Showing 90001 words to 93000 words out of 171073 words

Chapter 31 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7835

amince ba sabida nafi kowa sanin wacece ke, babu ruwan ki da ita ki daina shiga abinda ya shafe ta na fad'a miki" ya fad'a fuskar nan a had'e yana nuna Anty Amina da yatsa. Kallon sa tayi itama tace, "Zaid Baby y'a tace nice na haife ta, ina da iko a kanta fiye da kowa a duniya." "Oh really? A ina kika haife ta d'in? Oh kina so ki kashe ni shiyasa kika fara shirya wannan series d'in?" A hannun kujera ya zauna yana kallon ta yace, "Baza ki tab'a nasara a kaina ba na fad'a miki, ki daina wannan dramar dan kinga ina sonta, ki daina k'okarin amfani da ita wajan ganin baya na" ya fad'a yana sake nuna ta da yatsa hannun sa.

Kallon Ibteesam tayi da take kallon su kafin ta kalli Zaid tace, "Zaid kar ka b'ata min rai ina cikin farin ciki yau, ka k'yale ni dan Allah" ta fad'a tana fuskar ta a d'aure". "in nak'i na daina fa akwai abinda zakiyi?" Ya fad'a yana mik'ewa tsaye kamar zai dake ta.

"Wai lafiyar ka kuwa? Yau naga Mama na maimakon ka taya ni farin ciki amma sai kazo kana mata rashin kunya kuma a gaba na?" Ta fad'a tana mik'ewa tsaye tana kallon sa, "wannan kike kalla kike kira Maman ki precious? Kin san ta kuwa? Inda kin santa baza ki fad'a abinda kika fad'a ba yanzu....." katse shi tayi ta hanyar fad'in, "Ya ishe ka! Kar ka sake fad'ar irin wannan maganar a kan Mama na fad'a maka, ina jure komai a duniya amma bana jure a fad'awa iyaye na magana mara dad'i ka gane?" ta fad'a itama a fusace tana kallon sa.

"Wannan matar da kike gani ko shaid'an ganin ta yayi ya k'yale, tafi shaid'an iya makirci fuska biyu gare ba....." "Zaid!" Ta furta cikin d'aga murya tana d'aga hannu da niyar kai masa mari.





*Kar a fitar min da littafi dan Allah.*

*?ASAITAR SO!*

*52_53*

Not edited>??



Zuba mata ido yayi yana jiran yaga abinda zatayi masa, kamar an rik'e mata hannun haka taji ta kasa sauke shi a fuskar sa ta nuna shi da yatsa tace, "Zan jure komai a duniya amma bazan jure ka tsaya a gaba na kana fad'awa mahaifiya ta maganar banza ba, zamuyi fad'a da kai fad'a kuwa na har abada" ta fad'a tana zaro masa ido.

Kallon ta yake da tsananin mamaki ganin tana yi masa ihu kamar ba ita ba ya saka shi yace, "you're my wife right?". Cikin masifa tace, "Eh na sani, amma ka manta me Daddy yace? Har gobe ina da damar da zance bana son ka kuma dole ka rabu dani na auri wanda nake so, dan haka ka shiga hankalin ka duk son da kake min zan ajjiye shi a gefe na rabu da kai sabida mahaifiya ta". "U too late precious, tunda har kin yadda ke matata ce babu wani ko wata a duniyar nan da zai saka na rabu dake koda Daddy ne" ya fad'a muryar sa a hankali amma fad'a yake.

"Precious! Kar ka sake kira na da wannan sunan sabida bazan zama mai daraja a wajan ka kana wulaqanta min uwa ba, indai ni mai daraja ce a wajan ka dole Mama na ma ta zama me daraja a wajan ka in ba haka ba kar ka sake nuna ka sanni ko ina ne" ta fad'a tana hararar.

