Showing 144001 words to 147000 words out of 171073 words

Chapter 49 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7857

ya tashi dan yanzu ba sakkowa zaiyi ba in yana cikin wannan yanayin sai ya kwana uku bai lek'o k'asa ba". Da to ta amsa ta tashi ta tafi saman, mamaki ne ya kamata ganin falon tass kamar ba shine wanda ya lalace d'azu ba hatta tv da ya fashe babu shi a wajan, a hankali ta tura k'ofar d'akin ta shiga nan ma tass kamar babu baiyi fashe-fashe ba sai khamshi ma da d'akin yake yi, shiru d'akin babu alamun mutum a ciki ta k'arasa k'ofar toilet tayi knocking amma shiru ba'a amsa ba, tura k'ofar tayi ta shiga band'aki babu kowa a ciki, fitowa tayi ta sake k'arewa d'akin kallo amma bata ganshi ba sai ta nufi velconcy ta bud'e nan ma wayam, fitowa tayi ta kulle ta shiga gym room d'in sa nan ma baya nan dan a kulle ma yake da mukulli ta waje sai da ta bud'e, ta rufe ta lek'a small cafe d'in sa nan ma baya nan.

Kiran layin sa ta shiga yi amma ba'a d'auka ba kusan 5 missed call tayi masa amma ba'a d'auka ba, da sauri ta sakkowa tana d'akin, "Mama! Mama!!". Anty Amija tace, "lafiya?". Tace, "na duba ko ina na saman sa amma baya nan na kira shi kuma bai d'auka ba." Da mamaki Anty Amina tace, "baya nan kamar yaya kenan?." "Wallahi Mama baya sama na neme shi na rasa" ta fad'a cikin tabbatarwa tana kallon ta.
"To ina ya shiga?" Ta fad'a tana fara laluben number wayar Daddy ta kira shi ta sanar dashi.

Kiran Daddy take amma call waiting alamun waya yake amma bata hak'ura ba haka take kiran sa wai ko zai katse waccan ya d'auka amma bai katse ba da alama mai mahimmaci ce, "kinga Daddyn nasa bai d'auka ba" ta fad'a tana sake kiran sa amma bai d'auka.

A wannan lokacin aka rasa samun Zaid ko Daddy a waya shi Zaid baya d'auka shima daga baya Daddyn bata d'auka, hankalin su duka ya tashi an rasa wanda za'a nema aji abinda yake faruwa a haka har akayi sallar la'asar biyar ta wuce sannan Daddy ya shigo gidan.

Anty Amina ta mik'e tsaye tana kallon yanayin Daddy tace, "Sannu da zuwa" ta fad'a tana kallon yanayin sa ganin. Bai amsa ba ya zauna tare da yin shiru baice komai ba, shigowar falon da aka kuma yi a fusace ya saka su kalli wanda ya shigo, muryar sa a shak'e tsabar b'acin rai yace, "Daddy why?" Ya fad'a yana kallon idon sa da idon sa wanda ya koma ja ya kumbura fuskar sa tayi ja sosai.

Daddy ya mik'e yaja hannun sa ya zaunar dashi ya kalli Anty Amina yace, "bani ruwa mai sanyi". Ba musu ta bud'e fridge ta d'auko ta mik'a masa ya bud'e ya mik'a masa alamun yasha, karb'a yayi amma bai sha ba yace, "Daddy answer me please" ya fad'a muryar sa har rawa take yi sabida b'acin ran da yake ciki. Daddy ya zauna kusa dashi ya dafa shi yace, "Abdallah meyasa zaka aikata hakan ba tare da shawara ta ba?". "Daddy kenan kana so na zuba ido wanda suka kashe min uwa sun kashe banza kenan,? Sabida gudun abinda duniya zata fad'a ace d'an ambassador ya kai yayyen baban sa police station k'ara? Naje fa station ne dan kar nace zan d'auki mataki ka hana shiyasa naje hukuma ta d'auki mataki amma Daddy kaje da kanka da kayi cancelling case d'in ka kuma ce k'arya nake wai bani da lafiya, yanzu Daddy a kan su kake kira na mara hankali?" Ya k'arasa fad'a yana jefar da ruwan hannun sa ya mik'e tsaye a fusace.

