Showing 51001 words to 54000 words out of 171073 words

Chapter 18 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7813

bud'e baki yayi yana kallon sa da mamakin abinda yace, "Au bama kasan abinda kayi ba?" Hajiya Batula ta fad'a a fusace tana kallan sa.

Bai amsa mata ba dan bata kai ya bata amsa sai ya mayar da kallon sa ga Daddy yace, "Daddy ina da abinda zanyi fa" ya fad'a bayan ya zuba hannu a aljihu, "Haba Zaid ka yi k'okarin karyawa yarinya hannu kuma a tambaye? ka kace me kayi?." "Au wai daman bata k'arye ba? Damn it, naso na b'alla mata k'asusuwan hannun ta yadda baza ta kuma moruwa ba balle tazo inda nake" ya fad'a yana kallon Anty Amina da tayi maganar tana watsa mata banzan kallon da ya saka bin ta dashi.

"Wallahi da kotu ce zata raba mu da kai dan baka isa ka wulaqanta min y'a ka zauna lafiya ba, dan ma ka samu ta aure ka? Wacce mace ce zata aure ka da wad'an nan banzayen halayen naka,? Dan ta taimaka maka ta rufa maka asiri shine ka samu bakin magana har haka?" Hajiya Batula ta fad'a lokacin da ta mik'e tsaye.

Kallan up and down yake yiwa matar cikin kask'anci da wulaqanci ya d'ago idanun sa yace, "Inda nasan ban b'alla ta ba wallahi sai nayi mata illar da ko ke baza ki gane ta ba, ai na fad'a mata kar ta sake zuwa inda nake amma bata ji ba ita ga karuwa wacce ta saba bin maza baza ta iya zama babu namiji ba shiyasa take kwaso k'afa da wani yamushshen jikin ta tazo inda nake a ganin ta ni mate d'in ta,? A yanzu ma ba k'yale ta nayi ba yadda nace sai na b'alla ta tabbas saina karya mata hannu in yaso ki kaini inda yafi kotu ba kotu ba kinji?" Ya fad'a yana zaro mata manyan idon sa yana kallon ta yana kad'a mata eyelashes d'in sa masu tsaho.

"Ni kake fad'awa wannan maganar Zaid?". "Na Fad'a miki wacece ke d'in? Uwa ta? Ki kuma iya bakin ki akan zancen wai taimaka min y'ar ki tayi, ai bara kiji kaff duniyar nan babu macen da zata ce ta taimaka min balle wannan kod'ad'iyar y'ar taki mai zubin almajirai, in kuma kina so nasan kinji haushin abinda na yiwa y'ar ki dan Allah ki rok'i alfarma a wajan Dad kice na sake ta kiga aiki da cikawa" ya fad'a yana jan kujerar dining ya zauna dan kansa ya fara juyawa.

Ai a fusace tayo kansa zata mare shi Anty Amina tayi saurin tare mata hanya tace, "kiyi hak'uri ki taushi zuciyar ki" ta fad'a tana dafa kafad'ar ta, "ki k'yale ni na mari shegen yaron can da yake kallon ido na yana fad'a min wad'an nan kalaman dan bashi da kunya bashi da tarbiyya."

"In kika sake kuskuren cemin shege wallahi tallahi sai na b'arar dake a wajan nan kinji kuma na rantse baza ki saka ni kaffara ba, rashin tarbiyya kuma ya biyo bayan ahlin ki" ya fad'a yana nuna ta da yatsa.

"Abubakar kana kallon abinda d'an ka yake min ka kasa hana shi sai zuba masa ido da kayi? Kenan ya fad'a min duk abinda yake so ko?" Ta fad'a tana kallon Daddy da ya zubawa Zaid ido cikin zallar b'acin rai da k'unar zuciya, "Mama dan Allah kiyi hak'uri kizo ki zauna" Eman ta fad'a a inda take a zaune.

Kallon da yaga Daddyn sa yana yi masa ya saka shi saurin mik'ewa dan yasan yanzu zaice ya bata hak'uri shi kuma da ya bata hak'uri gwara ya saka an masa duka da k'arfe babu riga a jikin sa, banzar harara ya watsa mata yayi hayewar sa sama a guje, sai a lokacin Daddy ya lura ya fara k'wala masa kira amma ina har ya k'ulle k'ofar sa.

