Showing 27001 words to 30000 words out of 171073 words

Chapter 10 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7822

Halisa,? Bawai banyi imanin da k'addara bane koda hakan ta kasance ba a'a sai dan gwara ace da auren sa a kanta a lokacin da ace babu, ki fahimce ni wallahi banyi da niyar cutar da rayuwar Ibteesam ba nayi ne ni sabida inganta rayuwar ta, yadda zan aurar da Asiya haka zan aurar da Ibteesam duka y'ay'a nane Halisa kuma kome mutanen duniya zasu ce a game damu ya dai fi ace duniya tana zagin mu akan sabida ba y'ar mu bace mun bari tayi ciki ko kuma mun bari an lalata mata rayuwar ta." Ajiyar zuciya Umma tayi ta goge hawayen idon ta tace, "Haka ne, amma ka duba yaron da ka bata, bashi da inganci ko kad'an bai kama da miji na gari da ko wanne uba yake zab'awa y'ar sa ba, meyasa uban sa bai tsawatar masa ya dawo mana daa y'ar mu ba sai aure shine za'a ce mafita?."

"Halisa auren nan na rashin mafita ne shima mahaifin nasa ya sani, auren sirri ne Halisa dan Allah ki hak'a rami ki bunne maganar nan yadda na fad'e ta nida ke bana so kowa yaji maganar nan koda ita Ibteesam d'in ce mu jira zuwa dawowar ta mu gani." "Shikenan naji, muyi yaya da yaron nan Khalid da yake zarya koda yaushe akan maganar Ibteesam d'in? Ka sani tana son sa shima kuma yana sonta ya zamuyi dasu?". "Shiyasa nace miki auren sirri ne ko ita bana so ta sani da zarar ta dawo zan koma wajan mahaifin ta a warware auren ba tare da kowa ya san da hakan ba." "Shikenan Allah ya kyauta". Ya amsa da amin ya mik'e ya fita.

Washe gari.

Juya PT stick d'in take a hannun ta tana zaga d'akin, bud'e k'ofar da akayi aka shigo ya tsayar da ita daga zaga d'akin da take ta kalli wanda ya shigo, "Amina lafiya kike kuwa?" Daddy ya tamabaya yana yi mata kallan tuhuma. Batayi magana ba sai mik'a masa PT d'in da tayi tare da kawar da kai, karb'a yayi yana kallan fuskar ta tare da juya PT d'in yace, "meye wannan d'in?". "Pregnant test ne ya nuna min positive kuma" ta fad'a a d'an sanyaye tana kallan sa.
Baki Daddy ya bud'e ya kalli abinda ya bashi ya d'ago ya kalle ta yace, "Wai kina nufin kina da ciki kenan?" Ya tamabaya a rud'e yana washe baki.

D'aga masa kai alamun eh, raba ta da k'asa yayi ya fara juyi da ita a cikin d'akin yana dariyar farin ciki, sai da ya gaji da kansa kana ya dire ta ya kalli gabad yayi sujadda ya godewa Allah ya mik'e ya ja hannun ta suka zauna a kan gado yace, "Alhamdulillah, Amina Allah yayi miki albarka ki fad'a min abinda kike so ko meye yanzu na baki shi" ya fad'a da murmushin farin cikin shinfid'e a fuskar sa. Itama murmushi tayi tana jin farin ciki a wani b'angaren na zuciyar ta wani b'angaren kuma tana jin fargaba da tashin hankali yana k'okarin rinjayar farin cikin nata, "abinda nake so guda d'aya ne kuma gashi kayi, buri na na saka ka a cikin farin ciki gashi kuma nayi" ta k'arasa fad'a da murmushi a fuskar ta. "Sai kin fad'i abinda kike so Amina domin ki bani abinda na jima ina nema, shekara sama da talatin kenan rabon da na samu abinda nake so amma gashi ta sanadin ki yau Allah ya bani, ki fad'i ko meye kike so zan baki Amina".

"Ka zauna dani a ko wanne irin da zan riski kaina ko yanzu konan gaba, ka yafe min duk wani laifi da zan maka ko nayi maka wanda na sani da wanda ban sani ba, wannan shine kad'ai abinda nake so kuma nake buk'ata a waja ka" ta k'arasa fad'a kamar zatayi kuka.

