Showing 69001 words to 72000 words out of 171073 words

Chapter 24 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7833

ni,? Ni kad'ai ce mace a duniya a samo wata mana, kuma ni tunda haka ne bazan sake yi masa koda magana ba babu ni babu shi" ta k'arasa fad'a cikin masifa sai kuma ta saka kuka.

Dariya Umma tayi sosai har taso ta k'ware da abincin da take ci, Jidda ma dariya kamar zata fad'o daga kan kujera dan gani kishi k'iri-k'iri a tare da Ibteesam, "To wai ke kina son sane?" Umma ta fad'a bayan ta gama dariyar tana kallon Ibteesam da take kuka. "Allah ya kiyaye naso wanda ya sace ni, har abada bazan so shi ba kawai tausayin sa nake kuma shima na daina" ta fad'a tana share hawayen ta.

"Abinda na gani nima kenan ai Ibteesam keda ba son sa kike ba ina ruwan ki da matar sa da har zata dame ki haka?" Umma ta fad'a tana kallon ta, "ni Umma matar sa bata dame ni ba kawai naji haushi ne da ya b'oye min, ina ruwa na da matar sa?." "To meye na jin haushin?" Jidda ta tambaya tana daga bayan Umma.
"To ma tsaya, ai ba hurumin ki bane yace miki yana da aure kin san irin auren soyayya irin nasu ba kowa ake fad'awa ba, ke aikin ki kawai ki yi k'okarin saita shi ita kuma matar sace ta aure ina ruwan ki da ita?" Umma ta sake fad'a tana kallon ta.

Ina wuta take Ibteesam ta fad'a sai kuwa ta k'ara sautin kukan ta ta wuce d'aki a fusace ba tare da tasan dalilin fusatar tata ba.
Umma da Jidda suka bita da kallo suna dariya dan sunyi dad'in tsokanar ta.

Tana shiga d'akin kiran wayar Khalid yana shigowa maimakon ta d'auka sai kawai ta zuba wayar ido har ta tsinke bata d'auka ba wani kiran ya sake shigowa, tsaki tayi ta kashe wayar gabad'aya dan shi kansa Khalid d'in haushi yake bata.

******

"Amina ya haka? Kin san baza ki iya wannan aikin ba kika karb'a,?" Yaya Babba yake fad'a daga cikin wayar dake hannun Amina. Marairaicewa tayi kamar yana gaban ta tace, "Wallahi nima ban san ya akayi hakan ta kasace ba, a yadda na zuba masa ban d'auka bazai mutu ba ashe nayi kuskure da ban juye ta gabad'aya a ciki ba, kuma tsoron da naji kar na juye duka ruwan ya canja kala shiyasa na saka kad'an dan ma kamar gishiri gubar take shiyasa ba'a gane ba, amma nima nayi mamaki da naga kwana d'aya kacal yayi a kwance ya tashi kamar bashi ba" ta fad'a cikin takaici.

Daga can b'angaren Yaya babba yace, "nima abinda ya bani mamaki matuk'a ace kwata-kwata awan sa ashirin da had'u aka sallamo shi, mu da muke so e yanzu muna nan muna karb'ar gaisuwar mutuwar sa, amma babu komai ya tsallake rijiya da baya baza mu k'yale shi ba next target duk yadda zakiyi kiyi ya shanye ta duka a cikin sa, cikin kwanakin kuma fa za'a bashi? ba sai anja wani lokaci mai tsayi ba."

Girgiza kai tayi tace, "Insha Allah babu matsala za'ayi hakan, tunda har aka samu ya fara shiga tarkon mu ai zance ya k'are sai munga bayan sa hankalin mu zai kwanta, zan koma falo yanzu mayi waya anjima" daga haka ta kashe wayar ta sauke ajiyar zuciya, fanfo ta kunna ta wanke fuskar ta tana k'arewa band'akin kallo kamar wacce ta ajjiye wani abun, bud'e k'ofar tayi ta fito tana goge ruwan da yake fuskar ta ba tare da ta lura wanda yake zaune ba, d'ago idon da zatayi suka had'a ido da Daddy a zaune a gefen gadon ta ya zuba mata ido kawai yana kallon ta.



