Showing 42001 words to 45000 words out of 171073 words

Chapter 15 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7849

mik'e tsaye ya kama k'ugu yace, "Kenan tana sane tayi amfani da turaren? To amma meye dalilin ta na hakan?."

_ka manta kai mijin tane,? Wata k'ila tayi haka dan neman kasancewa da kai,_ ai a fusace ya sakko k'asan duk da ciwon da yake ji bai hana sakkowa a a guje ba, had'uwa sukayi da ita tana niyar hawa saman bai mata magana ba sai marin da ya sauka a fuskar ta, wuyan ta ya damk'a ya d'aga ta sama a haka k'afar ta na wutsul-wutsul kamar wacce aka rataye tana k'okarin mutuwa, ganin yadda idon ta ya fito yayi ja bakin ta a bud'e tana neman hanyar numfashi ya saka ya cilla ta kan kujera, Daddy da Anty Amina da shigowar su kenan suka ga lokacin da ya cilla ta suka nufo wajan sa a guje suna fad'in, "Zaid meye haka?" Suka fad'a a tare suna k'arasowa wajan.

Har lokacin Eman bata dawo dai-dai ba tana zaune hannun ta rik'e da wuyan ta tana tari, "kashe ta kake so kayi Zaid?" Daddy ya fad'a yana kallan sa. "Daddy zan kashe ta in bata fad'a min dalilin ta na saka turaren da ya saka ni a rashin lafiya" ya fad'a yana niyar yin kanta a fusace.

"Kai wai meyasa baka aiki da hankali ne Zaid?" Anty Amina ta fad'a tana rik'e da Eman, "bazan yi d'in ba ina ruwan ki,? Duk ba bakin ku d'aya ba? Duk k'ulle-k'ullen naku ba tare kuke yi da ita ba? ya fad'a yana kallan ta da harara.

"Zaid ya ishe ka, kayiwa mutane shiru kar na sake jin bakin ka a wajan nan" Daddy ya fad'a?yana nuna shi da yatsa, hannu ya saka ya share plates d'in da suke kan dining a fusace suka tarwatse a k'asan tiles d'in, babu wanda bai dafe kunnen sa ba sabida yadda sautin fashewar su ya cika falon.

Kawai kallan sa suke ko wanne ya rasa me zaice masa, d'aga k'afa yayi da niyar fara tafiya Daddy yace, "Dawo ka zauna" ba musu ya dawo ya zauna, Daddy ya kalli Eman yace, "Amina kaita d'aki ta huta" kama ta tayi suka mik'e a take suka bar cikin falon.

"Zaid na tambaye ka mana" Daddy ya fad'a a tausashe yana kallan sa,"Ina jinka" ya fad'a kansa a k'asa, "meyasa baka iya sarrafa kanka a lokacin da ranka ya b'aci?". "Haka Allah yayi ni ne" ya bawa Daddy amsa har lokacin bai d'ago ba. "Kai ka mayar da kanka haka amma ba Allah ne yayi ka a haka ba" Daddy ya fad'a? yana kallan sa.

Shiru yayi bai amsa ba bai kuma d'ago ba dan shi kam bai san me zaice ba, "me ya had'a ku?". "Daddy yarinyar itace silar rashin lafiyar da nayi d'azu da har yanzu ban dawo dai-dai ba." Murmushi Daddy yayi yace, "Kana buk'atar matar kenan Zaid?". Sai a lokacin ya d'ago ya kalli Daddy irin kallon nan na? lallai ma, "wace matar tawa?" Ya tambaya yana d'aure fuska.

Murmushi Daddy yayi yace, "Ka san wacce nake nufi, dan d'azu Dr Auwal ya sanar damu ciwon mara kayi." "Daddy itace silar ciwon ai, na shiga kitchen na d'auko apple ina fitowa ta fad'o jiki na sai na shak'i khamshin wani turare a jikin ta daga nan na fara rashin lafiya, Daddy in bata fad'a min abinda tayi niyar yi min zan saka a sare mata hannu wallahi, fyad'e zata yi min ko me?" ya fad'a yana girgiza kai da k'wafa. Daddy da ya zuba masa ido baice komai ba har sai da ya kai k'arshen maganar sa sannan yayi murmushi jin yace wai fyad'e zatayi masa yace, "Ta ya akayi kasan turaren tane ya saka maka ciwon?." "Ban tab'a tsintar kaina a irin mood d'in ba sai d'azu, Daddy ka barni dan Allah na sab'a mata kamanni, in ban canja mata halittar fuskar ta ba bazan dawo dai-dai ba" ya fad'a yana niyar mik'ewa.

