Showing 147001 words to 150000 words out of 171073 words

Chapter 50 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7850

ana rawa mai hoto da video suna aikin su, anayi ana ci ana kuma sha dan abinci da abin sha a wajan har yayi yawa, kafin kace wani abu hotunan Ibteesam da videos d'in ta wani tana rawa wani tana shan mocktail wani tana cin cake sun baza social media kowa sai fad'ar albarkacin bakin sa yake a kanta, wasu suce ita ce best beautiful bride at 2022 haka dai comments babu wanda babu.

A lokacin Zaid yana kwance yana aikin danna wayar sa haka kawai yayi sha'awar kunna data wayar sa ya shiga Ig yana tafiya a hankali ba tare da yasan abinda yake yi a ciki ba, har ya wuce hoton sai ya dawo yayi zooming d'in face d'in ta tare da mik'ewa zaune, "kai!" Ya furta tare da cigaba da kallon hoton nan ya ga Zahra da Jidda abinda ya saka shi mik'ewa tsaye ba tare da ya sani ba, hoton da ya kusa tarwatsa masa zuciya yayi karo dashi wanda take ita da Khalipha yana bata cake a baki itama tana bashi suna dariya kamar shine angon nata, comments ya shiga nan ya fara ganin yadda ake yabon kyawun ta da kuma surar jikin da yadda wasu suka d'auka Khalipha ne mijin nata.

Tsabar b'acin rai da bak'in ciki ko kyawun nata bai gani ba jikin sa ya fara rawar ya yayi unblocking d'in number d'in duk da yayi blocking ya fara kiran layin ta amma ba'a d'auka, ya d'auke ta daga kunne da niyar sake kira fuskar wayar ta sake kawo masa hoton ta da Khalipha again ya rik'e ta ita kuma ta d'ora hannun ta a kafad'ar sa suna murmushi.

Ai bai san lokacin da ya d'auki mukullin mota ba ya fita da saurin gaske.

Gudu yake sosai amma gani yake kamar ba tafiya yake ba burin sa ya bai wuce ya ganshi a gidan Mummy ba gashi lokacin har anyi magariba, tun daga bakin gate d'in yake ganin mata suna fitowa wasu suna shiga ga kuma k'arar kid'a nan da alama har yanzu bikin suke yi, parking d'in motar yayi yazo zai shiga security d'in da aka saka a wajan ya tare shi ta hanyar fad'in, "kayi hak'uri babu maza a bikin." Wani banzan kallon ya gefa masa tare da jan tsaki zaiyi magana asalin mai gadin gidan yazo wajan ganin da yayi ya san Zaid har yana duk'a masa ya saka bai sake magana ba har ya wuce ciki.

Ibteesam tana tsakiyar y'an mata sun zagaye ta ana rawa hannun ta rik'e da glass cup tana rawa sosai tana bin wakar da ake yi, kallon ta kawai yake ganin yadda rigar ta fito mata da surar ta gashi d'ankwalin ma an cire shi yanzu babu komai a kanta sai wata hula da aka yi mata ado da ita a tsakiyar kan nata, zuga ta kawai m.c take ita kuma tana kuma dagewa wajan dik'ar rawar ta tana dariya.

Juyi take idon ta ya sauka akan fuskar sa har ta juyar da fuskar ta ta sake dawowa tana kallon sa, tana so ta tabbatar shine ko kuma dai gizo yake mata, tabbas shine kuwa a tsaye ya had'e fuska kana ganin yanayin sa kasan ran maza a b'ace yake kawai yana kallon ta.
*?ASAITAR SO!*

*80_82*

Not edited >?'?



Ganin inda take kallo yanayin tsoro ya bayyana a fuskar ta ya saka sauran matan suka kalli wajan da take kallo, ya had'a cikin suit blue mara haske sosai ya zuba hannu a cikin aljihu yana kallon ta fuskar nan a tamke kamar bai tab'a dariya ba.