Mayar da kai Daddy yayi ya sunkuyar wani abu mai kama da kunya da takaici yana shiga jikin sa ya kasa d'agowaya had'a ido da kowa na parlourn. "lallai ta tabbata d'an ka ya raina ka tunda gashi ka kasa komai duk irin d'ibar albarkar da yayi min, yafi k'arfin ka kamar yadda ake fad'a ban tabbatar ba sai yau, shikenan ni zan ramawa kaina nayi alqawarin sai ya d'urkusa ya bani hak'uri" ta fad'a tana ficikar jakar ta ta bar falon a fusace.

Kuka Eman take yi sosai dan taji haushin abinda ya yiwa Maman ta ta wani b'angaren kuma bata fargabar a rabata da Zaid dan tana son sa har zuciyar ta, mik'ewa tayi ta bar falon tana share hawaye kalaman da ya fad'awa Maman ta suna dawo mata.

Falon ya rage daga Daddy sai Anty Amina da ta ke zaune kusa dashi, shiru falon yayi babu abinda ake ji sai sautin tv kad'an-kad'an, ajiyar zuciya Daddy kawai yake saukewa kana kallon sa kasan yana cikin b'acin rai sosai da damuwa sosai, ruwan sanyi Amina ta tashi ta d'auko masa ta mik'a masa, karb'a yayi ya ajjiye a gefe ya juyo yana kallon ta yace, "Amina Abdullah, ya zanyi dashi ne? Me zan yiwa Abdullah Amina,? Nayi fad'an nayi nasihar amma duka a banza, kowa gani yake bana iya yi masa fad'a sabida shine kad'ai wanda na mallaka a duniya tunda a gaban su zan masa magana yak'i ji, ina jin wani irin zafi a raina Amina in Zaid yana nuna irin wad'an nan halayen nasa" ya k'arasa fad'a kamar wanda yake shirin yin kuka.

Ajiyar Zuciya Amina tayi ta kalle shi tace, "Addu'a ita kad'ai zata canja Abdallah, ko anje saudia yanzu ka mayar da hankalin ka a kan Allah ya sassauta masa wannan zuciyar tasa, sannan Allah ya bashi wacce zata dinga nuna masa dai-dai da ba dai-dai ba in akayi haka Abdullah zai dawo kamar yadda kake so insha Allah."

"Sam baya jin tsoron b'ata min rai a gaban kowa, me y'an uwa na suka tare masa da har baya iya b'oye tsanar da yake musu a gaban kowa ne,? Me suka tare masa? Da anyi magana yace basa son sa ya akayi ya san masa son sa,? Shin baya tunanin ko bana da rai sune wanda zai kalla a matsayin iyayen sa ne? Shin baya tunanin komai lalacewar naka naka bane Amina? A ina Zaid ya gado wannan bak'ar zuciyar da rashin hak'urin nan,? Nidai ba haka nake ba haka mahaifiyar sa sanyin hali gare ta fad'a baya had'a ta da kowa balle har ta kai ga fad'a musu magana, Allah ya sani na fara gajiya da halayyar Zaid" ya fad'a yana dafe kansa.

"Ka manta Allah yana halittar bawan sa a duk yadda yaso a kuma duk yanayin da yaso,? Ai ba sai lallai halayyar ku tazo d'aya ba shi haka Allah yayi niyar halittar sa, matsalar Zaid d'aya ce shine baya sarrafa fushin sa a kan komai haka baya bari harshen sa ya tauna magana kafin ya furta ta daga zuciyar sa ta gaya masa baya jiran komai zai furta, baya sarrafa komai da kwakwalwar sa da zuciya yake aiki, bashi da hak'uri ko kad'an haka bashi da tsoro ko kad'an, wad'an nan halayen nasa zai d'an yayyafawa ruwan sanyi suyi k'asa matuk'ar hakan ta kasance wallahi sai kafi kowa farin ciki a duniyar nan" ta k'arasa fad'a cikin sanyin murya.

