Showing 117001 words to 120000 words out of 171073 words

Chapter 40 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7866

lafiya Baby? Na d'auka ai so kike ki kashe shi tunda bakya k'aunar sa". Da sauri Ibteesam ta kalle ta cikin mamakin abinda tace, Anty Amina ta d'ora da cewa, "na tura ki sama nace ki tambaye shi zaki fita dake ban isa na fad'a miki kiyi ba sai kika dawo kika ce min kin tambaya ashe k'arya kike zuwa kikayi kika tayar masa da hankali sabida bakya son sa, kin sani ba baki sani ba yana da ciwon zuciya kuma kece abu mai girman da yake tayar masa da ciwon, tun rasuwar mahaifiyar sa ciwon zuciyar sa bai kuma tashi ba sai a kanki, na lura burin ki kawai ki ganshi a asibiti a kwance dan wannan shine na uku da kika saka shi jinya amma na yau yafi na kullum, shikenan Baby burin ki ya cika yana kwance a asibiti yanzu bai san inda kansa yake ba yana cikin doguwar suma wacce ba'a da tabbacin zai farfad'o, ga ciwon zuciya ga kuma ciwon kansa da ya tashi, hankalin ki ya kwanata yanzu ai tunda ki saka shi ciwo sai ki zuba ruwa a k'asa kisha Baby, shima mahaifin nasa a dalilin haka? gasho can a kwance ana k'ara masa ruwa" ta k'arasa fad'a cikin? fad'a tana kallon da hawaye ya wanke mata fuska.

Girgiza kai take tana fad'in, "wallahi Mama ba so nake ya mutu ba abinda yake yi miki ne bana so bana jin dad'i shiya......" da sauri ta katse ta da fad'in, "Amma mun riga mun gama wannan maganar dake tun ba yau ba ko? Ko kece kike zuwa kike ganin ana zuba min magani a abinci wanda zanci na mutu dole ki ji haushi na tunda zahiri kika gani, to haka shima Zaid d'in kaf duniya babu wanda yake ji dashi kamar mahaifin sa yasha gani na ina zuba magani a abincin mahaifin sa to shi ba d'a bane da bazai ji haushi na ba,? Ko shi bashi da zuciya? Ko kuwa ke kad'ai ce wacce kike son iyayen ki,? Na fad'a miki ko me yake yi da hujja yake yin sa baya d'aukar mataki sai ya tabbatar kawai matsalar sa rashin bincike, me mahaifin sa yayi min da zan kashe shi bayan zaman lafiyar da muke yi dashi? Alkhairan da mahaifin sa yake yiwa Hajiya ta ai ko karan gidan sa bazan bari a cutar ba balle shi da tilon d'an sa mafi soyuwa a gare shi, ya bawa mahaifiya ta gida da mota da kuma driver da zai kaita duk inda take so ya kuma biya shi, ya kaita umara ya kaita hajji bai tsaya iya nan ba ya kaita cairo an mata maganin ciwon k'afa to ni kuma dake nice butulu sai na saka masa da sharri,?".

"Tunda Zaid yasan ni mahaifiyar kice yayi sanyi na lura da hakan nayi mamakin hakan kuma amma daga baya na kula k'arfin son da yake miki ne yaja hakan, yana cikin tsaka mai wuya yana buk'atar wanda zai kula dashi yaja shi a jikin sa duk da mahaifin sa na k'okari amma ba kamar ke wacce yake mutuwar so ba, dangin mahaifin sa basa son sa ko kad'an burin su su kashe shi su kashe mahaifin sa suci gado kullum cikin cillo masa aikin asiri ake dame kike so yaji,? Damuwar ki kota dangin sa,? D'azu bayan tafiyar ki zubewa yayi a gaba na yana kuka kamar wanda aka yiwa gagamar rasuwa yake cewa nayi hak'uri na yafee masa sabida sonki, wallahi tunda nake da Zaid ban tab'a ganin yayi kuka ba sai a kanki amma da yake baki da tausayi kin kasa ganewa, lokacin da aka fad'a min Zaid mijin kine Allah kad'ai yasan irin farin cikin da nayi dan nasan kin samu miji wanda zai rik'e ki a ko wanne irin hali domin nasan halin sa yana girmama abinda yake so."

