Showing 60001 words to 63000 words out of 171073 words

Chapter 21 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7810

Amina da ta tawo da breakfast ta kalli Daddy da yake zaune yana hamma kana kallon sa kasan da tarin gajiya a tare dashi tace, "Daddyn Zaid ya kamata kaje gida in anjima sai ka dawo na bar maka breakfast d'in ka a can". Juyowa yayi ya kalle ta kana yace, "bazan iya tafiya na bar Zaid a nan shi kad'ai ba zan jira har ya tashi". Kallan Eman tayi ta dawo da kallon ta ga Daddy tace, "Shi kad'ai kuma? Nida Eman ba mutane bane ba?". "Mutane ne amma bazan iya tafiya barshi a nan ba" ya fad'a yana k'okarin fito da waya daga aljihun sa, dan shi a yanzu tunda aka bawa Zaid guba yake tsoron barin sa da kowa.

Shigowar Dr Auwal Daddy ya dakata da buga wayar ya kalli Dr yace, "Dr sannu da aiki". "Yauwa Alhaji, an tashi lafiya, ya me jikin?". "Lafiya lau, me jiki gashi nan a kwance har yanzu bai tashi ba". Bai amsa ba kawai ya nufi inda Zaid d'in yake yana canja masa ruwa, "Alhaji ya kamata kaje gida ka huta sai ka dawo anjima" Dr Auwal ya fad'a yana kallon Daddy. "Yauwa Dr gwara ka fad'a masa abinda nake fad'a masa kenan nima" Anty Amina ta fad'a tana kallon Daddy.

"A'a Dr bazan koma gida ba gaskiya Amina zata koma gida yanzu ta d'auko min kaya ka bani key d'in office d'in ka na shirya a ciki" ya fad'a yana kallon Dr Auwal.?

"To shikenan Alhaji babu komai" ya fad'a yana fita daga d'akin, shiru ne ya ratsa d'akin babu wanda ya kuma magana a cikin su, bud'e k'ofar d'akin da akayi aka shigo ya sanya suka mayar da hankalin su ga wanda suka shigo d'in, Su Yaya Babba ne suka shigo fuskar su a sake babu alamun damuwa, "Sannun ku da zuwa" Daddy ya fad'a yana mik'ewa tsaye tana basu wajan, "Yauwa Sannu Abubakar, ya jikin Zaid?" Yaya babba ya fad'a yana k'arasawa inda Zaid d'in yake a kwance, "Da sauk'i gashi nan dai bar farka ba har yanzu" Daddy ya fad'a yana bin Yaya Babban da kallo.

"Me yake damun sa ne to?" Yaya Bala ya tambaya yana kallon Daddy, "Ciwon sane ya tashi" Daddy ya samu kansa da b'oye musu asalin abinda yake damun sa, "Allah sarki, gashi kwance kamar matacce babu ko motsi" Yaya babba ya fad'a yana kallon Zaid. Wani irin zafi Daddy yaji a ransa amma sai ya daure yace, "Bai farka ba har yanzu."

"Allah sarki, in cutar ta warkewa ce to, in kuma ta tafiya ce Allah ya bada sa'a Abdallahi" Uncle Saifullahi ya fad'a cikin muryar da take nuna zallar shak'iyanci. "Amin dai Saifu, dan yanayin jikin nasa naga sai a hankali" Uncle Bala ya fad'a yana kallon Saifullahi. Bin su kawai da ido Daddy yayi yana jin zafin duk wata kalma da suke furtawa sai kawai ya sunkuyar da kai yana sauke numfashi a hankali, "to mu zamu koma lokacin tafiya nema yayi, Allah ya zab'a abinda yafi alkhairi" daga haka suka fita daga d'akin Daddy ya bisu da kallo kawai har suka b'ace.

Babu wanda yace Allah ya bashi lafiya a cikin su, babu wanda yayi masa addu'ar waraka da neman sauk'i a cikin su, me hakan yake nufi,? Shigowa da akayi d'akin ya katsewa Daddy tunanin da yake yi ya kalli wanda ya shigo, "Ambassador barka da safiya" Abba ya fad'a yana mik'a masa hannu suna gaisawa da Daddy, "Barkan ka dai Alhaji Yusuf, ya gida da mutanen gidan?" Daddy ya tambaya yana sakin fuska.

