Showing 45001 words to 48000 words out of 171073 words

Chapter 16 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7815

abun" Daddy ya fad'a yana mik'ewa tsaye.

A kwance ya same shi yayi pillow da hannun shi yana kallon sama, a hankali Daddy ya k'arasa inda yake ya cire glass d'in fuskar sa ya kalli Zaid yace, "Me yake damun ka?". Kallan Daddy yayi tare da mik'ewa zaune ya rik'e hannun Daddy idon sa duk ya kawo ruwa yace, "Daddy meye aibu a jiki na da yarinyar can zata dinga cewa bata sona ne?". D'an murmushi Daddy yayi shima ya rik'e hannun sa sosai yace, "Baka da aibu a jikin ka Abdullahi, Allah ya baka cikar halittar da ba kowa ya bawa ba."
"To meyasa bata sona?" Ya tambaya yana rausayar da kai, "dabi'ar ka Zaid itace bata so, inda zaka canja ka koma mutum kamar kowa zata so ka Zaid ina da tabbacin hakan." Kallan kansa yayi yace, "Dad meye aibun dabi'a ta?".

"Ka kalli kayan dake jikin ka mana Zaid a haka kaje har gidan su matsayin su na sirikan ka tunda y'ar su kake so, ka duba kanka ji wani zane da akayi yi maka kamar arne, baka saita harshen ka in zakayi magana, baka da hak'uri ko kad'an, zafin ka yayi yawa komai kace zaka yi duka ko ka nuna iko da k'asaita dole ai tace bata son ka Zaid."

Tab'e baki yayi yace, "duka sai na canja wannan zata so,? Tab ashe kuwa bata tab'a sona ba tunda ba nine nayi kaina ba, ka taya ni da addu'a kawai Allah ya cire min ita daga raina na huta" ya fad'a yana d'age kafad'ar sa. "Zaid kenan, to shikenan kayi yadda kake so amma nima banga laifin ta dan tace bata son ka ba" ya fad'a yana cika hannun sa tare da mik'ewa tsaye.

Wayar sa da tayi k'ara ya saka ya d'auka ganin sunan mahaifin Ibteesam, sun jima suna magana gabad'aya Zaid baya gane mai suke cewa har suka gama, "Zaid yaushe ka fara k'okarin kisa ban sani ba Zaid?" Daddy ya fad'a da mamaki yana rik'e had'a,?yana fad'ar haka yasan daga inda maganar ta fito hakan ya saka yace, "Dad nayi mata warning akan ganin ta da wannan yaron amma bata ji, nan gaba na sake ganin sa a wajan ta sai na harbe shi a k'afa" ya fad'a lokaci d'aya fuskar sa na juyawa yanayin b'acin rai.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Zaid me kake so ka koma ne har haka,? Kayi kidnapping yanzu kuma kisa kake so yi Zaid,? Wacce irin banzayen halaye ka sake d'aukowa kanka haka?" Daddy ya fad'a cikin fad'a da alamaa ran sa ya b'aci.

"Yanzu Daddy ina kallo sai na dinga ganin wani da matata na k'yale shi,? Matata fa? Wallahi bazai yu ba indai ba wanda suke ciki d'aya da ita ba sai nayi masa hukunci dai-dai dashi". Zuba masa ido kawai Daddy yayi har ya shige band'aki ya bar Daddy a tsaye baki a bud'e.

Ya lura lamarin Zaid ba jajayen ido yake buk'ata da fad'a ba addu'a ce kawai zatayi maganin abinda yake yi, k'wafa Daddy yayi ya fice daga d'akin.

Washe gari.

Da wata irin yunwa Zaid ya tashi dak'yar ya samu yayi wanka ya shirya ya sakko k'asa dan yadda yake jin cikin sa a lokacin fruit bazai d'auke shi ba, kitchen ya tarar Anty Amina tana ta aikin had'awa Daddy breakfast kamar kullum, bai kalle ta ba balle ta saka ran zai mata magana ya d'auki k'aramar tukunya ya kunna gas ya d'ora tare da zuba ruwa, a jefe suke ita dashi kasancewar gas d'in bashi da nisa da d'an uwan sa, drower ya bud'e ya tsiyayi mai ya zuba a tukunyar, kayan miya ya gani a inda ake ajjiye su ya d'auka ya wanke su ya kunna blender ya mark'ade su ya zuba a tukunyar.

