Showing 21001 words to 24000 words out of 171073 words

Chapter 8 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7824

shi da addu'a Allah ya sassauta masa zafin zuciyar tasa dan addu'a ita kad'ai ce mafita a gare shi "

"Ance mace na canja mutum anya akwai macen da zata iya canja Zaid kuwa?" Daddy ya fad'a cikin tunani da al'ajabi. Dariya Amina tayi tace, "Tsaf kuwa, indai yana sonta wallahi babu abinda bazai yi ba, ina tabbatar maka mamaki ma zaka fara yi anya kuwa shine." D'an murmushi Daddy yayi yace, "Ai kuwa zan fara addu'a daga yau Allah ya had'a shi da wacce lokaci d'aya zaiji yana son ta kodan ta koya masa hankali". Kawar da zancen tayi ba tare da tace amin ba tace, "Yanzu dai breakfast d'in ka yana jiran ka kar yayi sanyi." "To shikenan, yanzu zan sakko" ya fad'a yana mik'ewa ya shiga bedroom d'in sa.

Da kallo ta bishi tana zuba masa harara har ya wuce tayi wani irin munafukin murmushin samun nasara tana aiyana abubuwa da dama a zuciyar ta.

*Kaduna.*

Kamar kullum tana zaune a d'aki tayi tagumi tana tunani kala-kala, tsaki tayi dan har ga Allah zaman kad'aici nan ya ishe ta wacce take d'an taya ta hira baje gida bata nan shiyasa zaman gabad'aya ya ishe ta, ajiyar zuciya tayi fuskar Khalid yana yi mata yawo a idon ta zuciyar ta cike take da kewar sa da san ganin sa, bud'e k'ofar da akayi ya saka? ta d'ago kai tana kallan wanda ya shigo, gaban tane yayi mummunar fad'uwa ganin wanda ya shigo yana jifan ta da wani irin kallo, gyara zama tayi kafin ta kalle shi tace, "Lafiya?". Kulle k'ofar yayi kafin ya shigo cikin d'akin yace, "Lafiyar ce ta kawo haka y'an mata, zuwa nayi na taimake ki na kub'utar dake daga hannun wannan mai gidan namu amma fa in kin amince" ya fad'a k'asa-k'asa yana jifan ta da wani irin murmushi irin na y'an bariki.

Jin za'a kub'utar da ita ya saka tayi murmushi tace, "Na amince indai zaka fitar dani daga gidan nan ni kuma zan yi ko meye." Murmushi yayi ya zauna akan bedside yace, "Yauwa y'ar gari, so nake ki bani had'in kai mu more wannan lokacin ni kuma na miki alqawari zaki bar gidan nan a yau" ya fad'a yana lashe baki yana sake zuba mata idanu. "Mtsww wato ku dukkanin ku halayyar duka d'aya ce da kai da Ogan naku ko? To wallahi nafi k'arfin ku wanda ya fiku ma nafi k'arfin sa balle kuma ku, dallah malam tashi ka bani waje ban amince da buk'atar ka ba zan cigaba da rok'on Allah ya bani ikon fita daga nan lafiya ba tare da taimakon kowa a cikin ku ba" ta k'arasa fad'a cikin fad'a da rashin kunya.

D'aure fuska yayi ya mik'e tsaye ya fara b'alle ma6allan rigar yana kallan ta yace, "Daman ai zab'i biyu gare ki in kin amince na huta dake sannan na fitar dake, in baki yadda ba kuma na huta dake kuma ki cigaba da zama a nan d'in, kin san Allah ina ganin abinci bazan k'i ci ba" ya k'arasa fad'a yana zame rigar jikin sa. Yunk'urawa tayi zata mik'e ya tankad'a ta ta fad'a kan gadon a kwance, ta yunk'ura zata mik'e zaune ya fad'a kanta ya sakar mata nauyin sa ta kwalla k'ara mai k'arfin gaske.

A dai-dai Wizzy yayi parking a harabar gidan, gaban Zaid ne ya fad'i jin k'arar da yayi har tsakiyar kansa kasancewar tagar d'akin a harabar gidan take kuma a bud'e hakan ya saka aka jiyo k'arar rad'au, bai san dalilin fad'uwar gaban tasa ba hakan ya saka ya kalli Wizzy da shima shi yake kallo, kafin Wizzy yace wani abu Zaid ya fita daga motar da saurin gaske ya shiga cikin gidan, bai tsaya kulle motar ba shima ya bita ya bi bayan sa a guje suka hau saman.