"Daddy in baka bari na d'auki mataki a tsari ba in ka hana hukuma ta hukunta su wallahi zan saka thugs suyi musu abinda baza su tab'a mantawa ba kamar yadda nima bazan manta ba, in kuwa kak'i zan bar gidan nan ne ban kuma san lokacin da zan dawo ba" ya fad'a yana niyar barin wajan Daddy yayi saurin rik'e hannun sa yace, "Zaid zo ka zauna". "Akan me zan zauna Daddy? Na zauna ma bani hak'uri kace komai zai wuce abinda yasa kake so na zauna kenan ko?." "Nace ka zauna kaji abinda zan fad'a maka" Daddy ya sake fad'a yana sake rik'e hannun sa.

Zama yayi yana girgiza kai cikin taushi murya da kwantar da hankali Daddy yace, "Zaid waye ya halicce mu?". "Allah" ya bada amsa kansa na gefe ba tare da ya kalle shi ba, "Allah da kansa muna yi masa laifi ya yafe mana duk girman sa balle kuma mu y'an adam, meyasa baza kayi hak'uri ka yafe ba kaima?". Kallon Daddyn nasa yayi da idanun sa da suka koma ja sosai yace, "meye hukuncin wanda ya kashe musulmi baiji bai gani ba ba?". Ya gefe masa tambayar yana kallon sa, Daddy yace, "Shima a kashe shi, amma....." ya katse Daddyn da fad'in, "Amma me? Hukuncin da Allah ya fad'a zaka hana ni aikatawa? Kaima gashi ka shaida haka Allah yace to akan me zaka hana ni aikatawa?".

"Zaid ba hana ka aikata hakan nayi ba so nake kayi amfani da tunanin ka da hankalin ka akan wannan maganar, duk abinda suka aikata kansu fa suka yiwa mahaifiyar ka kuma daman Allah yayi lokacin barin ta duniya ne yayi ko sun zama sila ko bazu zama ba sai ta bar duniya, kayi imani da Allah ka amince da k'addara ka bar wannan maganar ka barsu da BAK'AR ANIYAR su (up coming book, bak'ar aniya)." zuba masa ido kawai yayi yana kallon sa har ya kai k'arshe kafin yace, "Daddy ni na fara doubting anya kana son Mama na kuwa? Anya ba auren k'iyayya kuka yi ba?".

Daddy yace, "ba rashin so a wannan Zaid ina fad'a maka gaskiya ne". "Babu batun wata gaskiya a nan Daddy, dan inda kana son ta babu abinda zai hana kasan da wannan maganar tun farko kayi shiru baka d'auki mataki ba, akwai wanda ya isa a duniya ya tab'a min mata a yanzu ya zauna lafiya,? Babu shi sabida ina sonta ne amma kai sai ma hak'uri da kake bani akan kada na d'auki mataki sabida sun kasance y'an uwan ka ni kuma sun kashe min uwa ranta ya tafi a banza, wallahi basu isa ba" ya fad'a cikin masifa da alama ya manta da Dady yake magana.

Daddy ya rasa abinda zai ce masa amma baiyi shiru ba yace, "Zaid mahaifiyar ka mutuniyar kirki ce baya da abokin fad'a ta bar duniya kowa yana yabon kyawawan halayyar ta, tana cikin rahamar Allah ina ji a jiki na Zaid ko iya wannan ne ta ci riba tunda ta bar duniya ba tare da hakkin kowa a kanta ba, dan Allah ka bani nutsuwar ka" ya fad'a cikin sigar kwantar da hankali.