"Lafiya lau, ya me jikin?". "Me jiki gashi nan a kwance bai farka ba dai har yanzu". "Subahanallahi, nazo jiya ban ganku ba na kira ka kuma ban same ka ba, Umman Ibteesam ce ta sanar dani a yadda Zaid d'in ya bar k'ofar gidan koda naje gidan naji lafiya akace kun tawo asibiti". Ajiyar zuciya Daddy yayi ya kalli su Amina da suke zaune yace, "Alhaji Yusuf muje waje muyi maganar" a tare suka fita daga d'akin suka bar su a ciki.

"Ai jiyan nan nima jini nane ya hau shiyasa kai ta kira baka same ni ba" Daddy ya fad'a lokacin da suke zama a kujerun da aka tanada.

"Ashsha, ya jikiin naka?". "Nawa da sauk'i Zaid d'in ne dai yake a kwance". "Me yake damun sa to?". Daddy ya ja numfashi ya fesar kana yace, "akwai wani ciwon zuciya da yayi fama dashi tun baifi shekara sha uku a duniya ba to mun d'auka ya warke ashe bai warke ba shine ya tashi jiya aka dawo dashi."

"Ai Maryam ta fad'a min yadda abinda ya faru a jiyan, ganin su da yayi da Khalid wanda yake son ta daga haka ciwon ya tashi, Hasbunallahu wani'imal wakil har ciwon zuciya da kuruciyar sa" Abba ya fad'a cikin tausayawa had'i da jimami. D'an murmushi Daddy yayi kafin yace, "Ashe kishi ne ya tayar masa da ciwon da ya jima bai tashi ba, lamarin Zaid sai shi" ya fad'a yana girgiza kai.? Abba yace, "Tana can itama hankalin ta a tashe tun jiya take kuka har yanzu, shiyasa nace bara nazo naga yanayin da yake ciki in yaso sai suzo ta ganshi". Ajiyar zuciya Daddy yayi tare da cewa, "Alhaji Yusuf bayan ciwon zuciyar Zaid yasha poison" ya fad'a cikin sanyi? murya.

A rud'e Abba yace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, poison Ambassador? Duk akan abinda ya faru jiyan,? Ni a gani na da Allah ya bashi lafiya a fad'a masa Ibteesam matar sace koda ita ba'a fad'a mata ba sabida gudun sake shigar sa wani hali" Abba ya fad'a cin tsantsar nuna damuwa da tashin hankali a fuskar sa k'arara. Wani sanyi Daddy yaji wanda tun aka sanar dashi abinda ya faru da Zaid baiji wannan sanyi a ran sa ba sai yanzu dan ganin ya samu wanda yake taya shi jimanta halin da Zaid yake ciki yace, "A'a ba a kan wannan bane ciwon zuciya daban gubar da yasha daban, lokacin da aka shigo dashi ruwa yace a bashi aka d'auko ruwan aka bashi to a cikin wannan ruwan a ciki gubar take, a yadda Dr yake fad'a guba ce wacce take kashe mutum lokaci d'aya, a tak'aice dai kawai an so a kashe Zaid ne ta hanyar zuba masa guba a cikin ruwa" Daddy ya k'arasa fad'a cikin wata irin murya mai nuna zallan rauni.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil, Allahumma a jirni fil musibati" abinda Abba yake maimaita kenan cikin tashin hankali da rud'ani. Daddy yace, "Abin ya kulle min kai yife da tunanin ka na rasa me zanyi tunani a raina, waye wannan yake neman ganin baya na?". "Dole ka rasa abinda zaka ce abu a cikin gidan ka aka d'auko ruwan aka bashi sha, to amma yanzu duka ba tunanin zaka mayar da hankali a akai ba, yanzu a samu Allah ya amshi addu'ar mu ya samu lafiya in yaso daga baya duk abinda za'a sai ayi, amma ka kula da zaman sa a asibitin nan da wanda zai zo duba shi sabida gudun samun matsala, Allah ya bashi lafiya, Allah ya tashi kafad'un sa" Abba ya fad'a cikin sanyin murya.