Dambe sosai ake tsakanin Gaye da Ibteesam tana kuka tana ihu da k'okarin kwatar kanta zuwa lokacin ya zame kayan jikin sa daga shi sai boxer, k'okarin dira take daga kan gadon ya jawo rigar ta ta baya ta yage ta sake fad'awa kan gadon, "ke har kin isa ki hana ni abinda zanyi? Baki isa ba wallahi dole na samu abinda nake so a tare dake ko bakya so" ya fad'a yana k'okarin zame boxer d'in jikin sa. Bud'e k'ofar da akayi ya saka shi tsayawa cak tare da juyawa yana kallan wanda suka shigo gaban sa yana fad'uwa tsoro da fargaba suka taru suka masa yawa, a guje ta dire daga kan gadon tayi bayan Zaid tare da k'ank'ame shi tana sakin wani irin kuka mai ban tausayi.

Runtse ido yayi jin yadda ta kwanta a baya ta ziro da hannayen ta ta rik'e cikin sa tana kuka, wani irin abu yaji yana masa yawo tun daga kansa har yatsun k'afar sa, wani irin d'umi jikin sa ya d'auka lokaci d'aya tsigar jikin sa na tashi kasala ta saukar masa a lokaci d'aya, hannu ya saka ya fincike ta daga jikin sa ya tura ta gefe ya mayar da kallan sa ga Gaye da yake rawar jiki gumi yana tsatstsafo masa daga jikin sa, "Gayee meye haka,? Kai a ko ina sai ka nuna halin ka na y'an bunshuru?" Wizzy ya fad'a yana kallan sa cikin b'acin rai.

Kar kar kar haka jikin sa yake rawa sabida bala'in tsoro ganin mai gidan nasa ya zuba masa ido kawai baice komai ba, Mugu da suke zaune yare da Gaye a gidan ya kalli Gaye cike da takaici yace, "Haba Gaye wannan wacce irin dabi'a ce? A gidan mai gida kake k'okarin aikata haka? Daga fita ta na siyo kati shine ka samu wannan damar?". Juyawa Zaid yayi kawai ya fice daga d'akin da saurin sa, bai jima ba ya dawo hannun sa d'auke da sabuwar wuk'a fil sai k'yalli take, "Wizzy ku danne min shi" ya fad'a muryar sa na wani irin shaking sabida yadda yake ransa a b'ace.

"Na shiga uku, dan Allah dan Annabi Mai gida kayi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne ya jani ga aikata hakan, ka yafe min dan Allah" ya fad'a yana d'urkushewa tare had'e hannayen sa waje d'aya alamun rok'o, Wizzy da suka fahimci abinda mai gidan zai aikata duk sai suka tsorata Wizzy yayi saurin amsar wuk'ar hannun sa yace, "Ayi hak'uri mai gida a sassauta masa yaci darajar Maman mu". Fincike wuk'ar yayi daga hannun Wizzy ya nufi inda Gaye yake yana tattare hannun rigar sa, "dan Allah kayi hak'uri mai gida na tuba bazan sake ba" ya fad'a yana ja da baya Zaid yana sake tunkarar sa.

Da k'arfin gaske ya naushe shi a baki haqorin sa d'aya yayi tsalle ya fad'i a gefe jini ya fara fita daga bakin sa.

"Mai gida kayi hak'uri dan Allah ka sassauta masa, yayi kuskure babba mun sani amma dan Allah kayi hak'uri" Mugu ya fad'a yana kallan Mai gidan nasu cikin tsoro da kuma tausayin Gaye, da wani ne ba Gaye ba tabbas da kansu zasu rik'ewa Mai gida shi yayi abinda yake niya amma Gaye ana tare ko babu komai tun kafin had'uwar su da Mai gida a waje d'aya suke.

Ihun da Ibteesam tayi tare da kulle idon ta shine ya dakatar dashi ga k'okarin farka gajeren wandon jikin Gaye,? sakin wuk'ar hannun sa yayi ya dafe kai yana runtse ido, "ke...." bai k'arasa abinda yake so yace ba ya fad'i a wajan a sume.

