Showing 63001 words to 66000 words out of 141223 words
Chapter 22 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
zaune Suma abunsu, AKEEL ke Jan AQEEL da Hira wanda shi kuma Hakan ya takura shi ne, kunsan dai surutun AKEEL, dan ma yanzu ALLAH yaso AQEEL ɗin yana ɗan saurarar sa ba kamar da ba, "magana fa nake jarabuna! Cewar AKEEL yana daga kafaɗar AQEEL, tsonaka ce da ma tasa shi faɗar wannan sunan, dan AQEEL ɗin yayi magana ne, ai kuwa yayi ɗin cikin ɗaure fuska yana gyara zaman medical glass din da ke fuskarsa, wanda yake ƙara ƙawata Masa fuskar tasa!
" Kasan ALLAH ko! Ka ƙara kirana da wannan sunan zan haɗaka da Abbu" nace maka banason wannan sunan yariga ya mutu, tun da jimawa! AQEEL ya ƙarasa maganar da alamun ƙosawa dan kuwa maganar tayi Masa tsayi ne
"ALLAH ya wuce zuciyar brother ɗina bazan kuma ba, karka gayawa Abbu yaimun bulala"
AKEEL ya faɗa yana dafa kafaɗar AQEEL ɗin, wanda yaci kunu, alamun ba bu raini,
ai yana dafa kafaɗar AQEEL ɗin dai kuma murmushi ya ƙwashe Masa, jin abinda ɗan uwan yace cewa, sai fuskar tasa ta ƙara ƙawatuwa da kyau abun gwanin burgewa, Daga Abbu! har Mommah! Suna lura da ƴaƴan Basu na cewa lalläi suna cikin farin ciki, kuma Hakan shine burinsu musamman ma ga AQEEL da yake da matsala da Hakan.
Suna tsaka da wannan nishadin ne kuma aka sako labarai, su ma suna saurarar labarai, kamar Abbu ɗin, shiyasa ma suka sauko falour dan su saurara tare d Abbu ɗin, dan nanne wajen saurarar labaransa.
Adaidai lokacin kuma aka sako labarai aciki harda na fashin da akayiwa Kawu isma'il ɗin, gaba ɗaya sai falour yayi tsit jin irin ta'addancin da ƴan fashi sukayi na sace dukiyar marayun ALLAH data Kawunsu kuma wanda yake kular musu da ita, dakuma dukan da sukayi Masa shida mai ɗakin sa. Da daga bakin wanad akaiwa fashin sukaji maganar, bayan mai labaran ya faɗi kanun labaran.
Sai bayan labarin ya ƙare ne Mommah tace "Abu AQEEL kaji zalunci fa, wannan mutumin ai abun a tausaya ne a tallafa Masa yakamata kaima ka tallafa, naga ma mutane daban_daban suna son su taimaka Masa" mommah ta ƙarasa maganar da fuskantar Abbu ɗin!
Sai taga fuskar mijin nata fes Babu alamun tausayi wanda yasaba taɓa fuskarsa a Duk sanda akayi irin wannan ta'asar ko maiamancin Hakan,
"Ya isa Ummu AKEEL wannan ba kowa bane illah isma'il, ƙanin mahaifin su Tagwayen nan, da Alhaji wanda yake cibiyata,Kinga ta inda ya ɓullo ko? Da nayi tunanin tunda dukiyar marayun ALLAH ta dawo wajena zan rabu da shi kawai, Amma yanzu tun da tanan ya ɓullo mu zuba mu gani ni da isma'il, na tsani zalunci a rayuwata shiyasa banayi kuma idan na samu mai yi bana bashi da ɗi, musamman ma isma'il, lokaci yayi da zan fito Masa a mutum, Duk wani ƙulli da makircinsa ya zo ƙarshe,
Ba Mommah da Abbu yakewa bayani ba, hatta su AKEEL Saida su ka girgiza, dajin batun Kawun su ƴan biyunnan, sai mai da zance ake tsakanin Mommah da Abbu "kajifa Abu AQEEL wai har dukiyar marayun ALLAH ƴan fashin suka sace, yanzu da ba Kaine ƙasa Abbas ya ƙwato dukiyar nan ba shikenan, yaci bulus, Amma ina Dole ya girbi abinda ya shuka, Mommah ta ƙarasa maganar idanta yayi jajur alamun tausayi gasu Hidayah, da kuma ɓacin ga Kawu isma'il ɗin.