"U see kaji kace mutuniyar kirki ce bata da abokin fad'a kuma kake bani hak'uri a kan na bar wanda suka zama silar barin ta duniya suna walwala kamar kowa, bazan iya ba Daddy" ya fad'a yana mik'ewa tsaye, Daddy yace, "Zaid kar kaje kayi wani abu na fad'a maka ka bar komai a hannu na". Juyowa yayi ya kalli Daddyn yace, "nine zanyi handling case d'in nan in kuma ba haka ba zan bar k'asar nan baza ku sake gani ba" ya fad'a yana juyawa tare da fara tafiya, "Zaid!" Daddy ya fad'a Anty Amina tayi saurin katse shi ta hanyar nuna masa da hannu ya kyale shi.

"Amina wacce irin zuciya Allah ya bawa Zaid? Ashe tun d'azu ya bar gidan ya tafi ya kwashi police suka je har gida suka tafi da y'an uwa na yace kisan kai sukayi, daga can station d'in aka kira ni shine lokacin da kike ta kira na ban d'auka ba, naje nayi abinda zanyi na dawo dasu, me Zaid yake so nayi masa ne? Nasan an b'ata masa amma meyasa bazai hak'uri ya bar su da Allah ba,? Baya ganin BAK'AR ANIYAR su ta komawa kansu ne, ina murna yayi hankali ya daina wad'an nan dabi'n ashe ba haka bane, na d'auka yanzu ya ajjiye wannan zafin ran nasa ashe da sauran aiki" Ya fad'a yana dafe kansa dan shi kam rigimar Zaid tafi k'arfin sa. Anty Amina tace, "nifa banga laifin Zaid ba wallahi ko kad'an ma kuwa, babu wanda za'a zagi mahaifiyar sa a gaban idon sa ya tsaya yana kallon mutum balle a kalli idon ka ace nine silar mutuwar babar ka ai a gani na babu kalmar da ta kai wannan d'acin a duniya, kayi hak'uri da abinda zance amma y'an uwan ka sam basu da imani ko kad'an ni nasan irin abubuwan da suke kullawa, dan haka ka k'yale shi ya d'auki mataki dai-dai da abinda suka aikata shine zai sami sauk'i azabar da yake ji a zuciyar sa."

Kallon ta Daddy yayi yace, "kema baza ki rarrashe ki ba kenan? Meyasa baza ki bashi shawarar ya yafe ba, Allah muke masa laifi yame yafe mana balle mu mutane? Amina ki daure ki taimaka min wajan ganin mun shawo kan Zaid a kan maganar nan, nima bance ba'a b'ata masa ba amma tunda komai ya wuce ba sai a bar zancen ba? Yau shekara nawa da rasuwar ta? Sama da shekara goma ba, mu barsu da Allah zai musu hukuncin da mu baza mu iya yi masa ba kuma zamu ji dad'in sa yife da wanda zamu yi musu, dan Allah ki daure mu shawo kansa." Ajiyar zuciya tayi bawai dan ta amince ba tace, "kasan halin sa a yanzu bazai ji komai zaka ce masa ba yana kan dokin fushin ne ka jira ya sauka tukunna, yana buk'atar hutu a yanzu mu barshi ya huta."

"Ina daughter?" Ya fad'a yana kallan ta, "suna ciki" ta bashi amsa a tak'aice, "kira ta" ya fad'a yana dafe kansa yana sauke numfashi, juyawa tayi bata jima ba suka dawo tare da Ibteesam ta zauna a k'asan carpet, "Daughter kece kad'ai zaki tankwara shi a yanzu kema kuma zaki sha wahala kafin ya saurare ki, nasan anyi masa ba dai-dai ba dan mahaifiya ba abar wasa bace balle ace silar barin ta duniya akayi amma ya duba matsayin su a wajan sa ya kuma duba ido na da yake bud'e a duniya ya bar maganar nan, inda bana raye sai yayi musu duk abinda yake so amma yanzu suci albarkaci na ya k'yale su ya? barsu da Allah tun yanzu ya fara yi nuna masa sakayya balle gaba, Allah yana sane da komai shi ya k'addara hakan zata kasance kuma shine zai yi sakayya meyasa bazai bar lamarin a wajan Allah ba, ki taimaka min ki rarrashe shi nasan tsaf zan neme shi na rasa kamar yadda yace amma ki daure dan dan Allah ki bashi baki yak'i ya yafe kuma ya zauna a gida" Daddy ya fad'a muryar sa a sanyaye yana kallon ta.

