Showing 51001 words to 54000 words out of 141223 words

Chapter 18 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

Advertisement

Zahra yake miki da mukaje, mu ka ganta, ku ma zancen na ce zan dawo da ita, tun zuwana Ɗaurin Auren yakemun zancen uwar shiyasa nace zan dawo Masa da ita'
Mukhtar ya ƙarasa zancen cikin kwantar da murya alamun rarrashi.


Bilkisu Dai da take jikinsa bata kuma magana ba ta lafe a jikinsa, ta na ajiyar zuciya alamun ran ta da zuciyar sun samu salama, batada wata fargaba kenan, a dai dai lokacin ne kuma.............






Muje next page ƴan Amana danjin meke faruwa


Ga dai Zakiyyah a gadon asibiti


Ga kuma madam Bilkisu itama ta na wasu zantuka da sauran wasu batu su na ga ba......




✍️ OUM ARQAM ce ontop😍
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*






*PAGE THIRTY FIVE 35*


Ƴan team ɗin Zakiyyah fa su 🤣🤣....
Seeerat
Mummy Waleed
Aisha sulaiman
Haseena
Maman eyshat
MamaGee...


Wayyo ALLAH nah ni uwar ARQAM🤔🙆‍♀️🥹 nasha caccaka fa a PAGE 34 fa nida Habiebtieh yasin Duk kun haɗe kun koma team ɗin Zakiyyah


Ita Bilkisu bata da team kenan🥹🤔🙆‍♀️ daga ni uwar ARQAM sai habiebtieh kawai lallai kam Babu gudu ba bu ja da baya koma dai menene Zakiyyah ita ta janyo wa kanta eye muje zuwa PAGE 35 ALLAH yasa bayan caccaka karmusha tsatstsaga kuma a wannan Page ɗin🤣🤣🤣🤣


*---------------*
OGA Ea Duk wank bayanai Akan wannan mutumin na samu!har unguwarsu na bishi har sai da ya shiga cikin gidan sa sannan na jiyo!
ROCI kenan yake sanar da uban gidansa SNAKE" cewa ai ya bi Kawu isma'il yanzu yasan komai a kansa, yanzu kawai ranar operation suke jira,kamar yadda suke kiran fashin na su dashi, yawwa mutumin ai nasan Babu wa sa cikin aikinka cewar snake bayan ya gimtse wayar, domin yanzu shida yaransa shirin tunkarar gidan Kawu isma'il ne a gabansu,domin gaskia kuɗin da suka ga ya cire a banki sunsan ba shi kaɗai gareshi ba, za'a samu fiye da hakama, shiyasa suka Fara shiri, oh ALLAH sarki Kawu isma'il ko yaushe waɗannan muyagun zasu zo gareshi, Nikam zan sanyashi cikin addu'a ta.


Koda Kawu isma'il yaje gida da waɗannan kuɗin ya ajiyesu bigire ma kyau,kafin Fara Masa aikin gidan sa .


Yaiwa Hauwa gargaɗi Akan sake shiga sabgarsa,Amma yana shigowa da kuɗin sai da taji wani abu ya soki zuciyarta! Wai shin mijinta me yakeso ya zamane? Waɗannan kuɗin kuma da ga ina suke? Amma ba bu komai za ta saka mai Ido gaskia,zataga zuwan da dawowar,kullum addua take Masa ta shiriya,idan ba bu ita kuma ALLAH ya tona ma sa asiri muddin da dukiyar marayu yake wannan wadaƙar?! ALLAH sarki Hauwa mutuniyar kirki zakiga sakayyah kam ga mijinki, in kuma dukiyarsa ce ALLAH zai iya jarrabarsa sanadin zaluntar marayun ALLAH, ƴaƴan yayansa,wanda ko ba bu kuɗi shi nai jiɓantar al amarinsu ne, Amma ina kwata_kwata ya Mance da rayuwar su ta tasa da ƴaƴana yakeyi, to dan ALLAH ta ina zaiga dai_dai a komai nasa ne!?