"Koma ka zauna Abdallah". Ba musu ya zauna yana cize leb'e, "ni ban amince da wannan hujjar taka ba Zaid,in ma hakan ne ai bata da laifi tunda matar kace tana da hakki a kanka tasan kuma baza ka sauke mata shi ta dad'in rai ba." Pillow d'in kujera ya d'auka ya cillar tare da fad'in, "Daddy meyasa yanzu baka so nane? Yanzu har fata kake min na had'a shinfid'a da waccan mahaukaciyar yarinyar da bata sona bata k'auna ta ita da iyayen ta,? Ko dan yanzu matar ka tana da ciki shiyasa ka daina sona tunda zaka samu wani d'an?" Ya tambaya cikin kin haushi yana kallon Daddyn nasa.

D'aure fuska Daddy yayi yace, "Na hana ka magana a akan y'an uwa na kak'i kaji ko? Yadda kake d'ana itama haka take y'a ta duka d'aya na d'auke ku ka gane ko?". "Wallahi da banbanci ko a wajan Allah, ni kaine mahaifi na kai ka haifan ita kuma fa,? Jini kuka had'a da mahaifin ta bama da ita ba" ya fad'a yana d'age kafad'ar sa. Daddy zuba masa ido kawai yayi yana kallan sa jin yadda yake magana direct daga zuciyar sa baya bari harshen sa ya sarrafa ta kafin ya furta, "naji, daga yau ko d'akin ka taje tace zata kwanta kar ka hana ta sabida matar kace in ta nemi wani abun kuma dole kayi mata."? Wani murmushi yayi mai kama da murmushin takaici ya kalli Dadyn nasa yace, "Abinda bazai tab'a yuwa ba kenan har a tashi duniya, ai na rantse da Allah k'afar ta na gani a inda nake sai na b'alla mata k'afa gwara ma kaja mata kunne ni ba sa'an yin ta bane, dajarar ka taci dan da tuni an fara lissafa ta a k'ananun zawarawan unguwar su." Daddy ya bud'e baki zaiyi magana yayi saurin dakatar dashi da fad'in, "Kar ka tilasta ni Daddy bazan iya ba wallahi."

Ajiyar zuciya Daddy yayi kana yace, "Na dai fad'a maka tana nan matsayin matar ka kuma dole ta tare da inda kake in lokacin hakan yayi". "Hmmm" kawai ya furta tare da kawar da kansa gefe, "ga maganin ka Dr Auwal ya kawo kana bacci" Daddy ya fad'a yana mik'a masa maganin, "No Daddy basai nasha ba daman ai ciwon k'irk'irar min shi akayi" ya fad'a yana tab'e baki.

"Antyn ka cikin jikin ta anyi test wata uku kenan" Daddy ya fad'a yana kallan sa, "yayi kyau" yana fad'ar hakan ya mik'e tsaye yana kalle-kalle da alama neman Eman yake yi, "Zaida kada ka yiwa yarinyar nan komai na fad'a maka, umarni nake baka" Dady ya fad'a yana nuna shi da hannu. D'aga k'afa kawai yayi zai fita Daddy yace, "Ina zaka?". Dan sosa kai yayi kana ya zuba hannu a aljihu yace, "Gidan su zani bazan iya bacci ba in ban ganta ba". "Ita wa kenan?". "Yarinyar da nace ina son ta mana". "Ohh Maryam zaka ce min ai". Da sauri ya juyo ya kalli Daddy yace, "Sunan Mama na gare ta daman,? No wonder nake son ta da yawa" ya fad'a yana d'an lumshe ido.