"Kar kiga mahaifin sa yana yi miki kawaici ki d'auka baya jin zafin abinda kike yiwa d'an sa, yana ji yafi kowa ji ma sabida shine kad'ai abinda ya mallaka a duniya a yanzu bayan shi bashi da wani, y'an uwan da yake tak'ama dasu ba son sa suke ba Zaid ne kad'ai ya rage masa, shima yanzu gashi can a kwance sabida jikin d'an sa kina tunanin bazai ga laifin ki akan yunk'urin kashe masa d'a ba,? Ko dan kinji yana cewa kinyi dai-dai ya saka ki sake yin wanda yafi wancan,? Sai ki cigaba in ya tashi sai a raba auren naku tunda ba son sa kike ba in so cuta ne hak'uri ma ai magani ne" Mama ta fad'a tana kawar da kanta daga kallon Ibteesam dan tayi bala'in b'ata mata rai, dan mutane da dama gani zasu dan Zaid baya shiri da itane take zuga Ibteesam itama.

Zuwa lokacin Ibteey kuka take kamar ranta zai fita hankalin ta yayi bala'in tashi cikin rawar murya tace, "Mama zanje na ganshi dan Allah." Hararar ta tayi tace, "kije ki ganshi ki k'arasa shi tunda bai mutu ba ko? To baza kije ba dan ko kinje ma baza ki ganshi ba yana ICU". Dafe k'irji tayi ta zaro ido tace, "Mama ICU?". D'aga kai tayi tace, "Eh ICU, d'akin da in mutun ya shiga da wuya ya fito da ransa ba nan, balle ma ko ba'a ICU yake ba baza kije ba Baby bazan so ace jini na ce take son kisan kai ba dan kawai kin????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ga yana sonki over."

"Dan Allah Mama......" saurin dakatar da ita tayi ta hanyar cewa, "kar kice min komai malama tashi ki bani waje kije ki fara tsara abinda zakiyi in ya mutu" Mama ta fad'a tana d'aga mata hannu.

Jikin sanyin jiki Ibteesam ta mik'e ta shiga d'akin ta ta fashewa da wani kuka mai tab'a zuciya.

Da kallo Anty Amina ta bita dan tasan tana son Zaid kawai jan aji ne irin na mata da kuma abinda yake yi mata d'in.

Ibteesam kuwa abin duniya ya taru yayi mata yawa kuka kawai babu kakkauwa sabida gani take kamar Zaid d'in ua mutu b'oye mata Maman nata tayi, sosai hankalin ta ya tashi zazza6i mai zafi ya rufe ta ga wani irin ciwon kai da take ji kamar kanta zai fad'i sabida kukan da tasha, kewa take ji a tare da ita kamar k'aton rami a zuciyar ta haka take cikin buk'atar abinda zai toshe mata wannan ramin, "Ina son shi, ina son shi wallahi bana so ya mutu ya barni" ta fad'a tana sake fashewa da kuka jikin ta har rawa yake yi mata.

_ko baza ki soni ba precious ki amince ki zauna dani nayi miki alqawarin zan baki dukkan abinda kike so zan kuma nisanci duk abinda bakya so,_ kalaman Zaid suka fad'o mata lokacin da ya rik'e hannun ta yana rok'on ta, kuka taji ya kuma kwace mata kamar waccee ta haukace haka take zubar da bedsheet da pillow tana kuka mai sauti, Mama da ta jiyo ta ta tawo d'akin tana shiga ta tawo a guje ta rungume ta tana fad'in, "Wallahi Mama ina son sa in ya mutu nima mutuwa zanyi, kiyi hak'uri ki barni naje na ganshi" ta fad'a cikin kuka.

Bayan ta take shafawa a hankali tana fad'in, "Shikenan is okay ki daina kuka kinji temperature ki tayi high, bazai mutu ba insha Allah zaku rayu tare" ta fad'a ciki sigar lallashi. Zaunar da ita tayi ta fita ta kawo mata magani ta bata tasha kafin tace, "ki bari gobe sai kije ki ganshi yanzu dare yayi ga kuma kema bakya jin dad'i, kuma ko kinje ma yanzu baza ki ganshi ba gwara kiyi hak'uri sai goben." Kuka take har lokacin tana fad'in, "Kiyi hak'uri Mama bazan sake ba ki yafe min". "Shikenan ai ya wuce, ki daina kuka kinga kanki na miki ciwo sosai" Anty Amina ta sake fad'a mata cikin kula.

