Showing 120001 words to 123000 words out of 171073 words

Chapter 41 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7817

ga Zaid a kwance ga kuma rasuwar da akayi sannan ga jikin Yaya Babba duk sai ya rud'e ya rasa abinda zaiyi, Yaya Bala da Uncle Saifu da suke tsaye a cikin d'akin jikkunan su yayi sanyi suka kalli Daddy Yaya Bala yace, "Ka zauna a nan kafi samun nutsuwa sabida Zaid d'in kaima kuma ba lafiyar ce da kai ba, mu zamu bi gawar ayi komai damu in yaso sai mu dawo" Daddy ya d'ago jajayen idon sa ya kalle su sukayi d'aga masa kai alamun hakan za'ayi, Daddy ya kalli Anty Amina yace, "kuje tare Amina in akayi jana'izar sai ku dawo ni zan zauna wajan Yaya Babba" ya fad'a muryar sa a shake.

Da to kawai ta amsa ta bi bayan su ita da Ibteesam da ba haka taso ba.

Dake rasuwar safiya ce ana azahar aka d'auki gawar aka tafi kaita gidan na gaskiya yaran ta na ta kuka haka y'an uwan ta da dangin ta baki d'aya.

Bayan an dawo daga kai gawar Anty Amina da Ibteesam suka dawo asibiti a nan suka tarar da Mummy da Abban Ibteesam d'in a zaune wajan Daddy, duka suna zaune a cikin d'akin da Yaya Babba likitan da yake ta aikin sa yace, "Alhaji ya samu karaya hannu sannan kuma ya samu buguwa k'afa, amma Alhamdulillah mun samu an d'ora hannun tunda Allah ya tak'aita karayar ba mai jini bace, yanzu k'afar kuma anyi mata treatment d'in da ya kamata insha Allah komai zai dawo dai-dai. " Daddy yace, "Dr in kana ganin da matsala kawai ayi visa a tafi dashi Egypt ayi gyaran a can". Dr yayi murmushi yace, "Babu damuwa insha Allah komai zai dawo dai-dai da izinin Allah." Mummy tace, "Ya jikin Zaid d'in?". Dr yace, "Jikin nasa da sauk'i an samu bugun zuciyar tasa ya fara daidaita abinda ya rage kawai ciwon kan ya sake shi in ya sake shi ya dawo dai-dai shima zai samu lafiya". Ajiyar zuciya dukkanin su sukayi Ibteesam kuwa lumshe ido tayi tana hango Zaid d'in kawai a idon ta.

Yaya Bala da Uncle Saifu da suke tsaye a wajan suka kalli juna a tare Yaya Bala ya fita shima Saifu ya bi bayan sa, a zaune ya same shi yayi tagumi yana tunani shima ya zauna kusa dashi, "Saifullahi kalli bawan Allah can ka duba irin abubuwan da muka aikata masa a rayuwa musamman ma Yaya Baba amma kalli yadda yake? zaune a kusa dashi har yana batun za'a kaishi k'asar waje ayi masa aiki, in Allah ya baka kyakykyawar zuciya ya gama yi maka komai a duniya da kuma lahira, Saifullahi kalli fa yadda yake nuna damuwar sa akan Yaya Babba bayan duk tarin abubuwan da yayi masa, yau d'in ma sun tafi nemon maganin kashe shi Allah ya nuna musu basu isa ba, tabbas in mutun ya kasance bai nufi kowa da sharri ba yana zaune da kowa da zuciya d'aya Allah yana bashi kariya ta musamman wacce ba kowa yake bawa ita ba, kai in banda kariyar Allah Abubakar ya isa ya tsallake abubuwan da Yaya Babba ya aiko masa dasu ne?" Yaya Bala ya fad'a muryar sa a sayanye.