A hankali a tashe Wizzy suka yi kansa suna jijjiga shi amma babu alamun numfashi a tare dashi, "Wizzy ina jin ciwon sane fa ya tashi" Mugu ya fad'a hankali a tashe yana kallan Zaid da yake kwance a k'asa, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, kinga d'an bamu d'ankwalin kanki" Wizzy ya fad'a yana kallan Ibteesam da take kallan su tana mamakin wanne irin ciwo ne wannan. "D'ankwali na kuma?". "Kinga babu lokaci dallah malama ki bamu" ya fad'a a tsawace yana zare mata ido, cirewa tayi ta mik'a masa ya karb'a da hanzari ya kama kan Zaid ya d'aure da k'arfin gaske, "Yanzu ina zamu samo likita a garin? nan?" Mugu ya tamabaya yana kallan Wizzy.

"Is better mu kaishi asibiti kaga babu likitan da muka sani a nan Kaduna balle mu kira shi yazo." "Ba magana ba Wizzy mu fara bashi taimakon gaggawa" ya fad'a yana ficewa daga d'akin ya nufi dakin ya Zaid d'in dan nema masa magani.

Wizzy ya kalli Gaye da yake rakub'e a jikin bango yana kuka yayi tsaki yace, "Dallah malam tashi ka bamu waje tun kafin ya farfad'o ya ganka a nan ranka ya b'aci". Ai da gudu ya kwashi kayan sa ya fice yana waiwayen Zaid.

Ibteesam kuwa tunda aka ambaci Kaduna ta d'auke wuta ta fara tunanin dama wai ba'a Kano take ba,? Ita duk a tunanin ta a Kano take shiyasa take tunanin guduwa, Hankalin ta ya k'ara tashi kawai itama ta fashe da kukan tausayin kanta.

Mugu ne ya dawo d'akin da magani a hannun sa da kuma gorar ruwa mara sanyi, bud'e rufin robar sukayi aka tsiyayo ruwan suka yayyafa masa a fuska a hankali ya motsa idon sa, kallan juna sukayi tare da yin murmushi cikin murnar motsawar sa, "Sannu mai gida" suke fad'a ganin yana k'okarin bud'e idon sa, k'okarin mik'ewa zaune yake suka taimaka masa ya mik'e suka bashi magani ya karb'a yasa idon sa a kulle, taimaka masa sukayi ya mik'e suka rik'e shi suka kaishi d'aki ya kwanta, Wizzy ya kalli Mugu yace, "Allah ya taimaka ciwon bai yi nisa ba da dole mu sanar da Daddy, mtswww amma gaskiya Gaye anyi d'an akuya wallahi."

"Bari kawai Wizzy ban d'auka zai aikata haka a gidan Mai gida ba wallahi, ai Mai gida kamar uba yake a wajan mu tunda babu abinda baya mana muda iyayen mu". "Muje k'asan kawai" Wizzy ya fad'a suka sakko daga saman.

Bayan wasu awanni Ibteesam tana zaune tana tunanin y'an uwan ta da masoyin ta kamar koda yaushe aka shigo d'akin, kallan sa tayi ganin sa rass dashi kamar bashi ne ya fad'i d'azu a sume ba, saurin d'auke kai tayi ganin yadda yayi mata kyau a ido sai take ji kamar tai ta kallon sa, gefen gadon ya nufa ya kalle ta fuskar nan a d'aure kamar kullum yace, "kin shirya?". Gaban ta ya fad'i amma sai ta daure tace, "Me?". "Zama karuwa mana" ya fad'a kansa tsaye yana kallan ta. "Meyasa d'azu baka bari shi yayi min hukuncin ba?". "Ni nake so nayi miki da kaina ba wani ba." "Amma meyasa ranka ya b'aci har kayi ciwo?". Kallan ta yake cikin mamakin tambayar ta kafin ya tab'e baki yace, "Bana san yawan tambaya" ya fad'a yana mik'ewa zaune tare da zuba hannayen sa a cikin aljihun wandon sa, "koma meye sunan ki ina so ki sani babu abinda zai fitar dake? daga gidan nan matuk'ar ban d'auki mataki a kanki ba ba'a yi min na k'yale ina fatan kin gane?".

