Showing 54001 words to 57000 words out of 171073 words

Chapter 19 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7847

tana kallon zanen k'unshin hannun ta, "kin damu da lafiya ta ne?" Ya tambaya idon sa a kanta, "eh mana". "Meyasa?". "Sabida kana matsayin Yaya na".

Duk da yanayin da yake ciki sai ya samu kansa da sakin murmushi baice komai ba ya kalli titi ganin traffic d'in yana raguwa, shagala tayi da kallon sa ganin yadda murmushin yayi bala'in karb'ar sa, duk da kana gani kasan ba murmushin farin ciki bane amma yayi masa kyau kamar bashi ba,? sakar mata hannu yayi ya gyara zaman sa kana yace, "Bana son hawa napep ina fad'a miki ne a matsayin na k'arshe kar na sake kama ki da hawa napep, in hakan ta faru zan b'ata miki raine fiye da tunanin ki" ya fad'a lokacin da ya taka motar ya suka fara tafiya.

"To bani da motar da zan dinga fita ne shiyasa dole na hau napep". "Ni ina da ita ai, duk lokacin da zaki fita just call me". "Ai bani da number ka" ta fad'a tana juya gefen mayafin ta, yadda ya d'ago ido ya watsa mata su ya saka ta diririce tace, "Na tuna ka kira ni da ita jiya" ta fad'a da sauri tana kallon sa.

D'auke idon sa yayi ya mayar kan titin, gani tayi ya d'auki wata hanyar daban ba hanyar gidan su ba tayi saurin kallon sa tace, "Gida fa zanje." "I know, wani waje zaki raka ni". Narai-narai tayi da ido cikin shagwa6a tace, "Dan Allah ka kaini gida wallahi Umma jira na take." Yanayin da tayi magana ya saukar masa da wata irin kasala ya lumshe ido ya bud'e yace, "Ba zamu dad'e ba."

"Nidai a'a ka mayar dani dan Allah" ta fad'a tana shirin yin kuka, "meyasa baza ki raka ni ba?". "Babu komai gida nake so naje kawai". "You are lie, kina tunanin zan kai ki wani waje ne nayi miki wani abun wannan shine tunanin ki" ya fad'a? ba tare da ya kalle ta ba fuskar sa kuwa ta koma kamar ta koda yaushe. Sai da ta kalle shi gaban ta ya fad'i jin tsaf ya karanto abinda yake ranta sai ta d'an rud'e tace, "A'a ba haka bane."

"Ban san meyasa mutane suke son yin k'arya ba, aha fad'a min dalilin ki na cewa nayi raping d'in ki that time" ya fad'a har lokacin yana tuk'in sa ba tare da ya kalli inda take ba, "ni bani da wani dalili, dan Allah ka mayar dani gida" ta fad'a har da bubbuga k'afa. Kallon ta yayi ya d'auke kai tare da d'an tab'e baki yace, "kina so kiyi k'arya naga alama ni kuma bana zama inuwa d'aya da mak'aryaci, so kika yi nayi zaman prison a kan hakan".

Sai da ta zaro ido waje sabida d'ubin mamaki kafin ta saita kanta tace, "Eh kusan hakan". "Okay, let me do it in yaso sai ki kaini k'ara da hujja" ya fad'a yana sake tamke fuskar sa, "dan Allah ka mayar dani gida". "In kika sake cemin na mayar dake gida wallahi yau baza ki kwana a gidan ba, hotel zan kai ki mu kwana a can" ya fad'a yana zaro mata manyan idon sa dan ta soma bashi haushi.

Kamar an saka mata padlock haka ta kulle bakin ta kawai ta zuba masa ido yana tuk'in sa bai sake ce mata komai ba, wayar sace tayi k'ara ya kalle ta ganin sunan Daddy ya saka yace, "D'auki ki saka a speaker" ya fad'a ba tare da ya kalle ta ba, Hakan tayi ta ajjiye masa daga can b'angaren Daddy yace, "Zaid ka shiga ka duba Eman kafin ka fita?". D'an yastine fuska yayi yace, "Na manta Daddy da ita sai dai in na dawo maybe". "In ka dawo d'in ma maybe ne babu lallai kaje d'in kenan?". "Uhum" ya bawa Daddy amsa, "in ka dawo ka tabbatar kaje har inda take ka duba ta". "Toh" kawai yace bai sake cewa komai ba Daddy ya kashe wayar a dai-dai lokacin da ya iso gate d'in company.