Girgiza kai Daddy yayi yana murmushi yana kallon sa tare da fad'in, "A daren nan zaka je gidan su Zaid,? K'arfe takwas da wani abun fa." "Ganin ta kawai zanyi na dawo" ya fad'a yana d'an yastine fuska, "kai da baka da lafiya taya zaka ita driving?". "Wizzy ne zai kaini" ya fad'a yana d'an dafe kansa. Had'e rai Dadd??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????y yayi yace, "bana son abotar ku da yaran nan Zaid duk wata dabi'a mara kyau a su suke koya maka."

Kallan Daddy yayi kafin yace, "Au ina da dabi'a mara kyau Dad?". "Of course" ya bashi amsa yana d'aga kai alamun eh, tab'e baki yayi yace, "ni komai nake yi akan dai-dai nake yin shi bana ganin wani abu da nake yi ba dai-dai ba, kuma ni basa koya min komai" ya fad'a yana fara tafiya, sai da yaje jikin k'ofar yace, "bye" daga haka ya bud'e k'ofar ya fita.

Da kallo Daddy ya bishi yana addu'ar Allah yasa had'uwar sa da Ibteesam ta zama silar gyaruwar halayyar sa.

A b'angaren Ibteesam kuwa tana zaune a falon Umma suna kallo wayar ta tayi k'ara? ta duba ganin suna? Khalid ya saka ta mik'e ta gyara zaman hijjabin jikin ta tace, "Umma yazo zanje na karb'o". "Me zaki karb'o ne wai?". "Umma na fad'a miki fa, wani littafi zai bani wanda zai taimaka min a b'angaren karatu na tunda kinga yanzu zaman gida muke".
"To ki daiyi sauri kar ki jima" da to ta amsa tayi saurin fita.

Gate d'in gidan ta bud'e ta fita dan tasan dare yayi bazai shigo ba, a jikin motar sa ta hango shi a gefen gidan su wajan da babu mutane sosai ba kuma shi da wadataccen haske amma kuma babu duhu a wajan, k'are masa kallo take dan sosai yayi mata kyau cikin farar jallabiya tasha guga har d'aukar ido take, murmushi tayi a hankali? ta fara takawa inda yake har lokacin fuskar ta da murmushi, "barka da dare" ta fad'a tana kallon k'asa.

"Barkan ki kyakykyawa ta, ina fatan daren yazo miki a yanayi mai dad'i" shima ya fad'a da murmushin a fuskar sa, "kamar kai" ta bashi amsa a tak'aice, "lallai kina cikin nishad'i tunda kamar ni ne, dan ni in ina tare da ke bana iya misalta farin cikin da nake ciki".


Murmushi tyi ta sake k'asa da kanta ganin yana jifan ta da kallon da yake kashe mata jikin ta, "kar na barki ki jima dare yana sake yi" ya Fad'a yana bud'e motar sa ya d'auko wani littafi mai tudu ya mik'o mata, ta kai hannu zata karb'a kawai taji an tankwab'ar da hannun ta littafin ya fad'i k'asa, d'ago kai tayi dan taga aikin waye wannan, gaban tane yayi mummunan fad'uwa? ganin Zaid ya murtuke fuska ya rife idon sa da bak'in glass wanda ya mashi fuskar tasa sosai, "ban miki warning akan kar na sake ganin ki da wani ba ko,? Bakya jin magana ne?" Ya fad'a yana kallan ta ta cikin glass d'in.

"Ina ruwan ka dan ka ganmu tare,? Wai kaine ka haife ta ne kome?" Khalid ya fad'a yana kallan sa ransa a b'ace, Zaid bai kalle shi ba kuma bai kula shi ba ya cigaba da fad'in, "kina ganin kamar abinda nace wasa ne ko,? Okay bara a nuna miki example yadda? nan gaba baza ki sake gangancin tsayawa da wani ba". Juyawa yayi ya kalli Wizzy yace, "ku bashi hukunci just for jan kunne" ya fad'a yana jan hannun Ibteesam suka matsa daga wajan.

Wizzy da Mugu kamar jira suke Mugu ya kaiwa Khalid wani naushi a baki take bakin sa da hancin sa ya fashi jiki ya fara b'ata masa farar jallabiyar sa.

