Showing 57001 words to 60000 words out of 171073 words

Chapter 20 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7856

d'an k'arfi da taga ta sake gyara tsayuwa yana kallon su.

Gaba Khalid yayi ya riga ta zuwa inda Zaid d'in yake kafin yayi magana ta k'araso a guje tace, "Na d'auka motar kace da nazo shiyasa na shiga dan naga da kalar ta kake zuwa ban d'auka ba kai bane ba" ta fad'a tana hawaye. Wani irin kallo yake musu su duka biyun yana ji kamar ana zubo masa ruwan zafi daga kwakwalwar sa zuwa zuciyar sa, sai tafasa zuciyar sa take bakin sa yana futar da wuci, bai kula su ba sai dai har lokacin su yake kalla idon sa ya rikid'e ya koma ja haka fuskar sa.

So yake ya aikata masu wani abun da zai bar musu shaida a jikin su amma b'acin rai ya hana shi ko motsi sai kallo kawai da ido ya rasa ma abin fad'a, Khalid ya kalli Ibteesam itama a lokacin ta kalle shi suka mayar da kallo su ga Zaid da suke ganin kamar baya hayyacin sa, wannan kallon junan da suka ya sake tunzara masa zuciya ya fara wani irin tari mai k'arfi a dai-dai lokacin da Wizzy da mugu suka iso wajan.

Khalid suke k'okarin rik'ewa amma ganin yanayin da mai gidan su yake ciki ya saka suka yi kansa a guje, "mai gida lafiya? Meya same ka?". Tarin yaci k'arfin sa har ya kai k'asa jini ya fara fitowa daga bakin sa,? "gida" abinda ya iya furtawa kenan kawai yana hakki numfashin sa na up and down.

Wizyy ya kama shi ya saka shi a mota ya shiga motar tasa ya fita a guje, shi kuma Mugu ya hau wacce suka zo a da ita suka tafi.

Tunda suka tafi Wizzy yake fad'in, "Sannu mai gida, kodai mu wuce asibiti ne?". "A'a gida" abinda yake fad'a kenan hakan ya saka Wizzy ya sake take motar yana gudu.

Suna shiga gidan Wizzy ya bud'e k'ofar ya fito dashi yana rik'e dashi suka shiga cikin gidan, mik'ewa daddy Anty Amina sukayi ganin yanayin da aka shigo dashi, "Subahanallahi, meya same shi?" Daddy ya tambaya a rud'e yana yo kansa tare da rik'e shi.

"Daddy ruwa" abinda yace kenan, "yi masa ki d'auko masa ruwa" ya fad'a yana kallon Amina da take tsaye a kansa. Da sauri ta tafi ta d'auko ruwa ta kawo aka bud'e murfin gorar aka kafa masa a baki yana sha har ya kusa shaye rabin ruwan kafin ya kawar da kansa, "ina tambayar ka me ya same shi?" Daddy ya fad'a yana kallon Wizzy.

"Wallahi ban sani ba, ni dai nasan yayi mana waya yace muzo k'ofar gidan su yarinyar nan mu same shi muna zuwa muka gansu ita da saurayin ta a kusa dashi shi kuma yana tsaye yana tari".

"To amma....." maganar Daddy ta tsaya cak sakamakon idanun Zaid da suka juye suka koma fari tas babu bak'i a cikin su, bakin sa na fitar da wani farin abu kamar kumfa numfashin sa yana wani irin fita da sauri-sauri.



* Dan Allah kar a fitar min da littafi.*
*?ASAITAR SO!*

*37_38*

Not edited>??




"Innalillahi, Khalid jini ne fa yake zuba a bakin sa, na shiga uku me na aikata ne haka? In ya mutu nice silar mutuwar sa fa" ta fad'a tana rufe k'asan fuskar ta da tafukan hannayen ta tana kuka.

"Bazai mutu ba insha Allah ki kwantar da hankalin ki ki daina kuka dan Allah" Khalid ya fad'a cikin damuwa yana kallon ta, "na kwantar da hankali fa kace? Kana ganin a yanayin da aka tafi dashi da wanne ido zan kalli Abba na?". "Baki da laifi ai ke, shine mai laifi bake ba inda ya tsaya yaji abinda ya faru ai da duk hakan bata faru ba" ya fad'a shima a yanayin na b'acin rai da damuwa a fuskar sa.