"Haka ne, amin nagode sosai". "To zan wuce Allah ya bashi lafiya" Abba ya fad'a yana mik'ewa tsaye, gaisawa sukayi Daddy ya sake masa godiya ya tafi.

Cikin sanyin jiki Daddy ya nufi d'akin da Zaid yake, ya saka hannu zai murd'a handle d'in d'akin abinda ya jiyo daga d'akin ya d'auki hankalin sa ya tsaya da bud'e k'ofar yana sauraron kalaman da Amina da Eman suke tattaunawa.

* Dan Allah kar a fitar min da labari.*
*?ASAITAR SO!*

*39_40*

Not edited>??



Muryar Eman ya jiyo tana fad'in, "Meyasa zaki saka gubar Anty Amina? Ni bana so ya mutu bana so a kashe shi ina son miji na." Anty Amina tace, "Ke dallah gafara can kashe shi shine burin mu kuma dole mu aikata kin gane,? Ki cire wannan soyayyar ki ajjiye a gefe mu aiwatar da abinda yake gaban mu" ta fad'a murya can k'asa.

Bud'e k'ofar da Daddy yayi ya shiga ya katse musu maganar da suke yi, kallon su yake one by one ko wacce rud'ani ya bayyana k'arara a kan fuskar ta, ganin yanayin su ya canja ko wacce ta zuba masa ido ya sanya ya d'an yi murmushi yace, "bai farka ba har yanzu?". "Eh bai farka ba wallahi" Anty Amina ta fad'a cikin rauni. "Yauwa kinga tashi kije ki d'auko min duk abinda kika san zanyi amfani dashi yanzu da kuma na anjima" ya fad'a lokacin da yake zama a kan kujera. "Baza kayi breakfast d'in ba?" Ta fad'a tana niyar d'auko abincin da tazo dashi.

"Noo kin san ban wanke baki ba kin san bana cin abinci sai nayi wanka, ki tashi Musa yana nan yaje ya sauke ki ya dawo dake ina jiran ki, Eman ko kema zaki koma gida ki huta tunda kema ba lafiyar gare ki ba?" Ya fad'a yana kallan Eman da ta zubawa Zaid ido. "To Daddy bara na koma amma anjima zan dawo" ta fad'a tana mik'ewa, "Yauwa to Allah ya kaimu anjiman, kiyi maza Amina jiran ki nake" da to ta amsa suka fita tare da Eman yabi bayan su da kallo.

Tsaye ya mik'e ya fara zaga d'akin cikin tsananin fargaba da tashin hankali, "kenan Amina ta dad'e tana son kashe Zaid? Meyasa take so ta kashe shi,? Ita da wa suke so suga bayan Zaid tunda gashi Eman ma tasan da batun kisan tabbas ba ita kad'ai bace, to su waye,?" Shine abinda Daddy yake fad'a yana zagaya d'akin, wani irin bugu zuciyar sa take masa fargabar sa ta k'aru hankalin sa ya kai k'ololuwar tashi in ya tuna bai san tsahon lokacin da suka d'auka suna farautar rayuwar Zaida ba, kallon sa ya mayar ga Zaid wanda yake bacci har lokacin yace, "Allah kad'ai yasan abinda suka yi masa da na fita,? ya Allah, kenan Zaid yasan nufin Amina shiyasa baya son ta ko kad'an? Hasbunallahu wani'imal wakil, ya akayi ya riga ni saurin gano ta haka?" Daddy ya fad'a yana dafe kai tare da zama a kan kujerar cikin rashin sanin abinda zaiyi.

"Dad!" Da sauri ya juya jin maganar Zaid, ido biyu sukayi dashi ai da sauri Daddy ya k'arasa kusa dashi yana fad'in, "Zaid ka tashi? Bara na kira Dr" ya fad'a yana juyawa ya fita da saurin gaske, bai jima ba suka dawo tare da Dr ya k'arasa wajan Zaid yace, "Sannu Zaid, me kake ji yanzu a jikin ka?". Lumshe ido yayi ya bud'e kana yace, "kaina yayi min nauyi haka chest d'in na, sai ciki na da yake zafi" ya fad'a yana d'an yatsine fuska kad'an.
"Ciwo cikin yake ko zafi yake maka?". "Zafi yake" ya bashi amsa lokacin da mayar da idon sa ya kulle, "Alhamdulillah, insha Allah komai zaiyi dai-dai poison d'in bai tab'a masa ciki sosai yadda muke tunani ba, ina zuwa" Dr ya fad'a yana fita daga d'akin da sauri.

