Showing 18001 words to 21000 words out of 171073 words

Chapter 7 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7823

yanayin damuwa da tashin hankali, zuwa wani lokaci zazza6i mai zafi ya sauka a jikin ta jikin ta ya fara rawa haqoran ta na garuwa da juna sabida sanyin da take ji, knocking d'in k'ofar aka fara yi a hankali, tana ji amma bata tunanin zata bud'e dan tasan bazai wuce mugun da ya zane taba ko yaron sa hakan ya saka ta sake kwanciya sanyin tiles na ratsa jikn ta, "baiwar Allah kizo ki bud'e an turo ni na taimaka miki ne" aka fad'a daga waje ana cigaba da buga k'ofar, jin muryar mace ya saka hankalin ta ya kwanta ta d'an mik'a hannu ta cire lock d'in k'ofar taja baya k'ofar ta bud'e aka shigo, babbar macece wacce a shekaru zatayi shekara talatin da wani abun ta shigo d'akin ta mayar da k'ofar ta rufe ta mayar da kallon ta ga Ibteesam cikin tausayawa ganin yadda jikin ta yayi ja tace, "Sannu y'ar nan, tashi ki samu ki gasa jikin ki zaki fi jin dad'i." Ba musu ta yunk'ura ta taimaka mata ta mik'e ta kaita band'aki ta had'a mata ruwa ta fito ta barta, bata jima sosai ba ta fito hannun ta dafe da kanta sabida ciwon da yake mata, doguwar riga kawai ta zura ta kwanta a kan gadon tana sauke numfashi.

Magani ta b'allo mata ta bata tasha kafin ta kwashe kayan abincin da aka kawo mata bata ci ba ta kulle mata d'akin ta sauka, da kallo Ibteesam ta bita tana mamakin hali irin na Zaid, ya gama jibgar ta ya turo kuma a bata magani.

Zaid kuwa cikin nutsuwa ya kalli Wizzy yace, "Su Gaye basu k'araso ba har yanzu?" Ya fad'a lokacin da yake fitowa daga d'aki, "eh mai gida amma sunce min suna kawo". "Sun zo ma kenan, muje kawai" ya fad'a yana fara sauka daga saman Wizzy yana bayan sa. A falo suka gamu da Atine mai dafa musu abinci tana ganin sakkowar su tayi murmushi ta kalli Zaid tace, "yallab'ai Allah ya kaiki lafiya". Iya fatar bakin sa ya amsa da amin kafin ya d'auko kud'i ya bata yayi ficewar sa.
Mota suka shiga Wizzy yaja motar suka fita daga gidan motar su Gaye ta shigo gidan.

*******

Da sallama Khalid ya shiga gidan su Ibteesam kansa a sunkuye gaban sa na fad'uwa, Abba da yayi masa izinin shigowa yace, "Shigo m??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ana Khalid". Takalimin k'afar sa ya cire ya shiga cikin falon har lokacin bai d'ago kai ba.
A kan carpet ya zauna cikin nutsuwa yace, "Umma ina wuni" Umma da take zaune tana jan jarbi ta amsa da fad'in, "Lafiya Lau Khalid ya mutan gidan naku?". "Lafiya lau, duk sunce ayi miki jaje Allah ya bayyana ta." "Amin Khalid nagode. "

"Abban Jafar? basu yo wayar ba har yanzu ko?" Umma ta tamabaya tana kallan Abba, sai da yayi ajiyar zuciya kana yace, "Basu yo waya ba koda yaushe cikin jiran wayar su nake muji abinda zasu buk'ata amma har yanzu shiru." Shiru tayi bata sake cewa komai ba sai addu'a da tayi a zuciyar ta. Jiki a sanyaye Khalid yayi musu sallama ya fita daga gidan ya shiga motar sa da ya bar abokin sa a ciki, kifa kansa yayi a kan sitiyarin motar ba tare da ya shirya ba hawaye suka zubo daga idon sa, "Abdul ban san haka nake san Ibteesam sai a yanzu da aka neme ta aka rasa nake? jin zuciya ta tana wani irin zafi kamar ana dafa ta, A yadda nake jin zuciya ta a yanzu ji nake kamar ana saka wuk'a ana yankar ta sabida bala'in radad'in da nake ji a cikin ta, Abdul ina san Ibteesam ina santa in na rasa ta basan ya zanyi ba" ya k'arasa fad'a cikin kuka sosai kamar yaro k'arami.