Kasa bashi amsa tayi sai kawai ta nufi gida da sauri ba tare da ta sake kallon sa ba, da kuka ta shiga falon Umma ta fad'i a kan kujera tana cigaba da kuka sosai, "Shine sak'on da ya baki kenan?" Umma ta fad'a dan tasan dak'yar su had'u ba tare da tayi kuka ba.

"Umma wallahi bani da laifi ban san bashi bane a motar ba naje na shiga, Umma zai mutu jini yana ta fita daga bakin sa Umma" ta fad'a tana sake fashewa da sabon kuka, "kee yi min bayani yadda zan gane ban fahimce ki ba." "Umma lokacin da na fita na hango mota na d'auka tasa motar ce sai naje na shiga ashe Khalid ne Umma, shine na fito muka je nida Khalid d'in muna fad'a masa abinda ya faru, tunda muka fara fad'a masa bai magana ba sai kallon mu da yake k'arshe sai ya fara tari jini na zuba a bakin sa, wallahi Umma ban san bashi bane, na san da bak'ar mota yake zuwa shiyasa da naga bak'a naje" kuka take sosai har da sheshshek'a.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanzu yana ina?" Umma ta tambaya tana mik'ewa tsaye cikin tashin hankali, "Yaran sa sun zo sun tafi dashi tun lokacin" ta fad'a tana tsagaita kukan nata. "Bara na sanar da Abban ku ya kira mahaifin sa aji lafiya yake" ta fad'a tana ficewa daga falon.

A can asibitin da aka kai kuwa hankalin Daddy yayi bala'in tashi in ya tuna a yadda suka kawo Zaid d'in baya numfashin kirki kamar matacce sai hankalin sa ya kuma tashi fad'uwar gaban sa ta kuma tsananta.

Anty Amina da take kusa dashi itama hankalin ta a tashe yake kawai jiran fitowar likita suke daga d'akin, ba jimawa Dr Auwal ya fito ai da sauri Daddy ya k'arasa inda yake yace, "Dr ya ake ciki?". "Alhaji ka kwantar da hankalin ka mun dai-dai komai ya samu bacci ma a yanzu haka, muje muyi sallar i'sha sai nayi maka bayanin yadda abin yake" ba musu kuwa suka fita tare dan gabatar da sallah.

Bayan an idar da sallah suna fitowa daga masallaci Daddy ya kalli Dr Auwal yace, "Dr me yake damun Abdallah?". "Mu k'arasa office sai nayi maka bayani yadda zaka fi ganewa" ya fad'a yana kallon Daddyn.


A tare suka k'arasa har cikin office d'in bayan sun zauna Dr Auwal ya zare glass d'in idon sa yace, "Abu biyu ne suke damun Zaid a lokaci d'aya, na farko daman Zaid yana da matsalar zuciya ne?". Daddy ya gyara zama yace, "Ban gane matsalar zuciya ba?". "Ina nufin daman yana da ciwon zuciya ne tun yana k'arami?".

"Eh to, bana ce eh ba bana ce A'a ba kuma, dan lokacin yana k'arami ina jin baifi 10 to 13 yrs ba ya tab'a wani ciwon k'irji da wani tari wanda in yana tarin jini yana fita a bakin sa, a lokacin muna Finland muka je asibiti ake ce zuciyar sace ta motsa a lokacin aka bashi magani ya warke, daga baya muka koma aka yi x-ray d'in k'irjin nasa akace ya warke babu ciwon, daga nan bai sake yi ba sai lokacin rasuwar Maman sa shi amma bai fitar da jini ba yai ta fama da ciwon k'irji dai."

"Daman binciken mu ya nuna ciwon ya jima a jikin sa, to gaskiya Alhaji a yanzu ciwon nasa ne ya tashi ta dalilin wani abu da ya tab'a masa zuciya sosai, irin wannan abun yafi kama da soyayya ko kuma mutuwa ta wanda ya shafe shi sosai da sosai, a yanzu gaskiya zuciyar sa ta tab'u ta dalilin abinda na fad'a maka zan iya cewa yanzu yana da ciwon zuciya, amma Alhamdulillah mun samu munyi k'okarin ganin komai Ya dai-dai ta ta wannan b'angaren a yanzu tunda ciwon ne ya motsa ba zuciyar ce ta kunbura ko wani abun mai kama da haka ba."