Tashin Hankali wanda ba'a saka ma sa rana kenan! Dan kuwa dai da ƴan damfara ALLAH ya haɗa Kawu isma'il waɗanda ya turawa 15millions ɗinnan, yayi odar mota Babu su ba bu labarinsu,da ma hake sukeyi, sai su buɗe account da emails na wucin ga di wanda suke damfarar mutane daban_daban da shi, ire_iren su Kawu isma'il, saboda ba kowanne mai hankaline sai iya Hakan ba, na tausayawa Kawu isma'il sosai fa, Amma kuma sai na ga shima bai da mu ba, saboda ya sawa ransa cewa dan wannan ƴan kuɗin! Ai ALLAH yakusa kawo ma sa riba mai girma da tsoka wacce zata ninka ma sa fiye da waɗannan kuɗaɗen, shiyasa ba bu wanda ya gayawa ko Hauwa bata sani ba sai shi kaɗai.
Sai wani bala'in kuma again! wanda shima dai kawu isma'il ɗin bai gayawa kowa ba,shine ya wayi gari da nemar Asusun Alhaji Abbas mai mallakar kamfani a Japan, wanda ya zuba zunzurutun kuɗi har 50million na marayun ALLAH ga shi yau alamu sun nuna wannan account ɗin ba'a amfani da shi kwata_kwata an gogeshi, sai sannan ya shiga binciken sa ya ga alamun ba bu wa su mutane ma su bibiyarsa in ba shiba, wanda a farko beyi wanan tunani da lissafin na sanin bayanai Akan Alhaji Abbas ɗin ba sai yanzu in da a bincikensa da yakeyi ne, ya samu haƙiƙanin gaskiyar zance na account ɗin Alhaji Abbas na gaske, gaskiya Duk wanda ya ga Kawu isma'il yanda ya shiga firgici abun zai baka tausayi, Amma kuma yayi kurum bai gayawa kowa ba,saboda mugun abu, ko tsoron ALLAH bai ji ba yanzu kenan ƴan marayu ba su da tsuntsi ba su da tarko kenan, in banda gidajen da Suka mallaka shikenan Amma ko ƙadan Basu da kuɗi wanda zasuce wannan kuɗin gadon sune,shin waima yace ina yakai kuɗaɗen ne? Ko zaice da su yaiwa Zahra wahalar aure ne? Ko kuma zaice da kuɗin yaiwa su ƴan biyu wahalar makaranta ne? ALLAH yasa biyar d'insa ba bu aciki muje dai zuwa fans.


Gani kawu isma'il yake abun kamar a shirin film ko a novels dan haka ma ya ɗau hanya har lagos inda, reshen kamfanin sarrafa fata na Japan mallakin Alhaji Abbas ɗin domin ya shigar da ƙorafinsa, Amma ina ba shi da wata hujja cewa ai ya tura waɗannan zunzurutan kuɗin, can dai ya haɗu da ƴan damfara ne sun yashehi, Amma kam, su ko mai kama da shi ba su sani ba, sai da Kawu isma'il ya fa ɗi aka yayyafa ma sa ruwa, kafin yadawo cikin hayyacinsa, ana ta ba shi baki Akan ya fawwalawa ALLAH komai, Amma karya kuma wannan gangancin da yayi, in zai saka hannun jari ko zaiyi odar abu a irin wannan yanayin yafara zuzzurfan bincike a account ɗin yasan tabbas ana bibiyarsa kuma shine aininhin wanda ake oda ko saka hannun jari, sannan sai sunyi a rubuce da komai da komai kafin ya tura kuɗin sa.


shi dai kawu isma'il jinsu kawai yakeyi Amma ba ya fuskantar komai,yana can tunanin yadda zasu ƙarke da Sa'adatu ne yasan wallahi bazata ƙaleshi Akan dukiyar ƴaƴanta ba,sanadin abunda ya gifta tsakaninsu,in ya cuci su Hadiyyah ya zauna lafiya yasin yasan ƙarya ne ya cuci Sa'adatu,yasan yanzu ma wannan shirun datayi Masa yanada,ma'anoni sosai , Sa'adatu da kuɗi ai kamar Annabi da kafiri ne.yana warwarewa ya na kwancewa ne yaga Hakan bazai fussheshiba dan haka ya samu hotel ya kama, dan tafiya gida yau bai kama shi ba wannan ta shin Hankali ai kowa ya na ganinsa zai san ba lafiya ba,gwanda ya ɗan samu nutsuwa kafin yakoma gida kanon dabo.


Zuciyarsa ta yi Sanyi lokacin da abokan kasuwancinsa suka kirashi cewar oda fa ALLAH ya kawo ta,dan haka an lodo kayan daga china nan da gobe ko jibi in Sha ALLAH kaya zasu shigo 9ja sai fatan samun riba mai girma kamar yadda suke fata,shiyasa Duk wannan fargabar ta Kawu isma'il ta kau washe gari ya hawo jirgi dan dawowa gida.






