kuma bakya ganin akwai ƙura in Kika ɓullowa isma'il tabayan gidan? Zuciyar Sa'adatu ta bata wannan sar! A daidai lokacin da tunanin ta yazo gaɓar nan! Ajiyar zuciya ta sauke ta na zuba ta gumi wan da ya zamar MATA kamar shine mafita yanzu a gareta.


A wannan halin Alhaji gambo ya shigo gidan ya sameta, har yashigo da mota da hour ɗin da yayi Duk bataji ba! Tana tunani!
"Haba irin albarka iri na gari"likita fa ya hanaki tunani barkatai, saboda Magajin Alhaji dake cikinki,ai in ALLAH ya yarda namiji ne Zaki Haifa, sai a saka Masa sunan Marigayi Alhaji Ammar BN Yasir ko? Ku ma bazamu ɓoye ma sa suna ba haka zamu dinga Kiransa dashi ko? Iri na gari! Yana ƙarasa Zama a kusa da ita Akan sofa!
Yana kai hannu ya na riƙo hannunta,
Ai da ma sunan ɗan nan inda amana ai Ammar, Sa'adatu ta faɗi ta na cire hannun ta daga na Alhaji gambo! Sannan ta ce Alhaji kar ya ra su dawo su ganmu a Hakan man, ka san banson Hakan ya na faruwa(kunji ƴar banza kuma) "to iri na gari an dai na, za'a kiyaye kodan saboda magajin Alhaji da ke cikinki, ni fa banson koda da minti ɗaya in miki abunda bakya so, ai ke alkhair ce a gareni, shekara ma wa na ɗauka, ALLAH bai ba ni ɗa ba sai a kanki, aikinga kuwa faranta miki da Duk abunda kikeso ya Zama dole,Yanzu ha ka me kikeso na baki ne? Ni da ma inason kabani kuɗi zanyi amfani da su, yah fa'iza zan ɗan ba wa jari kasan jarinta ya yi ƙasa! aikuwa ba bu musawa Alhaji gambo yaiwa Sa'adatu transfer na 200k ga wannan in da kuma wani Abu ki....
Wayarsa ce ta yi ƙara alamun an kirashi! Hakan ya hanashi ƙarasa maganar da yakeson yi
"Hajiya Babba shine rubuce a screen ɗin wayar! Ɗagawa yayi, dagacan Hajiya Babba tai magana"Alhaji ya dai baka da wo gida da wuri ba,ince ko lafiya?
Hajiya Babba kenan ban da abinki ai kinsan bana kaiwa iyanzu ban dawo gida ba, ka fin naƙara fita Kuma, ina gidan Sa'adatu ne,dole ku dinga haƙuri da Hakan,kunsan dai ba ita ɗaya ba, ku fa haka kuke zagargar mene abun damuwa? In dai Kunga ban dawo da wuri ba ina wajenta to! Cikin muryar faɗa ya ƙarasa maganar da kuma ka she wayar bai bari Hajiya Babba ta kuma wata maganar ba.!


Wacece ku ma take kiranka ne Alhaji? Cewar Sa'adatu ta na wani yatsina ita ga matar so an tawo wajenta, alhalin yau ba a gidanta yake ba ya na can gidansa.
Ikilima ce mai kiran Alhaji gambo ya faɗa, Lallai kam meyasa waini sukemun Hakan, sun Mance cikinka nake ɗauke da shi, ne dole abani kulawa, kodan su juyoyine ALLAH bai ba su ba shine,suke baƙin ciki! Sa'adatu ta faɗa tana kishin giɗa a kan sofa ɗin, alamun ko a jikinta, shi kam Alhaji gambo haka ya ce "rabu da su Iri na gari Duk ina kallon take_taken da suke tun samun cikinki, dan ALLAH bai Basu ba sai ke da kikazo Yanzu, zan takawa kowacce birki, dan Akan cikin nan zan iya sallamar su gaba ɗaya,to mene amfanin su gareni, aike kinfiye mun su, ƴan Iska sai dai aci ati kashi shekara da shekaru
Alhaji gambo, Amma ba bu amfani! Ai kuwa da yafi sauƙi Alhaji dan Basu da amfani kwata_kwata gareka, riƙi_riƙi da su ko kunya, Kowacce Babu ƙwan haihuwa ai anyi ASARA! Ƙalesu Sa'adatu ina ciki da sune zanyi maganin Kowacce! Ki kwantar da hankalin ki kece Ta gaban goshin Gambo,uwar maganin sa! Alhaji gambo ya faɗa haɗe da shigewa turaka, ya bar Sa'adatu a kishin giɗe,ta na murmushin mugunta na ganin taiwa Hajiya ikilima zarra haɗe da sauran matansa.. lallai Sa'adatu anya bakiyi zalunci ba?