"Sai abu na biyu kuma, Alhaji me Zaid yasha ko yaci wanda ya zama shine na k'arshe daga shi aka kawo shi nan?". D'an jimm Daddy yayi kafin yace, "Ruwa yasha,? dan yana gam shan ruwan ba'a jima ba idon sa ya k'afe."

Girgiza kai Dr yayi kafin yace, "To tsakani da Allah a abinda yasha na k'arshe a kawai guba a ciki, guba kuma mai k'arfin gaske wacce aka yi nufin kashe shi da ita badan Allah ya saka an kawo shi asibiti a kan lokaci ba da yanzu ba wannan maganar ake yi ba." "Hasbunallahu wani'imal wakil, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, guba fa Dr Auwal?" Daddy ya tambaya cikin mamaki da tsoro da ya bayyana a kan fuskar sa, "Guba Alhaji, kuma gaskiya gubar tana da k'arfi sosai dan lokaci d'aya take kashe mutum wallahi, Allah ne ya tak'aita kuka kawo shi da wuri kuma anyi sa'a bai sha gubar da yawa ba da ko bai mutu ba tabbas zata tab'a masa wani abu a cikin sa."

Zare glass d'in idon sa Daddy yayi ya d'auko abin goge gumi a aljihun sa ya goge fuskar sa ya tura hular kansa baya ya furzar da iska daga bakin sa yace, "Guda a gida na, kuma aka bawa d'a na d'aya wanda na mallaka a duniya" ya fad'a cikin mamaki da kuma al'ajabin maganar, "abinda za'a mayar da kai a duba kenan a gidan Alhaji, dan gaskiya gubar da aka bashi ba k'arama bace kawai dan bata bi jikin sa sosai ba shiyasa Allah ya tak'aita yake raye, but I'm sorry to say a cikin gidan aka zuba gubar tunda ruwan na gidan kane ba'a waje aka siyo ba."

"To yanzu ya yake ciki?" Daddy ya tambaya muryar sa a d'an shak'e, "yanzu dai mun samu an saka masa ruwan da zai kashe dafin gubar amma zamu jira ya farka mu gani in Allah ya saka gubar ta mutu a jikin sa shikenan zai tashi kamar bashi ba". "To shikenan" Abinda Daddy ya fad'a kenan ya mik'e zai fita daga office d'in, jiri ne ya d'auke shi yayi luuu zai fad'i Allah ya bashi iko yayi saurin dafa bango, da sauri Dr ya taso ya tare shi yana fad'in, "Subahanallah sannu Alhaji" ya fad'a yana rik'o shi sosai.

"Kaina na juyawa Dr Auwal". "Sannu, muje ka kwanta ka kwatar da hankalin ka dan Allah " ya fad'a yana rik'e dashi suna takawa a hankali har kan gadon dake d'akin ya taimaka masa ya kwanta, auna jinin sa ya fara yi ai kuwa abinda yayi tunani ne dan jinin sa ya hau yayi saurin d'aura masa ruwa tare da cewa, "Alhaji jinin ka ya hau sosai, ka daure ka kawar da abinda kake ji a ranka tunda har Allah ya kiyaye." Shi dai Daddy yana jin sa baice komai ba zuciyar sa tana wajan tunanin wanda yake son kashe shi tun kwanan sa bai k'are ba.

Fita Dr yayi ya bar Daddy a d'akin dan kwakwalwar sa na buk'atar hutu sosai, had'uwa sukayi da Anty Amina tace, "Dr ya jikin Zaid d'in?". "Da sauk'i yana bacci ne yanzu". "Ina Daddyn Zaid d'in?." "Shima baya jin dad'i an saka masa drip yanzu yana buk'atar yayi bacci". "Subahanallahi, meya same shi?" Ta tambaya a rud'e tana kallon sa. "Ki kwantar da hankalin ki jinin sa ne ya hau amma komai zai dai-dai ta da ya tashi daga bacci insha Allah."