Nan da nan ya kammala dafa Indomie ya juye a bowl ya saka fork yana niyar fita Anty Amina da take kallan sa tun shigowar sa bata ce komai ba sai da zai fita tace, "Akwai zob'o a fridge in kana so". Ba tare da ya juyo ba yace, "Na sha na mutu ko?" Abinda yace mata kenan ya fice ya barta baki a bud'e.

Eman da take tsaye tana kallon su ta k'araso kitchen d'in ta kalli Anty Amina tace, "Anty nifa gaskiya na gaji da zama haka kawai, sunan ina da aure amma dani da wanda bashi dashi duka d'aya muke, babu wani abun a k'asa ne har yanzu wai?". "Eman har yanzu Abban ki baice komai ba yayi shiru nima kuma jiran maganar sa nake yi". "Gaskiya da sake nikam na gaji wallahi" ta fad'a tana ficewa daga kitchen Amina ta bita da kallo.

K'arfe sha biyu na rana su Uncle Sani suka dira a gidan a ranar harda Mama Asma'u suka zo kaf d'in su, suna zaune ana ta hira sama-sama ana d'an motsa baki Yaya Babba yace, "Nikam bana baza mu leke madina bane Abubakar?". Daddy ya d'an yi murmushi kad'an yace, "Insha Allah baza'a fasa zuwa ba" abinda yace kenan kawai yaja bakin sa yayi shiru.

Takun da suka jiyo ne daga bayan su ya sanya duka suka juya suna kallon wanda yake tawowa, Zaid ne yayi kyau cikin k'ananun kayan da ya saba sakawa sai dai wannan masu mutunci ne dan wandon har k'asa yake rigar ma tana da fad'i ga tsayi, tsayawa yayi ya kalle su d'aya bayan d'aya har sai da yazo kan Mama Asma'u sannan da saki fuska kad'an yace, "Mama yaushe kika zo?". "Ban wani jima da zuwa ba, kai nake ta baza ido nake nema tun d'azu" ta fad'a da murmushi a fuskar ta.

"Meyasa baki kira ni nazo mun gaisa ba, ya gida?". "Lafiya lau Zaid, ya aikin naka?". "Alhamdulillah" ya bata amsa, "masha Allah, ashe kuma ka girma kayi aure duk da auren naka babu gayyata" ta fad'a da niyar zolaya tana kallan sa da murmushi. Annurin da ya bayyana a fuskar sane ya d'auke ya tamke fuska ya kalle ta yace, "Wace matata,? Ni bani da wata mata a duniya sai wacce nake niyar yi, ki daina fad'ar hakan ina ganin girman ki" ya fad'a yana niyar tafiya.

Cak ya tsaya ya kalli su Uncle Sani yace, "Ohh sorry na manta bamu gaisa ba ko,? Ina kwanan ku?" Ya fad'a yana niyar tafiya, "Zaid!" Daddy ya kira sunan shi cikin taushin murya. "Dad ina da aiki ana ta nema na a company kar kace na tsaya pls" ya fad'a a shagwa6e kamar zaiyi kuka.

"D'ana daman shawara muke nema akan tafiyar mu saudia ya kake gani za'a je ko kuma kawai a bari sai Allah ya kaimu azumi?" Unlce Sani ya tambaya da murmushi a fuskar sa, kowa kallan Uncle Sani yake da mamaki a fuskar sa shima kansa Zaid d'in mamaki ne a kan fuskar sa, "D'an ka? Kuma ni,? Tab" Zaid ya furta a hankali yana kawar da kansa gefe.

"Kai muke jira ya kake gani?" Ya katsewa Zaid tunani, "ba da kud'i na za'a je saudia ba, haka sai naga dama zanje so ba matsala ta bane in wanda zai biya mukun yaga zai biya fine" ya fad'a yana d'age kafad'ar sa tare da ficewa daga falon. Da kallon takaici Uncle Sani ya bishi sam shi ba haka so abin ya kasance ba.