______ Hmm Hajiya kenan bana faɗa miki ba maybe ya na wajen waccen tsinanniyar! Hajiya Sahura ta faɗa ta na mai kallon Hajiya ikilima ba ki a sake! Da alamun mamaki dan Duk wayar da tayi da Alhaji gambo a handsfree ta saka ta!


Lalai ne sahura naji zahiri, ai na shaida kuma, Amma wannan kam lokacin cin ubanta ya zo, ƴar Iska waccen a haka zata ƙare, cewar Hajiya ikilima ta na furzar da hucin baƙin ciki,
Sai yanzu Hajiya suwaiba ta magana"aini Hajiya mamakin Sa'adatu nake ta iya aure miki miji, Duk irin amintarku da ita ba ta duba wannan ba, in mu rai Mana haka ai dama can ba ma shiri, Amma ke fa!? Ta na kallon fuskar Hajiya ikilima ɗin!
Banda abinki suwaiba ni wacece? Kun manta da amintarsu da faccalarta, sunsan sirrin juna fa, kamar miji ɗaya suke aure, Amma daga ƙarshe ba aure MATA miji taiba, nan suke zuwa gidannan da Hauwa kamar ƴan uwa ƙarshe me tai MATA! Ai ta Saba cin amana, Alhaji Ammar BN Yasir ma ai Hakan tai Masa badan ALLAH ya aureta ba,kuma ta zo ta so ta tarwatsa zaman sa shida marigayiya Ummu Ruman har sakinta da yayi, ƙarshe da yake ALLAH yayi da sauran ƴaƴa tsakani da kuma xatai Masa takaba, kuma matarsa ce har a aljannah in Sha ALLAH ai gashi sun zauna! Hajiya ikilima ta ƙarasa musu zancen da sauke ajiyar zuciya ta ɓacin rai karo ba bu adadi.
Suma ajiyar zuciya ɗin sukayi, suna saƙa wa da kwancewa.


Dan kuwa yanzu tsakanin Hajiya ikilima da Hajiya suwaiba da Hajiya sahura sun ƙulle ga ba ɗayan su, wannan kishin na da sun zubar, mafita kawai suke nema Akan Sa'adatu, ganin zata rabasu da mijinsu, ga shi kuma shekara da shekaru suke tare ALLAH bai bashi Haihuwa ba sai akanta, kuma sunsan yadda Alhaji yake da son yara,komai zai iyayi akanta, da ma ga ta makira ƴar iska,Hakan suka cigaba da tattaunawa tsakaninsu ta yadda zasu wargaza Sa'adatu ta yadda ba bu wanda zai san shirin sune,yanzu aka Fara wasan Sa'adatu kintaro masifa da bala'i ƙarshen ki na cin amana ya zo ba bu wanda Zaki Kuma wa cin amana , Inji Hajiya Sahura tana kallon sauran ƴan uwanta.