Horn yayi aka bud'e masa ya shiga da motar yayi parking ya kalle ta yace, "muje" yana fad'ar hakan ya bud'e murfin motar ya fita.

Ma'aikatan wajan ne suka tawo wajan kowa yana mik'o gaisuwa yana amsawa a hankali, cikin nutsuwa ya fara tafiya tana biye dashi tana kallon company dan babu k'arya ya had'u sosai, sai da suka hau escalator sannan suka isa office d'in sa saura kad'an tayi k'auyanci, office ya bud'e ya shiga itama tabi bayan sa, kallon office d'in take dan gaskiya yayi mata kyau sosai ga girma kuma ba'a yi masa wani ado na hauka ba, hoton ta da ta gani a kan table d'in sa yaja hankalin ta ta kai idon ta wajan tana dubawa cike da mamaki, yana kallon ta ya share ya bud'e frigde ya d'auki ruwa ya zauna akan kujera, "Haba Zaid tun d'azu muke aikin jiran ka sai yanzu zaka zo?" Hameed ya fad'a yana shigowa office d'in.

Kallon sa yayi ya kalli Ibteesam da sai a lokacin ya lura da ita yace, "Ibteesam kece yau a company mu?" Ya tambaya da murmushi yana kallon ta, "ina wuni" ta fad'a tana d'an sakin fuskar ta. Zaiyi magana suka had'a ido da zaid yayi saurin cewa, "Lafiya lau, Zaid ya zamuyi ne za'a samu yanzu?". "Me kenan?". "Sample". "Wai daman abinda ya saka ka kira ni kenan?". "Eh mana." Banzan kallo yayi masa yace, "Mtsww inda na d'auka abinda zakace kenan da ban b'ata lokaci na nazo ba, ni na d'auka meeting nake dashi" ya fad'a yana mik'ewa.

"Dan Allah Zaid kayi hak'uri ka bamu sample d'in nan sai ka tafi" Hameed yayi saurin fad'a cikin rok'o. Dak'yar ya samu ya amince ya yadda ya fara zana sample d'in yana yi yana jan tsaki.

Ita dai tana kallon sa ganin yadda yake sarrafa pencil a hannun sa kamar bashi ba, sosai ya burge ta sai a lokacin ta gane zana hoton ta yayi kenan, bai wani jima ba ya gama Hameed ya karb'a shi kuma ya kalle ta kawai baice komai ba yayi ficewar sa, kamar tasan abinda yake nufi ta mik'e ta bi bayan sa.

Tunda suka d'auki hanya babu wanda yace wani abu sai aukin washh da yake furtawa ita kuma tana kallon sa ganin wanne aiki yayi da zai dinga kiran washh, har suka isa unguwar su Ibteesam, tunda suka shiga layin ya hango mak'iyin sa Khalid a zaune a saman mota da alama jiran ta yake yi, cak ya tsaya da motar yana k'okarin juyawa tayi saurin cewa, "Ba waje na yazo ba akwai gidan kakan sa nan baka ga ba a k'ofar gidan mu yake ba?" Ta fad'a cikin taushin murya tana kallon sa.

"Zaman ki lafiya ki wuce ba tare da kin kalle shi ba in ba haka ba wallahi dake dashi ranku ne zai b'aci a yanzu" ya fad'a yana cigaba da tafiya, a gaba da Khalid yayi parking ta bud'e ta fita da sauri ko kallon inda Khalid d'in yake batayi ba tayi saurin fad'awa gida, shi kuma ya sauke glass suka had'a ido da Khalid da yake kallon motar ya zuba masa wani mugun kallo yaja motar sa ya bar unguwar.

Da murmushi Khalid yabi motar da Ibteesam ta sanar dashi komai game da abinda aka saka ta zata yiwa Zaid d'in

Bayan kwana biyu.