*Ibteesam da alama ta fara kishi fa=??=??=??*


*Dan Allah kar a fitar min da littafi.*

?ASAITAR SO!*

*43_44*

Not edited>??




Rud'ewa tayi lokaci d'aya kana kallon ta zaka ga alamun rashin gaskiya a tare da ita, "Daddyn Zaid yaushe ka shigo?" Ta fad'a a d'an diririce tana k'ak'alo murmushin dole, kallon ta yake shi kawai kafin ya danne zuciyar sa yace, "Ban jima ba, ina key d'in d'aki na" ya fad'a yana mik'o mata hannu, "daman yanzu nake shirin naje na bud'e na d'an gyara maka" ta fad'a tana bud'e drower ta d'auko makullin.

"A'a bar shi kawai bani" ya fad'a yana mik'ewa tsaye, mik'a masa tayi ya karb'a ba tare da ya kuma kallon ta ba ya fita daga d'akin nata, da kallo ta bishi tana dafe k'irji tare da fad'in, "Wai Allah yasa bai ji abinda nake fad'a ba."

Bayan ya fito daga d'akin sa saman Zaid ya nufa ya same su a zaune shida yaran sa ya kalle shi yace, "Zaid ka taso muje part d'ina ka kwanta bazan iya barin ka a nan kai kad'ai ba". D'ago kai yayi ya kalli Daddyn kafin yace, "Zan iya kwanciya a nan ni kad'ai ga kuma Wizyy ma suna nan". Daddy ya kalli Wizzy yace, "Da gaske kuna nan?". "Eh Daddy muna nan."

Ajiyar zuciya yayi dan ya yadda dasu ganin yadda suka dinga zirga-zirga a asibiti kuma tunda shi Zaid d'in da kansa ya amince dasu yasan basu da matsala, "meye sunayen kune na gaskiya?" Daddy ya fad'a yana kallon su. Sosa kai Wizzy yayi yace, "Ibrahim". "Ikon Allah kana da suna mai dad'i ka mayarwa da kanka suna Wizzy? Kai fa?" Daddy ya fad'a yana kallon Mugu, "Kamal" ya bawa Daddy amsa yana d'an sunkuyar da kai.

"Dukkanin ku sunan ku da dad'i amma kuka b'ata sunayen ku haka,? Ina d'ayan da ai ku uku nake gani" Daddy ya tambaya yana kallon su. Kallon mai gidan nasu sukayi suka ga kamar ma baiji me ce ba ya kawar da kansa gefe hakan ya saka Wizzy yace, "Ya d'an yi tafiya ne". Daddy yace, "To shikenan, dan Allah ku kula dashi dakyau in wani abun ya faru cikin dare ku kira ni a waya, kar ya hana ku yace baza kuyi min waya ba ." "Insha Allah Daddy zamuyi abinda kace" Mugu ya bashi amsa, "sai da safen ku" ya fad'a yana fita daga falon.

Dogon tsaki Zaid yaja yace, "ni in badan kun takura da yawa ba banga abinda zai saka ku kwana ba, Hameed ma yaso kwanan na hana shi kune kuka nace" ya fad'a yana d'an yatsine fusks tare da d'an kwanciya a kan kujera, "Haba mai gida a wannan hali da kake ciki kai ba mata gare ka ba wacce zaku kwana tare ai ya kamata a kwana da kai ciwo bai san dare ba ai" Wizzy ya? bashi amsa, kallon Wizzy yake kamar me tuna wani abu kafin yace, "Very soon zanyi matar ai, ya za'ayi da kwanciyar kun san bana sharing bed". Y'ar dariya Mugu yayi yace, "Baka da case mai gida ai a nan zamu baje mu" ya fad'a yana sake zama a kan kujerar.

"Falo?" Ya fad'a da alamun tambaya, "Eh mana mai gida ai lafiya lau" Wizzy ya fad'a shima yana gyara zaman sa, "noo baza'a yi haka ba, let me call my cleaner yayi order na small bed yanzu a kwashe machines d'in can d'akin saka muku, kwanan falo sai kace tv" ya fad'a yana k'okarin kiran waya. "Haba mai gida kwana d'ayan shine sai an siyi gado? Kuma mu yanzu sai mu zauna har a kawo gado a d'aura muna zaune k'arfe tara fa ta wuce,? Ai ka barmu a nan kawai bacci zamuyi mai kyau a nan" Wizzy ya sake fad'a yana d'an murmushi.

