Showing 75001 words to 78000 words out of 171073 words

Chapter 26 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7837

wayar a kusa dashi yana amsa sallamar tata, waje ta samu ta zauna sannan tace, "Ina wuni". Murmushi yayi mai kyau kana yace, "Lafiya lau gimbiyyar mata, yasu Umma?". "Lafiya lau" ta bashi amsa tana wasa da yatsun hannun ta.

"Gani na kawo kaina ayi min hukuncin da ya kamata" ya fad'a yana kallon ta da murmushi, kallon sa tayi tace, "hukunci kuma?". "Eh mana, tun jiya rabon da ki d'auki waya ta, nayi message no reply shiyasa nazo kiyi min hukuncin da ya dace dani amma ban da wancan da bazan iya jurewa ba." D'auke idon ta tayi daga kansa tace, "Ni baka yi min komai ba, bana jin dad'i ne kawai." D'an murmushi yayi kafin yace, "abinda ya faru a asibiti ne jiya yake damun ki?". A fusace ta d'ago ta kalle shi cikin fad'a tace, "Akan me zai dame ni?". Da mamaki ya kalle ta ganin yadda ta juya fad'a lokaci d'aya yace, "Maida wuk'ar nima ai tambayar ki nayi." Sai kuma taji wani iri ta dan kawar da kai tare da jan tsaki kad'an bata san meyasa yanzu tuna Zaid yake hasala mata zuciya ba, gyara zama yayi ya fuskance ta yace, "Yanzu duk ba wannan ba, Ibteesam mun fahimci juna nida ke tun ba yau ba ina sonki kina sona, lokaci yayi da maganar aure zata shiga tsakanin mu Allah ya sani kuma bana so a d'auki lokaci". Fad'uwar gaban da bata san dalilin ta ba ta kawo mata ziyara a lokacin ta kalle shi tace, "Aure? Da wuri haka?" Ta fad'a muryar ta a sanyaye.

"To me zamu jira Ibteesam? Allah ya hore min babu abinda na nema na rasa iyali kawai ya rage ni dashi, kin ga kuwa gwara na cikashe ko?" Ya fad'a yana kallon ta, "eh haka ne, amma kaga ina level 300 ne a makaranta why not ka bari na kammala school d'in in yaso sai ayi maganar" ta fad'a cikin marairaicewa. Dariya yayi kad'an yace, "banda abinki Ibteesam wannan makaranta taku ba sai a kai sabuwar shekara ba'a koma ba, nayi miki alqawarin cigaba da makaranta ba iya matakin digree ba ko matakin phd ne baki da damuwa" ya fad'a yana d'an murmushi kad'an.

"To zanyi shawara a kan hakan" ta fad'a a sanyaye tana kallon sa, "shawara a kaina zakiyi ki a akan aure na?" Ya tambaya da mamaki yana kallon ta, "A'a babu d'aya". "Yauwa har naji dad'i a raina, zan sami Abba anjima zamuyi magana akan hakan". Da mamaki itama ta kalle shi tace, "wai da wuri haka?". "Eh mana, kin san ance da zafi-zafi ake dukan k'arfe, in na tsaya kallon ruwa kwad'o ne zai min k'afa".

Ajiyar zuciya kawai tayi bata ce komai ba, shima shirun yayi yana kallon ta yana mamakin canjawar ta lokaci d'aya haka, inda da ne ba haka zata zauna tayi shiru ba hira zasu dinga yi cikin raha da dariya har ya tafi, "Ibteesam" ya kira ta a hankali yana kallon ta. "Na'am" ta fad'a tana d'agowa ta kalle shi, "fatan dai komai lafiya?". "Me ka gani?". "Ganin ki nayi kamar an canja ki". "Hmmm babu komai na fad'a maka bana jin dad'i ne kawai" ta bashi amsa cikin k'osawa da maganar.

"To shikenan bara na tafi na k'yale ki ki huta, amma dan Allah kar a k'i d'aga min waya kinji" ya fad'a kamar zai mata kuka, kai kawai ta iya d'aga masa sukayi sallama ta shiga cikin gida shima ya fita.

