Showing 123001 words to 126000 words out of 171073 words

Chapter 42 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7851

nan ne" ya fad'a yana kallon ta.

Shigowar Abban Ibteesam d'akin ya saka kowa yake masa barka da zuwa, gaisawa sukayi da Zaid d'in ya a yi masa ya jiki kafin ya zauna shima, bai jima da zama ba ya mik'e yana yi musu sallama Mummy ta mik'e itama Ibteesam ma ta mik'e alamun zasu tafi kenan, "Amma Daddyn da ka koma gida ka huta tunda yanzu ya farfad'o kuma alhamdulillah yaji sauk'i ke Baby sai ki zauna a wajan sa ko Amina?" Mummy tana kallon Anty Amina. Anty Amina tace, "Gaskiya hakan ne ya kamata tunda yaji sauk'i." "Noo Mum taje kawai Hameed yana nan" suka tsinci muryar Zaid a sama idon sa a kulle.

Haka Ibteesam ta mik'e jiki a sanyaye suka fito tana kallon sa ta gefen ido taga ko kallon inda take baiyi ba har suka fita.

Ajiyar zuciya yayi tana fita ya runtse ido yana furzar da iskar bakin sa yayi ya sake kulle idon sa, Daddy da Anty basu tafi na sai wajan sha d'aya na dare sannan suka tafi aka bar su Wizzy da Hameed a wajan sa.

Juyi kawai Ibteesam take a kan gadon ta kalli Zahra ganin tayi bacci ya saka ya mik'e zaune tayi tagumi tana tunani, "Meyasa yak'i kallo na? Haushi na yake ji kenan?" Ta tambayi kanta cikin damuwa, dan share ta d'in da yayi ya bata mamaki taji kuma babu dad'i sosai har cikin ranta, komawa tayi ta kwanta tana ta tunani har bacci ya kwashe ta.

Washe gari da wuri ta tashi tayi wanka ta shirya cikin riga da siket na atampa wanda suka yi mata kyau suka zauna a jikin ta d'am, a falo ta tarar da Abban ta ya kalle ta da murmushi yace, "Baby na ya gana kin rame?" Ya fad'a yana kallon ta da kulawa. Bata ce komai ba tayi murmushi tare da sunkuyar da kanta, "me yake damun ki?" Ya tambaya yana kallon ta. "Babu komai Abba" ta bashi amsa a sanyaye, "maza kiyi breakfast ku tafi asibitin to". Da to kawai ta amsa amma bata tunanin zata iya saka wani abu a cikin ta.

Basu jima sosai ba Zahra ta d'auki mota suka tafi asibitin bayan sun tafi da abinci.

A asibiti kuwa yana zaune a kan gado yayi wanka ya shirya cikin dogon jeans bak'i da kuma riga body hope mai d'an d'ame jiki kamar ba mara lafiya ba dan fess dashi dan in badan ramar da yayi ba babu wanda zaice bashi da lafiya, hannun sa rik'e da cup d'in shayi amma ya kasa sha sai juya spoon d'in yake a cikin kofin, Anty Amina da ta lura dashi tace, "Zaid kasha tea d'in mana?". D'agowa yayi ya kalle ta sai ya d'an sha kad'an ya cigaba da juya spoon d'in.

Bud'e k'ofar da akayi ya saka ya kalli k'ofar yana jiran yaga wanda zai shigo, Mummy ce sai Zahra a bayan ta suka shigo cikin sallama, cikin sakin fuska Anty Amina ta amsa suka gaisa cikin mutunci kafin ta kalli Zaid tace, "lah lallai Zaid jiki yayi sauk'i irin wannan kwalliya haka?" Ta fad'a da murmushi tana kallon sa. D'an murmushi kad'an yayi kafin tace, "To ya jikin naka?". "Da sauk'i" ya amsa a tak'aice.