Kallon ta yake ya kalli Anty Amina zaiyi magana kamar ya tuna wani abun kuma sai ya fasa ya juya zai fita kenan Eman ta shigo falon, ganin sa ya saka tayi murmushi mai kyau tace, "Darling ina ta neman ka" ta fad'a cikin shagwa6a kamar zata fad'a jikin sa, baice komai ba ya motsa zai wuce ta sake tare masa hanya tana wani kad'a masa jikin ta, cije baki yayi tare da girgiza kai yana binta da kallon k'ask'anci, zatayi magana taji saukar marin da ya? kusa saka ta suman tsaye, cikin kakkausar murya wacce take bata tsoro a koda yaushe taji yace, "stupid fool" ya fad'a yana ficewa daga falon ransa a b'ace.

Eman da tayi abinda tayi sabida Ibteesam sai taji kunya tayi saurin barin wajan tana b'oye kukan da ya tawo mata dan taji zafin marin, "Ibteesam meyasa zaki masa rashin kunya haka? Kin manta ke matar sace?" Anty Amina ta fad'a tana kallon Ibteesam da ranta yake a b'ace.? "To Mama dan ina matsayin matar sa sai ya dinga fad'a miki abinda yake so a gaba na,? Kenan tun asali baya girmama ki tunda gashi a gaba na ya kasa b'oye hakan, baza mu shirya dashi indai a hakan ki ne, tun asali na haka nake ko a gidan Umma babu wanda zai fad'awa Umma magana indai ina wajan na k'yale ballanta ke da kika haife ni, aure kuma ai ance ina da damar da zance bana son sa? kuma dole ya rabu dani daman ai ba son nasa nake ba." Anty Amina tayi murmushi tace, "Ai wannan auren naku mutu ka raba kenan Ibteesam, bana so ki sake masa rashin kunya kinji, ko babu aure tsakanin ku akwai tazarar shekaru." Ta fad'a mata cikin tattausar murya.

Kai kawai ta d'aga kafin Anty Amina ta sake cewa, "Ina Zahra?." "Tana ciki" Ibteesam ta bada amsa a hankali, "muje cikin" ta fad'a tana fara tafiya itama tabi bayan ta.

A d'akin suka tarar Zahra ta fito daga wanka tana shiga tace, "Anty Ibteesam wallahi tunanin ki nake ina ta sauri na fito nazo inda kike sai gaki". Murmushi Ibteesam tayi kad'an tace, "to gani nazo ai, da labari ne?". "Labarai kai, ai yau bazan barki bacci ba" ta fad'a itama tana dariya.

Anty Amina da take tsaye tace, "to a kwanta dai kar a kai tsakiyar dare ana hira". "To Mama" Zahra ta bata amsa tayi murmushin nishad'i ta kulle k'ofar ta nufi nata d'akin zuciyar ta kamar an wanke mata ita haka take ji.

Ibteesam ma wankan tayi ta fito ta? d'auki kayan sabbin kayan baccin da Anty Amina ta bata ta saka kana ta kwanta cikin kewar Jidda, wayar ta ta jawo ta kunna data nan tayi karo da messages d'in Jidda kamar hauka, murmushi tayi ta dinga bi tana bata amsa cikin kewar k'anwar tata, kashe datar tayi bayan ta gama bata amsa suka fara hira da Zahra tana bata labarin kakar su da take Gombe da cousins d'in su a haka har Zahra tayi bacci, ita kuwa kasa baccin tayi zuciyar ta cikin kewar Umman ta da Jidda da ta tuna wani abun sai tayi murmushi, Zaid ne ya fad'o mata a rai ta shafa lips d'in ta tana tuna abinda ya faru a tsakanin su a d'azu, ajiyar zuciya tayi ta lumshe idon ta tana kallon abin a idon ta kamar a lokacin ya faru, kenan daman yasan ni matar sace shiyasa yayi min abinda bai tab'a ba koda ya sace ni sai d'azu?

Juyawa tayi tana ajiyar zuciya zuciyar ta tana hasaso mata yanayin Zaid a lokacin, mik'ewa zaune tayi tana kallon wani wajan daban tace, "Bazan saurara masa ba indai zai wa Mama na rashin kunya kome nake ji a kansa zan ajjiye shi gefe ne balle ma kuma ba son sa nake ba". Sai kuma ta koma ta kwanta tare da fad'in, "ashe shiyasa su Umma basa hana ni duk wani abu da ya shafe shi,? Haba no wonder Umma bata yi min fad'a akan komai koda fita mukayi dashi muka jima bata cemin komai sai tsokana ashe miji nane, ko yaya? Khalid zaiji in akace masa ina da aure?" Ta furta a hankali gudun kar ta tashi Zahra da ta jima da bacci.