"Ku dai yi hak'uri dashi dan Allah, saudia kuma insha Allah za'a je kowa ya aiko min da passport d'in sa nan da sati d'aya zamu tafi insha Allah" Daddy ya fad'a dan ya wanke takaicin da Zaid ya d'ura musu. Baba Bala da Baba Saifullahi da Mama Asma'u sai godiya suke amma Yaya babba ya tamke fuska dan shi sam ba haka yaso ba, yaso Zaid yace baza'a je ba dan baya so aje Saudi d'in ne gabad'aya, yasan indai akaje Daddy zai ta addu'a Allah ya kare shi da duk mai nufar sa da sharri,Allah zai kare shi daga duk wani mugun nufi nasu wannan dalilin ya saka baya so aje.

Kamar yadda yayi alqawarin a ranar bazai je inda Ibteesam take ba hakan ce ta kasance duk da dak'yar ya jure garin Allah ya waye, yana tashi da safe aka yi masa kiran gaggawa a company dole sai da ya dawo yayi sallar la'asar ya shirya cikin k'ananun kayan da ya saba sakawa kullum, yana niyar fitowa daga d'akin sa suka had'u da Hameed ya shigo, kallan sa Hameed yayi yace, "Woww Zaid kaga yadda kayi kyau kuwa?'". "Tabarakallah" Zaid ya bashi amsa yana wuce shi, "nida nazo wajan ka ina kuma zake je,? Ka tsaya mana dan Allah" ya fad'a yana bin bayan sa da sassarfa, bai tsaya ba sai da ya kai tsskiyar gidan zai kunna mota Hameed d'in ya k'araso yana fad'in, "Haba Zaid ina zaka je ne dan Allah kasan muna da abin yi?". "Malam koma ka kulle min d'aki" ya fad'a yana hararar sa, "naji zan koma na kulle maka amma dan Allah ka jira ni na raka ka" ya fad'a yana komawa da sauri, bai jima ba ya dawo yayi sa'a ya ganshi a zaune a mota yana jiran sa ya bud'e ya shiga ya fizge motar a guje suka fita daga gate d'in.

"Yauwa Zaid ya maganar tamu?" Hameed ya fad'a yana kallon sa, banza yayi masa baice komai ba ya cigaba da tuk'in sa cikin k'warewa, "kaga abinda yake had'a ni dakai kenan Zaid, wulaqancin tsiya gare ka". Nan ma baice mai komai ba ya shiga da tuk'in sa har ya faka motar a barakat store ya bud'e ya fice ya bar shi a ciki, da kallo Hameed ya bishi kawai har ya daina ganin sa.

Ya jima sosai kafin ya fito hannun sa rik'e da zob'o mai sanyi bayan sa kuma ma'aikacin store d'in ne rik'e da manyan ledoji guda biyu, ya bud'e bayan motar ya saka Zaid ya bashi kud'i yana ta godiya ya shiga motar ya tafi, "Zaid wai ina zamu je ne?". "Yanzu kayi tambaya mai kyau, zan je wajan Baby na" ya fad'a yana cigaba da tuk'in sa.

Baice komai ba har suka isa k'ofar gidan su Ibteesam, "Ina ne nan kuma?" Hameed ya tambaya yana kallan sa yana kuma kallan gidan su Ibteesam, baice komai ba ya bud'e motar yana kallan k'ofar gidan kafin ya juya ya bud'e bayan motar yana niyar d'auko kayan da suke bayan motar, cak ya tsaya kamar an saka masa pause ya juyo a hankali har ya zube idon sa a kan fuskar Ibteesam da take tafiyar ta a hankali ita da Jidda, k'are mata kallo yake sanye take da riga da siket na atampa, rigar har giuwa siket d'in kuma street me tsaga y'ar kad'an a baya, kanta ta yafa bak'in chantily veil ya sakko har tsintsiyar hannun ta, sosai tayi kyau duk da ba kwalliya tayi ba amma tayi kyau sosai.

Mai napep d'in da ta gani shine ya sake d'auke hankalin ta ga kallon inda suke ta kalli Jidda tana fad'in, "Jidda kinga mun huta fita titi" ta fad'i haka tana tsayar da mai napep d'in.