Yawu ta had'd'iye idon ta ya kawo ruwa tace, "Dan Allah ka sanar da iyaye na ina hannun ka ko babu komai hankali su zai kwanta dan nasan yanzu suna ta tunanin inda nake" ta fad'a hawayen na sakkowa daga idon ta.

Hannu ya saka a aljihu ya d'auko waya tare da mik'a mata yace, "Kira su". Da mamaki ta kalle shi ta kalli wayar hannun ta na rawa ta karb'a, da hanzari take danna number Abba ta, buga biyu Abba ya d'auka tare da yin sallama, "Abba na" ta fad'a cikin muryar kuka hawaye na cigaba da zuba a idon ta.

A can b'angaren Abba da yake zaune cikin iyalan sa da hanzari ya saka wayar a speaker kafin yace, "Ibteesam! Kece?". Girgiza kai take kamar yana gaban ta kafin tace, "Nice Abba ina Umma?". Umma da take zaune muryar ta na rawa tace, "Ibteesam gani, kina ina? Ina kika shiga tsahon wannan kwanakin?". Kuka ne yaci k'arfin Ibteesam ta kasa magana sai kuka jin muryar iyayen ta ya taso mata da kewar su da take kwana da ita ta tashi da ita, "kiyi magana Ibteesam kina ina?" Abba ya fad'a da hanzari. Karb'ar wayar Zaid yayi daga hannun ta ya kara a kunne yace, "Tana hannu na". Abba ya kalli Umma itama ta kalle shi kafin Abba yace, "Kai waye? Meyasa ka d'auke ta?".
"Sanin ni waye bashi me mahimmaci ba abinda nake so shine mai mahimmaci". Da sauri Umma tace, "Mai kake so? Ka fad'a insha Allah zamu baka."

"Abinda nake so yana tare da y'ar ku amma tak'i ta bani gashi ni kuma ba ta k'arfi nake so na karb'a ba" ya fad'a yana yatsine fuska kamar yana gaban su, "Me kake so?" Abba ya tambaya cikin mamakin abinda Zaid yace, "Karuwa nake so na mayar da ita, y'ar ku ta kira ni d'an iska shiyasa nake so na mayar da ita y'ar iskar itama, kuyi mata fad'a ta amince dani ta dad'in rai tun kafin na nuna mata iko na". Babu wanda gaban sa bai fad'i ba tsakanin Umma da Abba, kallan juna sukayi kafin Abba yace, "Kayi hak'uri bawan Allah ka fad'i ko nawa kake da buk'ata mun maka alqawari zamu baka amma dan Allah kada ka raba ta da mutuncin ta."

Dafe kai Zaid yayi dan har ga Allah ya gaji da magana amma jin abinda Abban yace ya saka shi ya kama k'ugu kamar yana gaban su yace, "ohh kuma abinda zaku ce kenan? Okay to ku shirya ganin y'ar ku nan da shekara d'aya maybe tazo muku da baby". "Dan Allah kayi hak'uri ko nawa ne zamu baka amma kar ka cutar da ita dan Allah" Umma ta fad'a tana kuka sosai. Shifa b'ata masa rai suke in sukayi zancen ko nawa yake so d'in nan hakan yasa yace, "ko family d'in ku kaff za'a siyar baku da abinda zaku iya bani gwara ku daina zancen kud'i cos basa gaba na" ya fad'a yana runtse idon sa yana bud'ewa.

"Ka taimaka dan Allah ko nawa kake so zamu bayar mudai ka k'yale mana yarinyar mu". "Oh god wai baka ganewa ne? Meye a kanka ne har haka,? Na fad'a muku baku da abinda zaku iya biya na koda zaku saida kowa na dangin kune, ko kana da matsala toshewar basira ne ina fad'a baka ganewa?" Ya fad'a a fusace dan da a gaban su yake babu abinda zai hana bai kaiwa Abba duka ba.

"Kayi hak'uri bawan Allah ka dai duba dan Allah" Umma ta fad'a itama muryar ta a sanyaye sosai hawaye na bin idon ta.