"Bai isa ba wallahi bai isa ba, wani iri nake jina Yaya in na tuna abubuwan da muka yiwa Yaya Abubakar sai naji kamar k'asa ta tsage na shiga, ka duba yadda kaikayi ya koma kan mashek'iya lokacin da suka so kashe matar Zaid d'in, ka duba yau sun tafi nemo maganin kashe wani Allah ya kashe Hajiya Batula ba tare da an nemo maganin ba shi kuma yana kwance hannu babu lafiya k'afa ma babu lafiya, in baka ji tsoron Allah ba aduniyar nan kana tare da wahala, gashi a nan Allah ya nuna musu basu isa suyi abinda bai nufa ba" ya k'arasa fad'a shima kamar yayi kuka

Ajiyar zuciya Yaya Bala yayi yace, "Haka ne Saifullahi daman duk cikin mu yafi mu son y'an uwan sa haka kuma ya fimu zuciya mai kyau, har su Hajiya suka bar duniya kullum cikin saka masa albarka suke sabida yadda ya kula dasu da jikin sa da kuma aljihun sa, yana son mu amma mu muka muna nuna masa kiyayyar babu gaira babu dalili muka nuna dukiya ta fishi mahimmaci a wajan mu, Allah ka yafe mana dukkan abubuwan da muka aikatawa wannan bawan naka". "Amin Yaya Bala" ya amsa shima da yanayin da yake nuna rauni a tare dashi.

Daddyn ne ya fito ya gansu a zaune yace, "Yaya Bala ana kiran la'asar" ya Fad'a cikin kula da girmamawa, a tare suka tafi masallaci don gabatar da sallah.

Haka aka cigaba da jinyar Yaya Babba da Zaid da har lokacin ba'a zuwa inda yake har tsahon kwana uku zuwa lokacin anyi sadakar uku na rasuwar Hajiya Batula, babu laifi jikin Yaya Babba da sauk'i dan yanzu yana iya magana sosai sai dai hannu da yake a d'aure da kuma k'afar da baya iya motsa ta sosai, b'angaren Zaid kuwa yana nan a kwance kamar kullum yana samun taimakon numfashi ta na'urorin da suke taimaka masa, Ibteesam ta rame gabad'aya ta fita daga hayyacin ta sabida rashin lafiyar Zaid kullum da tunanin sa take kwana take tashi in tana kwance sai taga kamar zata ganshi hakan ya saka ta tattara ta koma gidan Mummy da kwana sabida acan gizo yake mata, duk ta dauki laifin rashin lafiyar sa ta d'orawa kanta kullum cikin damuwa da kuka sai Mumny ta rarrashe ta ake samu take shiru.

Rana ta hud'u itace wacce aka gano k'ashin k'afar Yaya Babba ne ya goce bayan anyi x-ray, babu yadda likitoci basu akan a barshi a asibitin ba amma Daddy yace sam dole a fita dashi waje, hakan ce ta kasance da Yaya Bala da Uncle Saifullahi aka yiwa visa zuwa k'asar Egypt.

Waje gari da yamma likitan ya shiga sake duba Yaya Babba wanda ya rage saura baifi awa biyu jirgin su ya tashi ba yana cikin duba Yaya Babba sai kace cewa, "Samun d'an uwa wannan zamanin kamar d'an uwan naku yana wahala, a wannan zamanin da muke ciki wanne d'an uwa ne yake tsayawa haka akan sabgar y'an uwan sa in ba wanda Allah ya zab'a ba? In kaga hankalin su ya tashi haka to matar su ko y'ar su amma ku duba ya bar d'an sa da yane cikin suma anan amma zai fitar da shi waje, gaskiya ku godewa Allah d'an uwan ku yana sonko" likitan ya fad'a yana kallon su su uku yana murmushi.? Suma murmushin kawai sukayi bayan jikin su yayi sanyi sosai.

Yaya Babba yace, "Bala kira min Abubakar". Ba musu ya mik'e a lokacin Daddy ya shigo yana fad'in , "zuwa anjima kad'an za'a tafi Airport an gama komai" ya fad'a yana k'arasowa cikin d'akin.? Yaya babba ya zuba masa ido sai kawai ya fara kuka, hankalin Daddy ya tashi sosai yace, "Yaya babba jikin ne? Dr!" Daddy ya fad'a da d'an k'arfi. "Ba jiki bane Abubakar, Abubakar ka yafe min na cutar da kai" Yaya Babba ya fad'a yana cigaba da kuka. Hannun sa Daddy ya rik'e wanda babu ciwon ya zauna yace, "Babu abinda kayi min Yaya Babba ko kayi min ma na yafe maka ka daina kuka dan Allah". Girgiza kai yayi yace, "A'a Abubakar nayi maka kaine baka sani ba, nine silar mutuwar matar ka Maryam, haka naso na zama silar rasuwar d'an ka Zaid da kai kanka da kuma sirikar ka, ka yafe min dan Allah Abubakar".