Alhaji tallafy kam sai kwantarwa da Mommah Hankali yake Akan cewa a yau ba sai gobe ba tun kafin jama'a su Fara tallafawa azzalumi zan fallasa sirrin da ya kasance a ɓoye, isma'il ga Ɗalhat nan gareka, a lokacin da bakayi tsammani ba!
Lokacin su AKEEL bayan sun ga ma jimama zancen Kawun su ƴan biyu, sun fice daga faloun zuwa ɓangaren su,su ma su mommah da Abbu dama suka haura, Abbu ya na ce matan in Sha ALLAH zuwa anjima da daddare dake da su AKEEL zan gaya muku wani abu da baku sani ba Akan alaƙa ta dashi, da kuma marigayi ɗan uwansa Alhaji Ammar BN Yasir baki ɗaya, buɗa baki mommah tayi zatayi magana Abbu ya ɗaga MATA hannu akan tayi shiru kawai, akwai anjima ta adana tambayoyinta zuwa jimawa ..........
Meyake shirin faruwa da fallasa sirrin da Alhaji tallafy yace zewa Kawu isma'il?
Wace alaƙa ce tsakanin Kawu isma'il da Alhaji tallafy da kuma Marigayi Alhaji Ammar BN Yasir?
Lallai akwai badaƙala a gaba kenan? Kubiyo oum ARQAM domin ta warware muku cwakwakiyar
✍️OUM ARQAM ce ontop 🥰
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*
*PAGE FOURTY 40*
"Kasan ALLAH Awale mutumin nan yai mana Sharri, abunda mukaje nema bamu samuba,dan ROCI sai da yagaya Mana cewa maƙudan kuɗaɗe wannan mutumin ya cira a bankin Ranar daya ganshi,Amma yanzu 15million muka samu,kuma ya gayawa mana yadda yayi da kuɗaɗen sa,da ma kuɗaɗen marayun daya gaya Mana, Amma shine yanzu yabimu da sharrin cewa wai mune mukayi Masa fashin da bai san adadin kuɗaɗen ba!
Da alamar ɓacin rai Snake yake duban yaran nasa duwalle da Awale,
Oga kenan ai sai mun ƙara Zuwa wajen wannan tsinannan mutumin,zuwan mu na biyu ba mai kyau bane,dole ya rasa wani abu nasa wanda ya mallaka!cewar Duwalle"
Yawwa nawajena ai kai da ma bakada yafiya,kuma ba ai maka ka ƙyale,shiyasa nake Al fahari dakai cewar Snake yana dafa kafaɗar duwalle,mu sake shiri Muje zuwa karo na biyu sunan wannan tafiyar operation haddi,saboda sai mun Masa haddi Akan Sharri dayayi Mana! Dawadaiiiiii oga suka haɗa baki...
_________kamar yadda Alhaji tallafy ya faɗawa Mommah bayan sun gama dinner,su AKEEL da AQEEL za su koma part ɗin su ne Abbu ya dakatar dasu da cewa inason zan ɗan tsakura muku alaƙa ta da Kawun su ƴan biyu, sannan kuma banson tambaya ko ɗaya da Zaku min, girgiza Masa kai kawai AQEEL yayi,yayin da AKEEL yace "to Abbu"
Dan haka daga kan dining table ɗin cikin falourn suka dawo kowanne ya zauna a kan sofa yana saurarar abunda Abbu zaice, hakama Mommah.