"Poison" Zaid ya maimaita a hankali har lokacin idon sa a kulle yake, Daddy ne ya jawo k'aramar kujerar da take ajjiye a wajan ya zauna kusa da Zaid ya rik'e masa hannu, "Sannu Zaid". "Dad poison" ya fad'a lokacin da ya bud'e idon sa yana kallon Daddy d'in.? "Yes Son, an baka poison a cikin wannan ruwan da ka sha lokacin da abokan ka suka dawo da kai gida" Daddy ya fad'a masa cikin sanyin murya. Numfashi ya sauke kana yace, "u see Daddy, i told you wad'an nan mutanen suna so su kas???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?he ni ne then su kashe ka amma baka yadda ba, oshhhhhh ciki na..." ya fad'a yana d'an daga cikin sa sama tare da juya kai.

Daddy ya kuma rud'ewa yace, "Ka daina magana Zaid ka bari ka samu lafiya" ya fad'a cikin tashin hankali da nuna zallar damuwar sa a gare shi, knocking d'in k'ofar akayi ba tare da an shigo ba, Daddy ya mik'e yaje ya bud'e k'ofar, "Alhaji ya mai jiki?" Musa driver ya fad'a yana rusunawa, "Da sauk'i Musa." "Allah ya k'ara lafiya, Hajiya ce ta ce na kawo maka wannan ta tsaya a gida ta had'a abinci" ya fad'a yana mik'owa Daddy ledar hannun sa.

Karb'a yayi yace, "to ba laifi" ya fad'a yana juyawa ya shiga ciki, zama Daddy yayi a kan kujerar yana duba kayan da suke cikin ledar Dr ya shigo, ya kalli Zaid da sirinji a hannun sa yace, "Zaid zan maka allura". Shagwa6e fuska yayi kamar zaiyi kuka yace, "Dole ne allurar?". "Dole ce mana Zaid ita zata saka ka daina jin zafin da cikin ka yake maka." Kallon Daddy yayi shima shi yake kallo Daddy yace, "Dr yi masa in zaka bi ta tasa ba za'ayi allurar nan ba". Ba musu Dr ya d'an juya shi kad'an ya zunk'ula masa k'arfe, k'iris ya rage Zaid baiyi kuka ba dan allurar ta ratsa shi sosai, murmushi? Daddy yace, "Yauwa ni yanzu bara naje nayi wanka a office d'in Dr" ya fad'a yana mik'ewa tsaye, Zaid baice komai ba har Daddy da Dr suka fita daga d'akin.

Wani amai ne ya fara taso masa ya lallab'a ya zare ruwan dake hannun sa ya mik'e zaune dak'yar, aman yaji sosai ziro k'afar sa da niyar sakkowa daga kan gadon aman ya tawo ya fara zuba a k'asan d'akin, sosai yake aman yana rik'e cikin sa yana jujjuya kai, bud'e k'ofar akayi aka shigo d'akin bai san waye ba a yanayin da yake ciki bazai iya juyawa ba, galabaitar da yayi ya saka shi yin gaba zai kita da goshi, runtse ido yayi dan babu k'arfi a jikin sa da zai hana shi fad'uwa jira kawai yake yaji ya fad'i a kan tiles, jin shi yayi ya fad'a jikin mutum an rik'o shi ta baya khamshin turaren da yake shak'a ya sanya shi lumshe ido ya kwanta sosai a kafad'ar wanda ya tare shi, "Jidda kiyi sauri kije waje ki kira likita ko nurse" Ibteesam ta fad'a tana rik'e da Zaid a jikin ta jikin sa duk ya saki babu k'arfi ko kad'an a tare dashi.

Da sauri Jidda ta juya ta fita suka dawo tare da Dr Auwal da ta gani yana niyar shigowa d'akin, k'arasawa wajan da Ibteesam take tsaye yayi ya d'aga Zaid dsga jikin ta ya kwantar dashi a kan gado har lokacin idon sa a kulle yake, "Zaid" Dr ya fad'a yana kallon sa, bakin sa ya motsa kawai hakan ya tabbatarwa da Dr yana jin sa yace, "Har yanzu cikin da zafin?". Girgiza masa kai yayi alamun a'a, "Good" ya fad'ar hakan ya juya zai fita ya turo madu shara su gyara wajan.