"Zan iya shiga na ganshi?" "Eh, amma kar ki tashe shi a bacci dan baccin yake buk'ata a yanzu" yana gama fad'a mata haka ya bar wajan ita kuma ta shiga office d'in.

*Abuja.*

Waje d'aya ta zubawa ido kana kallon ta kaga wacce ta nutse a cikin duniyar tunani sabida yadda tayi tagumi da hannu biyu ko motsin kirki bata yi, hannun ta rik'e da hoton wata yarinya kyakykyawar gaske wacce baza ta wuce shekara d'aya da rabi zuwa biyu a duniya ba, sanye cikin kaya y'an kanti kanta babu d'ankwali tayi dariya haqoran ta wanda suka fara fitowa sun fito, mayar da kallon ta tayi ga hoton ta shafa fuskar hoton tace, "ko ina da rabon sake ganin ki Baby Allah ne ya barwa kansa sani."

"Safiyya" aka kira ta daga bakin k'ofar d'akin cikin taushin murya, juyawa tayi ta kalli wanda yake mata magana ganin waye ya sanya ta goge idon ta ta ajjiye hoton a gefe tace, "Abban Zahra yaushe ka dawo?" Ta fad'a tana k'okarin mik'ewa. K'arasowa wajan yayi ya zaunar da ita yace, "Kina zaune kina tunani ya za'a yi ki san na dawo." Murmushi tayi kad'an tace, "Sannu da zuwa." "Safiyya baza ki daina wannan tunanin naki ba ko?".

Ajiyar zuciya Mummy tayi tace, "Bana tunanin zan daina tunanin Baby a rayuwa ta" ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa, "Safiyya nima kullum da tunanin Maryam nake kwana dashi nake tashi, ban san inda take ba ko tana raye ko tana mace Allah ne ya sani, amma yadda nake daurewa kema haka ya kamata ki dinga daurewa kina cire tunanin a ranki mu cigaba da addu'a ko Allah zai bayyana mana ita, dan Allah ya sani kwanakin nan ina yawan mafarkin wata yarinya budurwa mai matuk'ar kama dani amma ban san wacece ba."

Ajiyar zuciya tayi tace, "Allah ya biye bakin ka, ranar da Allah ya bayyana min Baby ban san irin farin cikin da zanyi ba, tabbas indai ina da lafiya zanyi azumi uku na godiya ga Allah" ta fad'a hawaye na gangarowa daga idon ta.

Murmushi yayi k'aunar matar tasa na sake shiga zuciyar sa yace, "Allah zai amince insha Allah, ku shirya zamu je Kano gobe akwai aikin da zai kaini na sati biyu ku shirya sai muje gabad'aya na saka a gyara gidan mu na can, ki sanar dasu Zahra tun yanzu su san da maganar da gobe da safe zamu tafi. "Kace zanje naga Zaid" ta fad'a da d'an murmushi a fuskar ta.

Shima murmushin yayi ya mik'e tsaye yace, "Azo a bani abinci Mummyn Baby da Zaid" ya fad'a yana ficewa daga d'akin nata.

*Kano.*

"Wai Ibteesam kukan ne har yanzu?" Umma dake tsaye a bakin k'ofar d'akin su Ibteesam ta fad'a tana kallon ta a kwance a kan gado tana kuka, goge hawayen idon ta tayi ta mik'e zaune tace, "A'a Umma kawai na kasa bacci ne". K'arasowa d'akin Umma tayi tace, "Me ya hana ki baccin?". "Hasken filita" ta fad'a tana mik'ewa da nufin kashewa.

"Abban ku yaje gidan su Zaid d'in aka sanar dashi an kaishi asibiti yaje asibitin kuma bai gan shi ba bai kuma ga mahaifin nasa ba shiyasa ya dawo yace gobe da safe zai koma insha Allah". Ruwan da ta d'auka zata sha ne ya sub'uce a hannun ta ya fad'i k'asa, ta juyo ta kalli Umma tace, "Abin har ya kai shi ga kwanciyar asibiti?" Ta fad'a tana zaro ido waje cikin tsoro da fargaba had'i da tashin hankali.