Tsayawa yayi ya matso kusa dasu yace, "Hajiya ina zaku je?". "Hotoro zamu je" Jidda ta bashi amsa, "duba d'aya zaku bayar" ya fad'a yana kallan su, murmushi Ibteey tayi jin rainin hankalin da yayi musu shima sai yayi murmushi sai take cewa, "kayi dariya mana kasan ka fad'i abinda bazai yu ba."

Fad'in irin k'unar da zuciyar Zaid ta yi a lokacin b'ata baki ne, ransa ya b'aci fuskar sa tayi ja kana ganin sa kasan yana cikin b'acin rai, a hankali yake takowa har ya iso ya rik'e k'arfin napep d'in a lokacin har sun shiga ya kalli mai napep d'in fuskar nan a had'e yace, "Wa ya saka ka ka d'auke su?" Ya tambaya yana sake tamke fuska.

"Kaji mutum aiki nake ina neman ciniki suka zo zasu yi min ciniki ba dole na d'auke su ba" ya fad'a yana kallan Zaid, "to daga yau ko wani d'an uwan ka me irin wannan abun ka gani zai d'auke su kar ka bari balle kai da kanka" ya Fad'a yana saka hannu aljihu ya d'auko dubu biyar ya bashi, had'a ido sukayi da Ibteesam da take zaune a cikin napep d'in kawai tana kallan sa, "ku fito" shine abinda ya fad'a yana barin jikin napep d'in.
Ganin basu fito ba ya sake kallan su yace, "Bana maimaita magana". Jidda ta fito sannan itama Ibteesam d'in ta fito tana d'aure fuska, tafiya yake suna bin sa har suka kai inda motar sa take ya bud'e back seat d'in ya kwashe kayan ya mayar boot kana yace yace, "ku shiga".

Ibteesam ta kalli Jidda itama ta kalle ta suka dawo da kallon su ga Zaid da ya kafe su da ido yana yi musu wani irin kallo alamun in baku shiga ba zaku jawowa kanku.


*Dan Allah kar a fitar min da littafi.*

*?ASAITAR SO!*

*33_34*
Cigaba.....


"Ina zamu je?" Ibteesam ta tambaya tana kallan sa. Kallan ta yayi tare da zuba mata harara yace, "Sai da kanku zanyi".

Kafin Ibteesam tace wani abun Jidda ta shiga motar ta zauna ganin hakan dole itama ta shiga, jan motar yayi ba tare da yayi magana ba suka fara barin cikin unguwar, "ina wuni" Jidda ta fad'a a sanyaye tana kallan su duka, Hameed ne ya saki murmushi ya juyo ya kalle ta yace, "Kin wuni lafiya?". "Lafiya lau". "Ya makaranta?". "Alhamdulillah" ta fad'a tana mayar da hankalin ta kan titi.

"Ina zaku je?" Zaid ya tambaya yana cigaba da tuk'a motar sa, "Hotoro bus stop zamu je" Jidda ta bashi amsa, "ita bata da baki ne?" Ya fad'a yana cigaba da tuk'in sa, shiru motar tayi babu wanda yayi magana sai daga baya ta bud'e a hankali tace, "Ina wuni" daga haka taja bakin ta tayi shiru dan tasan ba amsawa zaiyi ba.

Haka kuwa akayi Hameed ne kawai ya amsa shi kuwa sai tsaki ma da yaja ya kalli Hameed yace, "A hotoro ina ne bus stop?". "Baka san bus stop ba yanzu?" Ya tambaya da mamaki. Banzan kallo ya watsa masa kana yace, "Na sani k'arya nake maka nake tambayar" ya fad'a a fuska yana kallan Hameed d'in.

"Allah ya baka hak'uri almasifatu, muje sai na nuna maka" Hameed ya fad'a yana k'unshe dariya, Ibteesam kuwa mamaki ne ya kamata ganin yana yiwa d'an uwan sa namiji fad'a ashe fad'an ba ita kad'ai yake yiwa ba, "matar mu kin ga ni ban san sunan ki ba" Hameed ya fad'a yana kallon Ibteesam. D'an daga kai tayi ta kalle shi ta d'an tab'e baki tace, "Mata kuma? Ka gyara kalaman dai". Murmushi Hameed yayi yace, "Okay sorry our wife to be".