To abotar Ibteesam da Zaid dai babu wani cigaba kullum iya e yau, babu abinda ya canja ko yaushe tayi masa ba dai-dai ba make ta yake babu abinda kuma ya canja dangane da abinda tace bata so daga gare shi sai ma abinda yayi gaba.

Kamar kullum yau ta kama ranar juma'a Zaid yana tsaye d'aure da towel a k'ugun sa yana kallon kayan dake cikin wardrobe d'in sa, iska ya fesar yana sake duba kayan ya rasa wanda zai d'auka ya saka, rufe ta yayi ya bud'e ta kusa da ita yana kalla daga sama har k'asa, hannu ya saka ya zaro wani yadi kofi colour mai kyau rigar mai gajeren hannu, tsaki yayi yana kallon yadin yana yatsine fuska kamar bashi ne ya d'auko da kansa ba, cikin mintina kad'an ya shirya ya tsaya a mudubi yana kallon kansa.

Shi kam bai ga kyaun da kayan suka yi masa ba dan in badan Daddy yayi masa dole ba ya za'ayi ya saka manyan kaya, agogo ya d'auka ya d'aura a hannun sa ya mayar da azurfar hannun sa mazaunin ta, kama k'ugu yayi yana kallon tarin hulunan da suke ajjiye ya rasa wacce zai d'auka ya saka, dak'yar ya samo wata wacce tayi shige da kayan jikin sa ya saka ya fesa turarukan sa ya d'auki wayar sa ya fito daga d'akin.

K'asa yake sakkowa yana jan tsaki dan har ga Allah kayan sun takura masa dan bazai iya tuna rabon da ya saka manyan kaya bama, yana sakkowa suka had'a ido da Eman da d'aurarran hannun ta tana niyar wucewa ta kusa da inda steps d'in suke, shagala tayi da kallon sa ganin yadda yayi mugun kyau kamar bashi ba, har yazo kusa da ita bata sani ba sai da yaja dogon tsaki ya wuce ta sannan ta firgita ta dawo hankalin ta, khamshin turaren sa ta shak'a ta lumshe ido ta sake bin sa da kallon son sa na sake shiga ranta.

"Masha Allah Son, kayi kyau sosai fa" Daddy ya fad'a a lokacin da Zaid d'in yake shigowa falon, d'an tab'e baki yayi yace, "Ni sun takura ni wallahi". "A haka zaka saba, tashi muje" Daddy ya fad'a yana mik'ewa.

Anty Amina da ta fito a lokacin ta kalli Zaid tayi murmushi tace, "masha Allah, Zaid manya kaya suna yi maka kyau sosai". Kallan ta yayi ya d'auke kai ba tare da yace komai ba, "rabu dashi kuma wai a haka yake cewa kayan sun dame shi" Daddy ya bata amsa da murmushi a fuskar sa. Shi dai bai amsa ba ya fita daga falon dan sam baya son had'a inuwa da Anty Amina.

Daddy ya kalli Anty Amina sosai ganin cikin ta ya tasa amma dake tana da shekaru ba yarinya bace baza kace ciki bane ba sai a d'auka tumbi ne, "Cikin yayi miki kyau" ya furta yana kallon ta da murmushi a fuskar ta. Murmushi itama tayi tace, "Zaid yana jiran ka kaje ku tafi" tana fad'ar hakan ta juya ta fita daga falon ya bita da kallo.

A tsaye a jikin mota ya hango Zaid yana aukin danna waya tawowar Daddyn ya saka shi ya mayar da w??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ayar yana jiran ya k'araso, "to shiga mu tafi mana" Daddy ya fad'a yana zagaya tare ds bud'e gaban motar ya shiga. Mazaunin driver Zaid ya bud'e ya shiga ya zauna tare da kunna motar suka fita daga gidan ba tare da yasan inda zasu ba, "muje alfurqan muyi sallar juma'a, akwai d'aurin aure ma da zan tsaya bayan an idar da sallah daga nan sai muje inda zamu". Shi dai baice komai ba ya d'auki hanyar masallacin.