Duk dauriyar da Daddy yaso yi sai da yaji wani dummm akan sa da kwakwalwar sa jin abinda Yaya Babba ya fad'a duk da ya sani amma sai yaji kamar a lokacin yaji maganar rasuwar Maryam d'in, d'an runtse ido yayi kafin ya bud'e fuskar Maman Zaid na sake fad'o masa a ransa, yadda tasha wahala akan ciwon da aka rasa meye ya tuna sai ya sauke numfashi yace, "daman lokacin rasuwar tane yayi ko baka zama sila ba a lokacin zata mutu, ka daina fad'ar wad'an nan maganganun kaga baka da lafiya ka kwantar da hankalin ka samu lafiya mayi maganar" Daddy ya fad'a cikin rauni.

"A'a Abubakar ina ji kamar bazan sake dawowa Nigeria da raina ba shiyasa nake fad'a maka, ka yafe min Abubakar dan Allah bana so na mutu da hakkin ka a kaina, ka sanar da Zaid d'in ma ya yafe min Maryam d'in ce dai ta riga ni barin duniya ban nemi yafiyar ta ba" ya sake fad'a cikin kuka sosai. Daddy yace, "na yafe maka Yaya Babba na yafe maka da zuciya d'aya har kuma cikin raina, Zaid yana kwance shima bashi da lafiya insha Allah zaka dawo cikin k'oshin lafiya" Daddy ya fad'a cikin sanyin murya.

Daddy ya kalli Yaya Bala yace, "Yaya Bala gwara ku tafi Airport d'in kawai, bara na kira Musa yazo ya kaiku" ya fad'a yana mik'ewa da sauri dan zaman sa a wajan ba k'aramin karya masa zuciya yake ba, godiya yake yiwa Allah da saka ba a gaban Zaid Yaya babba yace shine silar mutuwar Maryam dan da mai raba su sai Allah, ya kuma ji dad'i da Mummy bata wajan itama, babu jimawa aka d'auki su Yaya Babba sai Airport.

Bayan tafiyar su ne Dr Auwal yace suzo dukkan su suje suga yanayin jikin Zaid d'in sabida damuwar da yaga sun yi sosai akan? rashin ganin nasa na kwana biyu, Dr ne ya fara shiga d'akin sannan suka biyo bayan sa, kallon Zaid d'in suke da yake kwance kamar koda yaushe kamar gawa, yayi fari sosai musamman fuskar sa da tafin k'afar sa har wani yellow sukeyi sabida haske, k'afar tayi karr sabida ba'a takawa har shek'i takeyi sabida sanyin a.c da yake ratsa ta, fuskar sa tayi gashi sosai sajen ya cika fuskar sa sosai haka kansa gashi ya fito sai dai ya rame sosai, a hankali kowa yake kallon sa kallon sa dan ba'a son yin motsi sosai gudun kar ya firgita, kuka Ibteesam ta fara tana kallon, girgiza mata kai Mummy tayi alamun ta daina kuka ta d'an rab'a a jikin ta tana bubbuga bayan ta.

Jikin gadon ta koma ta bar jikin Mummy tana kallon sa idon sa a kulle ita kuma tana kuka, bata sani ba ashe kowa ya fita ya barta a d'akin daga ita sai shi ta zame ta rik'e hannun da babu komai a jiki tana kuka hawayen na zuba a hannun sa, "meyasa baza ka tashi ba? Har yanzu baka gama fushi dani d'in bane,? Nafa baka hak'uri nace bazan kuma ba meyasa kak'i tashi? Kana so na mutu ko,?" Ta fad'a kamar zararrriya tana kuka.

"Ina sonka miji na ina sonka, ka daure ka tashi na furta maka wannan kalma ko da sau d'aya ne, ka tashi kaji ka tashi" ta sake fad'a tana fashewa da kuka mai sauti.