AKEELA ta na Gidan Aminatu, Amma Duk da Hakan zan gaya muku yadda abun yake Duk da Abun da ma bai shafi AKEELA yanxu ba tukunnah, daga AKEEL da AQEEL da kuma Mommah Duk sun bawa Abbu Hankalunsu suna jiran abunda zaice,,,
" Alhaji Ammar BN Yasir abokina ne tun na ƙuruciya, abunda ba ku sani ba kenan,mun haɗu da shi a secondary school inda abotarmu tayi ƙarfi,muka Zama kamar ƴan uwa, shi kuma isma'il Duk tare mukai school ɗin Duk da dai mun fishi aji, makarantar tun daga primary har senior school a tare ne,bayan kammala secondary ɗin mu mu ka Fara zuwa uni kowanne da wanda yake zuwa har mukayi aure ma, na rigashi Aure gaskiya'har Sannan muna zumunci abunmu, to lokacin da aka haifeku da AKEELA kuma shima yana da Zakiyyah da Kuma Zahra, har kun ɗan tasa Kuma cikin ikon ALLAH sai shima ALLAH yabashi twins Amma duka MATA ni da shi muka ƙulla wani al ƙawari mai tsauri, ba da jimawa ba Zaku sanshi in Sha ALLAH. Sannan kuma ya ƙara aurar wata matar wato Sa'adatu, nasanta farin sani, saboda tare dashi Muke zuwa zance, wajenta, kuma nayi murna da ALLAH baisa mun haɗu ba, da Abubuwan da nake sa ran warware su da Hakan bazata yiwuba
To bayan haihuwar ku, a haihuwar AKEELA kuma maman ku ta mutu, kunsan wannan,na Auri Hajiya jimmai, a lokacin kuma ALLAH ya yi rabuwar mu da Alhaji Ammar BN Yasir ɗin saboda haka kawai abotarmu ta lalace Babu mai neman wani tsakanin mu dashi, kuma har sannan akwai Wannan alƙawari da muka ƙulla, ƙarewa ma har mun cikashi. Duk wata yarjejeniya akai munyi shi, da Duk abunda yakamata acikin al ƙawarin kuma tare da isma'il akayi komai acikin shaidu har da shi, alaƙar mu da Alhaji Ammar BN Yasir ta kuma tsauri, Babu mai neman wani,har ALLAH ya azurtashi fiye da ƙima, sannan ya tara yara, nikuma ku ukune kawai,Ko ɗuriyarsa banaji shima bayajin tawa,daga cutarsa har rasuwarsa ban saniba, sai daga baya bayan rabuwarsu da Hajiya jimmai ne ashe itace tai Mana farraku dashi, wai kawai dan tun farkon Aurena da ita bai bada goyon bayaba, saboda ita mace ce Mara kamun kai ko ƙadan saɓanin mahaifiyar ku, to tun sannan saina so zuwa wajen Alhaji Ammar BN Yasir ɗin anan nakejin labarin ALLAH yai Masa rasuwa, kuma itama matarsa ta fari Ummu Ruwan ta rasu, nayi baƙin ciki da Hakan, kuma naje har wajen mahaifiyarsa nai MATA gaisuwa,ita ma sai sannan take mamakin ina na shige tsawon shekaru, ba'a jima sosai ba itama ALLAH yai MATA rasuwa, Duk wata badaƙala da isma'il yake sa dukiyar marayun ALLAH na sani, kawai dai na rabu da shi ne, na yi tunanin da Ya ga Alhaji Ammar BN Yasir ya rasu sai gayawa mahaifiyarsu alƙawarin da mukayi ni da Alhaji Ammar BN Yasir ɗin Amma koda naje wajen Hajiya Sakinah sai naji batayimun maganar ba, alamu sun nuna bai gaya mata ba,ni ma Kuka ban MATA zancen ba, sai kuma ba'a ɗau lokaci ba ALLAH itama yai ma ta rasuwa, naso fasa wannan ƙwai wajen Hajiya Sakinah Amma ina ALLAH baiyi ba, dan lokacin ku na New Delhi, Nima inacan na je dubaku kafin nadawo ta rasu, tun a gaisuwar Alhaji Ammar BN Yasir da muka haɗu da isma'il bai nuna mun wata alama ba,ta cewa wannan alƙawarin da mukayi da Yayansa ya tunamun ba ko na manta,Amma ina sai ya yi shiru abunsa,ni ma Kuma ban Masa magana ba, ku ma tun daga sannan ban kuma haɗuwa da shi ba har yau, zuwan Alhaji, tallafy foundation ma baisan tawa bace, saboda baisan ni da tallafy ba da Ɗalhat ya sanni, buɗe kungiyar Tallafy ma da wata manufata ta buɗewa, kuma sai murna takama ni lokacin da Shi isma'il ɗin da kansa ya kawo Alhajin cibiyar, da ma kuma ina bibiyar lamarunsu sosai, ina son kulasu Amma sanadin Sa'adatu da zalunci ta garesu na dakata bana taimaka musu, komai a kan idona,Shi ma isma'il na fice harkar sa, tun da har shine mai kasa cikawa ɗan uwansa alƙawarin da mukayi kuma shine shaida,tun da ni banyi maganar ba,kuma yasan akwai hatsari Akan ƙin cika Alƙwarin da fallasa komai ma" Alhaji tallafy ya kai iya nan wajen ya na mai ajiyar zuciya da nuna lalläi ya tuna Amininsa Alhaji Ammar BN Yasir da kuma Abubuwan da suke shuɗe tsawon shekaru.