"Amina wannan kamar anyi a gama ne nida ke mutu ka raba insha Allah, amma fa dole nayi miki kyautar da in kika tuna zaki ji dad'i kema kamar yadda nima nake cikin farin ciki a yau". "Sannan dan Allah alfarma d'aya" ta fad'a a sanyaye tana kallan sa. "Ina jinki fad'i ko meye kike so." "Bana so kowa yasan da wannan cikin dan Allah in aka cire Zaid shima dan yana da kyau a sanar dashi ne amma bayan shi dan Allah ka b'oye farin cikin ka a zuciyar ka kar ka bari ya bayyana" ta fad'a tana had'e hannayen ta waje daya idon ta na kawo ruwa. Sauke hannun ta yayi yace, "Kar ki damu Amina nayi miki wannan alqawarin duk da ban san dalilin ki na fad'ar hakan ba amma zan miki." Murmushi tayi tare da ajiyar zuciya tace, "Nagode sosai Allah ya inganta mana". "Amin Minali, ina zuwa" ya fad'a yana ficewa da sauri kamar zai fad'i.

Ajiyar zuciya tayi ta bishi da kallo tana aiyana abubuwa da yawa a ranta, fargabar ta d'aya bai wuce ace su Yaya babba sun san da maganar cikin jikin ta ba shiyasa ta saka Daddy yayi alqawarin bazai fad'a ba dan matsawar ya fad'a tabbas sai sun salwantar da cikin dan baza su tab'a bari ya rayu ba, murmushi tayi tana aiyana irin abubuwan da zata tara da cikin jikin ta.

Lokacin da Daddy ya sakko lokacin y'an uwan sa suka shigo gidan, turus yayi ya kalle su yace, "Sannun ku da zuwa" ya fad'a cikin fara'a da annushuwa tare da k'arasowa cikin falon.

Da yauwa suka amsa suka zauna suka gaisa, Yaya babba yace, "Abubakar kamar yadda na sanar da kai jiya hakan ce ta kasance, ga goro da alawa nan an d'aura auren Zaid da Eman d'azu a masallaci anjima kad'an zata tawo nan gidan mijin ta bama buk'atar wani shagalin biki." Tunda ya fara magana kawai Daddy ya zuba masa ido yana kallan sa cikin mamakin k'arfin hali irin na baban Yayan nasa, kasa furta komai yayi sai sauraran maganar su kawai da yake yi dan shi ban san abinda zai ce ba kuma, "to daman wanne shagali za'a yi abu na gida, anjima amarya zata tare sai kayi masa waya duk inda yake ya dawo amarya bata tare ango baya nan ba" Yaya Bala ya fad'a yana kallan Daddy da ya k'ame a wajan kamar an dasa shi.
"Kayi shiru baka ce komai ba?" Yaya babba ya katse masa tunanin da yake yi, murmushin k'arfin hali yayi yace, "To me zance tunda kun riga kun yanke hukunci? Allah ya sanya albarka" suka amsa da amin suka shiga wata hirar daban.

Shi dai Daddy kawai yana jin su ne amma baya gane abinda suke cewa dan yasan akwai gagarumar rigima dan babu ta yadda za'ayi Zaid ya amince da auren Eman har ya zauna da ita matsayin mata abu ne mai wahalar yuwa, duk sai fargaba ta kama Daddy domin duk abinda Zaid zai aikata cewa zasuyi da sanin sa yayi, a haka suka k'araci surutun su suka kama gaban su suka bar Daddy da tunani.

*Kaduna.*

A tsaye take sanye da towel iya guiwa da alama daga wanka ta fito, sauri-sauri take ta shirya dan ba son tsayuwa take ba sabida ciwon da yake kanta, hannun ta ta saka tana nad'e gashin kanta taji an bud'e k'ofar a shigo d'akin, idon sune ya had'u dana juna ta zaro ido tare da saurin juyawa baya idon ta a kulle, ta baya yake k'are mata kallo tun daga fararen k'afar ta har zuwa inda towel d'in ya tsaya, wani irin abu had'd'iye ya ja k'afar sa a hankali ya fita daga d'akin tare da kullo mata k'ofar.

