Showing 15001 words to 18000 words out of 171073 words

Chapter 6 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7820

hankali, "me zakayi min to?" Ta tambaya tana kuka tare da toshe bakin ta, banza yayi mata bai amsa ba sai tsayawa cak da yayi kawai yana kallan ta cikin tsana da jin haushi, "wayyo Allah dan Allah kar ka min komai na rok'e ka!" Ta fad'a cikin ihu tana sake mak'alewa a bango.

Hannu biyu ya saka ya dafe kunnen sa yace, "shiiiiii" ya fad'a da k'arfi yana runtse idon sa, Hannu ta saka ta toshe bakin ta tana girgiza kai tana cigaba da zubar da hawaye, "ban d'auka zaki bada hak'uri haka da wuri ba ai na d'auka baza kiji tsoron d'an iska d'an shaye-shaye ba" ya fad'a muryar sa a ciki yana cigaba da nufo ta, "Kayi hak'uri dan Allah kar ka min komai kaji?". D'an lumshe ido yayi ya bud'e yace, "Babu abinda zan miki kawai kema zan mayar dake y'ar iska ne kamat." Hannu ta d'ora a ka ta zaro ido waje tace, "Na matsayin Annabi kayi hak'uri wallahi ni ba y'ar iska bace."
"Ni kuma kinga d'an iska ne dan haka daga yau ki fara lissafa kanki a matsayin karuwa dan baza ki bar gidan nan ba sai na mayar dake karuwa mai lasisi" ya fad'a da tsawa b'acin ran sa yana k'ara k'aruwa tsanar ta kuwa kamar zuba masa ita ake yi a zuciyar sa, ji yake kamar ya shak'e ta ta bar duniya.

Cikin tsoro da tashin hankali da fargaba tace, "Kayi hak'uri dan Allah, kuma wallahi ina da ciwon HIV kar na goga maka" ta fad'a tana masa wani irin kallo mai nuni da zaka yiwa kanka, duk da b'acin ran da yake ciki sai da yayi murmushin gefen baki ya kalle ta ganin wai shi zata yiwa wayo, d'age gira d'aya sama yana kallan ta tare da tab'e baki yace, " kar ki damu ke kina da HIV ni kuma ina da condom so ba wani abun d'aga hankali bane" ya fad'a yana nufar ta gadan-gadan ganin yadda ya nufo ta ya saka ta saki wata gigitacciyar k'ara.


_*free pages dai basu da yawa ki biya kud'i k'alilan ki karanta labarin cikin kwanciyar hankali da nishad'i, naira 100 ne kacal ba tsada kamar ruwan pure water, tuntub'i wannan number domin biya but only WhatsApp +2347045242700*_

Comments and fisabinillah d'?=?O?>?p?
*g& ?ASAITAR SO!?g&*

? ? ? ? ? ? ? ?? *Nana Haleema*

*11?'?12*

"Shut up!" Ya fad'a a fircgice yana dafe kansa da duka hannayen sa sabida k'arar da tayi ba k'aramin shigar masa kai tayi ba, d'an yatsa d'aya ya d'aga mata ya karkad'a shi alamun a'a yana runtse idon sa, tsawar da yayi mata itace ta firgita ta sake rud'ewa ta mak'ale a jikin d'akin jikin ta na wani irin rawa, Juyawa yayi ya fita daga d'akin yana wani irin dafe kai jiri yana d'aukar sa kamar zai kifa yana hake tafiya, d'aki ya shiga ya fad'a kan gado yana wani irin juyi kansa na barazanar barin gangar jikin sa.

Lokaci d'aya jikin sa ya fara wani irin rawa hatta katifar da yake kai motswa take sabida yadda jikin sa yake yi, "Mai gida" Wizzy ya fad'a lokacin da yake shigowa d'akin da gudun gaske, "mai gida lafiya?". Da hannu yake nuna masa jakar sa da yazo da ita, ai da sauri ya nufi inda yake masa nunin ya d'auko jakar ya kawo masa kusa da ita, da hannu yayi masa alama da ya bud'e jakar hannu na rawa ya bud'e Zaid ya tura hannun sa ciki ya kwaso maganin sa, karb'a Wizzy yayi ya b'alla masa ya bashi ya zuba a baki ya bashi ruwa, dak'yar ya had'd'iye yana lumshe ido bacci ya d'auke shi.