Tsakanin Mommah da AKEEL da AQEEL Duk sunyi shiru, suna son ci gaban labarin, da Abbu ya ke ba su sunason jin wane Alƙwarin Abbu da Alhaji Ammar BN Yasir sukayi? sannan kuma meyasa Kawu isma'il yaƙi bayyana wannan alƙawari ga mahaifiyarsu har ALLAH yai MATA rasuwa?mene kuma yasa da ya ga Abbu Bai tuna ma sa da alƙawari tsakanin yayansa da shi ba? Tambayoyin da suke zukatan waɗannan ahali kenan.
Dan haka mommah zatayi magana Alhaji tallafy yace ma ta akwai lokaci Aisha, zakusan komai, kunji Alhaji tallafy ya faɗa ya na duban AQEEL da AKEEL waɗanda suka yi shiru, suka shiga tunani daban kuma may be wani abu daban su ke tunawa.
Ku Adana tambaya da sauran Abubuwan da Zaku nemi sani akansu, yanzu dai kunsan alaƙa ta da Alhaji Ammar BN Yasir da kuma isma'il ɗan uwansa sauran Abubuwan kum sai nan gaba lokaci shi zai bayyana su, ku tashi ku tafi kuje ku kwanta in Sha ALLAH gobe da ni da ku da Mommah ɗin ku zamuje asibitin Da isma'il yake kwance domin warware sauran batutuwan acan, may ba saina faɗa muku ba shi dakansa zai gaya muku.
Haka su AKEEL suka wuce zuwa barci zuciyarsu da Tarin tambayoyi da fatan kaiwa gobe lafiya, shima shi da Mommah sama su ka haura zuciyar kowa da abunda take saƙawa....
**************
Kawu isma'il jiki kam Alhamdullillahi da sauƙi, dan har hannun ya warke sai abunda ba'a rasa ba, itama Hauwa tuni ta warware kuma har sannan ba ta zuwa asibitin dan fushi take da mijin na ta, kuma ta na addu'a Akan ALLAH kar ya bawa masu ikon tallafa Masa suyi, saboda tasan mijinta azzalumi ne sosai, bulus zai ci Akan dukiyar marayun ALLAH, wanda take fatan in Sha ALLAH nan gaba abunda zai sameshi sai ya fi, haka kuma saita tona Masa asirinsa jira ta ke ya fito daga asibitin(ki kwantar da hankalin ki Hauwa ga Alhaji tallafy ga mijin ki nan)
Cikin farin ciki Kawu isma'il yake saboda wani ɗan siyasa ya buƙaci Kawu isma'il ya kawo account ɗin da za'a saka Masa tallafin, dan haka ƴan jarida sukayi alƙawarin zasu je asibitin su amso account ɗin isma'il ɗin,dan haka yanzu yana tsammanin zuwan su ne,kamar haɗin baki yau Zakiyyah da su Hadiyyah da Hidayah kai harma Hauwa wanda take da alwashin a yau saita kartawa mijin nata Rashin mutunci da ƴaƴanta, da Sa'adatu(batajin daɗi ma, angamu) Wanda Alhaji gambo ya tursasata Akan ta je ta duba shin, ai komai zata tura baya,darajar Alhaji Ammar BN Yasir da kuma ƴaƴansa zataje, , dan bata taɓa zuwa dubashi ba, kuma yadda ta ga Alhaji gambo ya na lallaɓata shiyasa ta ce zata na asibiti dai ma Sha ALLAH sai shige da fice akeyi, shi kuna Kawu isma'il yana ta zuba idon ƴan jarida zuwa karɓar account number, har ya Fara lissafin Abubuwan da zaiyi da kuɗaɗen, ba bu tension akansa ko guda na wasu kuɗin ƴaƴan Ammar,
________ Sa'adatu ba ta jin daɗi jikinta, saboda rabo da ga ALLAH cikine da ita na Alhaji gambo, gashi ku ma da ma bai taɓa Haihuwa ba sai a kan Sa'adatu ɗin, dan haka yake ta murna kunsan dai ace mutum kamar Alhaji gambo ga MATA uku Amma ba bu Haihuwa sai a kan Sa'adatu ALLAH ya kawo, ku hango min kulawar da zata samu, da riritawa, Amma ku tunamun da Hajiya sahura da Hajiya ikilima da Hajiya suwaiba, aikuwa kam zuwa gidan su sai ya ga dama, ba shi da magana sai ta cikin jikin Sa'adatu zaiyi kaza_zaiyi kaza, har ya Fara tattara dukiya da Abubuwa ya na cewa na Sa'adatu ne da ɗan cikinta, ALLAH ya sa ta Haifa masa magaji, ba damar ya zauna yana magana da su sai ya sako Sa'adatu da ɗan cikinta, hakane ku ma ya sa suka zage damtse Akan aiwatar da sani ƙudiri na su Akan ita Sa'adatu Wanda daga Hajiya ikilima da Hajiya suwaiba da Hajiya sahura suka haɗe kawunan su waje ɗaya, tun da sunga masifar ga ba ɗaya ta tunkarosu, in Sa'adatu ta haihu, haihuwar ma namiji mene makomarsu a Gidan, sun Zama sorry, wannan yasa su ka Fara shige da fice Akan Sa'adatu da ɗan cikinta....