"Woww masha Allah, kaga wani mai kyau, kai Tabarakallah ya had'u, Allahumma arzuk'uni" shine abinda y'an matan wajan wanda basu sanshi ba suke furtawa dan ba k'arya suit d'in jikin sa ta amshi fatar jikin sa, Ibteesam kuwa tattare rigar ta take tana neman guduwa ta yunk'ura zata gudu taku d'aya ya iso inda take ya cafki hannun ta, wannan tsayuwa da suka yi a haka tana kallon sa shima haka duk da fuskar su babu walwala ya bawa mai hoto damar fara sakar musu camera, zatayi magana ya zaro mata ido b'am taji bakin ta ya mak'ale sai raba ido da ta koma yi tana had'd'iyar saliva.

Jan hannun ta ya farayi ba tare da yacewa kowa komai ya dole ta bishi suka fita daga wajan bikin har bakin gate, ganin yana k'okarin fita da ita ya saka ta cize tace, "Ka tsaya muyi magana a nan pls". Juyowa yayi ya harare ta ya bud'e gate d'in suka fita dan dole. Zahra da take tsaye a wajan m.c ta kalle ta tace, "Ya haka zai d'auke mana amarya? Dan naga kin yi shiru ne ya saka na k'yale dan ina da tabbacin kin sanshi." Zahra tayi k'aramar dariya tace, "Mijin tane fa shine angon".

M.c tace, "Ashe gwara da Allah ya taimaka banyi magana ba, kai amma har yafi ta kyau masha Allah" daga nan aka cigaba da chashewa.

Tunda ya saka ta a mota ya fara tafiya ba tare da yace mata komai ba itama kuma bata ce ba sai kanta da yake kan titi tana tunanin hukuncin da zai yanke mata, sun d'an yi tafiya mai dan nisa suka isa chilla hotel, sai bayan yayi parking sannan ya kalle ta yaga ko d'ankwali babu a kanta gashi hotel suka zo, numfashi ya sauke dole ya kunna motar suka fita daga hotel d'in ya nufi super market mafi kusa.

Yana isa ya kashe motar ya fita bai kalle ta ba ya shiga ciki ta bishi da kallo, bai jima sosai ba ya dawo da leda a hannun sa ya shiga motar suka bar wajan suka koma hotel d'in, yana parking ya mik'a mata ledar yace, "Cover your hair". Hannu ta d'ora a kanta nan taji ashe babu komai a kanta nata ta karb'a cikin sanyin jiki ta ware mayafin ta d'ora a kan nata sannan ya bud'e k'ofar ya fito dole itama ta fito, ciki suka shiga suka nufi d'akin da yake ciki ya bud'e ya shiga itama ta shiga ta mayar da k'ofar ta kulle, zama yayi a kan kujera ya zare rigar saman ya cire ta biyun ya b'alla ma6allan rigar yana furzar da iska, a.c ya k'ara dan zafi yake ji sosai a jikin sa.

Ita dai tana tsaye tana kallon sa gashi batayi magariba ba tsoron yi masa magana da take yi kawai sai ta ajjiye mayafin Allah ya taimake ta an cire inda yake jan k'asa a rigar ta koma dai-dai ita ta nufi k'ofar da take tunanin band'aki ne, tazo wucewa ta kusa da gadon shi kuma a lokacin ya mik'e zai d'auki laptop sai kuwa ta zabura tayi wajan band'aki a guje ya bita da kallo yana girgiza kai kawai.

Takalimi ta saka ta shiga band'aki tana ajiyar zuciya ta wanke kwalliyar fuskar ta sannan tayi alwala ta fito, Allah ya saka mayafin da ya siya mata babba ne kuma mai kauri ta yafa ta tayar da sallah, tana idarwa taji ana kiran i'sha ya tashi ya fita itama ta tayar da sallar i'sha, bayan ta idar tana ta kallon d'akin tana mamakin kenan tsahon kwanakin nan a nan yazo ya zauna abin sa babu ruwan sa da halin da zasu shiga in basu ganshi ba, tana wannan tunanin ya dawo hannun sa d'auke da leda ya zauna yana bud'ewa,? tura mata d'aya yayi baiyi magana ba kawai ya fara cin nasa a nutse yana sake had'e mata fuska dole ta d'auka ta fara ci dan daman yunwa take ji.