Tsaki tayi ta k'arasa da sauri ta sakawa k'ofar key, "Aikin banza aikin wofi kawai a shigowa mutane ba tare da neman izini ba balle sallama, na tsane shi wallahi bana san ganin sa ko mafarki" ta fad'a tana cigaba da shiryawa.

Shi kuwa tunda ya fita ya jingina da bango idon sa a kulle yana jin wani irin yanayi yana ratsa ko ina na jikin sa, shifa ya rasa abinda yake ji game da yarinyar nan ko wanne second ji yake kamar ana bud'e jikin sa ana saka masa ita kad'an-kad'an, numfashi ya fesar ta dafe kansa da hannayen sa zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri.

Sai da ya tabbatar ta gama shiryawa kana ya koma d'akin ya same ta a zaune a kan gado ta buga uban tagumi tana kallan waje d'aya, lumshe ido yayi yana tuno yadda ya ganta d'azu, saurin kawar da tunanin yayi yace, "Ki shirya a mayar dake gida" ya fad'a murya a sanyaye kamar wanda yasha ruwan sanyi.

Da hanzari ta kalle shi ganin babu wasa a fuskar sa ya saka ta mik'e tsaye tace, "Da gaske gida za'a kaini?" Ta tambaya muryar ta na rawa. D'auke kai yayi daga kallan ta kana yace, "Na tab'a yi miki k'arya ne?." Saurin girgiza kai tayi alamun a'a farin ciki na bayyana a fuskar ta, "wayyo Allah yau zan ga Umma na" ta fad'a tana rufe fuska da hannun ta tana tsallem murna.

Ganin farin ciki a kan fuskar ta sai ya saka shi ya saki fuska kad'an ya kafin ya tab'e baki ya juya ya fice daga d'akin, ware mayafin tayi ta yafa ta zura takalmin ta ta fito daga d'akin ta sakko k'asa ta zauna jira, bata jima ba ya sakko da jakar sa a hannun sa kunne sa mak'ale da waya yana magana a hankali.

Mugu da Wizzy suka fito suma suna jiran suji abinda Mai gidan nasu zai ce musu, sai da ya kammala wayar gabad'aya kafin yace, "Ku kaita gida na wuce Abuja" daga haka bai jira mai zasu ce ba kawai ya fita daga falon yana kallon agogon hannun sa.

Tunda suka fita daga falon suka nufi mota bakin ta yak'i rufuwa har suka shiga suka zauna,? kunna motar Wizzy yayi wanda yake tsaron gate ya bud'e musu suka fita daga gidan.

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske tana ji kamar ta fita daga wuta ta shiga waje mai sanyi, ta lumshe ido maimakon taji tsanar Zaid na raguwa sai k'aruwa da tayi tana jin ta a ranta kamar a lokacin Allah ya dasa mata tsanar sa mai zafi.


_Tofa akwai rikici fa, Saura page d'aya mu gama free pages_=??=؃?



_free pages dai basu da yawa ki biya kud'i k'alilan ki karanta labarin cikin kwanciyar hankali da nishad'i, naira 100 ne kacal ba tsada kamar ruwan pure water d'auki hoton katin MTN ki turo ta wannan number but only WhatsApp +2347045242700......._


Comments and share fisabinillah
*g& ?ASAITAR SO! g&*

? ? ? ? ? ?? ?? *Nana Haleema*

*21?'?22*
*Last free page*


*Kano.*

A bakin layin su Ibteesam Wizzy yayi parking ya kalle ta ta mirror yace, "fita" ba musu ta bud'e ta fita da hanzari ta juyo ta kalle su tace, "duk bak'in halin ku ni Maryam nafi k'arfin ku wallahi, aikin banza duk abinda kuka yi min ka fad'awa Ogan naku ban yafe ba, ba kuma zan yafe na har a tashi duniya" tana gama fad'ar hakan ta harare su ta juya ta shiga cikin layin su.

