Showing 96001 words to 99000 words out of 171073 words

Chapter 33 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7865

Ji nake kamar ana tsaga zuciya ta Daddy ban san ya zanyi ba" ya k'arasa fad'a yana dafe kansa da hannayen sa duka biyun idon sa yayi ja sosai kamar wanda yayi kuka ya k'oshi.

Kallon Anty Amina Daddy yayi da take kallon Zaid cikin tausayi, tunda take bata tab'a ganin sa cikin rauni da karayar zuciya kamar na yau ba, lallai ta amince son da yake yiwa Ibteesam ba na wasa bane ba,? mayar da kallon sa yayi ga Zaid d'in yace, "Zaid hak'uri zakayi ka dinga rarrashin zuciyar ka kana addu'a sai kaga komai ya wuce, insha Allah Ibteesam zata soka kamar yadda kake son ta ka daina damuwa kaji ko?". Wani irin murmushi yayi mai bayyanar da zallar takaicin sa yace, "Nayi hak'uri ko Daddy? Na rarrashi zuciya ta bayan ni na rasa wanda zai rarrashe ni, shikenan" yana fad'ar hakan ya mik'e ya hau sama da gudun gaske.

Daddy da ya bishi da kallo zuciyar sa tayi bala'in karaya ji yake kamar ya zubarwa da gudan jinin nasa kuka ya kalli Anty Amina yace, "ki duba yadda power of love ya mayar da Zaid Amina, Zaid ne yau yake magana cikin rauni sabida wata d'iya mace a duniya
har hawaye na taruwa a idon sa, ina yi masa fatan Ibteesam ta so shi koda na rana d'aya ne" Daddy ya fad'a shima cikin sanyin murya.

Ita kanta Anty Aminan yayi bala'in bata tausayi sai tace, "Ibteesam na son shi wallahi, a iya kwana biyun nan na fahimci akwai soyayyar sa a tare da ita bata sani bane kuma tana yin wani abun ne sabida dalili na, laifi nane wallahi da ban saka ta tambaye shi zuwa Gomben nan ba da duk hakan bata faru ba, ka duba yanayin da yake ciki kuma yana da ciwon zuciya" ta fad'a kamar tayi kuka tana kallon Daddy.

"Babu abinda zai faru insha Allah, abinda Ibteesam take masa kuma shine dai-dai ni tun farko hakan naso daman, yana nuna mata tak'ama akan dole ta soshi ta zauna dashi ita kuma gashi ta nuna masa duk da auren sa a kansa bazai mata lallai a kan son sa, kuma ita y'a ta gari ce mai kare martabar iyayen ta yanzu ya kamata ya san mahimmacin ki tunda kin haifa ya aura kuma mutuwar so." Ajiyar zuciya tayi tace, "Duk da hakan dai ta sassauta masa tausayi yake bani matuk'a" ta sake fad'a tana kallon saman sa.

Wayar da aka yiwa Daddy ya katse musu zancen da sukeyi Anty Amina ta Mike ta wuce falon ta.

Eman da take sauraron komai tayi kwafa tace, "Hmmm sai dai ka zauna da gawa kuwa dan da ta dawo zan aiwatar da abinsa yake gaba na, babu yarinyar da zata zauna da Zaid matsayin mata sai ni" ta fad'a tana shigewa d'akin ta.

*Gombe State*
*Federal low cost.*

Tunda suka shiga cikin gidan Ibteesam take kallon girman gidan dan sosai yana da girma ga kyau gashi part part ne alamu ya nuna da mutane da yawa a gidan, b'angaren Hajiya aka shiga tana ganin su ta mik'e tana fad'in, "Maraban ku mutanen Kano, lallai sun sha hanya". Zama sukayi kafin a fara gaisawa, "Zo nan Maryam dan kowa ya ganki yaga fuskar Khabir" Hajiya ta fad'a tana kallon Ibteesam da take kallon ta itama.

K'arasawa wajan ta tayi kafin Hajiya tace, "Tabarakallah masha Allah, barka da dawowa cikin dangin ki Maryam, yanzu ku shiga ku huta ku ci abinci in yaso sai a kira kowa yazo yaga y'ar uwar sa" ta fad'a cikin hausar ta da ba sosai take fita ba kana jin maganar ta kaji ta fulani.? Ita dai Ibteesam murmushi kawai take aka kaisu masauki Ibteesam ta fad'a wanka.