"Insha Allah Daddy zanyi iya bakin k'okari na a kan hakan" ta fad'a murya a sanyaye dan ita tausayin Dady da Zaid d'in take ji. "Yauwa Allah yayi miki albarka, tashi kije wajan nasa" ba musu ta mik'e ta ta nufi saman nasa.

A bud'e taga k'ofar falon hakan ya saka ta shiga ciki yana tsaye yana ta zaga d'akin daga nan yaje can da alama tunanin mafita yake yi, "Baby" ya fad'a muryar ta a k'asa tana kallon sa, juyowa yayi ya kalle ta tare da bud'e mata hannu, ba musu ta k'arasa inda yake ta shiga jikin sa ya mayar da hannun sa ya rungume ta yana sauke numfashi, sanyi yaji yana shiga jikin sa ta ko wanne b'angare ga kamshin da yake tashi a jikin ta ya sake saka shi lumshe ido, "I'm sorry Baby" ta fad'a tana kwance a jikin sa tana jin bugun zuciyar sa.

"Bai kamata ka dinga yiwa Daddy magana a haka nafa baby kana d'aga masa murya kamar kana magana dani in rai ya b'aci bai kamata hankali ya gushe ba, na sani an b'ata maka rai anyi maka tabon da baza ka manta dashi ba zaka ji zafi fiye da komai a duniya amma hak'uri zakayi ka kwantar da hankalin ka ka barwa Allah na tabbata zai maka sakayya tun a yanzu gashi ka fara gani, Allah yana sane da komai baby shi ya k'addara hakan kuma shine zaiyi sakayya a akan hakan" ta fad'a har lokacin tana jikin sa shima kuma yana rik'e da ita. D'ago da ita yayi daga jikin sa ya kalle ta yace, "kina so kema kice na bar su kenan?" Ya fad'a yana binta da ido ganin yanayin ta duka ya canja.

Mayar da kanta tayi jikin sa tace, "Haba Baby ni na isa nace haka amma idon Daddy zaka duba, kayi imagine kana da y'an uwa wanda kuke ciki d'aya baka da wanda ya rage maka sai su a duniya zaka ji dad'i ace yau d'an ka ya kaisu kara har an kama su? Amsa nasan zaka ce A'a koda baka furta min ba to haka Daddy yake ji, Daddy yana son ka yife da komai dan kai kad'ai ya mallaka a duniya haka yana son Mama har ya fika sonta domin shi addu'a yake mata bai tsaya yace sai ya d'auki mataki ba kai kuwa da da wannan b'acin ran da ka saka kanka da kayi mata addu'a koda suratul ahad ne yafi wannan abin da kake tayi, bance kar ka d'auki mataki ba amma ka barwa Daddyn komai kamar yadda yace."

D'ago ta yayi daga jikin sa ya kalle ta kawai ba tare da yace komai ba, ji yayi zuciyar sa na k'okarin karyewa akan abinda yayi niyar yi ya san indai zai barta ta cigaba da magana tabbas zata karya masa zuciya, "Samo min tea a k'asa" ya fad'a muryar sa a sanyaye yana kallon fuskar ta.

Barin jikin sa tayi sannan tace, "to yanzu zan kawo maka ka jira ni" kai kawai ya d'aga mata ya koma ya zauna ita kuma ta fita, yana ganin fitar ta ya fesar da numfashi ya nufi wardrobe d'in sa ya jawo k'arar jaka ya zuba abinda yasan zai buk'ata ya, kama k'ugu yayi yana tunanin inda password d'in sa yake, daga ranar da ya fad'i a k'asa aka kwantar dashi a asibiti bai sake ganin saba wayar sama sai Daddy ne ya bashi kenan password d'in ma yana wajan Daddy, cize baki yayi tare da shafa fuskar sa ya ja jakar ya fita daga d'akin tare da sauka ya hau mota ya fita daga gidan da saurin gaske.