Yana kallon ta ta k'asan ido ya fahimci a tsorace take gabad'ayan sai satar kallon sa take da taga zasu had'a ido sai tayi sauri ta d'auke idon ta bata san yana kula da ita ba, bayan ta gama ta mik'e ta koma band'aki ta wanke bakin ta ta d'auke pack d'in abincin tana kallon agogo, tunawa da tayi itace fa da laifi sunyi da ita baza tayi rawa ba ba kuma zata saka kaya irin wanda ta saka ba amma ta saka dole itace zata bashi hak'uri, komawa tayi kusa dashi ta zauna khamshin jikin ta ya saka shi lumshe ido ya bud'e yana sauraron abinda zatace.

"Kayi hak'uri kaji" abinda ta iya fad'a kenan tana wasa da hannun ta, bai ma kalle taba balle ya kula ta sai ma cigaba da danna laptop d'in sa cikin nutsuwa, sai kuwa ta fara dire-diren k'afa tana fad'in, "Dan Allah kayi hak'uri kaima fa kayi min laifi babba amma nake baka hak'uri bayan kai baka bani ba ko rarrashi na bakayi ba" sai kuwa ta fashe masa da kuka sosai.

In akwai abinda yake saurin tayar masa da hankali a duniya bai wuce kukan ta ba ya cize baki ya sake daurewa tare da cigaba da abinda yake yi ba tare da ya kalle ta ba, ganin hak'ar ta bata cimma ruwa ba duk da volume d'in kukan da take k'arawa sai ta mik'e tsaye tans fad'in, "tunda baza ka kula ni ba ka mayar dani gida mana wanda suke son kula ni suyi min magana, kai da ka tafi yau kwana biyar kenan ko waya baka min ba balle kaji lafiya ta banyi fushi ba sai kai zakayi fushi dani? Ni ka mayar dani gida" ta fad'a cikin shagwa6a tana dire masa k'afa tare da yin hanyar fita, sai kuwa tayi kamar zata fad'i tana sane ta fad'a jikin sa yayi saurin kawar da laptop d'in ya rik'e ta ita kuma ta k'ank'ame rigar sa tana kuka.

Janye ta yayi daga jikin sa ya mayar da ita ta zauna a kan kujerar ya jawo laptop d'in ya cigaba da aikin sa, bata san karr yake kallon ta duk wani plan da zata had'a masa zai fahince shi ba sai kuwa ta bashi dariya yayi murmushi a zuciyar sa ganin k'aramar yarinya wacce ya bawa shekara sama da goma ko k'asa da haka wai zatayi masa wayo.

Ganin again fa babu nasara sai ta mik'e ta fad'a kan gado ta fara kuka bil hakki har zuciyar ta, dukan gadon ta fara tana cillar da pillows d'in da suke kai tana janye bedsheet d'in kamar sabon kamun hauka, d'agowa yayi ya kalle ta ya mayar da kansa ga abinda yake yi sai kuwa ta fasa k'ara tana kuka, cak ya mik'e ya kulle k'ofar ya zare key d'in ya d'auko BT ya saka a kunnen sa biyu ya cigaba da aikin sa.

Ina wuta take Ibteesam ta fad'a haka taji tsabar takaici, wato ga mahaukaciya tai ta ihun ta shi ko a jikin sa, ta sake fashewa da kuka gashi babu waya a hannun ta balle ta kira wani ko ta debe mata kewa haka ta cigaba da kukan ta tana kallon sa.

Sosai yake jin zafin kukan ta a ransa amma yake daurewa sabida yana so ya nuna mata kuskuren ta na bijirewa maganar sa sai ya danne ya nuna kamar bai dame shi ba, kallon ta yake ta k'asan ido sosai tayi masa kyau a idon sa ga wani fitinannan khamshi da yake bin jikin ta duk inda ta tashi ma khamshi yake amma da yake baya son bada kansa sai ya sake basarwa.

