Showing 129001 words to 132000 words out of 171073 words

Chapter 44 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7839

tare da dafe kansa.

"Daughter ya bakya jin abincin?" Daddy ya fad'a yana kallon Ibteesam, Anty Amina ta kalle ta sai Ibteesam tace, "Khamshin abincin ne babu dad'i" ta fad'a tana d'an yatsine fuska. "Khamshin abinci babu dad'i? Spices d'in ne bai miki ba ko meye?" Anty Amina ta fad'a tana kallon ta, d'aga kai tayi tace, "Eh kamshin su bai min ba." "Khamshi bai miki ba kamar wata mai ciki? Sau nawa kina cin abinci dashi yau zaki ce bai miki ba, Kawai dai kin k'oshi" Ta fad'a tana cigaba da cin abincin ta.

"Anty you said ciki,? Pregnant ko? Yes it can be possible" Zaid ya fad'a a rikice yana kallon Anty Amina da Daddy, duniyar tunani ya tafi kafin yace, "Daddy two weeks ko? Yes za'a samun cikin ai, Precious muje asibiti" ya fad'a yana mik'ewa tsaye itama ta mik'e da sauri ta bar wajan sai kuwa ya bi bayan ta da saurin gaske. Daddy da ya tallafe hab'a yana kallon ikon Allah yace, "Ni Abubakar naga abinda yafi k'arfi" ya fad'a yana zare glass d'in idon sa. Dariya Anty Amina tayi sosai Daddy ya kalle ta shima sai yayi dariyar yace, "Au dariya ma na baki?". Tafa hannu tayi tace, "To me zanyi in ba dariya ba?". Daddy yace, "Wato dai Zaid baya sirika dake na lura". Anty Amina tace, "Daman ai Mummy da Umma suna sirikan sa ni ai Maman Zaid ce." Daddy yayi murmushi yace, "Wai ni yake cewa 2weeks ko?" Ya fad'a yana y'ar dariya. Tace, "Kuma fa kawai ni na fad'a ne bada wani abun ba." Dariya Daddy yayi kafin ta kuma cewa,

"Sai ka hanzarta gyara masa part d'in sa in ka gaji da kallon abinda yake yi" ta fad'a tana mik'ewa ta fara tattare kayan abincin tana murmushi, Zaid ne ya fito ya kalli su Daddy yace, "Daddy ya kamata mu tabbatar da maganar a nan fa amma ta kulle k'ofa, kuma tana ta gudu kamar ba pregnant woman ba" ya fad'a yana yatsine fuska. Daddy baice masa komai ba ya d'auki glass d'in sa ya mayar ya hau sama baice masa k'ala ba bai kuma kalle shi ba, "Anty ki mata magana ta bud'e ai ba maganar wasa bane wannan" ya fad'a yana kallon Anty Amina, murmushi tayi kad'an tace, "kar ka damu zan mata magana kaje ka dawo yanzu" baice komai ba ya fita daga gidan ta bishi da kallo tana mamakin hali irin nasa.

Ibteesam kuwa tana shiga d'aki ta fashe da kuka tana fad'in, "haba dan Allah wannan wacce irin rayuwa ce? Shi sam baya jin kunya a rayuwar sa baya iya rik'e magana indai tazo zuciyar sa sai ya fad'a, ni wallahi na gaji bana son haka" ta fad'a ita kad'ai tana kukan ta.

Tsaki taja tace, "wai ciki, A'a haihuwa ba ciki ba" ta fad'a tana share hawaye ta, kallon fuskar ta take a mudubi sai abun ya bata dariya sai kawai ta fara dariya sai da ta gaji sannan ta daina tana jin sa yana yi mata magana tayi masa shiru. Bata fito ba sai k'arfe goma na dare ta sami Anty Amina a zaune tana waya ta samu wajs itama ta zauna hae ta gama wayar, Anty Amina ta kalle ta bata ce komai itama kuma batayi magana ba, sun kwashe kusan minti biyu a haka kafin Anty Amina ta mik'e tace, "Tunda baki da abin cewa ni na tafi" tana fad'ar hakan ta bar wajan ta shiga d'aki.