"In shi baya ganewa kema bakya ganewa ne? Mai kuke dashi da zaku bawa Zaid d'an gidan Ambassador Abubakar Ali huhh,? In?zaku bawa y'ar ku shawara a akan abinda nake so ku bata kun bi kun cika min kunne da surutan ku na banza da wofi mtsw" yaja dogon tsaki tare da datse wayar.

Duk da Ibteesam shiga rud'ani da jin waye shi amma hakan bai hana taji haushin abinda yayiwa iyayen ta ba, dan ita fushin ta yafi k'arfi in aka tab'a mata iyaye yanzu ranta zai b'aci ta fad'a maka abinda baza kaji dad'i ba, bata san lokacin da ta diro daga kan gadon tace, "Wai kai ba'a koya maka tarbiyya a gidan ku bane ba? Ba'a koya maka yadda zakayi magana da manya bane hala,? Ko da yake ma ai laifi nane nima kowa ya ganka ai yaga mara tarbiyya wanda bai san darajar na gaba dashi ba, ina k'yale komai amma bana k'yalewa in aka tab'a min iyaye kuma......" irin juyowar da yayi ya hana ta k'arasa abinda take son fad'a, baya take ja jikin ta na rawa tsoro ya cika mata zuciya dan yadda yake kallan ta bai tab'a yi mata irin kallon ba, k'afar ta ta dama ya saka k'afar sa ya dake ta ya raba ta da k'asa sai kuwa ta wuntsila ta fad'i da baya kanta ya bugu da tiles jini ya fara zuba.



_free pages dai basu da yawa ki biya kud'i k'alilan ki karanta labarin cikin kwanciyar hankali da nishad'i, naira 100 ne kacal ba tsada kamar ruwan pure water, tuntub'i wannan number domin biya but only WhatsApp +2347045242700...._


Comments Share fisabinillah =?O?d'?>?p?
*g& ?ASAITAR SO! g&*

? ? ? ? ? ?? ?? *Nana Haleema*

*17?'?18*


Cize baki take tana runtse ido jin yadda kan ta yake mata wani irin zafi kamar an saka wuk'a an yanka k'eyar ta haka take ji, jinin da a kan tiles ya tabbatar masa da kanta ya fashe sai ya girgiza kai ya nuna ta da yatsa yace, "Last warning" abinda yace kenan kawai ya fice ya barta a wajan a kwance cikin ciwo.

Kuka take so tayi amma ta kasa sabida yadda take jin azaba na ratsa ko wanne sassa na jikin ta, tabbas tsanar Zaid tafi kowai tasiri a zuciyar ta a halin yanzu ji take da tana da iko kashe shi tabbas zata iya kashe shi sabida yadda ta tsane shi tsana kuma mai muni.

Direct k'asa ya sauka ya zauna a kan kujerar da take kallan su Wizzy yana wuci, ganin hakan sai suka ja bakin su sukayi shiru suna jiran ya wuce, "yana wanne Station?" Ya tambaya bayan ya rank'wafo ya had'e hannayen sa guda biyu a waje d'aya. Sun fahimci wa yake nufi hakan ya saka suka kalli juna kafin Mugu yayi k'arfin halin cewa, "rashin lafiyar ka ta d'auke mana hankali har ya fita bamu lura dashi ba, kayi hak'uri". Cize bakin sa yana furzar da iska daga bakin sa kana yace, "Yana ina yanzu?". "Bamu sani ba muma." Shiru ya biyo baya babu wanda yayi magana sai da aka kwashe mintina k'alilan kafin yace, "a nemo dr yaje ya yiwa waccan yarinyar dressing" yana gama fad'ar hakan kawai ya mik'e ya fita daga falon suka bishi da kallo.

"Wizzy anya kuwa wannan yarinyar ba itace wacce ta taki sa'a ta sace zuciyar mai gida ba? Ka duba yadda ya kasa yi mata komai da kuma yadda ya shiga tashin hankali a d'azu?" Mugu ya tambaya yana y'ar dariya yana kallan Wizzy. Shima dariya yayi yace, "Anya kuwa Mugu? Kana jifa cewa yayi ayi mata dressing wata kila fasa mata baki yayi kasan yarinyar akwai tsinanniyar rashin kunya shi kuma akwai zuciya". "Yanzu dai muje mu nemo tun kafin yazo muma ya raba mana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login