Ajiyar zuciya kawai take saukewa ta kwanta akan gadon amma da ta kulle idon ta shi take hangowa a d'azu sai tayi saurin bud'e ido, ita kuwa Anty Amina tana sane ta hana ta zuwa dan tana so ta sake tabbatar da son da take masa dan duk wanda yake sonka yaji baka da lafiya kwanciyar hankalin sa yaje ya ganka wannan yanayin nata take so ta gani.



=?$?=?$?
*?ASAITAR SO!*

*66_67*

Not edited>?'?




Ko bayan fitar Anty Amina daga d'akin Ibteesam kasa baccin kirki tayi sai juyi take da ta rufe ido shi take hangowa a kwance cikin yanayi mara dad'i, ta k'agu gobe tayi kawai ta ganta a asibitin ji yake kamar ta jawo goben tazo kawai gashi daren yak'i yi mata sauri a haka bacci ya sace ta.

Koda tayi sallar asubayi taje suka gaisa Anty Amina kasa komawa bacci tayi tun lokacin ta shirya tana jiran gari yayi haske ta tafi, k'arfe bakwai na safe Anty Amina ta shigo d'akin kamae jira take ta zabura ta mik'e tana raba idanu, murmushi tayi tace, "Tawo mu tafi" abinda tace kenan suka fito, Ibteesam ta d'auki abincin breakfast suka fita suka shiga mota suka tafi. Gani yake kamar motar bata gudu dan ganin sunk'i zuwa asibitin duk da safiya ce babu mutane a titi amma gani take kamar drivern yana sane yak'i yayi gudu.

Shigar su asibitin Hameed ya fito fuskar sa duk ta tashi kana ganin sa kasan bai samu wani baccin kirki ba, "ina kwana Anty" ya fad'a tare da d'urkusawa har k'asa. "Lafiya lau Hameed, ya masu jikin?" Ta tambaya fuskar ta a sake. "Daddy dai yaji sauk'i Zaid d'in ne bamu sani ba Dr Auwal ne mai mana bayani sosai to kuma ba night duty yayi ba sai anjima zai shigo". Anty Amina tace, "To bara muje ciki" ta fad'a suna shigewa shi kuma yana fita.

A d'akin da Daddy yake suka shiga yana zaune a kan gado yana duba wayar sa suka shigo da sallama, amsawa yayi yana kallon su, "ina kwana Daddy?" Ibteesam ta d'urkusa har k'asa ta gaishe shi kanta a k'asa, sakin fuskar sa yayi yace, "Lafiya lau Daughter, da sassfiyar nan ta taso ki?". Murmushi kawai Ibteesam tayi tace, "Ya k'arfin jikin?". Ya amsa da fad'in, "Jiki Alhamdulillah na samu sauk'i." Ibteesam ta kuma cewa, "Allah ya k'ara lafiya" ya amsa da amin Anty Amina tace, "ya jikin?". "Alhamdulillah na samu sauk'i sosai ai" ya fad'a yana d'aukar wayar sa da yaji kira na shigowa, dubawa yayi ganin kiran bamai mahimmaci bane sai ya ajjiye wayar ba tare da ya amsa ba.

"Ya jikin Zaid d'in? Har yanzu basu ce komai ba?" Ta tambaya tana kallon sa, Daddy yace, "kin san dake Dr Auwal d'in baya nan shine zai mana bayani sosai to sai anjima zai shigo, har yanzu ban san ya jikin nasa yake ba tunda kinga ba ganin sa nayi ba". Ajiyar zuciya tayi tace, "To Allah yasa muji alkhairi". Ya amsa da amin d'akin yayi shiru babu mai magana.