A fusace Wizzy ya mik'e ya nufi d'akin da Ibteesam ya banka k'ofar rai a b'ace, tana takure a inda take har lokacin jikin ta bai bar rawa ba ya nuna ta da yatsa yace, "In kika kuma yi mana k'ara ko ihu a gidan nan sai na kashe ki har lahira, an fad'a miki nan gidan dambe ne ko kuma club da zaki zo kina cika mana kunne da ihu,? Ki shiga hankalin ki wallahi ki kula da duk abinda zakiyi kamar yadda zan kashe kiyashi haka zan kashe ki, shashasha mara hankali" ya fad'a yana jan k'ofar da k'arfi.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku na lalace ni Maryam, na jawo kaina bala'in da ban san k'arshen sa ba, ya Allah ina rok'on ka ka kub'utar dani daga hannun wad'an nan mutanen, ya Allah kada ka basu ikon cin galaba a kaina" ta k'arasa fad'a cikin kuka mai sauti, Sai da tayi kukan ta san ranta kafin ta koma sauke ajiyar zuciya ga yunwar da take d'awainiya da ita amma ta kasa cin abincin sabida rashin kwanciyar hankali da take ciki,tana zaune tana sak'a da warwara har bacci ya d'auke ta.

Tun k'arfe hud'u na asuba ta farka sabida yunwar da take ji dole ta tashi ta wanke bakin ta ta dawo ta fara cin abincin da aka kawo mata a daren, kamar za'a kwace mata abincin haka take ci sai da ta kusa cinyewa sannan ta sha ruwa ta koma gefe ta zauna cikin ta na wani irin k'ullewa, tana zaune har akayi kiran assalatu ta mik'e ta d'auro alwala ta dawo ta tayar da raka'ataul fijir, bata jima da idarwa ba aka tayar da sallah a masallacin da take jiyowa ta bi jam'i.

Tunda ta idar da sallar take ta d'ora kukan ta daga inda ta tsaya, babu wanda yake hangowa a idon ta sai Umman ta, ko waye yake mata aiki yanzu oho, sai ta sake fashewa da kuka, gari ya fara haske tana zaune a inda take kamar wacce aka tsikara da allura ta mik'e ta yaye labulen da yake d'akin akayi sa'a kuwa tagar da take d'akin ana hangon harabar gidan, kallan harabar gidan take babu kowa sai motocin da suke ajjiye a wajan sai sautin tsuntsaye da suke tashi a hankali, da azama ta juya ta nufi k'ofa da sauri ta bud'e ta fito falon, nan ma babu kowa sai duhu amma kana ganin gaban ka sai dai ba sosai ba, a hankali take tafiya har tazo steps d'in ta fara sauka a hankali har ta sauka falon da yake k'asan, kalle-kalle take tana tunanin wacce k'ofar zata bud'e ta sada ta da harabar gidan? Wacce take kallan ta kawai ta tunkara ta murd'a lock d'in ya bada sautin k'uttt ta murd'a handle d'in ta bud'e k'ofar, wani farin ciki ne ya ratsa ta ganin k'ofar ta bud'e ai da sauri ta sauka daga steps d'in dake k'ofar falon ta fita harabar gidan tare nufar gate din gadan-gadan dan burin ta a lokacin bai wuce ta bar gidan ba.

Har ta k'arasa gate din babu motsin kowa a gidan sai ita kad'ai hakan ya sake bata k'arfin guiwa ta isa inda gate d'in yake, a hankali take kai hannun ta ga lock d'in jikin gate d'in kamar mai jin tsoron wani abu a jikin gate d'in,tana d'ora hannun ta da niyar bud'ewa taji anyi sama da ita an cillar da ita can gefe kamar an cillar da kayan wanki kanta ya bugu da bayan mota, "washhh" ta furta dan ta bugu sosai ga wani irin zirr zirrr da take ji tun daga kanta har yatsun k'afar ta, hannun ta ta kalla da yayi sanyi yana wani iri kamar ba a jikin ta yake ba.