Da mamaki yake kallon su kafin yace, "Wai da gaske zaku kwana a nan d'in?". Kwanciya Mugu yayi a kan kujerar yace, "Ahh mai gida muda muka kwana a k'asan gada ma gamu ga kwata muka yi bacci lafiya lau balle nan?." "Okay, Wizzy shiga ciki a wardrobe akwai blanket ka d'auko muku" ya fad'a yana kallo Wizzy, mik'ewa yayi kamar yadda yace ya shiga ya d'auko manya-manya masu bala'in laushi guda biyu ya fito dasu yana fad'in, "Tab kace zamu rasa sallar asuba indai muka kwanta a wannan abun". "Mtsww, bakwa jin yunwa?" Zaid ya tambaye su da kulawa yana kallon su.

"A k'oshe muke" suka had'a baki wajan fad'a, mik'ewa tsaye yayi dak'yar yana d'an runtse ido ya shiga d'aki ba tare da yace musu komai ba,? su kam TV ma suka kunna suka fara kallon ball dan lokacin bacci baiyi ba, shima wanka yayi ya canja kaya ya kwanta badan yana jin bacci ba sai dan rashin k'arfin jiki da babu a tare dashi, daga haka bacci ya d'auke shi.

Cikin dare ciwon ciki ya tashe shi ya dinga juyi shi kad'ai a kan gado hannun sa dafe da cikin sa, garin juyi ya cillo bedside lamp ba tare ds ya sani ba, wannan k'arar fad'uwar lamp d'in ita ta tashi su Wizzy suka farka a firgice suka mik'e suka shiga d'akin da sauri.

"Innalillahi, mai gida ciwon cikin ne?" Suka fad'a suna k'arasowa inda yake da sauri Wizzy ya rik'e shi, "Mugu kira wayar Daddy da sauri" Wizzy ya fad'a yana kallon Mugu.? Ba musu ya dokawa Daddy kira ya sanar dashi halin da ake ciki.

A guje Daddy ya hauro saman ya shigo d'akin yana fad'in, "Ku kama shi mu tafi asibiti da sauri" Daddy ya fad'a yana kallon su hankali a tashe.

"A'a Daddy basai mun je ba" ya fad'a cikin murya a k'asa yana jan numfashi, "kamar yaya basai mun je ba Zaid,? A gida kake so mu zauna?". "Amai" ya fad'a yana yunk'urawa zai tashi sabida yadda aman yake taso masa, da sauri Daddy ya kama shi ya rik'e ya Mike tsaye suka shiga band'aki, aman ya fara a galabaice kamar zai amayar da kayan cikin sa haka yake aman yana rik'e shi, ruwa ne yake zuba a idon sa kasancewar aman sa bashi da k'ara sai dai idon sa ya tara ruwa kawai, ruwa ya saka ya wanke fuskar sa Daddy ya rik'o shi suka dawo kan gado ya zauna tare da dafe kansa da hannu biyu yana sauke numfashi.

"Daddy suna zo na tafi inda Mama na ta tafi ko? Meyasa suke so na mutu?" Ya fad'a hannun sa yana dafe da kansa yana kallon k'asa, Daddy da hawaye suks cika masa ido ya goge ya kalli Zaid d'in yace, "Zaid baza ka mutu ba yanzu insha Allah, asibiti zamu tafi yanzu." "Daddy na daina jin ciwon yanzu, ina so naga Mummy na da Ibteey". Kallon agogon d'akin Daddy yayi kafin ya dawo da kallon sa ga Zaid yace, "K'arfe biyu da rabi na dare fa Zaid, kayi hak'uri gobe in Allah ya kaimu zaka gansu." D'ago jajayen idon sa yayi ya kalli Daddy yace, "In ban kai goben ba kuma fa?". Kamar ya soka masa mashi haka Daddy yaji a lokacin ya kalli Zaid d'in da sauri shima shi yake kallo, k'arasowa yayi ya zauna kusa da Zaid d'in ya dafa shi yace, "Baza ka mutu yanzu ba insha Allah, ka daina fad'ar haka in ka mutu ya kake so nayi? Maman ka ta tafi ta barni kaima ka tafi ka barni,?". "To Daddy mai nayi musu suke so su kashe ni?" Ya fad'a kamar zaiyi kuka yana kallon Daddy.