Dr Auwal bai shigo ba sai k'arfe tara na safe a lokacin Daddy har Hameed ya kaishi gida ya dawo suka samu Dr ya shigo,suna gaisawa yace, "Bara naje naga yanayin jikin nasa". Zunbur Ibteesam ta mik'e tace, "Dr nima zanje dan Allah." Kallon ta Dr yayi yace, "muje" abinda yace kenan suka fita daga d'akin. Wata k'ofa ya bud'e suka yi tafiya kad'an suka k'arasa cikin unit d'in, tunda suka shiga d'akin ta hango shi a kwance sanb'al kamar gawa gaban ta fara fad'uwa hawaye suka ciko idon ta, oxgyen ce a mak'ale a hancin sa ga kuma ruwa da aka jona masa sai k'irjin sa ma a bud'e an manna abubuwan da suke taimakawa zuciyar wajan bugawa, sai kawai ta kama kuka Dr ya juyo da sauri cikin k'asa da murya yace, "Shiiiii ba'a son hayaniya a nan, dana san kuka zaki ai bazan tawo dake ba" ya fad'a yana fara duba yanayin Zaid d'in.

D'akin babu k'arar komai sai computer da take aikin ta ita kad'ai sai kuma a.c da take bada sanyi kad'an-kad'an, hannun sa wanda babu ruwa jiki ta rik'e ta zauna a gefen sa tana hawaye, kusa da kunnen sa ta matsa sosai? take furta, "kayi hak'uri ka tashi kar ka tafi ka barni dan Allah, ina sonka miji na ina k'aunar ka bazan rabu da kai" ta fad'a cikin muryar kuka. Kallon ta Dr yayi yaga alamun baza ta iya shiru ba yace, "Madam mu koma". D'ago jajayen idon ta tayi tace, "Dan Allah ka barni a wajan sa". Girgiza kai yayi yace, "kiyi hak'uri doka ce ba'a zama a wannan d'akin". Babu yadda ta iya haka dole ta taso tana waiwayen sa suka fito tana kuka.

Tana komawa d'akin ta fad'a jikin Anty Amina tana kuka sosai, "ki daina kuka Daughter addu'a zakiyi masa zai samu lafiya insha Allah" Daddy ya fad'a yana kallon ta.

Wayar Daddy ce tayi k'ara a lokacin ya duba ganin sunan wanda yake kiran ya saka shi ya d'auka tare da karawa a kunne, mik'ewa yayi cikin tashin hankali yana fad'in, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wanne asibitin ne?" Yayi shiru alamun yana sauraron abind ake fad'a masa, "to gani nan zuwa insha Allah" ya fad'a yana kashe wayar. Anty Amina das ta mik'e tsaye tace, "Lafiya dai ko?". Daddy yace, "ina fa lafiya, Yaya babba ne sukayi accident a hanyar su ta zuwa Katsina, ina Musa yazo ya kaini suna asibitin murtala" ya fad'a yana lalubo number Musa.

A tare suka had'a baki suna salati, yace, "ku zauna a nan bara naje na duba su" ya fad'a yana ficewa daga d'akin su kuma suka koma suka zauna.

Kasancewar lokacin y'an kasuwa sun fara fitowa ya saka suka tarar da traffic a hanya sai da suka jima sosai kafin su k'arasa asibitin murtala b'angaren A&E, a waje Daddy ya tarar dasu Bala ya kalle su yace, "Ya za'a kawo su wannan asibitin? Maza a d'auko su mu tafi al_ihsan". Yaya Bala yace, "ka shiga ciki kaga yanayin jikin nasu tukkuna" ya fad'a cikin sanyin murya kana ji kasan suna cikin hali mara dad'i.

Dole Daddy ya nemi alfarma suka shiga gabad'ayan su har inda suke, sun tarar da Yaya babba yana cikin hankalin sa amma Hajiya Batula ce take cikin mayuwacin hali dan gabad'aya bata cikin hankalin ta, Daddy yace, "Nifa ban aminta da nan ba gaskiya gwara mu koma al_ihsan d'in" ya fad'a yana kallon Bala, k'arasawa yayi wajan Yaya Babba yace, "Sannu Yaya". D'aga masa kai kawai yayi yana hakki sabida azabar ciwo.