Mugu ya kalli Wizzy sukayi dariya a tare Wizzy yace, "Ita dai yarinyar nan bakin ta baya shiru koda yake dan ta samu ya k'yale tane shiyasa take da bakin magana". "Wizzy Allah mai gida yana jin wani abu a kan yarinyar nan kawai taurin zuciyar sa ya hana shi ya fahimta". Kunna motar Wizzy kawai yayi suka bar unguwar dan dukkan su a gajiye suke.

Kamar an cillo ta haka mutanen Falon suka ga shigowar Ibteesam a gigice tana kalle-kalle, "Anty Ibteey" Jidda ta fad'a cikin ihu tana yo kanta da gudu, rungume ta tayi cikin farin ciki da kewar y'ar uwar ta ta d'ago da ita daga jikin ta tace, "Jidda ina Umma?". Umma da Jafar yaje ya sanar da ita ta fito kamar ana hankad'o ta tana so ta gasgata abinda Jafar ya fad'a, "Umma na" Ibteesam ta fad'a tana k'arasawa da d'an sauri ta fad'a jikin ta tana kuka. Itama Umman rungume ta tayi tana shafa bayan ta tana jin farin ciki mara misaltuwa a lokacin, "Umma na nayi kewar ku" ta fad'a tana sake k'ank'ame Umma tana cigaba da kuka.

"Ashe da gaske Ibteesam d'in ce" Mama ta fad'a da fara'a a fuskar ta tana kallan su, sakin Umma tayi taje wajan Mama ta rungume ta itama tana cigaba da kuka, "ki daina kuka mana Ibteesam tunda Allah ya kub'utar dake ai an gode Allah" Mama ta fad'a tana shafa bayan ta cikin rarrashi.

Cikin farin ciki aka dinga gaisawa da Ibteesam kafin a k'yale ta ta tafi d'aki dan ta huta.

Bayan sallar i'sha kasancewar Umma keda girki bayan ta kammala komai da yake k'ark'ashin ikon ta na ranar ta nufi falon Abba kamar ko da yaushe, yana zaune a falo yana kallan labarai ta shigo da sallama ya amsa yana kallan ta da murmushi a fuskar sa.

Har ta zauna bayan sallama bata sake cewa komai ganin hakan ya saka ya mayar da hankalin sa gare ta gabad'aya yace, "Na d'auka yau zan ga farin ciki kwance a fuskar ki amma sai nake k'okarin ganin akasin hakan, meya gusar da farin cikin dawowar y'ar mu akan kyakykyawar fuskar nan taki?". Gyara zama itama tayi kafin tace, "Allah ya dawo mana da y'ar mu lafiya ya maganar datse igiyoyin auren da suke kanta?". Murmushi yayi mai sauti kafin yace, "Haba Halisa kwata-kwata awan Ibteesam nawa da dawowa da zaki tayar da wannan maganar?." "Eh ai ya kamata ayi ta da wuri ne tun kafin lokaci ya k'ure, aikin gaggawa ma akayi in badan hakan ba da yanzu babu wani aure a kanta." "Halisa kenan, kin manta ya tsarin namu yake ne?". "Ban manta ba abinda ya saka nayi maganar kenan ma dan ni banga wata alama da a tare da Ibteesam da zata nuna yaron ya kusance ta." "Haka tace miki?" Ya tambaya yana kallan ta, "Haba dai yanzu har sai ta fad'a min zan fahinta,? Ai idon Ibteesam na kalla zan gane yanayin ta."

Dariya ta bawa Abba sai yayi murmushi kad'an yace, "naji, amma ki tambaye ta gobe in Allah ya kaimu nima kuma a goben zan dira a gidan su." "Amin, gwara dai a san nayi tun yanzu" tana fad'ar hakan ta mik'e ta shiga bedroom d'in da cikin falon.

Washe gari Ibteesam ta wuri ta tashi tayi wanka ta shirya ta tsaya a gaban mudubi tana gyara zaman bandage d'in da yake kanta ganin ya fara kwacewa, wuyan ta ta kalla nan tayi tozali da shatin dukan da tasha da belt yana nan da alama ya zamar mata tabon da zata je dashi lahira, "Allah ya shiga tsakani na dakai, na tsane ka bazan tab'a yafe maka ba har abada."