Zaid yana tsaye a jikin window hannun sa rik'e da cup yana kurb'ar coffee yana kallan ta, ganin yadda shocking d'in jikin k'ofar ya wancakalar da ita gefe ya saka shi wani d'an murmushi hakan ya saka ya saki fuska duk da baiyi murmushin ba amma fuskar sa ta saki, ajjiye cup d'in yayi kana ya fito daga d'akin ya sakko k'asan.

Ibteesam kuwa tana nan kwance jikin ta yayi wani irin sanyi bata da kuzarin da zata iya mik'ewa bata tare da tsanmani ba taji saukar maruka lokaci d'aya a fuskar ta, gigicewa tayi zata saki ihu ya saka k'afa ya take mata baki yana zaro mata idanuwan sa, ba k'aramin tsorata tayi ba ganin yayi mata tsayi sosai gashi babu abinda take gani sai hasken idanuwan sa da ya zaro su yana mata kallan gargad'i, d'auke k'afar yayi daga kan bakin ta ya tsuguna kusa da ita yana kallan fuskar ta da shatin marukan suka fito rad'au a farar fatar ta yace, "kina tunanin zaki iya barin gidan nan?, Huhhh kima ajjiye wannan tunanin tun kafindare yayi miki dan kin shigo kenan, in ma zaki fita yadda kika shigo ba tare da kin sani ba haka zaki fita." abinda ya kenan ya mik'e tsaye yana k'are mata kallo tun daga sama har k'asa.

kawar da kai tayi daga kallan sa ganin daga shi dai gajeran wando wanda ko guiwa bai zo ba sai farar vest wacce ta kama masa jiki sosai, hannun ta ya damk'a ya jawo ta da k'arfin tsiya ta mik'e tsaye tana layi kamar wacce tasha wani abun da zai saka ta maye, ganin yanayin da take ya saka kawai ya saki hannun nata ta koma da baya ta fad'i ba tare da ta shiryawa hakan ba, "Hasbunallahu wani'imal wakil" ta furta tana runtse ido dan k'ugun ta ya bugu sosai.

Banzan kallo ya watsa mata tare da jan dogon tsaki yace, "na baki 30 seconds ki tabbatar kin shigo cikin gidan nan" ya juya yana tafiyar izzah ba tare da ya sake kallan ta ya koma cikin gidan, dak'yar ta samu ta mik'e tsaye tana dafe bayan ta dan ta bugu iya buguwa daurewa kawai tayi tana tafiya, a haka ta koma falon ta baje a kan kujera tana kuka mara sauti.

Wizzy da ya fito daga d'akin da yake matsayin nasa ya ganta a kwance tana kuka shima ya tamke fuska yace, "Keee tashi ki koma inda kika fito kar na sake ganin ki a k'asan nan" ya fad'a cikin fad'a kamar zai zo ya dake ta, haka ta lallab'a ta mik'e ta koma saman ta zube a d'akin.

Bata san adadin lokacin da ta take a kwance akan tiles d'in ba sai bud'e k'ofar da akayi ne ya saka ta Mike dak'yar tana kallan mai shigowa, Zaid ne ya shigo ya shirya tsaf cikin k'ananun kaya yana taunar cingom yana wani irin shan khamshi kamar mace, ledar da ya shigo da ita jiya ya kalla tana nan da alama yadda ya ajjiye ta ba'a tab'a ba, d'aukar ledar yayi ya k'arasa inda take ya jefa mata a fuska cikin muryar sa da take a tausashe yace, "duk wani abu da mace zata nema akwai shi a ciki" ya fad'a yana niyar juyawa ya fita.