Kusa da Umma ta nema ta zauna Umma tace, "Har ya tafi?". Tab'e baki tayi tace, "Ya tafi, ni duk ya ishe ni da magana wallahi" ta fad'a tana hararar gefe d'aya.

"Khalid d'in?" Umma ta tambaye ta da mamaki, "shifa, wai maganar aure yake wai baya so a d'auki lokaci, dan Allah Umma ki fad'awa Abba kar ya amince yace sai na gama makaranta ni wallahi gabad'aya ya fice min a kai" ta fad'a kamar zatayi kuka.

Umma ta gyara zama tace, "Ya fice miki a kai bakya son sa kenan?". Kallon Umman ta tayi kafin tace, "A'a ba haka bane, kawai ni yanzu komai baya min dad'i ne ban san dalilin hakan ba". Tab'e baki Umma tayi tace, "Allah ya kyauta, batun makaranta kuma babu ruwa na duk abinda Abban ki ya yanke shikenan".

Shiru Ibteesam d'in tayi bata amsa ba tana ji kamar tayi hauka sabida takaicin da ya dank'are mata a zuciya lokaci d'aya, Umma dai tana lura da ita sai dai tayi murmushi kawai ta share ta.

***********

Daddy duniya tayi masa zafi ko masallaci kasa fita yayi yana zaune a d'aki tana aikin tunani ko k'asa ya kasa sauka, a hankali take takowa zuwa cikin falon nasa da alama bai ji shigowar ta ba hakan ya saka har tazo kusa dashi bai sani ba, zube guiwowin ta duka biyun tayi a k'asa tace, "nasan ni me laifi ce a wajan ka amma ina so ka saurare ni koda baza ka fahimci abinda zan fad'a maka ba ina so ka ji ne dan kasan ban tab'a kwana da niyar cutar da kai ba" maganar ta ya dawo dashi daga tunanin da ya tafi ya kalle ta kawai baice komai ba dan in ya bud'e baki tabbas zai iya fad'ar abinda zai kai shi ga dana sani.

"Wallahi tallahi, na rantse da Allah wanda ya halicce ni ya halicci sama da k'asa ban tab'a yin abinda zai cutar da kai da Zaid ba, dalilin na baka kariya kai da d'an ka ya saka na amince da auren ka a lokacin baya, kayi hak'uri da abinda zan fad'a amma y'an uwan ka maza su uku basu da burin da ya wuce su kashe Zaid sannan su kashe ka kaima dan su gaji dukiyar? da Allah ya baka, dalilin da ya saka suka had'a aure na da naka kenan dan basu b'oye min ba tun farko sun fad'a min manufar auren kasancewar ni kawar Batula ce, da suka same ni da magana na fad'awa Hajiya ta da farko nak'i amincewa Hajiya ta ta dinga bani baki tana fad'a min taimakon da zan maka kai da Zaid ya saka na amince da batun."

Ajiyar zuciya tayi ta cigaba da fad'in, "Lokacin da na shigo gidan nan matsayin matar ka hutun sati d'aya suka bani kafin a fara aiko min da maganganu ana cewa na zuba maka kai da Zaid kuci, lokacin Zaid ya bar k'asar sai aka dakata domin shi ake son fara kashewa ba kai, a cewar su in ka fara mutuwa ka bar Zaid a duniya an bar baya da k'ura,bayan dawowar sai aka samu akasi ranar yazo ya same ni ina zuba masa abu a abinci bai tsaya ya kula da kyau ba da zai gane abinda nake zubawa tun daga lokacin ya tsane ni baya cin komai nawa, ina zuba magani ba bana zubawa ba amma maganin tsari nake zuba muku kai da Zaid kasan mahaifi na malami ne sosai kafin rasuwar sa ya barwa Hajiya magungunan tsari wanda akaa samo su daga alkur'ani da hadisan Annabi Muhammad S.A.W, ni kuma sai takee bani nake musanyawa da wanda suka bani, dan da farko basu amince dani ba sai suka turo d'an leken asiri a matsayin ma'aikacin gidan nan da zan dinga zuba maganin a gaban sa to yaje ya sanaar dasu ai ina zubawa sai suka amince dani."