Murmushin itama tayi tace, "duk da dai ba sunan nawa bane amma bara na baka amsar tambayar ka, sunana Ibteesam". "Woww kaji wani suna na y'an gayu Zaid?" Hameed ya fad'a yana kallon Zaid, bai kula da yanayin da Zaid d'in ya shiga ba ya cigaba da fad'in, "makaranta fa?". "Ina level 300 a Yusuf mai tama sule but yanzu kasan ana strike."

"Ai daman private university ya dace dake Ibteesam dan wannan yajin aikin a kai new year ba'a koma ba". "Gaskiya dai kam, amma ni da na kusa gamawa ina ni ina canja school?". "Sai kiga kin kammala class mate d'in ki basu gama ba, ai karatu a Nigeria ya lalace gabad'aya, which course?". Sai da ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "microbiology". "Masha Allah, Allah ya taimaka, kefe k'anwa ta?" Ya fad'a yana kallan Jidda.

B'oye fuskar ta tayi a bayan Ibteesam tace, "dis year na gama SSCE" ta fad'a tana d'an murmushi, dariya yayi kad'an yace, "Ahh lallai kice ku yanzu zaku fara bokon ma, but in kin tashi neman school ki nemi skyline ko Maryam abacha is better ki zauna kina b'ata time d'in ki" ya fad'a yana d'an sake waiwayowa yana kallon ta. "Ni da yake ma college of nursing and widwifey nake so" ta bashi amsa tana d'agowa suka had'a ido.

Zaro ido waje yayi yace, "Babbar yarinya, kin d'auki course mai kyau kam Allah ya taimaka" ta amsa da amin, "Zaid kaga kuwa akwai inda nake so naje wallahi a hotoro sai ka ajjiye ni" ya fad'a yana kallan Zaid da yanayin sa. "Dake ga driver ka samu ko,? Wallahi haushin ka nake ji sosai ji nake kamar na fasa maka baki a motar nan, ka kula in ba so kake ka koma da hak'uri d'aya a hannu ba" ya k'arasa fad'a yana nuna shi da yatsa tare da yin k'wafa.? "To me ya tab'o ka kuma kaida abin fad'a baya maka wahala?." Bai bashi amsa ba sai girgiza kai da yayi ya cigaba da driving d'in sa.

"Ibteesamm" ya kira sunan ta a tausashe cikin k'asan mak'oshi wanda taji hakan har cikin b'agon dake cikin k'ashin ta, "Uhum" ta amsa murya a sanyaye dan kiran sunan ta da yayi a rana ta farko yayi bala'in tafiya da imanin ta, "As from today kar na ji kar na sake ganin ki hau wani abu wai shi keke napep bama ke kad'ai ba har wacce take kusa dake, i don't like it kin ji ko?" Ya fad'a cikin kakkausar murya yana kallan ta ta mirror.


Had'a ido sukayi ta mirror ta d'an d'auke kanta tace, "To" abinda tace kenan dan ita bata san abinda zata ce masa ba, dan Abba ya karb'i motar da ya bayar a dinga kaisu unguwa kasancewar ta zama rigima a gidan shiyasa ya hana kowa hawa indai ba matan gidan za'a kai unguwa ba, babu wanda ya sake magana har aka zo inda shi ya sani, Hameed ne ya dinga nuna masa har bus stop ya ana zuwa bus stop Jidda ta nuna layin gidan suka shiga layin suka tsaya a k'ofar wani gida mai kyau.

"Ina ne nan?" Ya tambaya yana kallan su, "Gidan Dada ne our granny" Jidda ta bashi amsa a tak'aice, "k'arfe nawa zaku koma gida?" Ya tambaya yana kallon taga, Jidda zatayi magana yayi saurin d'aga hannu yace, "ita ta bani amsa." "After magrib" ta bashi amsa a ciki.

"Okay ku jira zan aiko a d'auke ku, kar na turo ace kun tafi" ya fad'a yana danna lock d'in motar, "Sai anjima mun gode" Jidda ta fad'a tana fita daga motar Hameed yayi murmushi yace "To Jidda ku gaida kakar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login