Showing 30001 words to 33000 words out of 171073 words

Chapter 11 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7819

saka Jidda ta kawo miki abinci" ta fad'a tana mik'ewa ba tare da ta kalli Ibteesam ba ta fice daga d'akin.

Da kallo tabi Umman tata tana jin wani irin so da k'aunar Umman tata yana sake bin jikin ta, ta kasance mace mai kula da yaranta ko yaya taga canji a tare da d'ayan su sai ta tambaye shi abinda yake faruwa ko kuma ita ta bincika da kanta, lokacin da ta fara period ma ita ta koya mata yadda zata saka pad da hatta wankan da zatayi da jinin ya d'auke ita tayi mata da kanta, ita take zaunar dasu ita da Jidda duk wani abu da iyaye mata ya kamata ta sanar da yaran ta mata take fad'a musu tun suna jin kunya har suka d'an rage suna tambayar ta duk abinda ya shige musu duhu, hakan ya saka tasan ranakun period d'in ta ita da Jidda tasan lokacin da suke farawa tasan lokacin da suke gamawa, Ajiyar Zuciya Ibteesam tayi tana tuno kamanin Zaid a idon ta, tsaki tayi tace, "na tsane ka wallahi bana san ganin ka ko kad'an, sai kyawun fuska babu kyaun zuciya."

Umma na fita daga d'akin ta saka Jidda ta kaiwa Ibteesam abinci ta koma b'angaren Abba, ya fito daga wanka yana shiryawa ta shiga d'akin da hanzari ko sallama bata yi ba, da sauri ya juyo yana kallan ta yace, "Halisa lafiya?" Meya faru kika shigo haka kamar an cillo ki?". Maimakon tayi magana sai kawai ta fashe da kuka ta zauna a gefen gadon tare da d'ora hannuyen ta a kan fuskar ta, da hanzari ya k'arasa inda take ya zauna ya sauke hannayen ta daga fuskar ta ya rik'e yace, "ki sanar dani abinda ya faru". "Ibteesam" abinda ta iya furtawa kenan tana cigaba da kuka.

"Me ya faru da ita? Ki daina kuka kiyi min bayani magana". "Yayi mata fyad'e Abban Jafar, abinda muke gudu ya faru" ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da wani sabon kukan. Shiru Abba yayi shima hankalin sa a tashe jikin sa yayi sanyi sosai, matsowa yayi kusa da ita sosai kafin ya jawo ta ya rab'a ta da kafad'ar sa yace, "ita ta fad'a miki?". D'aga masa kai tayi kawai tana cigaba da kuka, "to amma ta sanar dake yaushe abun ya kasance? Ina nufin ranar yaushe kenan?". "Tace shekaran jiya ne" ta bashi amsa tana d'agowa daga jikin sa.
Shiru Abba yayi yana kallan ta cikin sanyin jiki yace, "To yanzu ya kike so ayi Halisa?".

"Kasan dai Yayan Dada da suke ciki d'aya shine alkhalin alkhalai na Kano, wajan zamu kai k'ara ya bi mata hakkin ta, na farko ya sace ta ta kwana shida a wajan sa ba tare da laifin komai ba, na biyu ya mata duka kai baka ga shatin belt a jikin ta ba bayan fasa mata kai d'in da yayi, jaka ce ita ko an fad'a masa bata da gata ne? Ko dan baban s Ambassador ne shiyasa yake ganin zaiyi abinda yaga dama,? Sannan yayi mata fyad'e na wulaqanci dan yana ganin kamar yafi k'arfin hukuma ne, to bai isa ba dole yayi zaman prison ko dan a nuna masa kud'i basu ne komai a rayuwa ba" ta k'arasa fad'a cikin fad'a hawaye na zuba a idon ta.

Shikam Abba zuba mata ido kawai yayi har ta kai k'arshen fad'an nata kafin yace, "Duka na amince da dalilin ki na farko na k'arshe ne ban amince dashi ba, kin manta da cewa a yanzu haka Ibteesam matar sace? Ko kin tab'a jin inda mace ta kai k'arar mijin ta tace yayi mata fyad'e Halisa?". "Nida kai mune kad'ai muka san mijin tane bayan mu babu wanda ya sani dan haka ka ajjiye zancen miji a gefe, ko da yake daman ai sai alkhali ya fara raba auren nasu kafin na zayyana masa duka tuhumar da muke masa."