Haka taci kukan ta ta godewa Allah ta kuma share kayan ta sai kuma ciwon kai da ya fara kawo masa ziyara, dafe kan tayi ganin hakan ya saka shi ya mik'e ya d'auko p.c.m ya ajjiye mata kusa da ita ya koma ya ciagaba da aikin sa. Ai kam tak'i kallon inda maganin yake ta kalli agogo ganin tara na k'okarin wucewa kuma bashi da alamun kaita gida ya saka tace, "In baza ka mayar dani gida ba ka bud'e min na tafi." Ai kamar da dutse tayi magana dan ko motsi baiyi ba balle ya amsa mata, ta kuma maimaitawa ya kuma yi mata banza haka ta hak'ura tayi shiru ga gajiyar da take tare da ita ga bacci, mik'ewa tayi ta shiga Band'akin dan wanka take so tayi.

Tana shiga ya bar aikiin da yake ya jingjna da kujerar da yake kai tare da dafe k'irjin sa yana sauke numfashi dan shi kad'ai yasan dauriyar da yake wajan share ta, k'ofar band'akin ya kafawa i????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? do har kusan mintina sha biyar sannan yaji motsi alamun fitowa sai kuwa ya d'auke kansa ya cigaba da aikin sa, da kayan da ta shiga ta fito dasu a hannun ta ta saka rigar wanka wacce iyakar ta guiwa dake me bud'ewa cee ba wacce ta kamata ba sai tayi mata dai-dai, rigar tata ta ajjiye a gefen gadon ta koma ta zauna tana jira taji zaice ta saka kaya su koma, tun tana zaune tana kallon sa har bacci ya d'auke ta ta kwanta a wajan bata sani ba.

Sai da baccin nata yayi nisa sosai sannan ya mik'e yana murmushi ya matso kusa da ita, fuskar ta yake k'arewa kallo kafin ya sunkuya ya shafi fuskar ta, wanka ya shiga bayan ya fito yayi shafa'i da wuturi ya rage wutar d'akin ya kwanta a kusa da ita, kallon ta kawai yake dan fuskar ta tayi masa kyau sosai sai kyalli take ga santsi da yake ji in ya tab'a, jawo ta yayi zuwa k'irjin sa ya d'ora hannun sa a kan jijiyoyin kanta yaji tana harbawa alamun har lokacin da ciwon kan, ya dinga mata addu'a har kan ya d'an saki a haka shima bacci ya d'auke shi tana jikin sa.

Bacci sukayi dukkan su sosai babu wanda ya farka sai asuba shine ya fara tashi yayi alwala sannan ya dawo kusa da ita, kanta ya rik'e yaji babu ciwon kan sannan ya fara tashin ta, jijjiga ta yake yi kad'an baice komai har ta bud'e ido ya kalle shi, yana ganin hakan kawai ya mik'e ba tare da yace komai ba ya koma kan sallaya ya tayar da sallah, mamaki take wai har gari ya waye kenan a d'akin ta kwana, sai kuwa ta zabura ta diro daga kan gadon tana fad'in, "na shiga uku na, kenan wai nan kwana na?" Ta fad'a tana shiga band'aki.

Babu b'ata lokaci ta fito tana tunanin abinda zata saka a jikin ta tayi sallah, bata da zab'i dole ta d'auki gown d'in ta ta zira ta yafa mayafin da ya wuce mata har guiwa har lokacin kuma sallah yake, tayarwa itama tayi tana idarwa akayi asslatu suka tayar tare.