**************




Alhaji tallafy ya na ƙarasawa ɗakin su Hadiyyah da Hidayah suka Fara miƙa gaisuwa gareshi, ha kama sauran ƴan ɗakin,yau sune ga su ga wannan mutumin mai tausayi da imani!ita ma Hauwa ai ta sanshi lokacin zuwa visiting ɗin Alhaji, sai yau AQEEL ya ga ƴan biyu dai, wanda aketa zancen su kullum yaƙi ci yaƙi cinyewa shi da baki abun magana wato AKEEL,ai kuwa dai a zuciyarsa sai mamakin kamar su da juna yakeyi, ba bu banbanci har muryar kuma,Sai yaji wani abu ya ɗarsu a ransa game da wannan mai yawan maganar, surutu ya na damunsa Amma ita dai gashi bayan gaisuwar da akayi da ita sai surutu sukeyi ita da wata(Husna ƙanwar Bilkisu) sai kallon ta yakeyi ta kasan Ido,ba bu wanda zai kula, idonsa ya kai kan ɗayar a fakaice, sai yaga ta yi shiru abunta bata magana, sai kuma ya ji bata burge shiba(kuji fa ɗan rainin Hankali ba gwanda Hidayah da shi ba) musamman ma da yaji ashe Abbu yasan su sosai ƴaƴan abokinsa ne, ya so yasan babansu, badon Inno(Hajiya jimmai)aida tare ma zasu ta so a gidan su may be, tunanin da AQEEL yake kenan!
Shima AKEEL haka yana kallon Hidayah data matsa tsan waje ɗaya, saɓanin ƴar uwarta,Hakan shi ma ya birgeshi, ya na son ya ga Mace mai shiru_shiru Amma aita magana ai Babu tsari ma(kunji fa shi kuma da yake surutun fa kamar lalataccen fanfo,har yake da mun AQEEL) iri iren zantukan da zuciyoyin su suke musu kenan.
Tun shigowar Alhaji tallafy ɗakin Kawu isma'il ya sake lamo Akan katifa,alamun dai yaji jiki, Alhaji tallafy ya tallafa Masa,yaji tausayin sa musamman dayaji ana gaisawa da Alhaji tallafy ɗin hayaniya ne daga waje cikin ma anata gaisawa shiyasa bai ɗau murya ba,shekarun da yawa ƴan uwan Kawu isma'il ba su gane Ɗalhat ba, domin kuwa da da yanzu ba ɗaya ba, ga dukiya ga kwarjini, da sauran su, da ma kuma ha kowane yasan Alhaji Ammar BN Yasir da Alhaji Ɗalhat ba. Alhaji tallafy har gaban gadon Da Kawu isma'il yake kwance Yaje, guard ɗin sa da su AKEEL da AQEEL su kam sunan tsaye kamar zamani, su suna tunanin da suka Saba,