*************


Mukhtar wayarsa ya ji ta na ringing daga gefen sa, Bilkisu ta fi kusa da wayar dan haka ta ɗauko zata miƙa Masa,shi kuma ya ce wa ke kirana da Daren nan kuma haka?
Bilkisu dubawa tayi ta ga ansa *Hadiyyah* nu na Masa ta yi, na gani, sai zuciyarsa ta shiga wasi_wasin yanzu kuma Hadiyyah da wannan Daren wajen goma ta kirashi a waya meya faru kuma? Kardai Zakiyyah ce ta ɗau wayar Hadiyyah ta kirashi,dan tasan In ta kirashi a wayarta bazai ɗauka ba, lallai tanan Zakiyyah ki ka biyo aikuwa bazan taɓa ɗagawa ba ehe!
Zata tsinke fa zaujin saleh! Ka karba man!
Bilkisu ta katsewa mukhtar tunanin daya lula ƴan sakanni!
"Ke Mar atussaliha ƙaleni ba bu wata Hadiyyah da take kirana,illah Zakiyyah domin tabbas nasan itace zata Kirani, tasan in ta Kirani da number ɗin ta ba ɗagawa zanyi ba, ta ma daina wahalar da kanta a kaina, domin Nikam ta ficemun a raina, Duk wani mutunci da alfarma da zan mata tun yaushe ta rushewa kanta a wajena, ni ko son ganinta banayi ma! Mukhtar ya ƙarasa maganar da ƙaraji!
Bilkisu ta ga abun na mijinta yafi ƙarfinta,ga shi ya barta da waya a hannu,harta katse,dawowa ku sa dashi tayi kafin ta fa ra magana cikin tausasa murya!
" Haba zaujin saleh kamar ba Kaine mai haƙurin nan ba mai yafiya mai karɓar uzirba! Kayi haƙuri Mana,kamance ne har yanzu Zakiyyah ta na matsayin matarka ne bari na tuna maka, kuma ma bakasan ita tai kiranka ba ko ba ita bace, bakada tabbas Akan Hakan, ko ma ita tai kiranta ka ɗauka Mana kasan da me tazo haba zaujin saleh!
Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin kwantacciyar murya alamun nuna rarrashi, tun da da ma tasan lagon mijinta,
A sannan kuma kiran ya sake shigowa, wanda har sannan wayar na hannun Bilkisu ne, saurin miƙa Masa wayar tayi da alamun, rarrashi a fuskarta alamun ya ƙarbi wayar,beyi musu ba kuwa ya karɓa yayi picking,to yan team ɗin Zakiyyah yau dai ga Bilkisu tai muku ra na ko? Ba don ita ba da bai amsa wayar ba ALLAH sarki Bilkisu baiwar ALLAH mar atussaliha kamar yadda mijinta yake kiranta dashi.


Ta ɗaya ɓangaren kam kiran farko da Hadiyyah taiwa mukhtar ta ga bai ɗaga ba, Hankalinta ya tashi sosai,ganin kowanne lokaci Zakiyyah na iya farkawa kuma akwai matsala idan bai amsa wayar ba,ta yi tunanin ya yi barci ne, wayyo ALLAH ,har ta haƙura da kiran sai dai kuma ta kuma Kira karo na biyu ko ALLAH zaisa inma barci yake ringing ya ta sheshi, tunda dai bata da tabbas ɗin in dai barci ba ya saka wayarsa a silent,cikin yanke tsammani ta kuma Kira karo na biyu wanda cikin ikon ALLAH ta ga mukhtar ya yi picking,hamdala tayi ga ALLAH,zata fara Masa magana cikin ku ka Sa'adatu tai MATA alama da ta daidaita Hankalinta,karta tayar Masa da Hankali da Daren nan haka.


Dan haka bayan mukhtar ya ɗaga yayi sallama ne, Hadiyyah ta Fara koro ma sa bayanin Rashin lafiyar da Zakiyyah da abunda likita ya faɗa musu na cewa lalläi ta farka da Mukhtar da take ambatarsa yazama shine abu na farko da ta Fara tozali da shi, Duk cikin kukan da Hadiyyah take ƙokarin shanyewa Amma ina Saida ya fito a Hakan tai Masa bayani, ta na mai roƙonsa Akan ya yi Akan ya taimaka musu ya ƙaraso asibitin kar Zakiyyah ta sake farkawa a karo na biyu,da to mukhtar ya kashe wayar.
Wanda yabar su ƴan biyu da Sa'adatu da mamakin Hakan! Anya kuwa zaizo? Zuciyarsu ta tsinke sa lamarin fa, sun san da ma ba abune mai sauƙi ba da Mukhtar zai zai sakko cikin sauƙi,la akari da yadda Zakiyyah ta dinga Masa Rashin mutunci da halaye marasa arziƙi, kuma sun san ya na da haƙuri Amma kuma bai iya fushi ba, dan haka su ka tsaya cikin jimamin ALLAH ya kawo mukhtar dai a wannan gaɓar Nima OUM ARQAM nace Allahumma Ameen ba tayasu da addu'a🙏