Mik'ewa tayi ta koma d'aki ba jimawa ta sake fitowa ta shiga d'akin Anty Amina taga bata nan ta kashe komai na d'akin haka ya tabbatar mata da tana saman Daddy, d'akin ta koma tayi wanka ta saka riga mara nauyi ta zauna tana danna wayar ta, bud'e k'ofar akayi tare da shigowa ta d'ago kai suka had'a ido ta mayar da hankalin ta kan wayar ta, zama yayi kusa da ita tare da fad'in, "Why kika kulle k'ofa d'azu?". Turo baki tayi tace, "to ba kaine ba kaita bani kunya a gaban Mama da Daddy". "Me nayi da na baki kunya?" Ya tamabaya da mamaki yana kallon ta dan shi baiga abin kunya ba

"Komai ma". Tab'e baki yayi yace, "nifa jiki na yana bani akwai cikin nan is better muje asibiti" ya fad'a yana d'ora hannun sa akan cikin ta, janye hannun nasa tayi tace, "Ni bani da wani ciki". "Ya akayi kika sani?". "Nidai nasan bani dashi". Sake mayar da hannun sa yayi yace, "Ni kuma nasan za'a iya samu sabida kinga ranar da abin ya faru....." saurin katse shi tayi da fad'in, "Dan Allah ka bari bana so".? Murmushi yayi ya zagaya da hannun sa a kan kafad'ar ta ya rik'e wuyan ta yace, "Wai ni kike jin kunya?". D'aga masa kai tayi alamun eh tana turo masa baki.

"Kina da aiki dan nikam ban san wani abu kunya ba, yanzu dai mu koma kan maganar cikin nan, ina so a tabbatar ne ina so na samu baby da wuri" ya fad'a yana kallon idon ta. "Nidai nasan bani da ciki" ta fad'a tana sauke idon ta daga cikin nasa. "Ya akayi kika sani?". Turo baki tayi gaba tana wasa da hannun ta amma ta kasa magana, "you're on menstrual blood right?" Ya fad'a yana d'aga mata gira d'aya.? Da sauri ta kalle shi tana mamakin ta yadda akayi ya sani sai kuma ta saukar da kanta k'asa bata ce komai ba, "Good ya kyautawa kansa da yazo yanzu" ya fad'a yana had'e fuskar sa da tata, "insha Allah next month kina da ciki" ya fad'a yana goga hancin sa akan nata.

"Ka bari kar Mama ta shigo ta ganmu" ta fad'a idon ta a kulle tana k'okarin kwace kanta, "Tana wajan mijin ta baza ta shigo ba" ya fad'a idon sa lumshe.? Abinda ya fad'a sai ya sake bata kunya matuk'a ya katse ta da fad'in,"by 10am zamu tafi Gomben ga ticket d'in a hannu na, harda Jidda da Zahra Daddy yace". Jin hakan ya saka ta yin murmushi tace, "Bara na sanar dasu yanzu su san da tafiyar" ta fad'a tana niyar lalubo wayar ta.

Kama hannun nata yayi yace, "Kya fad'a musu amma ba yanzu ba,? now it's my time". "In ban fad'a musu yanzu ba ta yaya zasu sani gashi kace k'arfe goma?". "Shiiiiiii kiyi shiru" ya fad'a har lokacin idon sa a kulle yake. Nan fa ya canja salon wasan ya shiga sarrafa ta son ransa itama dai ba'a barta a baya ba.

Sun kwashe lokaci mai tsahon gaske a haka kafin ta soma kwace jikin ta ta koma gefe tana sauke numfashi, shima kwanciya yayi yana sauke numfashin sannan ya dawo dai-dai, kallon ta yayi yaga har lokacin idon ta a kulle yake ya kasa d'auke idon sa a kanta yana jin soyayyar ta tana sake kama zuciyar sa, ya rasa wanne irin so yake mata da baya iya kasa nuna a gaban kowa in tana kusa dashi kasa sarrafa kansa yake yi sainya dinga jin wani abu na fizgar sa har sai ya d'ora hannun sa a jikin ta yake jin dad'i, ya sani Allah ya dasa masa k'aunar ta a ransa a lokacin da bai shiryawa hakan ba, ta shiga cikin zuciyar sa wanda duk ranar da yace zai fitar da ita tabbas sai dai ya fasa zuciyar sa, daman zuciya ta kasance kamar asusu take zaka saka kud'in ka lafiya lau babu wahala amma duk ranar da zaka cire kud'in sai ka fasa ta haka soyayyar Ibteesam take a zuciyar sa, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mik'e zaune, mik'ewa tsaye yayi ya shiga band'akin ta.