Tana fitowa tayi sallah ta kwanta dan sosai take a gajiye, bata farka ba sai magariba ta tashi tayi sallah ta shirya ta fito babban falon, tana shigowa kowa ya zuba mata ido itama kallon kowa take dan ganin kyawawan matasa maza da mata dake zaune an zagaye Hajiya,? "Shikenan ga Maryam d'in ma ta fito" Hajiya ta fad'a tana mik'a mata hannu alamun tazo inda take. K'arasawa tayi ta zauna kafin tace, "Sannun ku". Duka suka had'a baki wajan fad'in, "yauwa sannun ki Ibteesam" suka fad'a suna kallon ta da murmushi.

"Yanzu dai ki fara cin abinci dan kowa yaci nasa ke ce baki ci ba" wani babban mutum ya fad'a da alama shima d'an Hajiya ne, kafin kace kwabo an cika mata gaban ta da abinci kala-kala, ita kam rasa me zata ci tayi cikin sanyin murya da shagwa6a tace, "Wannan duka ni kad'ai?"" Ta fad'a tana kallon Mummy. Dariya sukayi gabad'ayan su kafin wani kyakykyawa kana ganin sa kaga fulani ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna yace, "bayan abincin kuma nine zan baki abincin da kaina dan bama so ki wahala, ko ba haka bane?" Ya fad'a cikin muryar sa mai dad'i yana kallon y'an uwan nasa.

"Haka ne kuwa babban yaya" suka amsa a tare suna kallon sa. Dariya Ibteesam tayi cikin nishad'in kasancewa da y'an uwan nata tace, "ni na k'oshi furar dai kawai zan sha" ta fad'a tana d'aukar furar ta fara sha, hira suke cikin jin dad'i har ta ajjiye tace, "na k'oshi". Hajiya tace, "kin tabbatar kin k'oshi?".? "Eh Hajiya na k'oshi sosai ma" ta fad'a cikin Jin dad'in yadda suke nuna mata kula.

Hajiya tace, "to masha Allah, yanzu bara a fara gabatar miki da kowa na nan, kin ganni suna na Fatima sunana Zahra'u taci, wannan shine babba a cikin yara na sai...." saurin katse ta wata budurwa tayi ta hanyar fad'in, "Hajiya kaka ai ke yanzu kunya baza ta barki kiyi bayani yadda ya kamata ba, kinga Ibteesam Hajiya kaka yaran ta hud'u duka maza bata haifi mace ba, Daddy shine babba, sai Abban Abuja sannan Abie sai Abba k'arami, ga Daddy nan yana da yara biyar, Anty Hafsa itace babba tana aure a nan gari sai wannan da ya zauna a kusa dake sunan sa Umar sunan mijin Kaka ne dashi ana ce masa Hamma Amir, sai Hamma Sagir shima gashi a zaune sannan ni Fatima sunan Kaka kenan ana cemin Ummi sai autan mu Khalil, Abban Abuja kuma akwai Hamma Khalipha yana Madina yana karatu, sai ke sannan Zahra ga Sulta da Sultana, Abie ma gashi a zaune, Anty Khadija itace babba tayi aure a Kaduna, sai Hamma Umar again gashi nan a zaune shi kuma ana ce masa Faruk sai auta Mufida, Abba k'arami kuma daga Amina sai Aisha sai k'aramin cikin su Al'ameen, kinji iyalan kaka gasu nan kuma a zaune wanda suke gidan miji ne babu sai kuma Hamma Khalipha" ta k'arasa fad'a da murmushi a fuskar ta.

"Ohh ni Faty wannan bayani da kika shinfid'a haka Fatima? Bakya gajiya da surutu?" Hajiya kaka ta fad'a tana rik'e hab'a tana kallon Fatima, dariya dukkanin su sukayi kafin Hajiya kaka ta rankwashi kan Amir tace, "kin ganshi nan shine babba amma har yanzu yak'i aure har mun fara kad'a masa gangar gauro ga Sagir nan zai auri Zahra k'anwar ki ya bar shi, mai gida na biyu ma zai auri Fatima sarkin surutu amma shi an barshi a baya."