"Wannan dalilin shine ya saka aka shigo da Eman gidan nan dan a samu nasarar kashe Zaid sai akayi sa'a asirin da aka dinga aikowa Zaid kafin ta shigo bai kama shi ba wannan ya dak'ile musu aiki da dama, dan ka sani na sani Eman bata ishe kallo ba balle har ya bata wani matsayi, na tsallake maka labarin farko wanda ya kamata na fara baka, matar ka Maryam sune silar mutuwar ta shiyasa lokacin rasuwar ta aka rasa abinda yake damun ta har ta bar duniya ba'a sani ba, an kashe ta sabida son da kake mata ana ganin zaka mallaka mata abubuwa da dama wanda su ya kamata su gada a fad'ar su."

"Dalilin da ya saka ni zubawa Zaid poison na zuba ne sabida su sakee amincewa dani dan bana so su kawo wata hanya da zata saka su cire ni daga cikin su dan gudun samun nasarar cutar da kai, an bani abu cikin cokali d'aya akace na zuba duka yasha zai mutu sai na dib'i d'an tsaya d'aya na zuba a lokacin da ka umarceni da na kawo masa ruwa da wannan damar nayi amfani, wannan aiki da nayi musu duk da ba haka suka so ba ya saka su sake amincewa dani d'ari bisa d'ari, nayi kuka da naga halin da Zaid ya shiga tsoro na Allah yasa kar ya mutu na zama silar mutuwar sa."

Shiru tayi tare da d'auko wayar ta ta kira layin mahaifiyar ta akayi sa'a ta d'auka da sallama, "Hajiya Daddyn Zaid yana zargi na akan zubawa Zaid guba, Hajiya ransa ya b'aci sosai yak'i tsayawa ya saurare ni" ta fad'a hawaye na zuba a idon ta. Daga can b'angaren wacce aka kira da Hajiya tace, "Amina hak'uri zakiyi ki daina kuka jahadi kike babba wanda Allah zai baki lada mai tsoka, ki daure kiyi masa bayani yadda zai gane kar ya dinga zargin ki da yunkurin kashe masa d'a, ki san dabarar da zakiyi kar ki saka sunan y'an uwan sa a ciki dan kar ya dinga ganin ki da abun dan komai lalacewar d'an uwa d'an uwa ne, kar ki sare Amina ki cigaba da k'okari Allah yana tare dake zai kuma taimaka miki akan taimakon bayin sa marayu da kike yi, sannan batun cikin nan kin fad'a masa gaskiya kuwa? In ya gano da kansa ransa zai b'aci sosai dan ya saka rai akan abinda ya jima da cirewa. "

Kuka take sosai kamar k'aramar yarinya tace, "Ban fad'a masa ba Hajiya amma zan gaya masa, ina jin tsoron hukuncin da zai yanke a kaina bana so ya dinga min kallon macuciya shiyasa tun farko banso karb'ar aikin nan ba kece kika tilasta min."

"Amina kiyi masa bayani koda bazai fahimce ki ba ki kuma gaggawar sanar dashi dalilin ki nacewa kina da ciki, ki jure Amina kome d'an sa zai miki ki daure dan Allah ina so ki samu lada ne Amina bana so a cutar dasu ne akan abinda za'a mutu a bar shi a duniya, in kuma bai fahimce ki ki k'yale shi kar ki tilasta masa kinji ko?". Kamar tana gaban ta take d'aga kai tace, "To Hajiya insha Allah" bata jira mai zata sake cewa ba ta yanke wayar ba tare da ta kalle shi ba ta cigaba da fad'in,