Abdul da yake sauraran sa jikin sa yayi bala'in sanyi tausayin abokin nasa ya kama shi cikin muryar rarrashi yace, "Kayi hak'uri Khalid insha Allah za'a ganta cikin k'oshin lafiya addu'a zaka taya ta Allah ya kare ta a duk inda take ka daina kuka dan Allah. " tissue ya zara ya goge idon sa kafin ya kunna motar su bar unguwar dan tunda Ibteesam ta b'ace ya bar zaman gidan kakanin sa a? Yakasai koma gidan su.

Bayan fitar Khalid Abba ya kalli Umma da take goge hawaye yace, "Yanzu Halisa baza ki sakawa zuciyar ki dangana ba? Wannan kukan da kike yi ba shine mafita bafa,ki duba yadda kika rame kika yi bak'i a cikin kwana biyu, addu'a ita kad'ai zaki yi mata ki taimake ta, Allah zai bayyana ta zata dawo gare mu da izinin Allah amma sai mun karb'i jarabawar da Allah ya k'addaro mana hannu biyu, in kina kuka Jidda da Jafar su kuma suyi mene? Dan Allah ki daina wannan kukan Allah yana tare da ita a duk inda take." Goge hawayen idon ta tayi kawai bata ce komai ba ta cigaba da jan jarbin ta.

Sallamar da akayi ne ya saka Abba ya mik'e ya koma d'akin sa dan gidan koda yaushe cikin bak'i y'an jaje ake.

**********

Bayan sallar la'asar Daddy yana zaune akan kujerar da yake babban falon gidan sa yana shan fruit Amina na zaune a kusa dashi tana canja cannel d'in tv, ajjiye remote d'in tayi tace, "Nikam kwana biyu ina Zaid yake?". "Yaje Abuja gidan Mummyn sa" ya bata amsa yana kallan tv ba tare da ya kalle ta ba.

Zatayi magana aka shigo falon nasu da sallama, amsawa sukayi suna kallan masu shigowa, mik'ewa Amina tayi taje ta d'auko mayafi dan ganin bak'in da suka shigo, takaici ya kama Daddy sam baya san irin wannan rayuwar duk da y'an uwan sane amma ai yaci ace sun nemi izinin sa kafin su shigo masa falo kai tsaye? tunda yana da iyali, "Sannu da Yaya Babba" ya fad'a fuskar sa babu walwala yana kallan yayyen nasa guda biyu.

Cikin fara'a Yaya Babba yace, "Yauwa Abubakar ya gida?". Mamaki ya kama ganin suna gaisawa da fara'a a fuskar su, shanye mamakin sa yayi yace, "Lafiya lau Alhamdulillah". Zama sukayi dukkan su kafin Yaya Babban yace, "Ina Zaid d'in?". "Yaje Abuja wajan yayar mahaifiyar sa". "Allah sarki ai gwara ya dinga zumunci" Yaya Bala ya fad'a da murmushi.

"Abubakar dama magana ce ta kawo mu akan shi Abdullah" Yaya Babba ya fad'a cikin nutsuwa yana kallan Daddy, gyara zama Daddy yayi yace, "To Allah ya lafiya." "Lafiya qalau sai alkhairi, wato gani nayi sabida sake inganta dank'on zumunci naga mai zai hana baza'a had'a yaran nan aure ba." Daddy da ya kasa fahimtar sa yace,"Wanne yara kenan?". "Zaid da mai sunan Mama Eman, in akayi haka zumunci zai sake k'ulluwa sosai kuma daman wannan burin mahaifiyar mu ne kafin ta bar duniya."

Shiru Daddy yayi yana nazari kafin yace, " abu ne mai kyau in akayi hakan kuma zamu fi kowa farin ciki, amma Yaya Babba zanyi magana dashi Zaid d'in in ya dawo muji meye ra'ayin sa akai ita ma Eman d'in sai a tuntub'e ta aji ko?'". "Eh hakan yana da kyau kam gwara a tambayi yaran aji ta bakin su" Yaya Bala ya fad'i cikin sakin fuska. Jimm sukayi babu wanda ya sake magana a cikin su kafin su Mik'e ko wanne yana fama da babbar riga suyi sallama su tafi.