Da wannan tunane-tunanen itama bacci ya d'auke ta, b'angaren Zaid kuwa sam bacci yak'i zuwa idon sa da ya kulle idon ita yake hangowa a yanayin su na d'azu, tsaki yaja ya mik'e zaune yace, "Matata ce ina da iko da ita waccan matar bata isa ta hana ni kula matata ba, oh my god ta yaya hakan zata kasance?" Da irin wannan tunanin shima yayi bacci.

Anty Amina kuwa saman Daddy ta nufa fuskar ta wasai haka ta shiga cikin d'akin sa da sallama, ya amsa tare da fad'in, "Ai na d'auka yau hak'uri za'a bani kina tare da Ibteesam" ya fad'a da murmushi a fuskar sa.

Itama murmushin tayi ta zauna a gefen gadon tace, "Ai suna tare da k'anwar Zahra shiyasa na barsu su kwana tare" ta fad'a har lokacin murmushi ne a fuskar ta, "kinga ikon Allah ashe kece sirikar Zaid" Dady ya fad'a da d'an murmushi a fuskar sa. Itama y'ar dariya tayi tace, "Zaid manya k'asa ba, abinda baka tab'a kawowa a ranka zai faru ba sai kaga Allah ya tabbatar dashi, tunda na bar gidan su Baby na manta da ina da wata y'a a duniya sai ranar dana ganta a asibiti taje duba Zaid, tun daga lokacin na fara tunani kamar akwai abinda na rasa amma na kasa, ashe aikin asiri ne yake yawo a jiki na har tsahon wannan lokacin" ta k'arasa fad'a cikin murya mai sanyi.

Daddy ya zauna shima yace, "haka rayuwar ta koma ai Amina, wanda baka san dashi ba baka san a inda yake ba amma shi da kai yake kwana yake tashi a ransa, burin sa ya samu dama guda d'aya ya rusa maka taka rayuwar, yanzu gashi ta bar duniyar ta barki a cikin ta me gari ya waya yanzu?". "Haka ne, tunda naji ance ta rasu nidai na yafe mata har cikin raina, Allah ya kare mu ya saka mufi k'arfin zuciyar mu". Daddy yace, "Amin, kin kyauta haka ake son mutum mai yafiya ga d'an uwan sa."

"Yauwa, wai ya akayi ka amince da abinda na fad'a maka a kaina? Na d'auka zaka d'an yi waswasi a kan hakan sai naga akasin hakan" ta fad'a tana kallon Daddy, d'an murmushi yayi kad'an yace, "Na amince dake ne tun farko nasan kuma baza kiyi min k'arya dan ki kare kanki ba". "Nagode da amincewa dani da kayi, naji dad'in hakan sosai da sosai, yanzu Zaid ne ya rage" ta fad'a a sanyaye.

Daddy yace, "shima zai gane hakan, zan sanar dashi komai ai so nake mu samu lokaci nida shi dan yanzu hankalin sa ba'a jikin sa yake ba". Anty Amina tace, "A'a ka barshi ya gano da kansa, Allah yayi masa baiwa ta saurin gane mara gaskiya ka k'yale shi ya gano zaifi amincewa, a yanzu in ka masa maganar zai ga dan ina matsayin mahaifiyar Ibteesam ne ya saka hakan." Daddy yace, "To ai shikenan, yanzu in suka ji labarin auren nan na Zaid ma nasan ba k'aramar rigima za'ayi dasu ba". Anty Amina da ta gane da wanda yake tace, "Haka zasu hak'ura babban tashin hankalin su in suka ji cewa nice na haife ta, amma Allah zai kare komai meye zai koma kansu". Ajiyar zuciya Daddy yayi yace, "insha Allah".

Washe gari.