"Nace maka ina da ciki ne sabida abubuwan da ake aikowa da Zaid yayi yawa yana neman yafi k'arfi na sai nayi dabarar nace ina da cikii yadda hankalin su zai bar kan Zaid ya dawo kan abinda yake ciki na dan nasan baza su tab'a barin sa,? hakan ce ta kasance kuwa dan sun gane dan ina sane nake fad'a a gaban Eman sai basu nuna min ba sai suke min aikin a b'oye suna farautar cikin hankalin su ya bar kan Zaid, banda wannan da ya faru sun bar kan Zaid sun dawo kan cikin jiki na, bance ka yadda da abinda na fad'a maka ba amma Allah ya san meye a zuciya ta wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Abinda nake fad'a maka gaskiya ne, baza ka saka ni kaffara ba dan bazan rantse akan abinda yake k'arya ba, y'an uwan ka suna farautar rayuwar Zaid da taka ni kuma ina k'okarin wajan ganin hakan bai faru ba, kasan dai bazan had'a baki da mahaifiya ta muyi maka k'arya ba kasan wacece Hajiya, haka kasan baza ta yi maka k'arya ba, amma bance ka yadda ba kayi amfani da abinda zuciyar ka take fad'a maka" ta k'arasa fad'a tana share hawayen ta tare da mik'ewa.

Daddy da ya daskare a wajan ya kasa furta koda kalma d'aya ya zuba mata ido kawai, kwakwalwar sa ta cure waje d'aya ya rasa wanne kalar tunani ma zaiyi, shin abinda ta fad'a zai amince dashi? Ko kuma akasin sa,? Ya rasa me zai tuna a lokacin idon sa har lumshewa yake sabida yadda kansa yake bugawa da sauri-sauri.

Ganin ya kasa magana sai kallon ta da yake yi ya saka tayi murmushi tace, "Nasan daman baza ka amince dani ba kamar yadda d'an ka yak'i amincewa dani, ban hana ka yadda da abinda zuciyar ka take fad'a maka ba amma ina so ka sani da ina son kashe Zaid da nayi amfani da kai na bashi guba ya mutu, dan nasan ka amince dani kome na baka nace ka bawa Zaid ba tare da yasan nice na bashi ba zaka bashi, ko a haka yaci ace ka fahimci wacece ni, wallahi ni ba muguwa bace ban tab'a cutar wani ba bazan kuma fara a kan Zaid ba" tana fad'ar hakan ta fice daga falon ta sauka k'asa da gudu ya bita da kallo zuciyar sa a cunkushe ya rasa wanne kalar tunani ma zaiyi.



_anya maganar Amina gaskiya ce kuwa fans?_>??

*?ASAITAR SO!*

*47_48*

Not edited>??



Ajiyar Zuciya yayi tare da lumshe ido kalaman ta suna yi masa amsa kuwa a kunne, wayar sa ya d'auka ya kunna karatun alkur'ani yana saurara yana bi kad'an-kad'an.

*

Bayan sallar i'sha Umma suna tare da Abba tace, "Nikam me ka yanke a kan batun yaron nan Khalid ne?". Ajjiye bowl d'in fruit d'in da yake hannun sa yayi yace, "Kin tuna min, yazo ya same ni fa yana so zai turo magabatan sa ayi maganar auren sa da Ibteesam". Rik'e baki Umma tayi kafin tace, "to me kace masa?". "Nace masa ya bani lokaci zanyi tunani a kai". D'an gyara zama tayi tace, "Nikam sai nake ganin ka fad'a masa gaskiyar magana zata fi kar mu zama k'ananun mutane in aka dinga masa yawo da hankali."

"Nayi tunanin hakan nima Halisa, amma bana so na yanke hukunci ne ba tare da nasan abinda yake zuciyar Ibteesam, bana so na k'ware ta gaskiya" ya fad'a yana fuskantar Umma cikin nustuwa. "Ban shiga zuciyar Ibteesam ba amma uwa nake a wajan ta na fahimci yanzu babu Khalid a ranta, hasalima yanzu Zaid ne a zuciyar ta amma ta kasa tantance hakan." Girgiza kai Abba yayi kafin yace, "Ai in hakan ta kasance zanfi kowa farin ciki, amma baza muyi amfani da hasashe ba gaskiya, na fiso ta fito ta fad'i abinda yake ranta in tana so falillahil hamdu zanje na samu mahafin Zaid a warware auren ba tare da tashin hankali ba, in kuma bata son Khalid d'in shikenan sai a k'yale ta."