*************
Sai zumuɗi suke ba bu uwa ba bu ƴaƴan na ta dan Haka da suka farka da wuri su ka shirya, ƴan aiki sun share gidan sun gama komai, tafiyar da za'ayi Alhaji tallafy acikin guard ɗin sa har da JIBO,wanda tuni Alhaji tallafy yai Masa registration da Duk wani abu ya ke buƙata ba Fara zuwa school, saboda shine shaidar komai shine ya san lagon abun,da haka suka kama hanya zuwa asibitin da Kawu isma'il ya ke kwance.
___________ mota guda uku ya ɗauka, Alhaji tallafy ya ɗauka, mai tambarin Tallafy 1_30, Alhaji tallafy sananne ne sosai dan haka sai fatan alkhair ake bin motarsa da ita, mota ɗaya shida Mommah ne aciki, sai ɗaya AKEEL da AQEEL,sai kun ɗaya ta guard ɗin sa,ai mutane su na ganin motar Alhaji tallafy ta yi parking a Asibitin nan kowa yake cewa "ba bu shakka kaakar Isma'il ta yanke saƙa, tun da suka ga Tallafy yazo gareshi may be ma ya mayar ma sa da dukiyar sa ta fi ta da,ire_iren zancen da mutane tun daga bakin asibitin suke faɗa kenan, sai ma da Alhaji tallafy ya fito da ga motar shi da Mommah, su AKEEL da AQEEL Suma suka fito haka ma guard ɗinsa, mutane sun cika gurin suna ta wa Alhaji tallafy addu'oi na alkhair da fatan ALLAH ya raya zuri'a, haya niya har ɗakin da Kawu isma'il yake,kuma har zance ya iske su ai Alhaji tallafy ne ya zo wajensa, sai su Hadiyyah da Hidayah su ka Fara murna sunsan Kawunsu ya warke, dan Alhaji tallafy akwai kyauta,shi m Kawu isma'il ya san alkhairin Alhaji tallafy ga al uma, sai wata murna yakeyi ya na da ga kwance, har Alhaji tallafy yasamu Hanyar silalowa ya tawo zuwa ɗakin jinyar Kawu isma'il ɗin, saboda mutane daƙar ya samu hanya, ɗakin yana tumbatse da ƴan uwa da ƴaƴa da abokan arziƙi ,wanda Sa'adatu ba ta samu karɓuwa ba, tun da ta zo dubiyar, in banda su Hadiyyah da Hidayah da sauran ƴan uwa aka gaisa da ita, Amma itada mai jinya da kuma Hauwa matarsa ko kallon su batayi ba, ta na da ga bakin ƙofar Ɗakin, ta na Shan iska dan haka Alhaji tallafy Sa'adatu bata ga ne shiba, to ita da ta sanshi a Ɗalhat wannan kuma Alhaji tallafy ne, dasu AKEEL da AQEEL da guard ɗin sa ke biye da bayansa, har ya danganta ga cikin ɗakin, Kawu isma'il ɗin, ita kuma Sa'adatu ganin mutane sun yawaita a wajen ku ma batason hayaniya sai tayi tafiyarta gida ta hau Agaidata sahu abunta, a dai lokacin ne kuma ƴan jarida suka ƙaraso asibitin su ma domin karɓar account number a wajen Kawu isma'il ɗin.........
Ya kuke ganin faɗa Kwan Alhaji tallafy zai kasance?
Ga dai ƴan jarida sunzo?
Wane sirrine tsakanin Alhaji tallafy da Alhaji Ammar BN Yasir?
Wane dalili ne ya sa Kawu isma'il ɓoye Alƙwarin yaƙi sanarwa kowa bayan ya ga ƙasa ta rufe idon mai fallasa sirrin?
Da Duk wasu tambayoyin da kuke da su Muje next page kawai........
✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*
*PAGE FOURTY ONE 41*
Ba'a jima ba Sa'adatu ta ƙarasa gida, ba