"Ki kwantar da hankalin ki ki kwanta zuwa gobe zamu san halin da yake ciki, kifa kwanta kar na dawo na ganki ido biyu" Umma ta fad'a lokacin da ta fita daga d'akin tare da kulle k'ofar.
Kan gadon ta koma ta zauna ta fashe da kukan da bata san dalilin zuwan sa ba a lokacin, babu abinda take gani a idon ta sai Zaid lokacin da yake tari jini na fita a bakin sa, ajiyar zuciya tayi tare da lumshe ido ta bud'e ta goge hawayen ta, kwanciya tayi ta rufe idon ta ba dan tana jin baccin ba sai dan rashin sanin wanne kalar tunanin zata yi.

*
Daddy bai farka ba sai k'arfe goma da wani abun na dare yana bud'e ido ya ga Anty Amina a zaune a kusa dashi tayi tagumi tana kallon sa, "Amina k'arfe nawa?" Ya fad'a yana mik'ewa zaune. Kallon agogon wayar ta tayi tace, "Goma ta kwata yanzu, sannu ya jikin naka?" Ta fad'a tana tasowa tare da matsowa kusa dashi, "Da sauk'i, Zaid d'in bai farka ba har yanzu?". "Bai farka ba". "Ina Dr Auwal d'in?". "Yanzun nan ya fita ya shiga theatre. "

Hannu ya saka yana share gumin da yake kan goshin sa yace, "Ina Musa yazo ma yar dake gida ni zan zauna da Zaid d'in". "A'a Daddyn Zaid kaima ba lafiyar ce da kai ba gwara ka bar ni nima n kwana a nan d'in ko dan kai." "A'a ni naji sauk'i bana jin komai yanzu a jiki na, ke kuwa ba ke kad'ai bace kema kina buk'atar hutu, ina waya ta?" Ya fad'a yana lalube-lalube, a gefen table d'in Dr Auwal ta hango ta ta d'auko masa ta kawo, d'an dannawa yayi kafin ya kara a kunne yace, "Musa kana ina?". Shiru yayi alamun yana bashi amsa kafin ya sake cewa, "To ga Amina na zata fito ka mayar da ita gida banda tuk'in ganganci" ya fad'a tare da kashe wayar, kallon ta yayi yace, "Yana waje kije ku tafi in Allah ya kaimu gobe sai ki dawo kinga an bar Eman ita kad'ai a gidan". Mik'ewa tayi jiki babu kwari tace, "bana so na tafi na barku cikin wannan yanayin da kuke ciki kai da Zaid" ta fad'a a sanyaye tana kallon sa, "Kar ki damu zamu warware insha Allah, kije yana jiran ki". Babu yadda ta iya dole ta gyara zaman hijjabin ta ta fita.

Tsaye Daddy ya mik'e ya d'auki hular sa ya saka tare da glass d'in sa ya fito daga office d'in, d'akin da Zaid yake ya shiga ya hango shi a kwance, jiki a sanyaye ya k'arasa inda yake yana kallon fuskar sa, yana kwance sanb'al hannun sa d'aya an jona masa ruwa ga wasu nan kusan roba uku wanda suka k'are, a hankali numfashin sa yake sauka kana ganin yanayin numfashin nasa kasan bai dai-dai ta ba, hannu Daddy ya saka yana shafa kansa yace, "waye yake neman rayuwar ka haka Zaid? Waye yake k'okarin yi min yankan qauna?" Ya fad'a a hankali yana shafa kansa.

Barin jikin gadon yayi ya zauna a kan doguwar kujerar da take d'akin yana kallon sa, wayar sa ya d'auko yana duba kiran da akayi masa nan yaci karo da kiran Abban Ibteesam ganin dare yayi babu damar ya bi kiran ya saka ya k'yale shi da nufin zai kira shi gobe.

Har garin Allah ya waye Zaid bai farfad'o ba yana kwance a yadda yake, a lokacin y'an dubiya suka fara dandazon zuwa duba shi, Daddy kam yana zaune kusa dashi ya kasa motsawa ko nan da can ne, har Anty Amina ta zo ita da Eman bai tashi ba bacci yake sai dai zuwa lokacin numfashin sa ya fara dai-dai ta, Anty

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login