Bayan an idar da sallar aka d'aura auren Daddy yayi musu Allah ya sanya alkhairi suka fito daga masallacin, ta gefen ido ya kalli Zaid yaga sai tab'e fuska yake fuskar a had'e kana ganin sa kasan a takure yake, murmushi Daddy yayi kawai suka k'arasa wajan motar suka shiga, sai da suka fara tafiya sannan Daddy yace, "Muje gidan su me sunan Maman ka". Kallon Daddy yayi da mamaki yace, "Muyi me a can?". "In munje zaka gani ai". Baice komai ba ya shiga da jan motar sa har k'ofar gidan su Ibteesam.

Parking Zaid yayi suka fito a tare Daddy ya d'auki waya ya kira Abba ya sanar dashi zuwan su, ba jimawa Abba ya fito da fara'a a fuskar sa ya tarbe su suka shiga cikin gidan, a falon Abba aka yada zango suka zazzauna Abba da yaji dad'in ziyarar tasu suka gaisa da Daddy kafin Zaid yace, "Ina wuni". Kafin Abba yayi magana Daddy yace, "Haka ake gaida manya Zaid? Barka da rana ake cewa ba ina wuni ba." "Barka da rana" Zaid d'in ya fad'a. Murmushi Abba yayi yace, "Barkan ka dai Zaid, ya aiki?". "Alhamdulillah" ya bashi amsa yana d'an kawar da kai dan shi har ga Allah a takure yake.

Umma da Mama ne suka shigo falon suka zauna tare da gaisawa cikin sakin fuska, "Umma barkan ku da rana" Zaid ya fad'a ba tare da ya kalle su ba, a tare suka amsa da Mama.

"Ina y'ar tawa ne?" Daddy ya fad'a yana kallon Abba, "yanzu zasu shigo ku gaisa". Abba yana rufe baki suka shigo su uku da sallama suka gaida Daddy ya amsa da fara'a tana tambayar su makaranta, idon Asiya ne ya fad'a kan Zaid da ko kallon su ma baiyi ba, murmushi tayi tana k'arewa masa kallo dan gani take kamar an sake k'ara masa kyau daga ranar da ta ganshi zuwa yau.

"Wacce ce y'ar tawa a cikin su?" Daddy ya tambaya yana kallon Abba, Abba ya nuna Ibteesam da kanta yake a k'asa tana satar kallon Zaid da ya nuna kamar bai san da zaman ta a wajan ba, "Maryam ya hak'uri da halin Zaid? Dan nasan kina hak'uri sosai ko?" Daddy ya tambaye ta cikin sigar wasa, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da zoben hannun ta.

"Dad wani hali ne dani da za'ayi hak'uri?" Ta tambaya yana kallon Daddy da shima shi yake kallo, "halayen kama ai da yawa wanda za'ayi hak'uri ai ba guda d'aya bane ba". "Amma Daddy sai ka fad'a a gaban yarinyar nan dan kawai ta sake raina ni?" Ya fad'a tana aika mata da harara.

Murmushi Daddy yace, "To uban y'an san girma ai gaskiya aka fad'a." Abba yace, "Ai da gaskiyar sa baka fad'a a gaban ta ba kar ta raina shi." Gabad'ayan su sukayi murmushi banda Asiya da Mama da maganganun suka d'aure musu kai suna mamakin har yaushe sukayi wannan sabon haka.

Wayar da take hannun ta ta kunna ta shiga message ta nemo number sa ta tura masa da gajeren sak'o, wayar na hannun sa yaga shigowar sak'on ya bud'e yana karantawa, "kayi kyau sosai fa kamar na sace ka na gudu". Murmushi yayi kad'an ya d'ago ido ya kalle ta ya d'auke kai tare da mayar da wayar aljihun sa.

A haka aka d'an tab'a hira kad'an kafin su Daddy suyi musu sallama su tafi gida.

Sosai Zaid yaji dad'in yabon da Ibteesam tayi masa d ya tuna sai yayi murmushi yana jin farin ciki a kan hakan sosai.