Fitar su babu jimawa Zaid ya shigo waya a mak'ale a kunne sa yana amsawa, tsayawa yayi a falon ya gama amsa wayar kafin ya kashe ya kalli Daddy yace, "Daddy sannu". "Welcome Son" ya fad'a da murmshi a fuskar sa, Daga haka Zaid bai sake cewa komai ba ya haura saman sa dan a gajiye yake sosai.

Lokacin Sallar magariba ne ya sakko dashi ya fita masallaci bayan an idar ya dawo yana niyar hawa sama Daddy yace, "Zaid dawo ka zauna" ba musu ya dawo ya zauna a akan kujera yana kallan Daddy. "Zaid yanzu abinda kayi ka kyauta kenan?". Zaro ido waje yayi yace, "Me kuma nayi?". "Ka saka y'an daba sun wahalar da iyayen ka mana, yanzu wannan halayya ce mai kyau Zaid?." "Daddy basa sona ba kuma sa k'auna ta tun mahaifiya ta na raye suke nuna mata tsana har ta bar duniya, tsanar ta dawo kaina a gaba na suke zagi na su zage ka kuma na k'yale su? Impossible Daddy in na k'yale su gani zanyi kamar na aika babba sab'o shiyasa na sanya a gyara musu zama" ya k'arasa fad'a yana tab'e baki tare? karkad'a k'afa.

Shiru Daddy yayi cikin rashin sanin abinda zai cewa Zaid d'in sai kawai yace, "D'azu sunzo sun same ni akan suna so a had'a ka aure da Eman." "Waye kuma haka?" Ya tambaya yana d'aga gira sama. "Y'ar wajan Yaya babba ce." "Kuma ni suke so na aure ta? Ai wannan labari kawai suka baka Dad because ni ko mata sun k'are mai zanyi da y'ar su? Kuma haka suke so su bawa d'an shaye-shaye auren yarinyar su,? Ko sun mata ni d'an iska ne,? Koda yake koma dai meye tasha zaman ni nikam bana son ta balle auren ta".

"Zaid! Ya kamata ka iya bakin ka akan y'an uwana, me suka tare maka har haka ne wai? Ko wanne lokaci zancen ka basa son ka yaushe kasan basa san naka,? Ka shiga hankalin ka ka daina fad'a musu duk abinda kaga dama a gaba na zan b'ata rai a kan hakan wallahi." "Okay sorry, but ka sanar dasu bana son y'ar? su bazan kuma aure ta ba, in suka yi gangancin aura min ita kuma...." ya k'arasa fad'a yana girgiza kai, yana fad'ar hakan ya mik'e kawai ya nufi saman sa da sauri.

Washe gari da wuri Zaid ya shirya ya tafi Company sabida meeting d'in da zasuyi shida company sarrafa talamin da yake Malaysia mai suna vinci, tunda ya fita bai dawo ba sai bayan azahar ya dawo gidan a gajiye jikin sa kamar an masa duka haka yake ji sabida gajiya.

Saman sa ya hau yayi wanka ya kwanta yana lumshe ido cikin gajiya, wayar sace tayi k'ara ya d'auka ya kara a kunne tare da fad'in, "Ya akayi?". "Mai gida batu ne akan Ibteesam." "Waye haka?". "Yarinyar nan da take Kaduna'". "Oh wani abun ne?". "Mai gida Gaye yana can kasan kuma halin sa ganin baka nan tsaf zai iya farwa yarinyar nan dan ba imani gare shi ba." Tab'e baki yayi ya d'an ja tsaki yace, "so what? Ba sai ya nuna mata halin y'an iska ba." "Amma mai gida kai da kanka kace zakayi mata hukunci ai bai kamata ace wani daban bane zai aikata." "Okay Wizzy zan san abinda za'ayi yanzu na gaji da yawa" yana gama fad'ar hakan kawai ya kashe wayar ya ajjiye akan gadon yana kulle idon sa.

Haka ya k'araci wunin sa a sama gabad'aya ya manta da wani batun Ibteesam sabgar sa kawai yake yi.