Amir ya d'ago ya kalli Hajiya yace, "Kar ki damu Hajiya kaka nima na kusa very soon zaki ga wacce zan aura zata baki mamaki". "Tafi can haka dai kake fad'a kullum, yanzu sai a kai Maryam b'angaren iyayen nata ta gaisa da kowa, Fatima, Zahra'u, Amina, Aisha ku tashi ku raka ta ko ina a gaisa kafin gobe kuma kuje gidan Hafsa". Da to suka amsa suka mik'e a tare har mazan suka fito ana tafe ana hira har suka gama zaga gidan cikin raya da wasa suka dawo b'angaren Hajiya.

Ranar ansha hira matuk'a Ibteesam taji dad'in kasancewa cikin y'an uwan ta, sai a lokacin taga kanen ta Sultan da Sultana da suke matuk'ar kama da ita wand'anda basu wuce shekara goma zuwa sha d'aya ba, bata samu kanta ba sai k'arfe sha d'aya na dare sannan mazan suka tashi kowa ya nemi makwancin sa, sai a lokacin ta d'auki wayar ta ta kira Anty Amina har ta katse bata d'auka ba, ta kira Umma nan ma bata d'auka ba dak'yar ta samu Jidda suka tab'a hira kafin ta yanke wayar, missed call d'in Zaid ta gani kira har sau biyu ta zubawa number ido dan batayi saving ba amma kuma ta gane number sa, ajiyar zuciya tayi tana tunani ta kira ko ta k'yale shi? Cillar da wayar tayi kawai ta share ta kwanta cikin kewar y'an uwan ta.

Washe gari haka suka had'u dukkan su aka karya ana yi ana nishad'i mazan babu wanda ya fita a cikin su hira kawai suke yi, gab da azahar suka shirya aka d'auki mota aka tafi yawon zaga garin Gombe da Ibteesam, gidan Yaya Hafsa aka fara zuwa a nan akayi sallar la'asar aka ci aka k'oshi sannan aka shiga gari, sosai Ibteesam ta sake a cikin su ta manta da damuwar Zaid ta saki jiki ana hira da dariya.

Basu suka dawo gida ba sai dare sunci sun k'oshi a babban gidan abincin dake garin sunyi sallah suna dawowa kowa ya shiga d'aki dan ya huta, d'akin Mummy Ibteesam ta shiga tana fad'in, "Mummy kin gan mu sai yanzu ko? Munsha yawo, ashe haka Gombe take dakyau?" Ta fad'a tana zama kusa da Mummy tana dariya, Mummy ta kalle ta da murmushi tace, "Ai naga alamun hakan gashi nan sai walwala kike, kin kira Maman ki?". "Eh yanzu muka gama waya har da Umma ma" ta bata amsa tana kallon ta.

"Mijin ki fa?" Mummy ta jefo mata tambayar tana kallon yanayin ta, gaban ta ya Fad'i ta d'ago kai ta kalli Mummy ta girgiza kai alamun a'a, "meyasa haka Baby? Har yanzu baki yanke hukunci a kan sa ba?" Mummy ta sake tambayar ta. Tace, "eh Mummy" ta bata amsa kai tsaye, Mumny tace, "Sai yaushe kenan?". Shiru tayi bata amsa ba sai sunkuyar da kai da tayi Mummy ta sake cewa, "Shikenan jeki ki kwanta kar ki takura kanki akan abinda kika san zuciyar ki bata so, amma ki kira shi ko gaisawa kuyi bashi da lafiya sosai banda Daddyn sama yayi da gaske da tuni ya tawo nan dan ya damu kansa a kan rashin ki" Mummy ta k'arasa fad'a cikin rauni tana kallon ta.

Da toh kawai Ibteesam ta amsa ga mik'e ta fita daga d'akin, maimakon ta shiga d'akin da yake nasu sai ta fita daga babban falon ta koma can baya inda babu hayaniya, wayar ta ta d'auko tana tunanin ta kira shi ko kawai ta share shi? Kira ne ya shigo wayar tata ta duba abin mamaki number Zaid d'in ce ta d'auka cikin sanyin murya tayi sallama, bai amsa ba sai shiru da taji yayi yana sauke ajiyar zuciya, kusan mintina biyar suna a haka kafin yayi k'arfin halin cewa, "Precious". Har cikin zuciyar ta taji yadda ya kira ta amma sai tace, "Ya jikin?". Yace, "Jiki babu sauk'i Precious, ina jin kafin ki dawo zaki samu labarin mutuwa ta" ya fad'a muryar sa har rawa take yi.