"To shikenan, kar kiyi magana da kowa ko Dada ce ki dai sanar da ita ta dawo ni kuma yanzu zanje unguwa daga nan zanje masallacin Juma'a bayan an idar kuma akwai d'aurin auren da zan tsaya, ki bari na dawo sai muyi maganar kinji ko?". "Yauwa gwara kaje ka dawo a san abin yi gaskiya" ta fad'a tana goge fuskar ta da hannun ta, murmushi yayi ya mik'e ya cigaba da shiryawa ya fita ya barta yana murmushin da shi kad'ai yasan ma'anar sa.

*Abuja.*

Zaune yake a falo yana kallan tv, a zahiri kallan tv yake amma a bad'ini wani tunanin kawai yake yi daban wanda bai san dalilin sa ba, ajiyar z??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????uciya yayi ya mik'e zaune sosai yana sake lumshe ido tare da bud'ewa, numfashi ya fesar tare da furta, "Meyasa nake ganin ta always?" Ya fad'a yana d'an dukan kansa yana jan dogon tsaki.

Ajiyar zuciya yayi yace, "A jini na ina jin na tsane ta why nake ganin ta a ido na koda yaushe?." A fusace kawai ya mik'e ya d'auki wayar sa da key d'in motar sa gabad'aya zaman Abuja ya ishe shi.

*Kano.*

Tun bayan fitar Umma Ibteesam take a zaune tana kallan waje d'aya, Shigowar Jidda ya katse mata tunani ta kalle ta tace, "Jiddalo na nayi kewar ki" ta fad'i da murmushi a fuskar ta.

"Yaya ta ga abinci" Ta fad'a da murmushi tana zama kusa da ita, "Bani labarin abinda ya faru bayan bana nan". "Lah kin san mene Yaya? Yawancin kullum sai Khalid yazo gidan nan a kan maganar ki". Zaro ido Jidda tayi cikin farin ciki tace, "dan Allah da gaske?". "Wallahi da gaske, baki ga yadda yake shiga damuwa kullum in yazo akace ba'a yo waya ba."

Murmushin farin ciki Ibteesam tayi tana jin k'aunar Khalid na sake ratsa ko jikin ta tace, "Allah sarki ashe yana sane dani." "Gaskiya yana sonki sosai Wallahi baki ga yadda ya rame ba". "Ina wayar ki?". "Tana d'akin Umma." "Kinga d'auko min na kira shi tawa ni ban san a inda take ba". Da to ta Mik'e ta fita ta shiga d'akin Umma ta d'auko wayar ta kawo mata.

Number wayar Khalid da ta haddace saka tare da kiran wayar, har ta katse ba'a d'auka ba ta sake kira ta sake katsewa ba'a d'auka ba sai ta ajjiye wayar a kusa da ita, ba'a fi mintina biyar ba taji k'arar wayar a kusa da ita tana dubawa taga Number sa ta d'auka tare da sallama, daga can b'angaren ya amsa tare da fad'in, "Wake magana?". Ibteesam ta lumshe ido jin yadda muryar sa ta daki kunnen ta har cikin zuciyar ta taji, "ka gano da kanka" ta fad'a murya can k'asa tana murmushi. "Ina aiki ne pls a fad'a min wake magana before na kashe wayar". "Ibteesam" ta fad'a a hankali.

Tana fad'ar hakan ya d'auki muryar ta, cikin rud'u ya mik'e tsaye yake furta, "Ibteesam da gaske kece? Yaushe kika dawo,? Kin san adadin damuwar da na shiga da bakya nan,?" Ya fad'a murya a sanyaye kamar zaiyi kuka. Jin yadda ya rud'e ya bata nishad'i ta gyara kwanciyar ta tace, "Jiya da daddare na dawo gida." "Alhamdulillah masha Allah, Ibteesam na shiga damuwa bana iya komai sai tunanin ki, ina son ki Ibteesam ina k'aunar ki wallahi, ban tabbatar da son da nake miki ba sai yanzu ji nake in na rasa ki zan iya rasa raina?."