Jin motsin sa sai ta d'auka fi?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 ta yayi sai ta bud'e idon ta tana raba ido kamar munafuka, dariya ta fashe da ita ganin yadda take raba ido ita kad'ai kamar munafuka, sai da tayi dariyar san ranta sannan tace, "Oh gaskiya ina jin kunya" ta fad'a tana mik'ewa tsaye tare da nufar band'aki, tana murd'a handle d'in k'ofar taji an canki hannun nata an jawo ta cikin band'aki.

Baki ta bud'e zatayi ihu yayi saurin toshe mata baki dole tayi shiru, sun d'an jima a band'akin kafin ya riga ta fitowa ya fita daga d'akin ba tare da yayi mata magana ba.

*?ASAITAR SO!*

*72_73*

Not edited >?u?


Tana jin fitar sa tayi maza ta fito tare da dannawa k'ofar key ya jingina a jiki tana sauke numfashi, kaya ta saka ta nemi wajan kwanciya amma baccin yak'i zuwa idon ta da ta kulle ido babu abinda take gani sai yanayin da suka kasance a lokacin, d'an marin kanta tayi tana murmushi tace, "Bashi da kunya ko kad'an" ta fad'a har lokacin tana murmushi a haka har bacci ya d'auke ta.

Sanin ba sallah zatayi ba bata tashi ba sai tara saura na safe tana kallon agogo ta diro daga kan gado ta fad'a band'aki tayi wanka cikin k'aramin lokaci, tana fitowa ta shirya cikin doguwar riga ta lace d'inkin ashape da bai kamata ba, d'aurin zahra buhari tayi ta fesa turare, kallon kanta tayi taga tayi kyau sosai sannan ta fara had'a d'akin.

Sai da ta gama komai sannan ta fito a lokacin Jidda na niyar shigowa, ganin ta ya saka ta koma tare da fad'in, "Gata nan ma". Anty Amina ta kalle ta tace, "kin san kuna da tafiya kika je kina ta bacci har lokaci yana neman k'urewa?" Ta fad'a cikin fad'a tana kallon ta.

Lokacin yake sakkowa yaji maganar da Anty Amina take sai ya kalle ta yace, "A k'yale ta ta gama abinda take so in munyi missing dis fight sai mu sake booking wani" ya fad'a hankalin sa na kan wayar sa. Daddy da ya sakko a lokacin yace, "Zaid maza ka koma ka canja kayan jikin ka zuwa manyan kaya, kar ka tafi kuma da k'ananun kaya na fad'a maka" Daddy ya fad'a yana kallon sa.

Baice komai ba kawai ya juya ya koma saman nasa ba tare da ya sake kallon kowa na falon ba, Anty Amina tace, "Maza kiyi breakfast ku tafi lokaci yana k'urewa tun d'azu su Zahra suke" ta fad'a tana wucewa daga wajan Daddy ma ya fita. Tea kawai tasha ta koma ciki ta d'auki kaya kala uku ta saka a cikin kayan Zahra da Jidda suka fito, a tsaye suka same shi yana sanye da yadi maroon colour mara nauyi d'inkin dogon hannu, k'arewa masa kallo take tun daga kan takalmin k'afar sa har wular da ya saka dan gani take bai tab'a yi mata kyau kamar ranar ba,? duk da fuskar sa a cunkushe take babu walwala kamar kullum amma yayi bala'in kyau kamar ka d'auke shi ka gudu, kayan su haske masa jikin sa sun zauna dass kamar a jikin sa aka d'inka su.

Yana jin yadda idon ta yake yawo a jikin sa hakan bai saka shi ya d'ago ba sai ma basarwa da yayi kamar bai san dasu a wajan ba, "Woww Yaya Zaid kayi kyau over wallahi" Zahra ta fad'a bayan ta gama k'are masa kallo. Sai a lokacin ya kalle su yace, "thanks". Anty Amina ce ta fito Daddy ma ya shigo falon yana fad'in, "yauwa Dr dan Allah ka k'araso mai gadi? nane bashi da lafiya dan sai amai yake tayi". Shiru Daddy yayi kafin ya kuma cewa, "Thanks you" daga haka ya kashe wayar ya kalli inda Zaid yake tsaye.