D'an murmushi kawai yayi yace, "Allah ya biye bakin ki, amma bana fatan abinda yake cikin ki ya d'auko abu d'aya daga cikin halayyar Zaid, Allah yasa ya zama me sanyi da hak'uri kamar ki". Itama d'an murmushin tayi tace, "Amin, yanzu ka tashi muje ka kwanta dare yna sake yi" bai musu ba ya mik'e zuciyar sa fal tunani ya hau sama Amina na biye da bayan sa.



Hajiya Batula kuwa a fusace ta cewa drivern ta, "Kai kaini gidan Hajiya Lubabatu". Ya amsa da to ya juya motar sa zuwa gidan Hajiya Lubabatu, da yake babu wani nisa sosai daga gidan su Zaid babu jimawa suka isa, yana parking ta futa a fusace ta shiga gidan da sallama, "Wa'alaiki salam, Hajiya Batula kece da daren nan?". "Bari kawai Hajiya Lubabatu dole ce ta saka hakan." Lubabatu tace, "To zauna muyi maganar". Zama tayi ta kalli y'ay'an ta da suke ta gaishe ta tace, "Lafiya lau yara na, kuyi hak'uri hankali na yana wani wajan daban, ku bamu waje yara na muyi magana". Ba musu suka mik'e gabad'ayan su suka shiga d'aya falon.

"Hajiya Batula lafiya na ganki a firgice haka?". "Bari kawai Luba ina cikin wani hali ne wallahi, yaron nan Zaid ya gotarwa Eman k'ashin hannun ta yanzu haka hannun yana can a d'aure, kinga rashin kunyar da yaron nan yayi min yanzu? Kinji maganganun da ya fad'a min kuwa" ta fad'a tana kallon Hajiya Luba.

"Ba kince min kawar dashi za'ayi ba?". "Eh hakan shine burin mu a kullum, amma a yau nayi alqawarin sai ya d'urkusa ya bani hak'uri dan haka so nake ki raka ni mu koma wajan mutumin nan ya bani abinda Eman zata mallake shi yaji duk duniya babu wacce yake so kamar ta, ni kuma sai nayi amfani da damar na saka ta wulaqanta shi ta yadda zai zo ya bani hak'uri yana kuka in yaso daga basa sai mu kawar dashi".

Dariya Hajiya Luba tayi tace, "Batula har yanzu kina nan da muguntar ki, hakan yayi abinda za'ayi kenan ki jira ni jibi zan zo muje dan kinga gobe ma mai gidan zai dawo ne da nazo munje goben." "Babu komai Luba Allah ya kaimu jibin, ni yanzu bara na wuce daman abinda nazo na sanar dake kenan" ta fad'a tana mik'ewa tsaye. "To shikenan ki gaida gida sai munyi waya" ta fad'a tana rako ta har bakin k'ofa kafin ta koma gida.



Washe gari.

Zaid bai sakko ba sai gab da azahar shima kuma dan zashi masallaci ne kuma yana so ya shiga company, saman Daddy ya nufa ya tura k'ofar a hankali ya shiga da sallama, amsawa Daddy yayi ba tare da ya kalle shi ba har ya nemi waje ya zauna, "Daddy ina wuni". Bai amsa ba yayi masa banza ya mayar da hankalin sa ga jaridar da yake karantawa, ganin hakan ya saka Zaid ya d'an gyara zama yace, "Dad I'm sorry" ya furta yana kallon carpet d'in falon.

Nan ma daddy baice komai ba ya cigaba da karanta jaridar sa, "Daddy kayi hak'uri" ya fad'a yana d'agowa ya kalli Daddyn nasa, "akan me kenan?" Daddy ya fad'a ba tare da ya kalle shi ba, "akan komai ma, Daddy babu yadda zanyi na canja kaina haka Allah yayi ni, Allah bai dasa min yin k'arya a zuciya ta ba duk abinda yake gaskiya shi nake fad'a hakan ya saka kalamai na suke yiwa mutane d'aci" ya k'arasa fad'a yana d'an yatsine fuska.