Ji take kamar an mata albishir da kujerar makka sabida farin cikin da take ji yana bin ko wanne sassa na jikin ta, bata ce komai ba sai sautin murmushin ta da yaji a kunnen sa, "Kinga yanzu ina Katsina amma yanzu zan tawo gobe zan shigo na ganki insha Allah". "Toh Allah ya kaimu ya dawo da kai lafiya." "Amin my love, ki rik'e wayar a hannun ki zan kira ki". Daga haka suka kashe wayar sukayi sallama.

Washe gari.

Zaid yana zaune a cikin Tahir guest palace ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'a k'afa, matashin saurayj? ne a zaune kusa dashi fari kyakykyawa wanda a shekaru bazai wuce sa'an Zaid d'in ba, "Zaid magana nake maka fa" Hameed ya fad'a yana kallan Zaid. "Hameed me zance maka ne? Bani da time d'in da zan zana shoe design bana cikin nutsuwa at now." Da mamaki yake kallan sa yace, "Me yake damun ka?". "I don't know why nake ganin ta a ido na, Hameed i hate her alot but yanzu koda yaushe indai na kulle ido na ita nake gani" ya fad'a yana lumshe idon sa.

Hameed zaiyi magana aka buga k'ofar d'akin, Zaid ya bada izinin shigowa Wizzy da Mugu suka shigo, "Sai yanzu?" Ya tambaya yana hararar su, "Sorry Mai gida traffic yayi yawa ne" suna fad'a tare da zama a kan kujera. Wizzy ya gyara zama yace, "Mai gida Gaye yana ta kuka yana cewa a baka hak'uri bazai sake aikata abinda yayi ba". Tab'e baki Zaid yayi yace, "Bana buk'atar sa yanzu ko ganin sa bana so." "Mai gida Hameed ka taya mu bashi hak'uri ya yafe masa" Mugu ya fad'a yana kallan Hameed da yake kallan su.

"Me yayi masa?" Hameed ya tambaya yana kallan su Wizzy, sosa kai Mugu yayi kafin yace, "Akwai wata yarinya da Mai gida ya saka aka d'auke ta to shine muka same shi yana k'okarin yiwa yarinyar fyad'e shine yayi fushi dashi over shi kuma ya shiga damuwa sosai dan bai d'auka yarinyar da mahimmaci a wajan a wajan sa har haka ba" Hameed ya kalli Zaid yace, "A'a daman ba kace min abinda zakayi mata kenan ba? To meye abin damuwa dan yayi maka aikin da kake so zakayi?" Hameed ya tambaya yana kallan sa, dan lokacin ds ya sanar dashi babu yadda bai masa akan ya k'yale ta ba yak'i ji.

"U know what? Ban san meyasa nake jin ta a jiki na ba, abinda na sani kawai na tsane ta amma ko? yanzu ma ina so na ganta" ya k'arasa fad'a yana runtse idon sa, Hameed ya zaro ido tare da kallon su Wizzy suka danne dariyar su Hameed yace, "Do you love her?". A firgice ya bud'e idon sa ya kalli Hameed yace, "What? Amma kamar yanzu na fad'a muku cewa i hate her ko baku da kunne ne? Na tsane ta bana son ta ko kad'an, but ina so na ganta" ya k'arasa fad'a a fusace yana mik'ewa tsaye. "Wai tsaya wacce yake cewa ya tsana din itace dai wacce Gaye d'in yayi attempting d'in yiwa fyad'e?" Hameed ya tambaya yana kallan Wizzy, d'aga masa kai yayi alamun eh dan baya so yayi magana tasa tayi zafi dan yaga ogan nasu ya hau sama, "Zaid kana son ta" Hameed ya fad'a yana kallan Zaid da yake tsaye.