"Tabarakallah Son kaga yadda kayi kyau,? Kana cutar kanka da kake saka k'ananun kaya" ya fad'a yana k'arasowa wajan, Anty Amina tace, "Gaskiya kam masha Allah kayan sun amshe shi". D'an murmushi yayi kad'an yace, "Nagode duka, wanda kuma suka gani suka yaba amma suka kasa fad'a ma nagode" ya fad'a yana kallon Daddy.

"To zaku tafi ko?" Daddy ya sake fad'a yana kallon su, daga kai kawai yayi alamun eh, "Daddy yace, "To Allah ya tsare ya dawo daku lafiya, but Zaid pls ka ka kula kaji?". "Okay Daddy" ya fad'a yana kallon sa. "Masha Allah, Allah ya kaiku lafiya". Suka amsa da Amin Anty Amina ma tayi musu addu'a suka fita daga gidan.

Ita dai Ibteesam mamakin sa kawai take ganin bai kalli inda take bama balle yayi magana sai wani had'e fuska da yake yi kamar ba shi ba, tab'e baki tayi tana tunani a ranta lallai hali zanen dutse duk da son da yake mata bai saka k'asaita da izzar sa ta bar jikin sa ba.

Suna fitowa Hameed yana shigowa ganin haka ya saka shi yin ajiyar zuciya yace, "Allah nagode maka banyi late ba". Harara ya watsa masa kafin Hameed yace, "Kai Zaid kaga yadda kayi kyau kuwa? Wannan sai ka saka y'an matan Airport sumewa" ya fad'a ya a kallon sa dan yayi masa kyau sosai.? Baice komai ba sai gaban motar da ya bud'e ya shiga su kuma suka shiga baya Ibteesam kamar tayi kuka jin abinda Hameed yace dan abun ya tab'a ta.

Bayan sun fita daga gidan Hameed yace, "Kuyi hak'uri bamu gaisa ba ko? Ina kwanan ku?". A tare suka amsa da fad'in, "An tashi lafiya?". "Lafiya lau". Daga nan suka yi shiru dan yaga gogan na kallon sa, babu wanda yake magana sai sautin wakar davido da take tashi a motar kad'an-kad'an, wayar Zaid ce tayi k'ara ya kalla sai yayi tsaki tare da d'auke kansa bai amsa ba, kiran ya sake shigowa Hameed ya kalle shi yace, "Kayi picking call d'in mana ana ta kira kayi banza." Sai da ta katse wani kiran ya sake shigowa sannan ya d'auka tare da fad'in, "What?". Dake a speaker ya saka muryar mace ta bayyana a cikin wayar tana fad'in, "I'm sorry daman bak'i kayi ne shine suka ce na tambaye ka ko zaka shigo?". "Shine kike damu na da waya?" Ya fad'a a d'an fusace, "I'm sorry" ta sake fad'a cikin kwantar da murya, "just tell them bana nan infact bazan shigo ba yau" yana gama fad'ar hakan ya yanke wayar tare da mayar ds hankalin sa kan titi.

Babu wanda ya kuma magana a cikin su kowa hankalin sa na kan wayar sa har suka k'arasa Airport, yana yin parking suma fito ganin lokaci ya tafi jirgi ya kusa tashi banda ma African time irin na d'an Nigeria da a wata k'asar ce da tuni jirgin ya kusa tashi, y'ar k'aramar jakar sa ya ja Jidda taja musu tasu suka yi gaba Hameed kuma ya juya ya tafi. Suna shiga babu jimawa sukayi komai suka k'arasa inda jirgi yake, duk da Ibteesam da Jidda basu tab'a hawa jirgi ba amma basu nuna tsoro ba suka dake suka shiga, kujera mai hud'u ce inda number seat d'in su ya nuna, Zaid ya shiga ciki Ibteesam tabi bayan sa sai Jidda da Zahra.