D'ago kai Daddy yayi ya kalle shi ya ajjiye jaridar hannun sa yace, "Zaid!". "Na'am Daddy". "Meyasa ka raina ni?". D'ago kai yayi suka had'a ido da Daddyn yace, "Daddy ya za'ayi na raina ka?." "To meyasa baka jin magana ta?". "Dad ina jin maganar ka mana duk abinda kace kar nayi bana yi". "Baka jin magana ta Abdullah inda kana ji baza ka dinga yin abinda kasan bana so kuma na hana ka ba." Shiru Zaid d'in yayi bai amsa ba Daddy ya cigaba da fad'in, "Zaid a gaba na kake yiwa y'an uwa na da matata duk abinda kaga dama ka fad'i duk abinda yazo bakin ka na hana ka kak'i ji ka cigaba a haka shine zakace kana jin magana ta?". "Daddy...." D'aga masa hannu yayi ya cigaba da fad'in, "Zaid ina son y'an uwa na kamar yadda kowa yake son y'an uwan sa, ina alfahari dasu kamar yadda kowa yake yi, bana so naga wanda zai ci musu mutunci a kaf duniya domin wanda ya zage su ni ya zaga dan abinda yayi su shi yayi ni, zan maka warning na k'arshe a kan yi musu rashin kunya da fad'a musu duk abinda kaga dama in kuma kak'i Zaid zanyi fushi dakai wanda baka tab'a ganin irin sa ba, ka girmama su kamar yadda zaka girmama ni, ka yi musu biyayya kamar ni, dan yau aka wayi gari akace bana duniya su zaka kalla ka nuna matsayin iyayen ka duk tarin tsanar da kayi musu, babu kai babu fad'a musu kalamai marasa dad'i daga yau, haka Amina ma." Shiru yayi yana sauraron Daddyn har ya kai k'arshe kana yace, "Daddy amma ita ai ta jiya ba y'ar uwar ka bace". Bud'e baki kawai Daddy yayi yana kallon sa kafin yace, "Amma matar baban yaya na ce ko?". "Eh itace, amma naga ita babu abinda ya had'a mu". "Yaya babba ya had'a mu tunda har ya aure ta, kai a yanzu sirika take a wajan ka tunda kana auren y'ar ta, na fad'a maka Zaid ya zama na k'arshe." "Toh Daddy" ya fad'a yana wani matse bakin sa.

"Sai batun matar ka Eman, zata koma b'angaren ka da zama da zarar ta samu sauk'i kafin na saka a gyara maka part d'in ka ku koma can". A razane ya kalli Daddy yace, "Daddy kayi min komai amma banda ka had'a ni waje d'aya da waccan yarinyar, wallahi Daddy na tsani na had'a ido da ita balle har mu zauna waje d'aya, ka taimake ni kayi hak'uri zuwa wani lokaci, in kuma aure kake so kaga nayi daman ina so nace maka aje gidan su Ibteesam ayi maganar aure tunda ita ina son ta" ya fad'a yana kallon Daddy kamar zaiyi kuka.

"Zaid bazan k'arbi wani uzuri daga wajan ka a akan maganar Eman ba abinda na yanke kenan da zarar ta samu lafiya zata dawo saman ka, ita kuma wancan har kun dai-dai kan ku ne?". Had'e rai yayi dan abinda Daddy yace akan Eman duk sai yaji komai ya fice masa a kai har maganar Ibteesam d'in sai kawai ya mik'e tsaye yace, "Shikenan ma dai, zan je company" daga haka kawai ya bar falon Daddy ya bishi da kallo.


Yana sauka k'asa masallaci ya shiga akayi sallar azahar dashi kafin ya fito, mota ya d'auka ya fita daga gidan, tuk'i yake amma gabad'aya hankalin sa baya wajan tuk'in yana wani wajan daban, gefee d'aya tunanin Ibteesam ne yake damun sa zuciyar sa sai azalzalar sa take a kai yaje gidan su wani b'angaren na zuciyar sa na hana shi yin hakan.

Yayi nisa da gida traffic ya rik'e shi a hanya yaja dogon tsaki ganin ya riga ya shiga tsakiya babu damar juyawa, yawan ac d'in motar ya k'ara yana sake sauke numfashi.