"Mtsww bakwa ganewa ne wai? Nace muku na tsane ta bana son ta bana son me son ta kar wanda ya kuma cemin ina son ta" ya fad'a cikin b'acin rai yana kallan dukkan su, dariya Hameed yayi ya mik'e tsaye shima yace, "Shikenan munji baka son ta amma kana son ganin ta, yanzu dai ya maganar mu?". "In anjima ka dawo nan ka same ni muyi maganar." "Ba'a gida ba?". Tab'e baki yayi yace, "Bazan koma gida yanzu ba har sai Daddy ya nemi ni, Wizzy muje ka kaini gidan su."

Zaro ido Wizzy yayi yace, "Gidan su wa?".

Maimakon ya bashi amsa sai yaja tsaki tare da ficewa daga gidan, da sauri Mugu da Wizzy suka bi bayan sa Hameed yana ta dariya.

A b'angaren Ibteesam kuwa suna zaune a harabar gidan su ita da Khalid suna hira, Ibteesam ta kalli Khalid tace, "kasancewar kai lawyer ne ina so ka tsaya min wajan bi min hakki na a wajan azzalumin da ya sace ni." Gyara zama Khalid yayi yace, "Baki da damuwa Ibteesam nake yiwa wani ma balle ke? Fad'a min akan abinda za'a yi k'arar sa." Ajiyar zuciya tayi kana tace, "Na farko kaga bashi da wani dalili mai k'arfi da ya sace ni, na biyu kuma duka babu irin wanda bansha ba gabad'aya jiki na shatin dukan sane......" ta k'arasa fad'a muryar ta na canjawa zuwa muryar kuka.

Hankalin Khalid ya tashi sosai ya rud'e ganin tana kuka ya saka yace, "Ki daina kuka dan Allah duk abinda kike so za'a amma ki daure ki goge hawayen nan ina jin zafin su a zuciya ta". Hannu ta saka ta goge idon ta ta kalle shi tace, "Yanzu yaushe za'a shigar da k'arar?". "Kinga yau saturday sai dai mu bari zuwa monday, amma bayan wannan bai miki komai ba?" Ya tambaya yana kafe ta da idon sa.

Zata yi magana kawai aka bud'e gate d'in aka shigo without excuse, d'ago kai sukayi dukkan su suka kalli wanda suke shigowa, mik'ewa tayi a gigice tana zaro ido waje tana nuna su da yatsa, caraf taji an rik'e yatsan nata dan bata san ya k'araso bama an lak'wasa shi da k'arfi, ihu take sosai amma hakan bai hana ya saki hannun nata ba, "Ke wace da zaki nuna ni da tsaya? Nace wacece ke?" Ya fad'a yana zaro mata idanu.

Cika mata hannu yayi ya zuba hannayen sa a aljihu yana k'arewa gidan nasu kallo tare da tab'e baki, "Wizzy" ya furta a hankali yana sake kallan gidan, "Mai gida" ya amsa yana matsowa kusa dashi, "ashe ma yarinyar y'ar matsiyata ce amma take min rashin kunya." "Mai gida ka gani da idon ka" ya fad'a yana kallan sa.

"Su waye ku? Daga ina kuke zaku shigowa mutane gida haka kawai babu neman izini?" Khalid ya fad'a yana kallan su da b'acin rai, kallan Khalid Zaid yayi ya mayar da kallan sa ga Wizzy tare da furta, "Shine?". Wizzy yace, "Shine mai gida." K'arewa Khalid kallo Zaid yake tun daga sama har k'asa kamar yadda shima yake k'are masa kallo, Khalid shima fari ne amma ba irin farin nan sosai ba yana da tsayi sosai, yana da kyau shima dai-dai nasa, "kai kasan wace waccan?" Ya tambayi Khalid yana nuna masa Ibteesam.

"Ban sani ba sai ka sanar dani" ya fad'a cikin gatse yana hararar sa, "Love shine fa wanda nake baka labari, shine d'an shaye-shayen da nake fad'a maka yanzu" Ibteesam ta fad'a daga can gefe tana hararar sa. "Ohh i see shiyasa kana ganin sa kaga mara tarbiyya, wannan abinda yafi abinda yayi miki ma ai tsaf zai aikata kalle shi fa." Bai kula Khalid ba sai takawa da yake a hankali ya zura hannayen sa cikin aljihun wandon sa, yana zuwa kusa da bai tsaya jiran wani abu ba ya d'auke ta da mari mai zafi, "kar a sake" ya furta yana d'aga mata gira d'aya.