Kafin Ibteesam ta tashi ita da Zahra Anty Amina ta gama komai kamar koda yaushe, lokacin da Ibteesam ta fito Daddy yana zaune suna breakfast tare ita dashi, kamar kullum tayi wanka sai dai kayan jiya ta mayar sabida bata da wasu a gidan, "Ina kwana Daddy" ta fad'a bayan ta k'araso cikin falon.

Murmushi Daddy yayi ya amsa da fad'in, "Kin kwana lafiya Maryam?". "Lafiya lau" ta bashi amsa ba tare da ta kalle shi ba kanta a k'asa, "ya kwanan bak'unta kuma?". Murmushi tayi bata ce komai ba ta kalli Anty Amina da take kallon da ta murmushi tace, "Mama maimakon ki tashe ni na taya ki aikin." Tace, "A'a ki huta abinki, ina Zahra bata tashi ba?". Ibteesam tace, "bacci take har yanzu?". Daddy yace, "Zauna kiyi breakfast in ta tashi tayi nata daga baya" ya fad'a yana nuna mata kujerar dining d'in.

Ba musu ta zauna duk da a takure take a gaban Daddy har sai da ya fahinta yace, "ki saki jikin ki kamar kina tare da Abban ki kinji ko? Kamar yadda Zaid yake a waje na haka kema kika kar ki takura kanki" ya fad'a yana kallom ta da kulawa.

Abincin Anty Amina take zuba mata kafin ta tura mata plate d'in gaban ta ita kuma ta had'a tea d'in, zata fara jin abincin kenan taji an rik'e hannun nata an zare doyar da ta d'auka an ajjiye an saka tissue an goge mata hannun, kallon sa tayi fuskar sa a had'e babu alamun murmushi a kan fuskar sa sai ma ramewa da fuskar tasa tayi, kafad'un ta ya rik'e ya mik'ar da ita tsaye, Daddy da yake kallon ikon Allah yace, "Zaid lafiyar ka kuwa? Meye haka?". Kallon Daddyn nasa yayi kafin yace, "Baza taci abincin da matar nan ta dafa ba". Da mamaki Daddy yace, "Sabida me kenan?". "Sabida itama zata iya zuba mata poison kamar yadda ta zuba min taso kashe ni" ya fad'a kansa tsaye babu tsoro ko fargaba a tare dashi.

"Zaid kasan abinda kake cewa kuwa? Waye ya fad'a maka itace ta baka guba dan ka mutu?" Daddy ya fad'a cikin tsawa yana kallon sa, "Daddy sai an fad'a min zan sani,? Ko tantama bana yi itace ta zuba poison d'in nan, to akan me zan bar matata taci abincin ta? Kaima kasan never" ya fad'a yana kallon Daddyn nasa.

Daddy yace, "Amma kasan mahaifiyar tace ko?". Tab'e baki yayi tare da d'aga kafad'a yace, "so what dan mahaifiyar tace? Ita nake aure ai ba ita ba, ina da iko da matata dan haka baza taci abincin nan ba." Daddy ne yayi k'okarin cewa, "Zaid anya kana da hankali kuwa? Yanzu nace maka mahaifiyar tace ka ce min haka?". D'an rausayar da kai yayi yace, "haba Daddy to me zance in ba abinda nace ba? Nifa ban amince mahaifiyar ta bace har yanzu dan haka ina da ikon da zan hana ta duk abinda naga bai min ba."

Anty Amina da Ibteesam kawai sun zuba masa ido ne suna kallon sa, Anty Amina batayi wani mamakin hakan ba dan tasan zai faru Ibteesam ce take ji kamar ta d'auke shi da mari amma idon Daddy ya hana ta aikata hakan, fincike hannun ta tayi kafin yayi wani yunk'uri ta d'auki wanda ya kwace a hannun ta ta saka a baki tana ci, bata kula shi ba ta koma ta zauna tana cin abincin ta ranta a b'ace matuk'a.

Zaiyi magana tayi saurin katse shi da fad'in, "In ma naci na mutu din Mama nace ta kashe ni so ba abinda ya dame ka bane ba" ta fad'a tana cigaba da cin abincin ta.