Shiru kawai Daddy yayi masa ya kwantar dashi a kafad'ar sa, "Daddy a kira min su ina so na gansu" ya kuma fad'a har lokacin yana jikin Daddy, bai amsa masa ba dan ji yake in ya bud'e baki a lokacin zai iya yin kuka shiyasa yayi shiru, a hankali ya fara jin saukar numfashin Zaid d'in alamun ya samu bacci, kwantar dashi yayi a kan gadon a hankali ya rufe shi tare da zuba masa ido, sai a lokacin ya kalli inda su Wizzy suke ya gansu tsaye kowa tausayin Zaid ya bayyana a fuskar sa, "Nagode kunji badan ku ba da yanzu ban san a wanne hali yake ciki ba, kuje ku kwanta kuma yayi bacci ai, zan zauna tare dashi a nan" Daddy ya fad'a yana kallon su.

Jiki a sanyaye suka fita daga d'akin suka koma suka kwanta badan suna son jin baccin ba.

Daddy ma alwala yayi ya tayar da qiyamal layli yana kaiwa Allah kukan sa a daren, haka ya kasance a zaune yana gadin Zaid har akayi assalatu sannan ya tashi da nufin tafiya masallaci, koda ya fito falon ya had'u dasu Wizzy har sunyi alwala suma a band'akin da yake falon, "Daddy kai da Wizyy kuje kuyi sallar ku dawo in yaso in kun dawo sai naje masallacin gaba kar a barshi shi kad'ai" Mugu ya fad'a yana kallon Daddy da girmamawa, haka akayi kuwa Daddy da Wizzy suka fita aka bar Mugu a wajan Zaid da yake bacci.

Bayan sun dawo Mugu ya sauka yaje masallacin gaba da gidan kad'an yayi sa'a a lokacin suke tayar da sallah ya bi jam'i bayan an idar ya dawo.

Daddy kasa baccin yayi ya zauna a gefen gadon Zaid yana kallon sa har gari ya d'an yi haske su Wizzy suka masa sallama suka tafi yana ta saka musu albarka kamar ya goya su.

Sai k'arfe bakwai Zaid ya farka a firgice sallah ce ta fara zuwa ransa sai kuwa ya ziro k'afar sa ya sakkowa daga kan gadon, sai a sannan ya lura da Daddy da yake zaune a akan bedside yana bacci a zaune, murmushi yayi ya k'arasa inda yake ya d'an tab'a shi kad'an yace, "Daddy". Bud'e ido yayi ya kalle shi yace, "Zaid ya jikin?". "Na warke Daddy, kaje ka kwanta ka huta ai safiya tafi" ya fad'a yana kallon Daddyn nasa da kulawa.

"Ka tabbata ka warke baka jin komai yanzu?". Ya sake tambayar sa, "naji sauk'i sosai, kaje ka huta." Jin hakan ya saka shi ya mik'e ya fita daga d'akin Zaid ya bishi da kallo kafin yayi murmushi ya shiga band'aki.

Shape-shape yayi wanka ya shirya ya tayar da sallah, bayan ya idar ya d'an zauna na wani lokaci kafin ya koma ya kwanta.

Bai farka ba har sha d'aya saura na safe duk minti goma sai Daddy yazo ya duba shi sai ya ganshi yana bacci, sai sha d'aya yayi wanka ya shirya ya zauna a falon sa dan sam baya son sauka k'asa, taku ya jiyo hakan ya tabbatar masa da akwai wanda yake hagowa saman sai ya mayar da hankalin sa ga k'ofa, kamar yadda yayi tunani kuwa Daddy ne ya shigo falon da sallama a bakin sa, amsawa yayi Zaid d'in ya kalli Daddy yace, "Morning Daddy". Sai da ya zauna kusa dashi ya dafa shi kafin yace, "ya jikin naka?". "Alhamdulillah naji sauk'i." "Masha Allah, breakfast fa?". D'an yatsine fuska yayi yace, "Wani abu nake so amma nasan babu lallai na samu" ya fad'a kamar zaiyi kuka.