Ihu Ibteesam tayi ta fincike hannun ta daga rik'on da yayi mata ta k'arasa inda suke tana fad'in, "dan Allah ku k'yale shi na yadda bazan sake kula shi ku barshi ya tafi dan Allah". Zaid ya k'araso wajan ya sake rik'e hannun ta a dai-dai lokacin da Mugu ya d'auko sabuwar wuk'a yana k'okarin lumawa Khalid a ciki.


*kar a fitar min da labari dan Allah...*

*?ASAITAR SO!*

*31_32*


K'arar da ta saki tare da d'ora hannu a kanta ta kulle idon ta ya saka Zaid ya kalli Mugu yace, "Ku k'yale shi, kuyi min gadin sa ina zuwa" daga haka yaja hannun ta zuwa cikin gidan su.

Suna shiga gate d'in gidan ta k'wace hannun ta ta kalle shi kamar zata yi magana sai kuma ta fasa ta zura a guje zuwa cikin gidan, inda tabi shima ya bita sai gasu sun shiga wata k'ofa da ta kaisu falon Umma direct ba tare da ka shiga ta babban falo ba.

Umma da ta ga shigowar ta a guje tana kuka ya bata tsoro ta Mik'e tana fadi fad'in, "Ke lafiya?". "Umma zasu kashe Khalid" abinda ta fad'a kenan tana cigaba da kuka. Umma zatayi magana Zaid ya shigo d'akin da sallama a bakin sa, "Umma banyi niyar saka ta kuka ba bata ji ne, nayi mata warning akan kar na sake ganin ta da wani amma bata ji, a? wannan daren me taje yi wajan wancan banzan yaron?" Ya fad'a a d'an fusace yana kallan Ibteesam lokacin da yake shigowa.

"To ina ruwan ka ko kwana nayi?wajan sa? Aure na kake yi da zaka takurawa rayuwa ta?" Ta fad'a cikin fad'a hawaye na bin idon ta, "shiiii bana son yawan magana da k'arfi" ya fad'a yana toshe kunnen sa da hannayen sa. A guje tayi d'aki tana kuka, ita ba kukan abinda yake mata take yi ba sai kukan wulaqanta mata masoyi da yake shine yafi komai bata haushi shiyasa take k'ara jin tsanar sa a ranta.

Zama yayi a kan kujera ya kalli Umma yace, "Umma ki sanar da mutanen gidan zan aiko da magabata na ayi maganar aure na da ita dan bazan zuba ido ina kallo tana kula wani ba" ya fad'a kansa tsaye yana kallan gefe daban, sai ya bawa Umma dariya tayi murmushi tace, "to amma naga baku dai-dai kanku da yarinyar ba." "Wannan ba matsala bane dole ta soni kuma dole ta aure ni, matuk'ar ina raye baza ta tab'a auren wani bayan ni ba." Umma tace, "To wannan maganar ai ta maza ce ba tawa ba".

"Wallahi Umma bazan aure shi ba dana aure shi gwara na mutu babu aure, ni bana son sa Khalid nake so kuma Khalid zan aura" ta fad'a tana fitowa daga d'aki, Ai sai kawai ganin sa tayi a gaban ta ya matse mata baki da k'arfin gaske ya zaro manya idon sa yace, "Dan nace ina son ki baki isa ki dinga fad'a min duk abinda yazo bakin ki bafa, son ki bazai hana na hukunta ki ba,baki isa ba wallahi indai ina da rai nine zan aure ki in kinga kin auri wani bani ba to ki k'addara bana numfashi a duniya" yana gama fad'ar hakan ya cika mata baki yana jifan ta da mugun kallo.

"haka ake soyayya a garin ku? Nace haka ake soyayya,? Ka tab'a jin inda akayi soyayya dole?". "Za'a fara daga kanki ko kina so ko bakya so sai kin soni, kuma na rantse miki da Allah kika sake na sake ganin ki da wancan yaron zan iya kashe shi na kashe ki nima na kashe kaina" ya fad'a yana nuna ta da yatsa tare da fita daga falon a fusace.

Zubewa tayi a wajan tana kuka sosai harda sheshshek'a, "Umma ya saka ana ta dukan Khalid a haka zanyi abinda Abba yace,? Wallahi Umma bazan iya ba shi komai bayayin na hankali komai cikin izzah da k'asaita yake yin shi, an fad'a masa izzah da k'asaita zata bashi duk abinda yake so a duniya ne?."