Bata amsa masa ba tayi shiru tana sauraron yadda yake sauke numfashi kana ji kasan bashi da lafiya, "Yaushe zaki dawo?" Ya tambaya. "Sai nan da kwana biyar". "Yanzu zaki iya kwana biyar ba tare da kin ganni ba Precious?" Ya fad'a cikin tashin hankali yana jiran abinda zata ce. "Eh zan iya mana" ta bashi amsa kai tsaye ba tare da tsoron abinda hakan zai haifar ba, shiru yayi alamun amsar ta ratsa shi baice komai ba, "Baby na!" Taji an fad'a daga bayan ta tayi saurin juyowa dan ta d'auki muryar wanda ya kira ta, kamar yadda ta zata Amir d'in ne a tsaye yana kallon ta, daga can b'angaren Zaid yace, "Waye yake kiran ki da babyn sa?".? Bata kai ga bashi amsa ba yace, "Damn it! Ibteesam wani namiji yana kiran ki babyn sa" Kit taji ya kashe wayar tabi wayar da kallo kafin ta kalli Amir da yake kallon ta.

"Da wa kike waya haka?" Ya fad'a yana k'arasowa inda take, "Yaya na Kano, kasan ni akwai yayu da yawa" Ta fad'a tana kallon sa, murmushi yayi yace, "Haka ne kuwa, ya kamata kije ki kwanta dare yayi fa". Da to ta amsa tayi masa sai da safe ta bar wajan da sauri.

*Kano*

Tunda ya yanke kiran ya dafe k'irji yana jin wani irin azaba da radad'i a cikin k'irjin sa, wani irin numfashi ya fara sama-sama kamar wanda numfashin sa yake niyar fita daga gangar jikin sa, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Zaid lafiya?" Hameed da ya shigo lokacin ya fad'a yana k'arasowa cikin d'akin nasa a guje.

Komawa yayi yana kiran, "Daddy! Daddy!!". Daddy da yake zaune a falo yaji kiran da Hameed yake masa ai da sauri suka yawo saman shida Anty Amina da Eman suka k'arasa cikin d'akin, zuwa lokacin jini ya fara fita daga bakin sa ga wani irin tari da yake yi kamar mak'ogwaron sa zai tsage, a guje Dadd yayi kansa ya rik'e shi yana jijjiga shi amma ina idon sa ya juye sai yawo kwayar idon take, "Hameed kama shi muje asibiti". Cikin sauri aka d'auke shi aka sauka ta k'ofar waje sai asibiti.

Al_ihsan suka nufa aka kira Dr Auwal aka karb'e shi da gaggawa aka shiga bashi taimakon gaggawa dan yana cikin bad condition.

Sun jima a kansa kafin Dr Auwal ya fito ya kalli Daddy yace, "Alhaji wacece Precious?". Daddy ya kalli Anty Amina itama ta kalle shi kafin Daddy yace, "Matar shi ce". Dr Auwal yace, "Tana ina?". Daddy yace, "Bata nan." Dr yace, "indai ba nisa tayi ba a kira ta tazo kusa dashi dan sunan ta kawai yake kira kuma kasan yanayin ciwon da yake damun sa zuwan ta inda yake a yanzu zai rage masa radad'in da yake ji" Dr Auwal ya fad'a yana kallon Daddy.

Cikin sanyin murya Daddy yace, "Gaskiya bata kusa hasalima tana Gombe." Dr Auwal ya kama k'ugu tare da fad'in, "Damn it! To bara mu gani" ya fad'a yana sake komawa d'akin da Zaid yake ya bar su Daddy a wajan da suke tsaye kamar zasuyi kuka.



*ayi hak'uri yau an jini shiru na shiga rububi ne.*=??
*?ASAITAR SO!*

*56_57*

Not edited>??



Komawa su Daddy suka suka tsaya suna jiran sake fitowar Dr suji abinda zaice, an kwashe a k'alla mintina ashirin kafin Dr ya fito dashi da likitan da ya taimaka masa, su Daddy suka kalla kafin Dr Auwal yace, "Alhaji ciwon Zaid ya sake yin gaba, misali inda a mataki na biyu yake a cikin goma yanzu ya kai mataki na bakwai,? gaskiya abinda ya firgita shi yanzu har ya tab'a masa zuciya yafi wancan muni, tsakani da Allah yana buk'atar kulawa mai kyau in ba haka ba ciwon sa zaita gaba ne k'arshe zuciyar sa ta kai ga kunbura" ya k'arasa fad'a yana kallon su Daddy da suke sauraron sa.