A lokacin Ibteey ta shigo d'akin cikin sallama k'arasawa tayi wajan Anty Amina suka gaisa kafin ta kalli Zaid da ya lumshe ido tace, "Ina kwana ya jiki?" Ta fad'a a had'e tana kallon sa, banza yayi mata bai amsa ba sai ajjiye kofin tea d'in hannun sa da yayi yana komawa ya kwanta a kan gadon,? d'uf Ibteey ta d'auke wuta ganin irin zallar wulaqancin da yayi mata a gaban idon kowa sai kawai taji hawaye ya cika mata ido don babu karya ya dizga ta, su Mummy duk dun lura tun jiya da ya farka bai mata magana ba gashi yanzu tayi yayi mata banza sai Mummy tace, "Zaid baka ji an gaishe ka bane?".

"Noo Mum banji ba waye ya gaishe ni?" Ya fad'a yana kallon Mummyn da itama shi take kallo da mamakin? abinda yace, sai kawai ta k'yale shi jin rainin hankalin da yayi mata bata ce masa komai ba, Dr ne ya shigo da takarda a hannun sa ya kalli Zaid yace, "to malam Zaid ga takardar na sallame ka kar kayi mana kuka dan na lura in ka sake kwana a asibitin nan tsaf zaka iya kuka" ya fad'a cikin sigar zolaya yana kallon sa, "Allah ya bada lafiya, ka kula dan Allah da shiga damuwa da kuma waje mai sauti sosai" ya sake fad'a yana kallon Zaid d'in.?

D'aga masa kai kawai yayi ya amshi takardar yana mik'ewa zaune, Mummy tace, "Zaid sai da ka takura aka yi sallamar nan?". "Mummy bana son zaman nan" ya fad'a yana sakkowa daga kan gadon, Anty Amina tace, "Zaman asibiti ai bashi da dad'i daman ai sai dole, amma dai Dr yaji sauk'i ba tisaltawar sace ta saka aka bashi sallamaba?" Ta fad'a tana kallon sa, Dr yace, "yaji sauk'i sosai ma kuwa dan da baiji ba ai bashi da bakin da zaice a bashi sallamar ni, ni mamakin ciwon nan nasa ma nake da ya farka shikenan kamar baiyi ba duk dai yana shan wahala" ya fad'a yana kallon Zaid d'in, "nima haka wallahi Dr, amma tunda dai an samu lafiyar an gode Allah" ta fad'a tana mik'ewa tsaye. Kayan abincin da aka zo dasu aka d'auka da kansa yake tafiya har wajan mota, Ibteesam na bayan su tana duba wayar ta da taga missed call, sautin wani saurayi yaji yana fad'in, "Yauwa gata nan ta fito Allah yasa ta saurare mu". Cak ya tsaya tare da juyowa ganin bata k'araso wajan su ba ita, kayan jikin ta yake k'arewa kallo yaga mayafin jikin ta ba wani babba bane ga kuma kayan sun d'an kamata sun fito mata da surar jikin ta sosai gashi da tana tafiya sai komai na jikin ta yake motsawa, lumshe ido yayi ya bud'e a kanta a lokacin ta k'araso wajan samarin, "Dan Allah en mata ki tsaya ki saurare mu" saurayin ya fad'a yana matsowa inda take.

Kallon sa tayi ta kuma kalli Zaid da yake kallon ta zatayi magana yayi ????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
mata wani irin kallo da taki bakin ta ya rufe gum kamar an saka allura da zare an d'inki mata, hanya ya nuna mata da hannu alamun tazo ta wuce da sauri ta bar wajan ta k'arasa wajan motar, dukka mutanen wajen babu wanda baiga abinda ya faru ba murmushi kawai sukayi suka shiga mota aka tafi gida.

Suna komawa gidan sama suka tafi shida su Hameed su kuma suka shiga cikin gidan, zaman falon duk sai ishe ta kawai ta koma d'aki ta kwanta bata son wainar da ake soyawa a falo ba, ta jima sosai a kwance kafin taji an bud'e k'ofar d'akin an shigo, Mummy ce ta shigo tana fad'in, "Baby kizo ki kaiwa Zaid abinci". Mik'ewa zaune tayi tana kallon k'asa tare da fara lalubar d'ankwalin ta da ya kwance, "Baby lafiya kike kuwa?". "Lafiya lau Mummy kawai bana jin dad'i ne" ta fad'a tana mik'ewa tsaye bayan ta d'aura d'ankwalin ta.