Wani mai napep ne ya kutso kusa da motar sa saura kad'an ya goge ta hakan ya saka ya d'aga kai yana kallan mai napep d'in duk da shi baya ganin sa, kamar ance ya kalli baya inda fasinjoji suke zama ya hango Ibteesam a zaune a bakin k'ofa ciki mace da namiji ne a zaune.

Bai san lokacin da ya dafe kai ya furta, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" sabida wani irin abu mai tsini da yaji ya soki zuciyar sa lokaci d'aya, ya sake kallon wajan ya tabbatarwa da kansa ita d'in ce ba wata ba, bai san lokacin da ya b'alle murfin motar ya fita ba.


*A rik'e amana dan Allah.*



*?ASAITAR SO!*

*35_36

Not edited>??



D'ago kan da Ibteesam zatayi ta ganshi a tsaye a jikin napep d'in ya zuba mata ido kawai yana kallon ta, gaban tane ya fad'i itama dan bata san yadda zasu kwashe dashi ba gashi a cikin jama'a tsaf zai dizga ta.

Wani irin takaici ne yake sake kama shi in ya hango namiji a zaune a inda take ga kuma wani a gaba yana tuk'a napep d'in sai yaji kamar ya jawo ta ya shak'e ta, "sai nace ki fito zaki fito?" Ya fad'a yana kallon ta ido cikin ido. D'an kawar da kai tayi kai tayi ganin kamar hankalin mutane zai yo kansu ya saka kawai ta fito daga napep d'in ta kalli me napep d'in tace, "Nawa ne kud'in ka?" Ta fad'a tana lalubar jaka. "Zaki wuce ki shiga mota ko sai nayi ball dake?" Ya furta yana zuwa inda take kamar zai mangare ta, ai a guje ta bar wajan ta koma inda motar sa take tana kallan sa, kud'i taga ya bawa mai napep d'in kafin ya fara takowa zuwa inda take da sauri ta bud'e motar ta shiga gaban ta na fad'uwa dan tasan zata sha bala'i.

Bud'e murfin motar yayi ya shigo ya mayar da belt ya wuro iska daga bakin sa, ganin yayi shiru itama sai taja bakin ta tayi shiru bata ce komai ba, kansa ya kifa a kan sitiyarin motar yana sauke numfashi a hankali yana matse yatsun hannun sa suna fitar da sautin k'ass, "meyasa bakya jin magana?" Taji sautin muryar sa cikin taushi kamar bashi ba, shiru tayi bata amsa ba ya cigaba da fad'in, "Na fad'a miki bana son hawa napep amma baki ji ba ko? Ina ma kika je?." "Gidan Yaya Rukayya naje, yaya tace." "Meyasa baki kira ni na saka anzo a kai ki ba,? Ibteesam kina so zuciya ta ta buga ne?" Ya fad'a lokacin da ya d'ago ido ya kalle ta, d'an kawar da kai tayi ganin yadda idanun sa suka koma jah kamar wanda aka zubawa barkono a idon nasa, hannun ta yaja ya d'ora a dai-dai saitin zuciyar sa, zaro ido waje tayi jin yadda zuciyar sa take wani irin beating kamar zata fito daga k'irjin sa sabida bugun da take yi da sauri-sauri.

Jingina yayi da kujerar motar ya kulle idon sa gumi yana keto masa daga goshin sa duk sanyin a.c dake motar amma gumi yake, hannun ta yana manne a k'irjin sa har lokacin ya saka nasa hannun ya dafe idon sa a kulle, "kina so na mutu ko?". Kallon sa tayi lokaci d'aya Allah ya saka mata wani irin tausayin sa wanda bata tab'a yin sa akan ko wanne d'an adam ba sai a kansa hakan ya saka ta samu bakin ta da furta, "Ya za'ayi naso ka mutu." "Amma meyasa bakya sona? Bakya son abinda nake so uhum?".? Shiru tayi bata amsa ba ta sunkuyar da kai k'asa sai ta canja maganar da fad'in, "Zuciyar ka na bugawa da sauri bugun yayi worst gaskiya ya kamata kaga Dr" ta fad'a murya a sanyaye.

Bud'e idon sa yayi ya kalle ta kanta a sunkuye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login