Bayan ka she wayar da Mukhtar ya yi zuciyarsa kam ta sosu jin Abubuwan da suke damun Zakiyyah ɗin, ya yi mamaki ita da batada kunya ko ƙadan, bata ganin mutunci da ko ƙadan, ta nuna ma ba ta damu da shi ba shine yanzu kuma zata wani dinga sambatu ta na ambatar sunansa! Ko dai Zafin ciwone dan kuwa shikam ya san Zakiyyah, Akan taurin kai da Rashin jin magana, Amma ko alama bai ga alamun zata saduda ba, Amma da ya tuno da zuwansa Auren Zahra ya daiga tabbas ta rame,kuma dai batayi mai magana ba, Amma kuma dai tayi hawaye,ga gwiwarta a ƙasa,ya yi tunanin kuma ganin ABIE Duk yasata Hakan,Amma ita da bata damu da ABIE ɗin ba? Ita dai ta sani!
"Zaujin saleh ka ji fa abunda yake faruwa da maman ABIE, kuma na ga ka zauna ba ka da alamun tashi ka saka kaya ka tafi asibitin fa? Cewar Bilkisu tana dafa kafaɗar mukhtar ɗin!


"Mar atussaliha ƙale wannan Ba tu me Zakiyyah zata gayan kuma ni mukhtar?mutuniyar da ta mayar da ni ba abakin komai ba! Yafiya ce da ta ne ma na yafe ma ta ALLAH ya yafe Mana ba ki ɗaya, bari na Kira Hadiyyah na gaya mata in ta farka ace Mana ni mukhtar na yafe mata ba dai shikenan ba! Inji mukhtar ya na shirin kwanciya da juyawa Bilkisu ba ya da wayar a hannunsa ya na shirin dannawa Hadiyyah waya ya faɗa MATA sakon da zai isarwa da Zakiyyah ɗin, Amma shikam ba ya ganin da abinda zai sa yaje asibitin nan.
Fisge wayar Bilkisu ta yi daga hannun sa cikin alamun tayi fushi!
"Kafin tace gaskya zaujin saleh idan kayi Hakan haka kyautawa Zakiyyah ba,kai baka yafiya ne? kamata yayi kamayar da Abubuwan da ta faru tsakanin ku da ita ya Zaki akasi Man, dan kuwa kowanne namiji da kaganshi da matarsa bakasan me take ma sa ba kuma haka yake haƙuri da ita, kamayar da Abubuwan da Zakiyyah tai maka baya ka yafe MATA sannan ka taso ni zan rakaka asibitin, zaujin saleh ka tuna alkhair ɗin iyayen Zakiyyah a gareka, kamar yadda kullum kake faɗa,sun so ka sun girmamaka, musamman kaakarta Hajiya Sakinah kaji zaujin saleh! Ta ƙarasa cikin kwantar da murya!
Tabbas Duk abunda Bilkisu ki ka faɗa gaskia ne na sani, kuma na ya fe ma ta Duk Abubuwan da tayimun, ALLAH ya yafe ma na baki ɗaya,


Yawwa zaujin saleh indai dagaske ka yafe matan ka tashi yanzu ka saka yakanka muje asibitin nan wajen ta, ta farka dakai a idonta ko zata samu sauƙi a zuciyarta kaji, lallai Bilkisu ALLAH yasaka miki da alkhair kinji tawajena.


Haka Bilkisu Duk da kishi ya na cin zuciyarta na mijinta haka ta danne ta ƙarfafa gwiwar mijinta har ta taimaka Masa dakanta ya shirya, ita ma ta shirya suka fito domin tafiya asibitin wajen Zakiyyah, Amma fa zuciyar mukhtar baiso Hakan ba,sai ɗan Bilkisu ɗin da ta san yadda take shawo kan mijinta ta sarrafashi ta sakashi aikata abunda takeso cikin hikima da iya karantar mijinta, lallai Bilkisu kinci sunanki na mar atussaliha.