K'arar computer kusa da ita ce taji ta k'aru ta kalli computer sai taga numfashi sa yana sake yin k'asa k'iris ya rage ya kai zero, a guje ta mik'e ta fito yana kiran Dr suka shiga da hanzari suka barta a wajan tana kuka kamar ranta zai fita, Mummy tazo ta kama ta ta zauna da ita tana aikin rarrashin ta.

Dr's d'in da suka sun jima kad'an a ciki kafin su fito su kalli su Daddy da kowa jira yake yaji abinda zasu ce.




*Ayi min hak'uri jiya an jini shiru wlh ciwon kaine yake damuna kwanakin nan, in na samu dama ko zuwa dare insha Allah zan sake update.*

*?ASAITAR SO!*

*68_69*

Not edited>?'?




Ko wanne jira yake yaji mai likitan zasu ce hankalin su ya tashi sosai ganin yadda Ibteesam ta fito daga d'akin, "Alhamdulillah ya farfad'o" Dr Auwal ya fad'a da murmushi yana kallon su dukkan su.

Alhamdulillah shine abinda suka furta dukkanin su cikin farin ciki, Daddy yace, "yanzu idon sa biyu?". Dr yace, "A'a anyi masa allurar bacci dan ya d'an samu sauk'i, amma komai yayi dai-dai sai dai a kula da shigar yanayi mara dad'i a cikin wannan yanayin da yake ciki, a kuma kula da sauti mai k'ara a kusa dashi ko hayaniya wacce ta wuce misali abi komai a hankali har ya gama warwarewa".

Mummy tace, "Yanzu zamu iya ganin sa?".Dr yace, "Yanzu ai an canja masa d'aki yana private room zaman sa nan ya k'are, zaku iya shiga amma banda hayaniyar da zata tashe shi daga bacci a barshi har sai ya farka". Anty Amina tace, "Ina ne d'akin?". Dr yace, "yana gaba kad'an dake ta ciki aka shigar dashi ne, muje na nuna muku" yayi gaba suka bi bayan sa har k'ofar d'akin da Zaid yake a kwance.

A hankali suka shiga ciki yana kwance yana bacci kana ganin yanayin yadda numfashi sa yake sauka kasan ya samu lafiya, dukkan su zama sukayi a d'akin kasancewar d'akin yana da girma sosai ga kuma saitin kujeru masu girma kamar falo a zube a d'akin, babu wani mai kwakwkwaran motsi hatta waya duk sun saka ta a meeting.

Suna zaune a nan akayi kiran sallar magariba dole suka mik'e akayi alwala Daddy kuma da Hameed dasu Wizzy da suka kawo ziyara lokacin suka tafi masallaci, har akayi i'sha suna zaune a d'akin a lokacin Zaid ya fara motsawa alamun zai tashi, bud'e idon sa yayi yana kallon sama har ganin sa ya dawo dai-dai ya juyo da kansa ya kalli mutanen d'akin, da Ibteesam suka fara had'a ido ya d'an kalle ta na wasu seconds kafin ya mayar da kallon sa ga Daddy, "ya tashi" Ibteesam ta fad'a cikin muryar da ta nuna zallar farin cikin ta.

Fad'ar hakan da tayi duk sai suka juya suna kallon sa cikin murna, a tare suka mik'e duka suka isa wajan gadon banda Ibteesam da take jin wani iri kamar ba itace take fatan taga ya farka d'in ba, zagaye shi sukayi kowa yana jera masa sannu, sai suka bashi ma dariya ma ganin yadda dukkan su suka rud'e ya d'an saki fuska kad'an kafin ya fara k'okarin mik'ewa, "Hameed maza ka kira Dr" Daddy ya fad'a yana kallon Hameed, ai da sauri ya fita ba jima suka dawo da d'aya daga cikin likitocin da suke kula dashi.

Kusa da Zaid d'in ya k'arasa yace, "Sannu Zaid, ya kake jin jikin naka?". D'an runtse ido yayi kad'an ya bud'e yace, "Babu dad'i" ya fad'a yana k'okarin ya mik'e tsaye, danna wani waje Dr yayi a jikin gadon sai gashi gadon ya mik'e ya zamar masa kamar kujera, "ina ne yake maka ciwo?". Zaid ya sake cewa, "Headache and chest pain". Dr yace, "Sannu zasu daina suma insha Allah, Alhaji yanzu a samu ya d'an yi wanka da ruwa mai zafi sai a bashi tea mai kauri yasha insha Allah zai dawo normal" Dr ya fad'a yana kallon Daddy.