Ba jimawa jirgi ya fara k'okarin tashi Ibteesam tsoro ya saka ta k'ank'ame hannun Zaid duk da ta d'aura belt amma tsoro take ji, murmushi yayi ya rik'e ta har jirgin ya d'aga.

Awan su kusan biyu a sama suka sauka a Sani Abcha International Airport Gombe oh ready Zahra tayi waya har driver ya iso suka shiga suka tafi.

A motar Zahra ta kalli Zaid da yake ta aikin danna waya ta kalli Ibteesam ta kama kunnen ta tace, "Wai ku haka soyayyar taku take y'ar shariya kuke?". Dariya Ibteesam tayi kad'an bata ce mata komai ba har suka k'arasa, parking sukayi suka nufi cikin gidan har lokacin Zaid baiyi magana ba.

Da sallama suka shiga falon Hajia Kaka ta mik'e taba fad'in, "lale lale da mutanen Kano sannun ku" ta fad'a tana nuna musu wajan zama alamun su zauna, zama sukayi Zahra tace, "Hajiya Kaka sannun ki kema".? Zaid ya kalli matar da itama shi take kallo tunda suka? shigo yace, "Barka da rana Hajiya". Sai kuwa ta washe baki tace, "Barkan ka dai ango, ya gida da mutanen gidan naku?". D'an sakin fuska yayi kad'an yace, "Lafiya lau Alhamdulillah, suna gaishe ku". "Muna amsawa, kai Tabarakallah masha Allah, ashe mijin nawa ba baya bane a wajan kyau" ta fad'a cikin raya tana dariya.

Murmushi yayi kad'an baice komai ba dan daman shi ba ma'abocin magana bane ba, shigowar su Fateema da Amina ya falon ya sake rud'ewa da ihu sai da ya toshe kunnen sa jin suna k'okarin fasa masa kunne, "Anty Baby sannu da zuwa" ko wacce ta fad'a tana rungume ta suna farin ciki, kallon Zaid sukayi a tare da bai kalle su ba suka zaro ido tare da kallon Ibteesam suka ce, "Shine?" A iya la66a maganar ta tsaya dan haka babu wanda yaji sai Ibteesam d'in, d'aga musu kai tayi sai kuwa suka ce, "Ina wuni mijin Anty Baby". Jin abinda suke ce sai ya saka shi ya d'an saki fuska ya kalle su yace, "ya kuke?". "Lafiya lau, ya hanya." "Alhamdulillah" ya furta yana d'auke kansa daga kallons ba dan sai yayi da gaske yane gane hausar su.

"To Fateema maza kaishi masaukin sa kafin mutanen gidan su dawo yaje ya huta" Hajiya Kaka ta fad'a yana kallon Fateema, ba musu ta tashi tayi gaba Zaid ya mik'e a nutse yabi bayan su, da kallo Hajiya kaka ta bishi dan babu k'arya nutsuwar sa tayi bala'in burge ta ta dawo da kallon ta ga Ibteesam tace, "Tashi kije ki raka shi sai kya dawo" batayi musu ba ta mik'e tabi bayan su.

Zahra ta kalli Hajiya tace, "Hajiya Jidda kenan k'anwar Ibteesam ta Kano". Hajiya najin haka sai ta washe baki dan ta fahimci y'ar wajan wanda suka rik'e ta ne sai tace, "Masha Allah gata itama tabarakallah mai jikin fulani, sannu Hauwa'u ya iyayen naki?". Jidda tayi murmushi tace, "Suna nan lafiya lau." "Masha Allah, Zahra kuje ku huta sai kuzo kuci abinci" ta fad'a tana kallon Zahra ta mik'e taja hannun Jidda zuwa d'aki.

Su Fateema kuwa a k'ofar d'akin suka tsaya suka nunawa Ibteesam suka ce, "Ga d'akin an gyara shi". Murmushi tayi tace, "Sannun ku". Suka juya tare da fad'in, "Muna jiran ki fa akwai labari". Ta amsa musu da to tana bud'e k'ofar ta shigar da jakar sa, yana tsaye har ta shiga sannan yabi bayan ta zuwa ciki, falo ne k'arami bashi da girma a gyare tsaf sai kamshi yake sai bedroom maidaidaici mai kyau, bedroom d'in ta shiga ta ajjiye masa jakar tana niyar fitowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login