Haka suka fito shi mukhtar ya fita dan ga fitar da mota, ita kuma Bilkisu ta tafi ɗakin ABIE ta ɗauke shi ta shiga ɗakin da taiwa Husna masauki ta ce mata ga ABIE Husna zamuje mudawone, to Aunty cewar Husna tana karbar ABIE da gyara Masa kwanciya, Amma dai lafiya ko ? Lafiya lau Husna kawai dai siyayyah zamuje,in zamu siyayyah sai ya dawo Muke fita,shikenan Aunty ALLAH yakaiku lafiya.


Haka Bilkisu ta fice lokacin har mukhtar ya fitar da motar waje ya kulle gate ɗin ma, dan haka waje ta fice bayan ta kulle kofofin gidan saboda tsaro,


Haka suka dau hanya zuwa asibitin da Zakiyyah take kwance, wanda dama Hadiyyah ta gaya Masa sunansa a wayar da sukayi da ita ..............


Up
Up
Up
Up


Gaskia wannan Page ɗin yaymin daɗi Allah ya ƙare mun ke ƙawata Bilkisu


ALLAH sarki Kawu isma'il yafara bani tausayi sosai fa zah tayashi d addu'a kuma please kutayashi




Muje zuwa dai yanzu aka Fara wasan akwai cakwakiya tausayi cin Amana maraici da kuma zazzafar soyayya a gaba muje dai zuwa yan amana


Nice dai


✍️ OUM ARQAM ontop😍
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*






*PAGE THIRTY SIX 36*




Ƴan team ɗin Zakiyyah hardai yanzu Bilkisu bata burgekuba 🤔
😳😒


Mukam ƴan team ɗin Bilkisu ta burgemu 100% ba kowacce mace bace zatayi abunda kikayi🥰🤝😄


"Gaskiya jibo ban taɓa tunanin wannan Aikin da muka ɗauko zai gamu a waɗannan ƴan kwanakin ba, lallai isma'il, na daɗa tabbatawar wa da Bashida imani ko ƙadan, kuɗaɗen marayu zunzurutun kuɗin har 50millinon,shu shiga hannun ƴan damfara Amma kabar maganar hakanan, ba bu wanda ya sani, shikenan kaci bulus kenan, ALLAH nai maka godiya da waɗannan kuɗaɗen suka dawo hannuna ,da ace ƴan damfarar gaske ne suka karɓe kuɗin ai da shikenan!
Shi dai jibo Duk da a wayane Alhajin yake Masa magana Amma akwai alamun rissinawa kamar ya na gabansa,kuma bai motsi ba sai da Alhaji yakai aya da zancen na sa sannan shi ma ya yi ajiyar zuciya! Yace' Ranka ya daɗe ai ni dai abun nan ya bani mamaki matuƙa, saboda yadda ba bu wani jayayyah ya turomin da kuɗin, bayan nagama shiga jikinsa sosai, Duk wani sirrinsa na sani, hatta 50million ɗin da ya turan sai da ya tabbatar min da ta marayu ƴaƴan yayansa ce,wai so yake ba da jimawa ba kuɗin na su yayi yawa, ƴaƴan nan ya na tausaya musu sosai,yanzu haka biyar baya ɗauka a kuɗin da yake juya musu, da kuɗin sa yake musu Kowacce wahala, kwanannan akayi bikin ɗaya daga cikinsu ma(Zahra) ya kashe kuɗi da yawa biyar bai ɗauka a cikin kuɗinba, yanzu haka akwai ƴan biyu(Hadiyyah da Hidayah) acikin ƴaƴan university suke zuwa pravet ce, shine ya ke biyan kuɗin, akwai ɗan sa saurayi(Alhaji) shima yanzu haka baya ƙasar, Duk dai yadda jibo sukayi da Kawu isma'il haka ya kwashe ya gayawa Alhaji tallafy, Alhaji tallafy kam dai jinjina kai yakeyi, bayan zalunci kuma harda ƙarya isma'il ya keyi,
Nan dai Alhaji tallafy yaiwa jibo godiya Akan namijin ƙokarin da yayi, da jajircewa wajen Cika ma sa aiki cikin lokaci ƙanƙani, a lokacin da baiyi tsammani ba,
Wannan Aikin da jibo yayi ya farantawa Alhaji tallafy Rai sosai, yo da ma jibo ɗan saurayine Just 28_30ne dan haka wannan ƙwazo da yayi Alhaji tallafy ya ɗauki nauyin karatunsa, har zuwa abunda ALLAH yayi, fannin shari'ah tun da kam yaga anan jibo zaiyi taimako sosai, ya yi godiya sosai, kamar zai ari ba ki, shi kam Alhaji sai murna yakeyi.


JIBO dama yana da burin karatu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login