Gyara zama Daddy yayi yace, "Ai duk abinda kake so Zaid ko a ina yake zan samo maka shi fad'i kawai." Kallon Daddyn nasa yake kafin yace, "Abincin precious nake so naci ni in ba nata ba bazan ci? komai ba." Da mamaki Daddy ya kalle shi yace, "Wace precious?". Kallon Daddyn nasa yayi kamar zaiyi kuka yace, "That pretty mana". Sarai Daddy ya fahimci wacce yake nufi amma sai yace, "Ban fa gane ba". "Ohhh Dad, Ibteesam nake nufi".

Murmushi Daddy yayi yana daga gira sama yace, "yanzu banda abinka ina zan ganta har nace abincin kake so kaci,? Kuma fa yarinyar nan ba ajjiye ta kayi ba wata kila ma bata nan yanzu kana takura ta." Sai kuwa ya tamke fuska yace, "Ni indai ba abincin ta ba bazan ci komai ba yau." Daddy zaiyi magana kira ya shigo wayar sa yana dubawa yaga sunan Abban Ibteesam sai yayi murmushi tare da d'aukar wayar ya kara a kunne, bayan sun gaisa Abba yana tambayar sai me jiki yace da sauk'i, daga can b'angaren Abba yace, "idan kana kusa dashi a bashi mu gaisa" ba musu Daddy ya mik'awa Zaid wayar, "Ina kwana" Zaid ya fad'a a hankali yana sauraron abinda Abban zaice, "Lafiya lau Zaid, ya k'arfin jikin?". "Da sauk'i". Abba yace, "Masha Allah, Allah ya k'ara lafiya." Zaid ya amsa da, "Amin, Abba ina precious take?." Abba yayi murmushi yace, "tana cikin gida, akwai wani abu ne?". Kamar yana gaban Abban ya wani shagwa6e fuska yace, "Ni abincin ta nake so naci na fad'awa Daddy yace ina takura mata." Kiris ya rage Abba bai saki dariya ba ya daure ya yace, "Amma Daddy bai kyauta ba, me kake so ta dafa maka?". Kwanciya yayi a jikin kujerar yace, "Anything". "To shikenan ka jira ta za'a kawo maka yau abincin ta zaka ci till down kar ka damu" Abba ya fad'a yana murmushi.

"Thanks you Abba" y fad'a tare da mik'awa Daddy wayar, Daddy yace, "Ka biyewa shirmen Zaid ka saka ta aiki?". Abba yace, "Banda abinka ai matar sace kuma ko babu aure tsakanin su ai yana gaba da ita ba wani abun bane, bara na shiga cikin gidan na saka a kawo masa da wuri zuw anjima zan shigo na duba shi insha Allah" daga haka sukayi sallama da Daddy yana ta godiya shima haka.

Daddy yace, "Zaid ina zuwa" daga haka ya sauka k'asa, bai jima da sauka ba Anty Amina ta hayo saman hannun ta d'auke da plate da flasks d'in tea, tunda ta shigo falon ya d'auke wuta ya tamke fuska kamar bai san da zuwan ta ba, "Zaid ya jikin?". Banza yayi mata daman kuma tasan bazai amsa ba sai ta cigaba da fad'in, "Ga abinci na kawo maka kaci" ta fad'a tana tura plate d'in kusa dashi.

Kallon abincin yayi ya d'ago ya kalle ta yace, "Dallah malama d'auke min wannan tsiyar taki ku fitar min dashi daga falo" ya fad'a murya a k'asa amma kana jin yadda take fita kasan cikin b'acin rai yake furta ta, kallon sa tayi ta kalli abincin tace, "Tsiya ta, abincin ne tsiya ta?". "Ke kanki ma ai tsiyar ce ba abincin ki bama" ya bata amsa yana kad'a k'afar sa yana zuba mata harara.

"Hmmm Zaid ko baka kalle ni matsayin wacce take auren mahaifin ka ba yana da kyau ka kalle ni a matsayin wacce ta girme ka, dan ko ban haife ka ba na tabbata na baka shekaru da dama a duniya, baka daraja na gaba da kai ne?" Ta tambaya cikin takaici tana kallon sa. "In kuma na kalle ki a matsayin banza, wacce bata san abinda take yi bafa?" Ya fad'a yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login