"Dan Allah dan Annabin rahama dan darajar iyayen ka malam ka sallame ni na tafi gida nayi maka alqawarin bazan sake yi wa wani rashin kunya bama balle kai" tsabar kuka muryar ta ta? dashe sai kad'an ake ji a haka take rok'on sa, "Gida! Kina so ki koma gida ne?". Da sauri ta d'aga masa kai dan yadda taji yayi maganar a hankali ta d'auka ya hak'ura ne, "good, get ready to be my prostitute ni kuma nayi miki alqawarin komawa gida har da tsarabar baby ma" ya fad'a yana kallan fuskar ta da tayi ja tare da d'age girar sa sama yana sake had'e rai.

"Kayi hak'uri na fad'a maka wallahi ni ba y'ar iska bace ban tab'a iskanci ba ban san ya ake yi ba kayi hak'uri kar ka lalata min rayuwa". Sai da ya kalle ta ya tab'e baki tsanar ta na sake huda tsokar sa yace, "Don't worry duka zan koya miki ko kin manta ni d'an iskan ne?". Girgiza kai tayi tace, "A'a kaima ba shi bane kayi hak'uri."? D'an runtse ido yayi bai cika son doguwar magana ba ya bud'e idon yace, "Kar kiga jiya na kyale ki ki d'auka ko zan k'yale ki d'in ne gabad'aya, u have to know inda maradin na mayar dake y'ar iska na rana d'aya ne baza ki kwana biyu a gidan nan ba tare da na aikata hakan ba, butt ni karuwa nake so ki koma y'ar iska kama ta kinga munyi 50-50 nida ke the same." Ta bud'e baki zatayi magana yayi saurin d'aga mata hannu ya bud'e k'ofar ya fice daga d'akin.

Komawa tayi ta kwanta a wajan tana cigaba da goge hawaye, tun tana tunanin har bacci ya d'auke ta.

Bata farka ba sai k'arfe goma na safe jikin ta duk yayi tsami haka ta mik'e ta fad'a band'aki tayi wanka ta fito tana kallan kayan da ya bata, mamaki take ganin hatta undies akwai kuma size d'inta sai taji tsoron kodai sun gama kalle tane lokacin da suka kawo ta gidan, haka take shiryawa cikin sanyin jiki da tunani har ta gama shiryawa tsaff ta mayar da sauran cikin ledar.

Wani tunani ne ya d'arsu? a ranta jin k'arar tv da ta jiyo a falon ta mik'e dak'yar hannun ta yana bayan ta sabida mugun ciwon da yake mata ta bud'e k'ofar ta fito, yana zaune akan d'aya daga cikin kujerun yana danna laptop da alama aiki yake mai mahimmaci dan kacakan hankalin sa yana kan screen d'in laptop d'in, a kan carpet ta zube guiwowin ta mik'e tare da had'e hannayen ta alamun rok'o tace, "Bawan Allah ban sanka ba sai a ranar da muka had'u ban tab'a ganin ka ba sai a ranar da abin ya faru, na rok'e ka dan darajar sunayen Allah kyawawa kayi hak'uri ka barni na tafi gida, ni nake yiwa Umma ta aiki k'anwata kuma tana da stickler nice nake komai a gidan dan Allah kayi hak'uri kayi min ko wanne irin hukunci ne indai zaka barni na tafi amma banda hukuncin da kake fad'a" ta k'arasa fad'a hawaye na sakkowa daga idon ta. Kamar bai san Allah ya halicci wata halitta a wajan ba ya cigaba da aikin sa yana yi yana joting a takarda bai ko kalle ta ba balle ya amsa mata, "Dan Allah in kana k'aunar iyayen ka" ta sake fad'a jin da tayi yayi shiru.