"Good" Daddy ya fad'a yana mai cigaba da cin abincin sa suka barshi a wajan a tsaye yana kallon su, k'wafa yayi ya fita daga falon ran sa a b'ace, Anty Amina tace, "Ibteesam ba nace kar ki dinga tanka masa ba?". Daddy ya tari numfashin sa da fad'in, "A kan me zaki hana ta taka masa burki? Kenan ya cigaba da abinda yake yi a saka masa ido,? Maryam duk abinda yayi ba dai-dai ba ki nuna masa kar kiji kunya ta ko a gaban ido nane ki tsawatar masa ke kad'ai ce zaki masa ya k'yale, dan a yanzu in ba dan ke bace da yanzu an d'auki yarinyar ko ya b'alla ta ko ya sumar da ita" Daddy ya fad'a yana kallon ta cikin bada umarni.

Duk sai abincin ma yafi a kanta ta fara tura abincin ranta a b'ace sosai haushin Zaid yana sake shiga ranta zuciyar ta cike da mamakin dalilin da ya saka baya girmama Anty Amina a matsayin ta na matar baban sa, Anty Amina ta lura da yanayin ta sai bata nuna ba ya cigaba da cin abincin ta, mik'ewa Daddy yayi yana goge bakin sa da tissue ya hau sama.

Kallon Daddy tayi ganin ba'a ganin sa ya saka ta dawo da kallon ga Ibteesam tace, "Baby bana fad'a miki Zaid mijin bane ki daina masa rashin kunya ba? Zunubi ake rubuta miki fa, kuma dan rashin kara a gaban mahaifin dan ya nuna miki yaji dad'in hakan amma babu dad'i fa" ta fad'a cikin nutsuwa tana kallon Ibteesam.? "Mama daga jiya da daddare zuwa yau na fahimci sam baya ganin k'imar ki kuma duk abinda yazo bakin sa fad'a miki yake yi akan wanne dalilin zan k'yale shi?" Itama ta fad'a tana kallon Anty Amina.

"Zan fad'a miki dalilin sa nayin abinda yake yi kema zaki ga bashi da laifi kawai rashin bincike ne ya jashi ga aikata hakan, amma dai ki daina na fad'a miki" Anty Amina ta fad'a tana mik'ewa tsaye. Shiru Ibteesam tayi bata ce komai ba itama ta mik'e amma a zuciyar ta ta d'auki alwashin indai bazai girmama uwa ba baza ta karb'e shi matsayin miji ba.

Jidda ce ta shigo falon da sallama, Ibteesam ta amsa ta rungme ta cikin murna da kewa, "Anty Ibteey munyi kewar ki sosai" ta fad'a tana sake rik'e Ibteesam d'in sosai a jikin ta, "Nima haka Jidda, ya jikin Jafar? Na kira Umma tace min yana bacci bai tashi ba". "Yaji sauk'i yanzu da na tawo ma yaso ya biyo ni" ta bata amsa bayan sun saki juna.

"Ina wuni" Jidda ta fad'a tana kallon Anty Amina, murmushi tayi tace, "Lafiya lau, ku shigo ciki mana" tare suka shiga ciki suka baje a k'aramin falo.

A lokacin Zahra ta tashi ta debo abinda zataci ta dawo kusa dasu ana hira tana cin abinci cikin nishad'i, Anty Amina ta fito ta kalle su tace, "Baby ki shirya zamu je gidan Hajiya". Ta amsa da to suka cigaba da hira kamar Zahra da Jidda sun jima da sanin juna.

Zuwa sha biyu na rana Ibteesam da Anty Amina suka fita Jidda ma ta tafi gida Zahra ma taje gida ta dawo, ranar Ibteesam da Anty Amina sunsha yawo gidan y'an uwa tana nuna musu ita kowa yana mamakin ashe yarinyar bata mutu ba, sai la'asar suka bar gidan kakar Ibteesam kafin su tafi gidan su Jidda.

Sai magariba suka tafi Jidda ta biyo su aka dawo gidan tare, a gajiye suka dawo suka tarar da Zahra har ta dawo tana jiran dawowar su, wanka Ibteesam tayi tare da yin sallah ta d'an kwanta sabida yadda jikin ta yake a gajiye.

*****

Eman tun bayan fitar su Anty Amina itama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login