Ibteesam ma juyawa tayi zata bar wajan ya rik'o hannun ta har lokacin kuma idon sa a kulle yake, juyowa tayi ta kalle shi ta kalli hannun ta, da k'arfi na d'an ja hannun amma ya rik'e hannun nata k'am idon sa kuma a kulle. Kallon Jidda tayi itama ta kalle Jidda tayi dariya tana b'oye fuskar ta a mayafi, gajiya da tsayuwar tayi ta zauna a akan kujera ta zuba masa ido, k'arewa fuskar sa kallo take ganin tayi haske sosai sai dai ta d'an rame, idon sa da yake a rushe eyelashes d'in sa sun kwanta a k'asan idon sa, lumshe ido tayi wani yanayi wanda bata san meye shi ba yana bin jikin ta kamar tafiyar kiyashi haka take ji yana zaga ko ina har cikin kanta take jin sa, bud'e idon sa yayi suka had'a ido tayi saurin janye idon ta shi kuma ya mayar ya kulle yana murmushi a zuciyar sa.

Knocking d'in k'ofar akayi tare da shigowa da sallama, amsawa sukayi mai shara ta shigo aka nuna mata inda zata gyara ta fara sharewa tana satar kallon Ibteesam da Zaid, sai da ta gama tass har zata fita ta juyo tace, "Bazan iya fita ban fad'a muku ba, gaskiya na jima banga perfect couples kamar ku ba, da ganin yanayin ku sabon aure ne, Allah ya bada zaman lafiya ya kawo zuri'a masu albarka" ta fad'a tana murmushi ta fita daga d'akin.
Kallon fuskar Zaid tayi sai taga ya saki fuska da murmushi a kwance a fuskar tasa ya amsa da amin a samman lips d'in sa, kallon Jidda tayi ta kawar da kai tana dariya itama sai abin ya bata dariyar.

Daddy ne ya shigo d'akin da sallama, amasawa sukayi Ibteesam ta fara k'okarin mik'ewa tana son kwace hannun ta amma ina ya rik'e ta gam, "A'a Maryam ashe kune a d'akin" ya fad'a da murmushi a fuskar sa yana zama a kan babbar kujerar. Jidda ta tsunguna har k'asa ta gaishe shi ya amsaa fuska a sake yana tambayar mutanen gidan, lura yayi da hannun Ibteesam da yake cikin na Zaid tana taso ta kwace ya hana sai yayi murmushi yace, "Yi zaman ki y'ar ta mu gaisa daga nan". Cikin jin nauyin Daddyn suka gaisa,? Dr Auwal ne ya shigo d'akin ya kalli Zaid yace, "yanzu ya kake ji?". "bana jin komai sai chest pain" ya fad'a a hankali kamar baya so yayi magana.

"Shima k'irjin zai daina ciwo amma sai ka cire damuwa a ranka ka, yanzu kana under heart attack patients dole ka kiyaye kasan irin yanayin da zaka dinga shiga a kan komai ma". Daddy yace, "gaskiya ne, ya batun ciwon cikin?". "Yace babu yanzu ai bayan fitar ka na shigo nayi masa allurar da ya amayar da duka poison d'in da ya rage a cikin sa yanzu babu komai a jikin sa insha Allah."

"Alhamdulillah, Dr Auwal nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi" Daddy ya fad'a da da farin cikin a fuskar sa, "babu komai Alhaji kayi min komai na rayuwa kar ka manta aikin da nake yi a yanzu kaine ka sama min shi, shi kansa Zaid d'in ya bani taimako masu yawa a lokacin da nake makaranta da kuma kwanaki da na shiga wata matsala, kun wuce komai a waje na wallahi shiyasa na san yadda nayi na saka aka kawo min allurar daga Abuja kuma Alhamdulillah tayi yadda ake so."

"Dr gida" Zaid ya fad'a har lokacin idon sa a kulle yake, "Bara mu gani zuwa anjima sai ku tafi naga jikin naka da sauk'i sosai, hala dai wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login