"To muje ki kai masa" da to kawai ta amsa mata ta biyo bayan ta sabida bata san abinda zata ce ba, suna fitowa falon taga Umma da Jidda da alama ma sun jima da zuwa dubiyar sai taji hankalin ta ya kwanta tana kuma buk'atar yin magana da Umman nata, "Umma shine ko a neme ni ko?" Ta fad'a cikin shagwa6a tana kallon Umma.? "Ni na isa nak'i neman ki, na d'auka bacci kike yi ne" ta fad'a tana kallon ta da murmushi.? Itama murmushin tayi ta Mummy ta bata tray d'in tace, "Kai masa maza kizo". Babu yadda zatayi ne yasa ta karb'a dan tana jin kunyar Mummy amma da babu abinda zai sake kaita wajan sa bazan dinga wulaqantata a banza ba.

Tunda ta doshi falon take jin hayaniyar mutane kad'an-kad'an bata kawo komai ba kawai ta tura k'ofar da k'afa ta shiga da sallama, maza ta gani a zaune a falon da yawan su gashi ta riga tazo tsakiyar falon ga kaya a hannun ta, sunkuyawa tayi zata ajjiye tray d'in akan table wuayn rigar ta ya d'an yi k'asa har kana hango sama k'irjin ta, a dai-dai lokacin Zaid ya fito daga d'aki hannu da sa rik'e da cup d'in tea yana sha.

Mugun ganin da yayi ya saka shi sakin kofin ya fad'i a wajan ya fashe ita kuma wannan sautin yaja hankalin ta ga kallon wajan, sai da gaban ta ya fad'i ganin yanayin sa da ya canja yana binta da mugun kallo wanda ya kusa saka ta fitsari a wando, "sannu da aiki en mata" d'aya daga cikin abokan nasa ya fad'a yana kallon ta da murmushi a fuskar sa. Kasa amsawa tayi sai kallon Zaid d'in da take yi shima kuma ita yake kallo, ta bud'e baki zatayi magana ya k'araso wajan ya ja hannun ta zuwa cikin bedroom d'in sa.

Hameed ya kalli wanda yayi magana a cikin abokan nasu yace, "Ahmad wa ya kaika?". Wanda aka kira da Ahmad yace, "ta burge ni ne". Zaro ido Hameed yayi yace, "Kar ka kuskura yaji ka kana fad'ar wannan maganar, matar sace fa". Bud'e baki sukayi dukkan su suna kallon Hameed da mamaki, Ahmad yace, "Matar sa? Dan girman Allah da gaske?". "Na rantse da Allah da gaske nake, kai in badan matar sa bace wacece zai jata d'aki haka? Kamar baku san halin sa bane ba". Mik'ewa Ahmad yayi yace, "Kaga tafiya ta dan bazan zauna ya fito ba ya dinga bina da wannan fitinannun idon nasa" ya Fad'a yana yin hanyar k'asa da sauri yana dariya.

Zaid kuwa kawai kallon ta yake amma baice mata komai ba ita kuma kallon ne bata so dan yana kashe mata jiki sosai, takaici ne yake sake kama shi ji yake kamar ya shak'e ta in ya tuna a yadda ya ganta ga maza a wajan gashi kuma wani ya tare ta d'azu ga wayar da yaji tana yi sai yaji wani irin bak'in ciki ya sake kama shi, zama yayi a kan gadon ya dafe kansa yana numfashi a fili k'irjin sa na sama da k'asa.

Ganin yanayin sa duka sai ta tsorata hankalin ta ya tashi sai kawai ta fara yi masa kuka, tun tana yi a hankali har ya fito fili dan yaji, runtse ido yayi yana jin kukan ta har kansa daman yasan wannan fushin da ya d'auka da ita babu inda zashi wuyar ta su kasance su biyu a waje d'aya, a hankali ya mik'e yazo inda take ya saka fingers d'in sa guda biyu ya d'ago da hab'ar ta yana kallon yadda hawayen suke sakkowa daga idon ta.

Hannu ya saka ya share mata hawayen yana fad'in, "Meye na kukan bayan nine ya kamata nayi kukan bake ba? Nayi miki wani abun ne?" Ya fad'a muryar sa k'asa yana kallon fuskar ta, girgiza masa kai tayi alamun a'a, "na dake ki?". Ya sake tambyar ta har lokacin yana rik'e da fuskar ta, nan ma girgiza kai tayi alamun a'a, "so why the cry now? Ko kina so na sake komawa asibiti?".
"A'a" ta furta kukan na sake kamata.