Nan ma bai kalle ta ba ya cigaba da aikin sa kamar ma bai san abinda take yi ba, ganin hakan ya saka ta zauna ta cusa kanta cikin guiwowin ta tana kuka mara sauti, cigaba da aikin sa yayi har ya kammala ya rufe laptop d'in ya d'auka tare da mik'ewa yana shirin barin wajan, da sauri ta d'ago ta watsa masa wani banzan kallo tace, "Anya kai musulmi ne kuwa? Dan banga danshin imani da tausayi a tare da kai ba duk yadda akayi baka san Allah ba, na had'a ka da Allah na had'a ka da Annabin rahama na had'a ka da iyayen ka amma kayi burus dani, to kayi duk abinda zakayi kuma baza ka tab'a cimma burin ka a kaina ba sabida Allah bazai baka ikon keta min haddi ba dan ni ba y'ar iska bace irin ka" mik'ewa tsaye tayi ta cigaba da fad'in, "Na fad'a d'an iska ke kai d'an shaye-shaye wanda bai san darajar Allah da Annabi ba, mtswww ka barni a nan kar ka sallame ni har a tashi qiyama in ma ka tashi yi min hukunci ka kashe ni kar ka barni rai aikin banza aik....." ai bata kai ga k'arasawa bakin ya rufe gam kwakwalwar ta ta d'auke diff ta daina gane fari da bak'i, ta rasa gane a ina take a lokacin sabida tsabar gigicewa da tsananin azaba.

Wani irin wuci yake hannun sa yana rik'e da wuyan ta ya shak'e ta idon ta ya firfito shima haka nasa, cillar da ita yayi gefe kanta ya bugu da gefen kujera ya bada sautin kummm, belt d'in jikin sa ya kwance ya nad'e ta a hannun sa ya nufe ta kamar zakin da aka kwanto daga cikin keji.


*_free pages dai basu da yawa ki biya kud'i k'alilan ki karanta labarin cikin kwanciyar hankali da nishad'i, naira 100 ne kacal ba tsada kamar ruwan pure water, tuntub'i wannan number domin biya but only WhatsApp +2347045242700*_


Comments and share fisabinillah =?O?>?p?d'?
*g& ?ASAITAR SO! g&*

? ? ? ? ? ? ?? ?? *Nana Haleema*

*13?'?14*



Kamar daga sama aka aiko shi haka yake dukan ta da belt tana ihu, jin kuka da ihun yayi yawa a guje Wizzy ya hauro saman ganin irin dukan da yake mata yayi saurin rik'e shi yana fad'in, "Mai gida kayi hak'uri Allah ya wuci zuciyar ka". Fincike jikin sa yayi daga rik'o da yayi masa ya kalle ta da jajayen idon sa ya nuna ta da yatsa alamun last warning ya cillar da belt d'in a wajan ya fad'a d'aki yana layi kamar wanda ya bugu da kayan maye.

Kuka take sosai fatan jikin ta duk ta tashi gefen wuyan ta ya fashe sabida dukan da ta sha, Wizzy bai tab'a tausaya mata ba sai a lokacin ya tsuguna a gaban ta yace, "Kinga in zaki nutsu ki daina masa rashin kunya gwara ki nutsu in ba haka ba wallahi zai kashe ki kuma ya kashe banza, duk zafin kanki ya dama ki ya shanye, ki kula da abinda yace miki baya so in ba haka ba wallahi a nan za'ayi jana'izar ki a binne iyayen ki basu ga gawar ki ba, ya wuce inda kike tunani duk inda kike kaishi ya wuce wajan, ina baki shawara a matsayin na na wanda nasan halin sa in kuma kina ganin yi masa rashin kunya shi zai saka ya k'yale ki sai ki cigaba ki gani, malama ki tashi ki koma inda ya ajjiye ki kisha magani in kuma ya fito ya ganki tsaf zai k'ara jibgar ki" Wizzy yana gama fad'a mata hakan ya sauka daga saman gabad'aya dan wannan lokacin bana yiwa Mai gida magana bane ba.

Da rarrafe take jan jikin ta zuwa d'akin da take tana shiga ta kulle k'ofar ta baje a bakin k'ofar daga cikin tana cigaba da kukan ta, ko wanne b'angare na jikin ta ciwo yake mata tun daga fatar jikin nata har cikin k'ashin ta ciwo take ji, tunda take ba'a tab'a yi mata irin wannan dukan ba kamar za'a kashe ta shiyasa nake ji kamar an tsamo ta daga wuta, runtse ido tayi tana kallo fuskar Umman ta da Abba cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login