Sai da Ibteesam ta kifa sabida yadda marin ya shige ta tunda unexpected taji marin, ganin hakan ya saka Khalid cikin masifa yace, "Kai waye da zaka zo har cikin gidan su ka dake ta? Wato shaye-shayen naka har ya kaika ga zuwa har gidan su ka dake ta bayan dukan da tasha da ka d'auke ta?". A fusace ya juya ya kalli Mugu yace, "Ku rik'e min shi". Ai ba musu suka kama Khalid suka bank'ara hannayen sa kamar kaza, dawo da kallon sa yayi ga Ibteesam fuskar sa a had'e kamar kullum yace, "Kee kalle ni daga da kyau ki fad'awa wannan kod'ad'an saurayin naki ya fita a harkar ki tun kafin na saka a illata shi" ya fad'a yana nuna ta da yatsa.

"Wallahi baka isa ka raba mu ba domin kuwa shine wanda zan aura" ta fad'a tana jifan sa da mugun kallo, "Keee! Har ni zaki kalli ido na kice min shine wanda zaki aura,? Kina da hankali kuaa" Ya fad'a yana yin kanta kamar zai dake ta.

Tsayawa yayi ya dawo da baya ya kalli Khalid yace, "Kana ji tun muna shaida juna da kai ka fita harkar ta, in ina tare da abu nawa ne ni kad'ai ba'a rab'ar sa in kuma kana so ka bak'unci lahira shikenan" ya fad'a yana d'age kafad'ar sa.

"A kan me zakace na rabu da ita? Kai waye d'in ta?" Khalid ya tambaya yana kallan sa, juyowa Zaid yayi ya zuba masa ido kafin ya mayar da kallan sa ga Ibteesam da take tsaye tana hararar sa, "baka buk'atar kasan waye ni d'in na fad'a maka ne kawai in kaji" ya bashi amsa yana d'an dafe jijiyoyin kan sa da suka fara harbawa, "wallahi baka isa ka raba mu ba kayi kad'an, kome kake tak'ama dashi nima ina tak'ama dashi".? Yana juyowa ya d'auke shi da mari mai zafin gaske ya nuna shi da yatsa yace, "bana magana ana magana ka gane ko? In naso yanzu a nan wajan zan saka a fito min da kayan cikin ka ina yi maka warning ne badan kafi k'arfi na ba ka gane?".
"Ke kuma in na sake ganin ki da wani ranki ne zai b'aci, zan b'ata miki rai irin wanda baki tab'a tunani ba" ya fad'a yana kallan inda Ibteesam take yana nuna ta da yatsa.

"A matsayin ka nawa? Wallahi baka isa ba kayi kad'an. "

"Matsayi na wanda ya isa dake in kuma kina ganin kamar hakan bazai kasance ba ki k'ara ki gani."

Juyawa yayi da niyar barin gidan sai ya juyo ya dawo inda take yace, "and in na sake ji in kira wannan da suna Love wallahi sai na fasa miki baki, in kina musu kuma kiyi naji".

"Wallahi baka isa ba sabida ba kaine ka haife ni ba, na tsane ka bana son ka ba kuma na qaunar ganin ka."

"Nima na tsane ki bana son ki bana qaunar mai sonki, but na tsani na ganki da wani, wallahi na sake ganin ki da wani ranar kin jawo masa dan sai na saka an canja masa kammani yadda ko iyayen sa basu gane shi ba, umarni nake baki bawai shawara ba, i hate u alot but kika sake na ganki da saurari wani ko kika tsaya da wani ina......" ya nuna ta da hannu alamun zaki gani.

_Tofa akwai rikici fa... ga Zaid ya fara nuna iko akan Ibteesam, Anya zata bi dokar da ya kafa mata,? meye dalilin Ibteesam na cewa Zaid yayi mata fyad'e bayan babu abinda yayi mata? Wanne shiri take dashi a kan hakan...? kar ku manta a gida Eman tana can tana jiran dawowar mijin ta Zaid, yaya kuke gani anya Zaid zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login