Da tray a hannun ta tana k'okarin hawa sama Zahra da ta dawo daga waje tace, "Anty Ibteesam yanzu naga Yaya Zaid d'in ya fita fa". Hakan ya tsayar da Ibteesam daga k'okarin hawa saman da take yi ta ajjiye tray d'in tace, "ya fita kuma? Shine fa yace na kai masa." "Wallahi ya fita na ganshi yanzu ya shiga mota har da jaka a hannun sa ma".

Daddy da Anty da suke zaune Daddy yayi murmushi yace, "Daughter wayo yayi miki shiyasa ya sakko dake shi kuma ya tafi, kira shi a waya". Ba musu ta d'auki waya ta kira ta saka a speaker tana ringing ba'a d'auka ba har ta katse, ta sake kira tak'i shiga, akayi akayi amma wayar tak'i tafiya, Daddy ya girgiza kai yace, "Zaid kenan indai yayi niya sai yayi, ya tafi kamar yadda ta inda Allah ya taimaka password d'in sa yana hannu na dan haka inda zaije bazai wuce cikin k'asar nan ba tunda ya kashe waya kuma baza'a same shi ba mu k'yale shi ya samu hutu" Daddy ya fad'a cikin rauni dan shi kad'ai yasan abinda yake ji.

Ibteesam duka ta damu duk minti biyar sai ta kira wayar sa ko zata shiga amma a kashe, a haka ta hak'ura suka koma gidan Mummy jikin ta a sanyaye babu walwala ko kad'an a tare sa ita har Mummy ta gane aka ce mata bata da lafiya kawai.

Akayi kwana d'aya shiru babu Zaid babu labarin sa na biyu ma haka na uku ya wuce ana tunanin Ibteesam ce weakness point d'in sa itama ya toshe duk wata hanya da zata same shi balle ma ta karya masa zuciya, an tambayi Hameed dasu Wizzy amma suma basu san inda yake ba har Kaduna suka je amma baya can, duk Daddy ya damu sosai amma baya nunawa yake dannewa sabida baya so ya nuna raunin sa a fili. cikin kwanakin y'an uwan Daddy dama Anty Amina sunyi kara suma an d'auki lefe an kai gidan Umma inda suka bada tukwici kamar yadda al'ada ta tanadar, Ibteesam dai haka take komai jikin ta kamar na nata ba tayi masa message yafi sau d'ari daga barin sa gida zuwa yanzu amma bai ma gani ba balle ya bata amsa, duka ta fita a hankalin ta ta rame kamar ba amarya ba tace ta fasa yin walimar Mummy da Anty Amina suka ce bata isa ba sai anyi.

A kwanakin ne Khalipha yayan Ibteesam ya dawo daga madina duk da bashi da shekaru amma jikin girma gare shi dan baza ka ganshi kace baiyi shekara ashirin da biyar ba ya ajjiye gashi a fuska kamar babban mutum, y'an matan Gombe sun sauka a Kano za'ayi Walima dasu su koma suka tawo tare da Ameer da soyayya ta shiga tsakanin sa da Jidda.

Yau ta kama asabar kuma yau ne Ibteesam zata gabatar da ladys eve lahadi kuma ta tare, an yiwa compound d'in gidan Mummy decoration sosai dj tazo haka m.c ga photographer duka mata ne, Ibteesam ta had'e cikin wedding gown fitted pink colour wacce tayi mata kyau sosai ta kuma fito mata da shape d'in jikin ta, a saman rigar ta baya daga wajan k'ugun aka mak'ala wani k'aton mayafi mai adon gaske wanda yake jan k'asa sosai, an d'aura mata abin kai shima pink an jashi baya gashin ta ya fito ta gaba an gyara gajin yayi bak'i sosai, tayi kyau matuk'ar kayan sun amshe ta haka make up d'in fuskar ta kamar y'ar tsana haka ta koma sabida kyau, kawayen ta kuma da y'an uwan ta sun yi ankon blue black d'in material wanda suka masa d'inkin dogayaen riguna.

K'arfe biyar suka fara event ana kid'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login