Kallon Uncle Saifullahi yayi yace, "Ku samu ambulance a biya mu bar asibitin nan". Da to ya amsa ya fita aka yi ciku-ciku aka samu aka kwashe su aka bar asibitin, Al_ihsan d'in suka koma nan da nan aka kai su Emergency cikin gaggawa, Su Daddy suna tsaye a bakin Emergency waya yake so yayi wa Amina yace su zo unit d'in amma hankalin sa baya jikin sa ya kasa, sun samu kusan mintina talatin ganin har lokacin basu fito ba ya saka Daddy ya kira Antu Amina ya sanar da ita babu b'ata lokacin suka iso wajan ita da Ibteesam.

Basu jima da zuwa ba Dr ya fito yace, "Kaine Daddyn Zaid?". Daddy ya d'aga kai alamun eh kafin yace, "Lafiya dai ko?". Dr yace, "d'aya daga cikin marasa lafiyan nan ce take son magana da kai cikin gaggawa, bismillah" ya fad'a yana komawa ciki dole Daddy yabi bayan sa da gaggawa.

Tunda suka shiga ya k'arasa inda suke kwance ko wanne an d'aura masa ruwa, kusa da gadon Hajiya Batula suka k'arasa wacce hawaye yake zubowa a idon ta ga numfashin ta da yake d'aukewa k'irjin ta ba d'agawa, "ina Daddyn Zaid? Yana ina?" Ta fad'a muryar ta na wani irin shakewa. Daddy ya kalli Dr kafin yace, "Gani nan". Jin maganar sa ya saka ta ta runtse ido tana bud'e baki alamun tana so tayi magana amma maganar tak'i fitowa, dak'yar aka samu numfashin ta na fizga kamar wacce ake shirin kwace shi ta k'arfin tsiya daga gare ta tace, "Abubakar ka yafe min, ka yafe min" abinda take ta maimaitawa kenan cikin azabar ciwon da ita kad'ai tame jin mai take ji.

Daddy zaiyi magana ta katse shi da fad'in, "mun cutar da kai mun so muga bayan ka kai da d'an ka Allah bai bamu iko ba, wannan hatsarin da ya faru a kan hanyar mu ta zuwa......" numfashin shine ya sake yin sama ta sauke shi dak'yar kafin ta cigaba da cewa, " muna kan hanyar mu ta zuwa Katsina wajan wani malami mu karb'o maganin da zamu kashe Zaid da matar sa ta yanzu....." runtse ido tayi tana ji kamar ana dukan kanta da katuwar guduma ta cigaba da cewa, "maganin da Eman tasha ta mutu shi muka bata ta bawa matar Zaid d'in, tun ba'a je ko ina ba mun fara ganin sakayya tun a duniya, ka yafe min Abubakar" ta fad'a tana kallo sa jikin ta na rawa over, Daddy ya kalle ta yace, "Babu komai na yafe miki Allah ya yafe mana gabad'aya". "Ina Zaid? Shima ya yafe min" ta sake fad'a cikin yanayin ciwo. "Yana kwance bashi da lafiya amma shima zai yafe miki insha Allah" Daddy ya fad'a cikin tausayin hankalin da take ciki, murmushin k'arfin hali tayi tace, "Matar ka Amina tana son ka ka rik'e ta hannu biyu, ka rik'e ta, ka rikeeeee.." wani iri ja numfashin ta yayi lokaci d'aya jikin ta ya rikice, da sauri likitocin da suke tsaye suka k'araso wajan ta aka shiga bata taimakon da numfashin ta zai dawo dai-dai, duk irin k'okarin da akayi wajan ganin numfashin ta ya dawo dai-dai amma abin yaci tura k'arshe sai ya tsaya cak, Daddy yana tsaye yana kallon ikon Allah likitan yaja mayafi ya rufe mata fuska ya kalli Daddy yace, "Allah yayi mata rasuwa".

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ya fad'a yana kallon inda Yaya Babba yaje kwance da alama yaji abinda akace dan hawaye be yake zuha a idon sa, jikin Daddy ne ya k'ara yin sanyi ya fita daga d'akin ya kalli su Anty Amina yace, "Allah yayiwa Maman Eman rasuwa". Salati sukayi a tare a lokacin y'an uwan ta suka bayyana a wajan, cikin lokaci kad'an aka d'auki gawar Hajiya Batula aka fita da ita y'an uwan ta suka bi bayan gawar zuwa gida.

Hankali Daddy ba k'aramin tashi yayi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login