"Kiyi shiru ki daina kuka, abinda nake so dake bai wuce nace miki kibi shi a hankali ba ki lallab'a ku rabu lafiya tun kafin kema bai miki tabo a jikin ki ba, na lura bashi da hak'uri ko kad'an kiyi abinda Abban ku yace ki zauna lafiya". Bata amsawa Umma ba ta mik'e a guje ta fad'a d'aki tana kuka Umma ta bita da kallo tana tunanin ranar da Ibteesam ta san Zaid mijin tane.

Yana fita daga gidan ya kalli su Wizzy da har lokacin suke rik'e da Khalid baice musu komai ba kawai ya nufi mota ya shiga, kallan Khalid Wizzy yayi yace, "Ka ki yayi shiga gonar mai gida in ba haka ba zaka d'and'ana kud'ar ka wallah" daga haka suka sake shi suka nufi motar da sauri suka shiga suka bar unguwar da gudun gaske.

Abokin Khalid da yake cikin motar tsoro ya hana shi fitowa ganin sun tafi ya bud'e motar da gudu ya zagayo inda yake, "sannu Khalid" ya fad'a yana kallan bakin sa da har lokacin yake fitar da jini.

Mazaunin mai zaman banza ya bud'e ya shiga shi kuma Abdul ya bud'e wajan driver ya shiga suka fara tafiya, basu yi nisa sosai ba ya tsaya a wani katafaran pharmacy ya bud'e motar ya fita ya zagayo ya bud'e masa, fitowa yayi suka shiga cikin pharmacy d'in.

Nan da nan aka bashi k'ank'ara ya d'ora a kansa jinin ya tsaya aka goge jinin da ya bata masa fuska aka bashi magani suka fito, a motar Khalid ya sauke ajiyar zuciya yace, "Kaina na ciwo Abdul" ya fad'a yana d'ora hannun sa a kansa.

"Khalid ka rabu da yarinyar nan dan Allah, ka duba abinda gayen nan ya saka aka yi maka yanzu har da k'okarin kisa fa, yarinyar gold ce ko kuma tana daga cikin matan aljanna,? Na kuma fad'a maka tun ba yau ba yarinyar nan ba'a san asalin ta domin wanda kakewa kallon iyayen ta ba sune suka haife ta ba a gidan marayu suka d'auko ta, ka k'yale ta yaje ya k'arata dashi da ita." Khalid ya kalli Abdul yace, "Inda a dane ka bani wannan shawarar zan d'auka, amma a yanzu ka makara Abdul ina mata son da ban san adadin sa ba, ina jinta a jiki na yafi da tunanin ka, zancen a gidan marayu aka d'auko ta duk ba matsala bane ba ai su marayun ba y'ay'a bane,? Ko kuwa su ba haifar su akayi ba? Ta taso a gidan tarbiyya tana kuma da tarbiyyar in badan kai da shegen bin k'wafk'wafin ka ba waye yasan ba su suka haife ta ba,? Ina son ta bazan kuma gaji da zuwa inda take ba zan jure ko meye za'a min ta dalilin ta ka gane ko?".

"Shikenan ai sai kai tayi, amma ina so ka sani wallahi aka cigaba da haka sai na fad'awa su Ummi kasan kuma mutuk'ar taji labari babu kai babu yarinyar can" Abdul ya fad'a a fusace.

"Hmmm Abdul kenan" daga haka bai sake cewa komai ba ya mayar da hankalin sa kan titi, Abdul yayi k'wafa yana tuk'ar motar.

Zaid kuwa lokacin da ya koma gida a fusace ya shiga falon gidan dan sosai yake jin haushin kalaman Ibteesam a ransa, ko kallon mutanen falon baiyi ba ya haura sama a guje.

Anty Amina ta kalli Daddy tace, "Anya qalau yake kuwa? Kaje ka ji ko wani abun yana damun sa." Kamar da Eman take ta mik'e zunbur tace, "Bara naje naji". "A'a Eman dawo a yanayin nan da yake tsaf zai iya yi miki wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login