Daddy ya amsa shi kuma Dr ya duba magungunan Zaid d'in kafin ya fita, Mummy ce ta shiga Band'akin da kanta kasancewar private hospital ne akwai water heater ta had'a ruwa mai zafi then ta fito daga band'akin, Ibteesam dai tana zaune kamar munafuka ko motsin arzuki ta kasa yi a wajan sai raba ido da take a zaune, yana kula da ita sai ya tab'e baki yana jin zafin hakan da take yi, dan kowa yazo yayi masa sannu amma banda ita ta nemi waje ta zauna kamar daman zaman tazo yi.

Hameed ne ya taimaka masa ya sakko daga kan gadon amma yana dire k'afar sa a k'asa ya koma ya zauna tare da dafe kansa, sai da ya huta yaji k'afar ta saki sannan ya iya tsayawa suka isa Band'akin a hankali ake tafiyar.

Har zasu shiga sai kuma ya tsaya ya kalli Hameed yace, "Kaya fa?". Juyowa Hameed yayi ya kalli Daddy yace, "Daddy akwai kayan sane a nan?". Daddy yace, "sai dai a d'auko yanzu". Kujerar dake wajan ya zauna a kai ya jingina yace, "aje a kawo" ya fad'a yana lumshe idon sa.

Hameed ne ya d'auki key d'in mota ya tafi d'auko masa kaya, bayan fitar sa Anty Amina tace, "To kasha tea d'in before a kawo maka kayan". Girgiza kai kawai yayi idon sa a kulle har lokacin. Jijiyoyin kansa ya dafe dan sosai suke masa ciwo ya saka hannu yana b'alle ma6allan gaban rigar sa saka bud'e lokacin da aka jona masa abubuwan da suke taimaka masa, Ibteesam duk ta tsargu zaman ya ishe ta ganin kallon kirki ta kasa samu daga wajan sa sak ya koma mata Zaid d'in Kaduna bana Kano ba, tayi shiru kamar bata magana wayar ta tayi k'ara, dubawa tayi taga sunan Hamma Ameer rangad'ed'e akan wayar tata, murmushi tayi kad'an tayi picking call d'in a hankali tace, "Hamma Ameer daman baka manta dani ba?". Shiru tayi alamun tana bashi amsa kafin ta sake yin murmushi sosai muryar ta a k'asa sosai tace, "Shikenan ayi min hak'uri zamuyi magana anjima yanzu bana gida". Shiru ta sake yi kafin tace, "To naji sai anjima d'in" ta Fad'a tana sauke wayar tare da kashewa har lokaci? murmushi ne a fuskar ta.

Kamar ance ta kalli inda Zaid d'in yake sai kuwa suka had'a ido tayi saurin d'auke idon ta amma har lokacin tana jin yawon da idon sa yake a kanta, sai ta sake shiga takura taita gyara zama kamar mai basir, duka suna zaune shiru har Hameed ya dawo d'auke da leda a hannun sa ya k'arasa wajan Zaid d'in ya kama shi suka mik'e suka shiga Band'akin.

A kan wani stool a dake band'akin ya ajjiye kayan shi kuma ya fito, ya jima sosai a Band'akin kafin ya fito tare da alwala, ya shirya cikin bak'ar jallabiya mai dogon hannu mai hula, a hankali ya tako Hameed yayi sauri ya rik'o shi suka dawo kan gadon ya koma yana sauke numfashi a hankali, "Sannu" Hameed ya Fad'a cikin tausayi, kai ya d'aga masa kawai kafin Daddy yace, "Amina ina akwai tea a flask d'in nan ko?". Jawo kayan gefen ta tayi taga akwai da kanta ta had'a masa tea d'in Wizzy ya mik'a masa, ba laifi yasha da d'an dama kafin ya ajjiye yace, "Ni na warke mu koma gida". Mummy tace, "Kai fa haka kake da ka tashi zaka ce a koma gida ka bari ka sake jin sauk'i." "Mummy naji sauk'i, bana son zaman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login