Hameed ya sauke ajiyar zuciya cikin tashin hankali ya kalli Dr Auwal yace, "Yanzu ya jikin nasa?". Dr yace, "Ya samu bacci a yanzu an saka masa oxygen tana taimakawa numfashin sa tafiya dai-dai, zuwa anjima sai ku shiga ku ganshi amma banda yanzu". Shiru sukayi dukkanin su kafin su koma su zauna kowa yana sak'a da warwara.

Hameed ya kalli agogon hannun sa kafin yace, "Daddy ya kamata ku koma gida dare yayi sosai ni zan kwana dashi" ya fad'a yana kallon su Daddy, "A'a Hameed matan dai su koma gida amma ni kam bazan iya tafi na bar Zaid cikin wannan yanayin da yake ciki ba, bazan sami nutsuwa ba gwara na zauna d'in." Hameed yace, "To Daddy, Anty ku zo na mayar daku gida" ya fad'a yana mik'ewa suka bi bayan sa ita da Eman suka tafi.
Hameed bai jima ba ya dawo a lokacin suka shiga d'akin suka saka Zaid a gaba suna kallo.

Assalatu ya farkar da Hameed yaga Daddy a zaune a kan sallaya, mik'ewa yayi ya kalli inda Zaid yake kwance yana nan yadda yake ha mik'e yayi alwala suka bi jam'i a masallacin da ake jiyowa, bayan an idar Hameed suka gaisa da Daddy kafin Hameed yace, "Daddy yana da kyau kaima ka huta sabida yanayin jiki ka, bakayi bacci bafa a zaune ka kwana hakan zai iya jawowa matsala a lafiyar ka, dan Allah ka amince kaje gida anjima sai ka dawo zan kula da Zaid dai-dai yadda zan iya" ya k'arasa fad'a yana kallon Daddyn da yayi shiru yana sauraron sa.

Bai jira amsar saba ya dokawa driver waya ya bashi umarnin yazo yanzu ya d'auki Daddy, babu b'ata lokaci ya iso Daddy ya tafi badan yana so ba.

K'arfe tara na safe Daddy na shigo Zaid yana bud'e idon sa, shigowar Dr Auwal yaga ya bud'e ya k'arasa inda yake a lokacin da Zaid yake cire oxygen d'in da aka saka masa, "A'a Zaid ya zaka cire? Shine yake taimaka wajan numfashi fa" Daddy ya fad'a da sauri yana k'arawa inda yake.

Da hannu Dr yayiwa Daddy alama da ya k'yale shi, kansa yana gefe idon sa a lumshe yana numfashi a hankali, "me kake ji yanzu?" Dr Auwal ya fad'a yana kallon sa, k'irjin sa ya nuna masa kai ba tare da yace komai ba, "har yanzu yana ciwon?". D'aga masa kai yayi alamun eh, allurai ya had'a yayi masa sannan ya fita yace ma Daddy yana zuwa.

Sai a lokacin Zaid ya kalli Daddy da Hameed da suke tsaye yace, "Daddy bata dawo baka ko?". Kallon Hameed Daddy yayi kafin yace, "Eh Zaid." Mayar da idon sa yayi ya kulle kafin yace, "Daddy a sama min flight zanje Gombe". Baki bud'e Daddy ya kalle shi yace, "Zaid kana kwance a asibiti farkawar ka kenan amma kace zaka tafi Gombe a yau? Haba Zaid ina ka sani a Gomben in kaje,? Ka bari zuwa ka samu sauk'i." Kallon mahaifin nasa yayi yace, "Amma Daddy......." saurin katse shi Daddy yayi yace, "Umarni ne Zaid babu inda zaka je sai ka samu lafiya". Mayar da idon sa yayi ya kulle tare da sauke numfashi ba tare da ya sake cewa komai ba.

*Gombe State.*

Tun bayan da ta koma d'aki hankalin ta ya kasa kwanciya ta dinga zagaye a d'aki tana tunanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login