"Isma'il ya jikin?ashe abunda ya faru kenan? Alhaji tallafy ya faɗa da muryar sa a nutse
Tashin Hankali wanda ba'a saka ma sa Rana, ai ko za'ai shekara na wa Bazai Mance wannan muryar ba,Amma kuma ai Wannan sunan sa Alhaji tallafy, may be murya ce ta zo ɗaya, dan ya ka yai saurin buɗe idonsa dan ya gasgata abunda zuciyarsa ta gaya Masa, ai ya na buɗe idonsa! sai ya sauke Akan Alhaji tallafy!
Bai san lokacin da ya Miƙe zaune ba, har ya na fa ma ciwon hannunsa,
Tare da cewa "Ɗalhat da ma kana duniya? Nai ta nemanka ruwa jallo! Kawu isma'il ya faɗa ya na tsire Alhaji tallafy da idonsa wanda suka firfito waje alamun fa ya na cikin ta shin Hankali, Amma sai fuske a zummar mamaki ne?
Hadiyyah ce ta ƙaraso wajen da su Meenal ƴaƴansa su na ma sa tambaya da ma Kawu kasanshi ne?
Shi dai Alhaji tallafy ya na tsaye zuciya ta yunƙuro Masa, dan arayuwa ya tsani zalunci da ƙarya da cin amana, wai da ma ya na nemansa ai,Amma bari ya ga gudun ruwan sa, ya ji wace amsa zai ba wa ƴaƴan da sukai ma sa tambaya!
Na sanshi man Hadiyyah ai Abokin Abban kune tun kafin a haife ku, ra na tsaka suka rabu aka nemeshi aka rasa,har ba yan rasuwar sa sai neman shi nake Amma ban same shiba, cewar Kawu isma'il ya na ƙarasa gawa su Hadiyyah Amsa!
Lallai Kawu ai to shine Alhaji tallafy nan ai wanda ka kai Alhaji foundation ɗinsa ku ma muma shine ya ɗauki nauyin karatun mu, Amma kuma Rashin sani ai da tun sannan kasan shine! Hadiyyah ta karasa maganar da alamun mamakin wannan abu!
"Ai Rashin sanine Hadiyyah yanzu ALLAH ba ga shi ya haɗamu ba, sanadin dukiyar ku da ƴan fashi su ka sace,ai dama Haƙƙin marayu ya na da hatsarin gaske, ai ƴan fa shi sun cuce ni kuɗin ku ma da suka sace yafimin ciwo, Kawu isma'il ya ƙarasa maganar da sa Kuka,wai na Duk Alhaji tallafy ya tausaya Masa,Aikuwa Alhaji tallafy zuciya tazo wuya na jin wannan miciyin amanar Shi ma da ace baisan wanene shi ba ai da yakuma damfarar sa, kuɗaɗe .
Ita dai Hauwa ta na gefe ta na kallon drama da mijinta lallai ma, aikuwa bazata bari wannan Alhajin ya bashi ko sisi ba, sai ta fallasa sirrin cewa ba ko sisin marayu a wajen sa, ya cinye musu ne,Su kuma da sukaga za ma bana kare bane da kujeru a ɗakin dan Haka guard ɗin suka daukowa Alhaji tallafy ya zauna bai Musa ba ya zauna, dan kuwa ya ga abun isma'il na Zama ne, hakama su AKEEL da AQEEL saƙa musu kujerar akayi ba bu musu suka zauna dan sun Fara gajiya, ga kuma game ɗin da wannan Mara imanin yafara bugawa tsakanin sa da Abbu amma suna jiran su ga waze wining, da kuma fallasa sirrin da Abbu zaiyi.
"To marar imani da tausayi! Duk halin da marayun ALLAH suke ciki ƴaƴan Aminina ina sane da shi, da Duk wani zalunci da ka musu, na sani, ba tun dukiyar marayu kuma da kace ƴan fa shi sun sace,su na wajena ni na saka guard ɗina yin hakan tun da bakada imani da tausayi, Duk da Hakan kuma shine baƙin nufinka bai ƙalesu ba,yanzu ma zaka ku ma zaluntar su na cewa ai harda kuɗin yan fashi suka kwamushe,anata haɗa maka kuɗi,to yai asirinka ya tonu! Alhaji tallafy ya ƙarasa maganar ya na du ban fuskar Kawu isma'il wanda shock ya baibaiye jikinsa, shin waya gayawa Alhaji tallafy wannan sirrin nasa, ko dai ƴan fashin da sukazo Alhajin ne ya kawo su? To Amma kuma ai yadda ya faɗa tun kan zuwansu,ya san da sirrin, kamar ruwa yaci Kawu isma'il haka yayi ya yin da Hauwa ta fashe da ku ka ta sa ba ki acikin maganar,Alhaji isma'il azzalumin mutum ne wanda kuɗi ba bu abunda kuɗi baza Susa ya aikata ba, ni ma yau nake da shirin fallasa asirinsa, dan kuwa agaba ya fayyacewa ƴan fashi cewa ai kuɗin marayu ya Sanya Hannun jari dasu kuma yanzu ba bu an damfareshi,da kuma kuɗin sa shima ya yo oda daga china jirgin ya nuste a cikin ruwa, ga bashin 30million da ya karɓo a banki, ya bada 15million zai sai mota nan ma an gudu da kuɗin, ragowar 15millions din shine ƴan fa shi suka zo suka saceta,Amma ya buɗi ba ki ya na ƙaryar har ita ƴan fashi suka sace, tsakanina da isma'il ALLAH ya isa bazan taɓa yafewa ba,Hauwa ta ƙarasa maganar cikin Kuka gwanin tausayi!
Ai ɗakin sai aka ɗau salati dafa yara har manya,su kam su Hadiyyah da Hidayah da Khadija da kuma Amarya Zakiyyah sai Kuka suke ga ba ɗaya najin yadda Kawun su ya ƙware a zalunci! Ashe da ma kudinsu salwantar musu yayi, Amma yace ƴan fashi ne suka sace, Zainab da Asiya yayyan Kawu isma'il ɗin sai Kuka suke suna tsine Masa albarka!
Gogan na ku ganin asirinsa ya to nu sai ya sunkuyar da kansa gwanin tausayi, su kam su AKEEL da AQEEL mutuwar zaune sukayi jin zalunci na wannan mutumin wanda a fuska kamar bazai aikata b.
Guard ɗin Alhaji tallafy ne sukayi gyaran murya Akan a saurara Alhaji ya na magana!aikuwa tsit akayi anason jin ƙarshen zance.
Jibo ne ya fita mota ya ɗauko wayar da sukayi kowanne alaƙa ta yadda Kawu isma'il ya amince Akan tura zunzurutun kuɗin nan,alhali bai san shi na, jita_jita ne bai tabbatar da shine Alhaji Abbas ba mai hannun jari na ƙasar japan,kawai ya amince dan ya ga ba kuɗin sa ban,Duk Saida JIBO ya karanta musu a bayyana yadda suka ƙulla alaƙa,da kuɗin da ya tura ɗin.
Alhaji tallafy ya yi ajiyar zuciya yace kunji halin wannan marar inanan,dan marar imani zance masa, wane irin ga ta ne Alhaji Ammar BN Yasir bai Masa ba,ni shaida ne,Amma shine dan ya ga ƙasa ta rufe ma sa idanu shine ya ci amanar sa,
Cewar Zainab yayarsa ALLAH wadaran ka isma'il,su dai su Zakiyyah sai Kuka kawai sukeyi su na tausaya rayuwarsu, da irin halin Kawunsu.