Cikin gamsuwa Umma tace, "eh hakan yayi, Allah ya zab'a abinda yafi alkhairi".? Shigo d'akin da akayi kai tsaye babu sallama ya saka suka d'aga ido dukkanin su suna kallon wanda ya shigo, "Zubaida! Lafiyar ki zaki shigowa mutane d'aki babu sallama?" Abba ya fad'a yana kallon Mama. Kama k'ugu tayi kamar k'aramar yarinya tace, "Eh daman zuwa nayi na fad'a maka a warware auren da yake kan Ibteesam da d'an ambassador a dawo dashi kan Asiya, domin tunda ta ga yaron take son sa so mai tarin yawa ma kuwa, na daina zuba ido komai ace Ibteesam, Ibteesam, bayan ga y'an gida ba, ko a warware auren ko kuma itama a aura masa ita" ta fad'a tana karkad'a jiki kamar yarinya.

Umma ta kalli Abba shima ya kalle ta kafin ya mayar da hankalin sa kanta yace, "Ni kika tsaya a gaba na kina fad'a min wannan maganar Zubaida,? Har yanzu baki san kin girma ba ko?". "Eh ban sani d'in ba a kan burin Asiya wallahi babu abinda bazan yi ba, dole asan abinda za'ayi domin baza'a fifita bare a kan y'ar gida ba, ai kowa yana so nasa yaji dad'in duniya" ta fad'a a fusace tana aikawa da Umma harara.

Kallon ta kawai Abba yake cikin mamakin halayyar ta yace, "An fifita bare a kan y'ar gidan akwai abinda zakiyi ne?" Ya fad'a ran sa a b'ace yana hararar ta.

"Ai wallahi ba'a isa ba babu ta yadda za'ayi bare wacce ba'a san asalin ta ba tazo tafi y'ar gida y'ar tushe y'ar asali ba, dole duniya tasan ba kune kuka haifi Ibteesam ba, yanzu ne lokacin da ya kamata ta sani ita kanta, ta san cewa ba'a san asalin ta ba daga gidan marayu aka d'auko ta" ta fad'a cikin hargagi.

Abba ya bud'e baki zaiyi magana ya tsinci Ibteesam a tsaye a bayan Mama tashin hankali ya bayyana k'arara a kan fuskar ta sai zare ido take hakan ya tabbatarwa da Abba taji kalaman Mama na k'arshe, "Ibteesam me ya kawo ki d'akin nan yanzu?" Abba ya tambaye ta cikin fad'a yana kallon ta. Wayar hannun ta ta nuna cikin sanyin murya tace, "Dada ce take ta waya ina jin abu ne na gaggawa shiyasa na tawo na kawo mata" ta k'arasa fad'a tana ajjiye wayar a kan kujera, juyawa tayi da nufin komawa kowa ya zuba mata ido sai ta tsaya cak ta juyo ta kalli Abba tace, "Abba da gaske ne a gidan marayu kuka d'auko ni,? Da gaske ni ba jinin ku bace?" Ta tambaya idon ta na kan iyayen nata.

Umma ta bud'e baki zatayi magana tayi saurin tarar numfashin da fad'in, "Dan Allah kar ku fad'a min abinda kun fad'a ne kawai dan naji dad'i, gaskiya nake son sani Umma". Umma ta kalli Abba shima ya kalle ta ya dawo da kallon sa ga Mama da itama jikin ta yayi sanyi dan bata zata Ibteesam zata zo d'akin a lokacin ba, "Ibteesam zo ki zauna" Abba ya fad'a yana rik'o hannun ta ya zaunar da ita akan kujera, fridge ya nufa ya d'auko ruwa mai sanyi ya mik'a mata.

Hannun na rawa ta karb'a ta kafa kai tasha sosai kafin ta sauke ta kalli iyayen nata da suma ita suke kallo, "Haka ne abinda kika ji Ibteesam ba mune muka haife ki ba" Abba ya fad'a bayan ya zauna kusa da ita muryar sa a sanyayee.

Sai a lokacin ta samu damar da ruwa ya taru a idon ta har ya fara zubowa, wani abu mai nauyin gaske ya tsaya mata a k'irji kanta yayi nauyi kamar an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login