Shigowar Umma ya saka ta mayar da hankalin ta ga Umma tana murmushi tace, "Ina kwana Umma na". Itama murmushin tayi tace, "lafiya lau, ya jikin naki? dan naga alamun baki da lafiya." "Da sauk'i Umma daman ciwon baya da ciwon k'ugu ne yake damu na sai wannan ciwon na kaina". Gaban Umma ya fad'i jin ta ambaci ciwon k'ugu ya saka ta ja hannun ta suka zauna a bakin gado tace, "duka me ya jawo miki wannan ciwon?". "Mugun ta mana Umma, wallahi wanda ya sace ni mugu ne bashi da imani" ta fad'a tana fashewa da kuka ta kwanta a jikin Umma.

Zuwa lokacin tsoro ya cika zuciyar Umma tana shafa kanta tace, "me yake miki?". Cikin muryar kuka tace, "Duka Umma, babu damar nayi magana kad'an sai ya zane ni sannan kuma ya saka a bani magani, ki duba kaina Umma haka ya saka k'afa ya fyad'e ni na fad'i a kan tiles, ya buga ni da mota dan ina k'ok'arin na bar gidan, ya zane ni da belt dan nace ya dawo dani gida bayan ya shak'e min wuya yana niyar kashe ni in badan wani yazo ya cece ni ba da yanzu sai dai kuji labarin mutuwa ta,Allah Umma ni bazan k'yale shi ba sai na kai k'arar sa wajan y'an sanda sai alkhali ya bimin hakki na". Shiru Umma tayi tana sauraron kukan da Ibteesam take yi tana bubbuga bayan ta, "Bayan wannan bai miki komai ba Ibteesam? Ina nufin bai san ki y'a mace ba?".

Shiru tayi tana tuna gamon da suka sha yi a kan hakan in ba dan Allah ya kiyaye ta ba da yanzu ba zancen aike yi ba, jin shirun ta ya saka zuciyar Umma cikin tsananin fargaba da tashin hankali ta sake cewa, "ki bani amsa." "Kiyi hak'uri Umma nayi iya k'okari na wajan ganin hakan bai kasance ba" ta fad'a tana d'agowa daga jikin Umma kanta a sunkuye.? "Sanar dani mana Ibteesam ya kusance ki?". D'aga mata kai Ibteesam tayi alamun eh, "Hasbunallahu wani'imal wakil" Umma ta furta tana dafe kai da hannun ta.

"Kiyi hak'uri Umma ba laifi na bane ya saka min k'arfi ne babu yadda na iya" ta k'arasa fad'a da kuka sosai tana fad'awa jikin Umman, goge hawayen dake idon ta Umma tayi tace, "Sau nawa ne?". Murya a shak'e Ibteesam tace, "Sau d'aya" bakin ta na rawa, runtse ido Umma tayi tana jin wani irin d'aci yana ratsa cikin zuciyar ta, "yaushe ne hakan ta kasance?" Umma ta tamabaya muryar ta na rawa sabida kukan da yake k'okarin kwace mata. "Shekaran jiya ne, ana e gobe zan tawo". Shiru Umma tayi tana jin wani d'an sanyi yana cikin zuciyar ta kafin tace, "Ya kike jin jikin naki,? Bakya jin zafi? In kina ji ki fad'a min na kaiki asibiti a duba ki". "Babu Umma sai kad'an" ta fad'a kanta a k'asa ta kasa d'agowa ta kalli Umma.

Ajiyar Zuciya Umma tayi ta d'ago ta daga jikin ta tana kallan fuskar ta, sunkuyar da kai Ibteesam tayi kafin Umman tace, "ki kwantar da hankalin ki kinji za'a bi miki hakkin ki insha Allah sai ya girbi abinda ya shuka, baban fata na bai wuce Allah yasa baki samu ciki ba dan lokacin zuwan period d'in ki ya kuwa Ibteey dan bana tunanin ya kai four day's nan gaba ko?". D'aga kai tayi alamun eh kawai dan ta kasa cewa komai, "Sai an bi miki hakkin ki insha Allahu, sai ya girbi abinda ya shuka haka sai ya zauna a prison matsayin sa na wanda yayi miki fyad'e, yanzu bari na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login