Zuba mata ido kawai yayi yana kallon ta, Allah ya sani bai san adadin soyayyar da yake yiwa Ibteesam ba kullum k'ara masa son ta ake da k'aunar a cikin ransa, "yanzu me kike so?" Ya fad'a cikin sigar tambaya. "Abincin na kawo maka" ta fad'a tana goge idon ta, "meyasa zaki zo haka babu mayafi a jikin ki?". "Ban san akwai bak'i ba." "Meyasa kika je asibiti da k'aramin mayafi?". Shiru tayi bata amsa ba tana kallon k'asa, yace, "tallan jikin ki kike yi ko kuwa neman mijin aure kike yi?". Saurin kallon sa tayi ya lumshe ido ya bud'e alamun abinda yakee nufi kenan, girgiza masa kai tayi alamun a'a.

"Dan raina ya b'aci ne kenan?" Ya sake fad'a yana kallon ta, nan ma girgiza masa kai tayi alamun a'a, "to meyasa?" Ya fad'a yana had'e hannayen sa a k'irjin sa yana kallon ta. Shiru tayi bata amsa ba kanta? a k'asa dan bata san abinda zata ce masa ba, a hankali ta iya furta, "I'm sorry" ta fad'a muryar ta na d'an rawa kad'an. Jan hannun ta yayi ya zaunar da ita a gefen gado tare da cewa, "Sorry for what precious?".

Kallon sa tayi shima ita yake kallo ta samu k'arfin guiwar tsayar da idon ta a cikin nasa tace, "for anythings" tana fad'a ta sauke idon ta daga cikin nasa ta kawar da kai, a kan bedside ya zauna yana kallon ta har lokacin sai kawai yayi murmushi sosai wanda gabad'aya haqoran sa sai da suka bayyana. Zuba masa ido tayi ganin yana murmushi shi kad'ai ya kalle ta ta k'asan ido sai ya mik'e tsaye tare da rik'o hannun ta yace, "dawa kukayi waya d'azu asibiti?". Kallon sa tayi kafin tace, "cousin d'ina ne Hamma Ameer". Girgiza kai yayi yace, "yasan kina da aure?". D'aga masa kai tayi alamun eh, "shi kuma wanda ya tare ki fa?". Sai da ta kuma kallon sa sannan tace, "ban san shi ba tunda muka zo Mummy tace ta manta wayar ta na d'auko mata yake bina nak'i kula shi shine ya tsaya." Shiru yayi yana kallon ta na wasu mintina kafin yace, "Let go" yana fad'ar hakan ya mik'e suka fito baiyi mamakin ganin babu kowa ba sai kofin da ya fasa suka tsallake suka sauka.

Hannun sa na rik'e da nata har k'asa babban falo inda suke zaune suna tattaunawa akan bikin Zaid d'in suka gansu sun shiga a lokacin su Umma sun tafi, dafe kansa yayi tare da yamutsa fuska Daddy yace, "Jikin ne?". Girgiza kai yayi alamun a'a har lokacin bai saki hannun ta ba, "ka sauko a dai-dai daman maganar bikin ku muke yi" Mummy ta Fad'a da murmushi tana kallon sa.

D'an zaro ido waje yayi yace, "bikin suwa?". Kallon sa dukkan su sukayi jin abinda yace Mummy tace, "ba'a sani ba". D'an murmushi yayi kad'an ya zauna sai a lokacin ya saki hannun ta yace, "Daddy gata nan ka tambaye tanada ra'ayin zama da Zaid if not babu wanda sai forcing d'in ta" ya fad'a yana kallon Daddy da shima shi yake kallo.