Nadawo gareka azzalumi! Meya hanaka fallasa sirrin da mukayi tsakanina ni da Alhaji Ammar BN Yasir!?ba ka gayawa Hajiya ba tun ba yan rasuwar Alhaji Ammar ɗin? Ko Haramci kake so a aikata nan gaba?
Alhaji tallafy ya faɗa cikin ƙaraji idonsa ya yi jajur( sai ya zamar mun kamar AQEEL fa)ya na duban Kawu isma'il da jikinsa ya yi Sanyi, ya sunkuyar da kansa ƙasa, alamun ruwa ya ƙarewa ɗan kada! Da ma nasan bazaka iya magana ba, ai da kunya ace Kaine ka aikatawa ɗan uwanka, wanda komai na gata yai maka shi, Amma ƙarshe kaci amanar sa da ƴaƴansa, wajen salwantar da dukiyar su.
Duk zaluncin ka da Mugun halinka ai dai ka faɗi wannan sirrin, ko da kaga ban bayyana ba, ko wani abune ayi Amma ina ka ƙiyin Hakan, hatta Mahaifiyar ku ka ƙi faɗawa, ni yau zan fallasa sirrin shine waɗannan ƴaƴan Hadiyyah da Hidayah surukai na ne, ma'ana da Aure tsakanin su da ƴaƴana AKEEL da AQEEL Yanzu, haka a matsayin matansu suke su kuma mazajen su,Amma ya ƙi faɗawa kowa ku ma bansan wace manufa ce da shi Akan Hakan na.............




Turashi fans. Ya haka kuma? Wata sabuwa lallali tsugunne bata ƙarewa ba ana wata ga wata kuma ya abun yakene ni Rãbiat🤔 ta yaya akayi Hakan kuma?ankuma kenan mace ta Haifi mace Muje zuwa dai.........



✍️ oum ARQAM ce ontop 🥰
2/7/24, 4:30 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*


*PAGE FOURTY TWO 42*




A lokacin da Alhaji tallafy yakewa Kawu isma'il wannan tereren ne kuma ƴan jarida sukayi wa ɗakin dirar mikiya,dan ALLAH Alhaji tallafy yaiwa guard ɗinsa JIBO nuni akan cewa su tsaya,daga waje ya na ganawa da marar lafiyar ne,Yan jarida dai sunsan Alhaji tallafy ba bu musu kuwa suka koma can gefe, suna jiran fitowar ne,su na ALLAH yasa su ma ya washesu da kuɗi kamar yadda zai washe majinyacin( A naku tunanin kenan, Amma shi kam Alhaji tallafy wankin babban bargo yakewa majinyaci).
Meyasa baka gayawa ɗaya daga cikin ƴan uwanka, cewa ƴan biyu suna da Aure tsawon wannan lokacin!? Alhaji tallafy ya kuma jefawa Kawu isma'il tambaya ya na tsire shi da idanuwansa wanda sukayi jajawur alamun ɓacin rai!
Shi dai kawu isma'il muzanta iya muzanta ya shata! Dan Haka ya kasa ɗago idanun sa ya dubi Alhaji tallafy ɗin!
"Ka ɓude baki kai Musu bayanin komai, da ma saboda kai kasan wane ƙulli ne a zuciyarka da yasa ka ƙi fallasa sirrin! Sannan wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login