Washe gari ta kama ranar talata da wuri ya sakko haka kawai yaji yana san sakkowa da wuri, kitchen ya shiga dan sha'awar cin noodles yake yi, baya jiran azo ayi masa girki indai yaso ci da kansa zai dafa, d'ora ruwa a tukunya yayi ya fara dafa indomie cikin k'warewa, magana yake jiyowa sama-sama daga cikin store hakan ya saka ya tsaya da aikin cak ya k'arasa bakin k'ofar store din ya tsaya yana jiyo abinda ake fad'a.

"Na Fad'a muku yaron nan baya cin abinci na sam wallahi na rasa yadda zan masa amma zan saka mahaifin sa ya bashi lemon dan naga yana san zob'o? sau da dama ina gani yana siyowa, in na bawa uban nace ya bashi zai bashi wata k'ila yasha" shiru tayi alamun tana sauraron me ake ce mata kafin ta cigaba da fad'in, "Mu gama da yaron tukkuna ta uban mai sauk'i ce kawar dashi daga duniya bazai yi mana wahala ba kamar yadda aka kawar da matar sa shima haka za'a kawar dashi" dariya tayi sosai kafin tace, "ahh to dole ai sai mun dage mu gama dasu suma su bi bayan Maryam d'in" ta fad'a tana murd'a handle d'in k'ofar ta fito tana cigaba da dariya.

Abinda ta gani ya kusa saka ta sakin fitsari a wando jikin ta ya soma rawa tana zare ido irin na marasa gaskiya, ta bud'e baki zatayi magana kawai taji saukar mari a kumatun ta, sai da ta tafi hutun wucin gadi sabida yadda marin ya ratsa ta kafin ta dawo hayyacin ta ta d'ago dak'yar ta kalle shi ya kuma marin ta a d'aya b'angaren.

Ihu tayi mai k'arfi tana tsalle a wajan kamar yarinya k'arama ta fashe da kukan azaba, noodles d'in da take kan wuta ya d'auki tunkuyar a fusace ya watso mata akayi sa'a tayi saurin sunkuyawa noodles d'in ta zube a k'asa tunkuyar ta daki k'ofar store d'in ta fad'i k'asa a dai-dai lokacin da Daddy ya shigo kitchen d'in, kafin Zaid yayi wata magana Daddy ya d'auke shi da maruka guda biyu zafafa kafin ya dawo dai-dai yace, "Amina a matsayi na na mijin ki ina baki umarnin ki tashi ki mari Zaid". Jikin ta har b'ari yake sabida ciwon kan da ya saukar mata lokaci d'aya, "ba magana nake miki ba?". Daddy ya fad'a a fusace yana kallan ta, aikam bata raga ba tana mik'ewa ta d'auke Zaid da mari ta koma bayan Daddy ta tsaya dan taga alama tsaf zai iya naushin ta.

"Zaid tsuguna ka bata hak'uri.". D'ago jar fuskar sa yayi ya kalle shi da jajayen idon sa bakin sa na rawa alamun yana so yayi magana, "Ba maganar ka nake so ba Zaid in dai ni na haife ka ka d'urkusa ka bata hak'uri".

Jikin sa na rawa ya d'an rage tsaho kad'an yana wani irin numfashi kamar numfashi k'arshe yace, "Sorry" abinda ya iya furtawa kenan ya mik'e a fusace ya daki glass din jikin oven ya tarwatse a kitchen d'in ya yanke shi a hannu, k'ofar baya ta kitchen d'in kawai ya bud'e ya fita, Saman sa ya haura ya d'auki wayar sa da key d'in motar sa ya sakko ya shiga mota ya jata da k'arfi ji kake k'iiiiiiiiii? ya fice daga gidan da gudun gaske.