Mummy tace, "Amma Zaid yau fa ka dawo daga asibiti har ayi wannan maganar? " ya kalli Mummy yace,"abinda za'a tambaya yanzu shine zai k'ara min lafiya daman a kansa ai na fara rashin lafiyar kuma na warke yanzu abinda ya rage shine abinda zata ce, pls Mummy mu bata chances itama, kar ku damu a kaina,". Daddy ya kalli Ibteesam da take zaune a kan carpet kanta a k'asa kana ganin ta kasan tana cikin matsananciyar kunya, "Daughter kinji abinda yace daman kuma nayi miki wannan alqawarin tun ba yanzu ba, kina son Zaid a matsayin mijin ki?".

Shiru bata amsa ba sai k'asa da tayi da kanta tana jin kunya da takaicin abinda Zaid yayi mata, dan a ganin ta wannan maganar da zasuyi ita dashi ne basai ya kawo ta gaban iyayen ta ba, ganin tayi shiru ya saka Daddy ya sake cewa, "Daughter ki fad'i abinda yake ranki dukkan mu nan iyayen ki ne babu mai miki abinda bakya so, kina son zama da Zaid a matsayin mijin ki." Kallon ta kawai Zaid yake yana so yaji abinda zata ce zuciyar sa na k'ara gudu sabida fargaba, ya rufe ido yana jira yaji mai zata ce.

A hankali Ibteesam ta d'aga kai alamun eh, Daddy yayi murmushi yace, "kenan kin amince?". Nan ma ta d'aga kai alamun ta yadda, maganar Daddy ita ta saka ya bud'e ido ya kalle ta lokacin ds take d'aga kan alamun eh, ai kawai sai suka ga Zaid ya zube a wajan yayi sujudul shukur ga Allah subahanahu wata'ala da ya bashi ikon ganin ranar da ya jima yana jiran zuwan ta a rayuwar sa.

*?ASAITAR SO!*

*70_71*

Not edited >?u?



Da kallo dukkan su suka bishi suna murmushi har ya d'ago daga sujjadar ya koma ya zauna sai kuma ya d'aure fuska, Daddy yace, "Masha Allah, Allah yayi muku albarka gabad'ayan ku, ya kuma saka albarka a cikin auren ku, ya albarkace ku da yara na gari." Suka amsa da Amin tana sunne kai a k'asa.

Daddy ya kalli Zaid zaiyii magana sai yaga ya zame daga kan kujerar ya zauna akan carpet abinda baya yi kenan a rayuwar sa sai dai ka saka shi yayi amma badan kansa ba, kallon Anty Amina yayi da murmushi yak'i barin fuskar ta yace, "Daddy, Mummy, ku saka baki tayi hak'uri akan komai, nayi mata laifi da yawa a baya ko ni ban san adadin su ba" ya Fad'a yana kallon Anty Amina da take murmushi.

Kafin suyi magana tace, "Kar ka damu Zaid komai ya wuce ni ban tab'a ganin laifin ka ba, domin duk abinda kake yi kana yi ne sabida mahaifin ka". Kallon ta yayi sai ya tuna lokacin da ya mare ta sai yayi saurin d'auke kansa daga kallon ta rana d'aya yaji wani abu waishi jin nauyin mutum a ransa, sai kuma ya tuna ai a lokacin itace da laifi, Daddy da yake murmushin farin ciki yace, "Alhamdulillah, yanzu Zaid in kaji sauk'i sosai zaku je can Gombe ka gaisa da dangin Abban na ta na can".

Kallon Daddy yayi yace, "Ba akwai flight Kano to Gombe ba? Gobe zamu je" ya fad'a kansa tsaye ba tare da tunanin komai ba, "Amma baka gama jin sauk'i ba" Anty Amina ta fad'a cikin kulawa, "No naji sauk'i zamu je goben ko precious?" Ya fad'a yana zuba mata idanun sa, Duk sai ta takura ta kasa sakewa a wajan ta kuma kasa bashi amsa, tab'e baki ganin yadda take wani sunkuyar da kai kamar munafuka shi kam baiga abinda sunkuyar da kai a nan ba.

Daddy yace, "Kaga kenan da kunje kun dawo sai ayi biki". Zaid ya kalli Daddyn yace, "bikin wa wai?". Hararar sa Daddy yayi yace, "wai maganar auren wa ake yanzu in ba naka ba?".? Yatsine fuska yayi yace, "Daman ana biki ne bayan an d'aura aure?". Mummy tace, "Sosai ma kuwa." Yace, "no

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login