Bayan sun idar ne tana bayan sa ita duk tsoro ya kamata da tunanin yadda zata tunkari iyayen ta tace a wajan sa ta kwana, "ina kwana" ta furta bakin ta har rawa yake yi sabida tsoron. Jin hakan ya saka shi ya kalle ta sai yaga duk yanayin ta ya canja kamar ba ita sai kuma ta bashi tausayi hakan ya saka yace, "kin tashi lafiya?". Wata irin nannauyiyar ajiyar zuciya ta sauke jin muryar sa da ta dokin dodon kunen ta wacce rabon da taji ta har ta manta sai wacce yayi mata a mota, lumshe ido tayi ta bud'e tana so ta amsa masa amma muryar ta ta fara rawa jin maganar sa ya tayar mata da mikin abinda ya jima a ranta sai tace, "lafi....ya.." sai kawai ta fashe da kuka sosai.

Matsowa yayi kusa da ita sosai ya jawo ta jikin sa tare da zame d'ankwalin kanta yana shafa kanta, "ki daina kuka mana kina so kanki yayi ta ciwo ne?". Jin ta a jikin sa har yana rarrashin ta sai ta sake k'ara kukan nata shi kuma yana aukin rarrashin ta, "ki daina kuka kar kanki yayi ciwo mana" ya sake fad'a yana d'ago fuskar ta.

"Meye na kukan fad'a min?" ya fad'a cikin sigar lallashi, "ba kai bane, kwana biyar ban ganka ba kak'i ka kunna wayar ka na maka message no reply kullum sai nayi kuka nake bacci sabida tunanin ka amma shine ka tawo dani ko kayi min magana ka a gani ina kuka, ni banyi fushi da kai ba kaine zakayi fushi dani" ta fad'a cikin kuka har lokacin tana jikin sa.

Murmushi yayi mai kyau sannan yace, "To kiyi shiru yanzu gashi ai ina miki maganar ko? I'm sorry ki daina kuka kin san bana so" ya fad'a mata cikin sigar lallashi da kwantar da murya. "Raina ne a b'ace jiya, ya mukayi dake a Gombe a kan event din nan?" Ya fad'a bayan ya d'ago da fuskar ta yana kallon idon ta. "Kace kar nayi rawa kuma kar na saka kaya fitted" ta fad'a cikin muryar kuka tana kallon sa.
"To meyesa kika ya bayan na hana ki? Ban isa ba dake kenan?".
"A'a ka isa dani."
"Gashi kin nuna min ban isa ba kinyi abinda nace kar kiyi."
"Ba haka bane ba."
"To yaya ne? Dan raina ya b'aci kenan ko?". Girgiza masa kai tayi tace, "Ba haka bane ba."

"To yane?" Ya fad'a har lokacin yana rik'e da fuskar ta, "I'm sorry" ta fad'a a hankali. "Sorry for what Ibteesam?". Gaban ta ya fad'i jin sunan da ya fad'a wato ta b'ata masa rai bazai ce mata mai daraja ba, "akan komai ma" ta fad'a hawaye yana ziraro mata daga idon ta.

Wayar sa ya d'auka ya shiga Ig ya dubo posting d'in jiya ya nuna mata yace, "Waye wannan?". Karb'a tayi jikin ta ya soma rawa haka ma bakin ta ta d'ago ta kalle shi fuskar sa a tamke kamar koda yaushe, kasa bashi amsa tayi ta sunkuyar da kai ya sake cewa, "Answer me mana, ba munyi dake babu maza ba? Waye wannan har yake tab'a ki kike tab'a shi!?" Ya tamabaya cikin tsawa har sai da ta firgita.

"Yaya Khalipha ne fa ka kallah da kyau zaka gane shi" ta fad'a kanta a k'asa kamar munafuka, tana fad'ar hakan sai kuma ya gane shi yana mamakin girman da yayi ga gashi a fuskar sa kamar wani babba, ajiyar zuciya yayi daman yasan bazai ba wani na waje bane ya d'auka cousin d'in tane ashe ma d'an uwan tane na jini, "nasan Khalipha ne na kuma ganshi tun kafin ki sanshi na sanshi, meye ribar ki na tab'a shi kuyi hoto?".

D'ago kai tayi tace, "Yaya nane fa". Idon sa a cikin nata yace, "koda yayan naki ne amma kin san mijin ki yana da kishi ko,? Duk da d'an uwan kine na sani? babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login