A can gidan su Ibteesam kuwa bayan tafiyar su Daddy Mama ta dawo falon Abba ta same shi a zaune shi kad'ai babu kowa yana kallon tafsir, "Nikam nace wai meye tsakanin Ibteesam da d'an wajan Ambassador ne?". Abba ya d'ago ya kalle ta kafin ya cigaba da kallon tv d'in yace, "Mijin tane." Kallon sa tayi da mamaki tace, "mijin ta? Kamar yaya ban gane ba?". "Kamar yadda kika ji na fad'a mijin tane". Baki bud'e ta kalle shi kafin tace, "Har yaushe aka d'aura musu auren bamu sani ba,? Ita naga kuma ai Khalid take so ko?".

Mayar da hankalin sa yayi kanta kafin yace, "ai tunda na fad'a miki ya kamata ace ki yadda ba ki tsaya kina yi min wasu k'ananun tambayoyi ba." Gyara zama tayi tace, "Amma abin ne da d'aure kai har yaushe ya zama mijin ta duka bamu sani ba? Ko dai siyar da y'ar mutane kayi dan kaga ba taka bace?". A fusace ya kalle ta yace, "Wannan wacce irin banzar magana kike min Zubaida? Ni zaki kalla kice na siyar da Ibteesam ehee,?". "Kayi hak'uri abin ne kawai ya bani mamaki ne" ta fad'a tana had'e rai tare da kawar da kai.

"To ya daina baki mamaki sannan kar naji kin fad'awa wani a cikin gidan nan kema na fad'a miki ne kema matsayin ki na uwa a wajan Ibteesam" ya fad'a cikin sigar gargad'i yana kallon ta.

Mik'ewa tayi ta fice daga falon tana sak'a da warwara a kan lamarin.

B'angaren Umma kuwa Ibteesam da Umma suna zaune a falo kamar koda yaushe Umma ta kalli Ibteesam tace, "Nikam Ibteesam a yanzu sai nake miki sha'awar auren yaron nan Zaid". Kallan Umma tata tayi tace, "Meyasa?". "Babu komai haka kawai yau naji ya shiga raina." Tab'e baki tayi tace, "Nikam Umma bana son sa har yanzu, Khalid ni nake so kawai dai ina tausayin sa ne". "To ai shikenan Allah ya zab'a abinda yafi alkhairi". "Amin" ta fad'a tana d'aga fuskar wayar ta jin wayar tana k'ara.

Sunan da ta gani ya bata mamaki ta d'auki wayar ta kara a kunnen ta, "Ki fito zan baki sak'o" yana fad'ar hakan ya kashe wayar ta bi wayar da kallo, "Umma Zaid ne wai naje zai bani sak'o." "To jeki mana" ta bata amsa tana mik'ewa ta shiga d'aki.

Hijjabi ta d'auka ta saka ta fita, bak'ar mota ta hango a inda yake ajjiye motar ta nufi motar a hankali har ta k'arasa inda motar take, bud'e gaban motar tayi ta shiga ba tare da ta kalli wanda yake zaune a motar ba, dan yayi mata warning akan in yazo tak'i shiga mota, juyowa tayi zata yi magana suka had'a ido da wanda yake zaune a cikin motar, zaro ido waje tayi gaban ta yayi mummunar fad'uwa ganin Khalid sab'anin Zaid, murmushi Khalid yayi yace, "ya akayi kika san nazo?" Ya tambaye ta da mamaki yana kallon ta.

Bata iya bashi amsa ba sai juyawa da tayi ta kalli gefen ta nan ta hango motar Zaid a ajjiye, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, na shiga uku" ta furta ba tare da ta sani ba,? "subahanallah, love lafiya?" Ta tambaya a tsorace yana kallan ta.

"Zaid!" Abinda ta furta kenan hawaye na gangarowa a idon ta dan ta hango shi ya fito daga mota ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon motar Khalid, "babu abinda zai faru, muje nayi masa bayani nasan abinda zance masa". "A'a Khalid ka tafi kar ka fito zai maka illa" ta fad'a tana bud'e murfin motar tana fitowa.

Fitowa yayi shima daga motar yana fad'in, "bazan barki dashi ke kad'ai ba komai zai faru ya faru". "Khalid dan Allah ka koma mota ka tafi, ka tafi" ta fad'a da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login