_free pages dai basu da yawa ki biya kud'i k'alilan ki karanta labarin cikin kwanciyar hankali da nishad'i, naira 100 ne kacal ba tsada kamar ruwan pure water, tuntub'i wannan number domin biya but only WhatsApp +2347045242700_



Comments Share fisabinillah =?O?d'?>?p?
*g& ?ASAITAR SO! g&*

?
? ? ? ? ? ? ? ? ?? ?? *Nana Haleema*

*15?'?16*

A fusace Daddy ya juya ya bar kitchen d'in cikin fushi da takaici, duk da irin tashin hankali da tsoro da Amina take ciki sai da tayi wani juyin farin ciki har taso zamewa da noodles da Zaid ya watso mata, "Harira!" Ta fad'a cikin d'aga murya tana kallan k'ofar kitchen d'in da zata kaika harabar gidan, da gudu wacce aka kira da Harira ta shigo tana fad'in, "Gani Hajiya." "Zo ki gyara wajan nan" tana fad'ar haka ta fita da sauri ta nufi d'akin Daddy da saurin ta.

A zaune ta ganshi a falon sa ya d'aga kai sama yana kallan ginin pop d'in dake falon, da sallama ta shigo ta tako a hankali zuwa inda yake ta zauna a kusa dashi ta rik'e hannun sa guda d'aya da duka hannayen ta tace, "an kammala breakfast". Shiru yayi bai amsa ba bai kuma kalle ta ba cikin sanyin murya tace, "Dan Allah kayi hak'uri ka cire komai a ranka addu'a zamu cigaba da yiwa Zaid sai kaga an wayi gari ya shiryu ya koma kamar bashi ba."

"Yaushe kenan Amina? Gobe? Jibi? Ko kuma gata,? Allah ya sani lamarin Zaid ya fara bani tsoro wallahi, marin kifa yayi mari fa, tunda har ya iya d'aga hannu ya mare ki nima wata rana zai iya duka na, ni na fara tantama anya wannan ciwon kan da yake damun Zaid bai yi affecting d'in brain din sa ba kuwa Amina?" Daddy ya fad'a yana fuskantar ta jikin sa a sanyaye haka ma muryar sa.

"Haba Daddyn Zaid da kanka kake fad'ar wannan kalma ta tab'in hankali ga Zaid? Wannan sam bai kamata a ji maganar nan daga bakin ka ba, kai in kace haka to su kuma mak'iyan ka suce mene?."

Ajiyar Zuciya Daddy yayi yace, "Amina Zaid shine kad'ai d'an dana mallaka a duniya bayan shi bani da wani, meyasa bazai kalle ki a matsayin uwa ba tund shi tashi bata duniya,? Ranar nan ya watsa miki miya a jiki in badan Allah ya tak'aita ba da ya k'ona miki jikin ki, yau ya mare ki ya kuma so ya k'ona ki d'in again akan me duka yake aikata wannan banzayen halayyar tasa,? Amina shi kad'ai ne mai zuciya ne a duniya? Ko shi kad'ai ne me saurin fushi,? Dukkanin mu muna dasu wata k'ila namu yafi nasa amma banbancin mu dashi muna sarrafa namu amma shi baya iya sarrafa fushin sa da b'acin ransa a kan kowa da komai, anya rayuwa zata yu a haka? Tunda har ya iya aikata miki haka a matsayin ki na matata uwa a gare shi nima zai iya yi min wata rana, ki duba abinda ya yiwa su Yaya babba kwanaki, a gani na ko bai kalle su da matsayin su na iyayen sa ba ai ya kamata ya kalle su matsayin wanda suka haifi kamar sa, Yana da buk'atar ganin Psychiatrist dan gaskiya ban aminta da lafiyar sa ba yanzu."

Shiru Amina tayi har sai da ya kai k'arshe maganar sa kafin tace, "Akwai halitta wacce Allah yaka yiwa bawan sa ba sai tab'in hankali ko matsalar k'wakwalwa ba, Zaid yana daga cikin wanda Allah ya halitta a haka, ka daina zancen tab'in hankali ko rashin lafiyar k'wakwalwa a gare shi sabida kai mahaifin sane bakin ka yana da kaifin gaske a kansa yanzu sai hasashen ka ya zama gaskiya a kansa kuma azo hankali ya tashi ana da an sani,? babu abinda yake damun Zaid sai zallar zuciya da fushi da yake dasu kuma ta bakin ka indai baya sarrafa su tabbas wata rana zasu kai shi su baro shi, kuma duka wannan abun nasa dan bashi da wanda zai dinga d'ebe masa kewa ne kullum shi kad'ai yake rayuwa dole fushin sa ya dinga gaba, ka dinga taya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login