Showing 132001 words to 135000 words out of 171073 words

Chapter 45 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7836

ya shigo.

Bai yi magana ba itama batayi ba ya wuce har zata fita yace, "zo ki bani ruwan wanka". Band'akin ta nufa ta shiga ta kalli sama nan taga akwai water heater ta kunna ta jawo bokiti ta had'a ruwan wankan dai-dai wanka baiyi zafi ba baiyi kuma sanyi ba kana ta fito, har ya cire riga lokacin da ta fito sai tsaki yake yana fad'in, "kayan nan damu na suke" ya fad'a yana ajjiye rigar a gefe wayar sa na hannun sa yana dannawa.

"Na gama" ta fad'a tana niyar ficewa, har zai magana sai kuma ya k'yale ta dan yasan itama a gajiye take, tana fita ta koma can ta zauna kusa da Hajiya Kaka tace, "Hajiya me kika ajjiye min ne?". Dariya tayi kad'an tace, "Ke ni ai lamarin nan yayi min dad'i, wannan miji da kika samu Maryama kyakykyawa ga nutsuwa da kunya, wallahi naji dad'in hakan baki ji murnar da nake miki ba". Jin ta ambaci kunya ya bawa Ibteesam tayi tace, "Allah Hajiya?". "Allah kuwa, maza kije kiyi wanka ki huta sai kuzo ki kai masa abinci kema kici naki". Bata ce komai ba ta mik'e ta shiga d'akin da tasan suna ciki.

Aikam duka suna nan sai Zahra da take wanka a band'aki tana shigowa suka hau ihu Fateema tace, "Anty wannan handsome haka, gaskiya kin iya zab'e." Hararar Fateema tayi tana cire d'ankwalin ta tace, "Kaji Fateema da wata magana, to har finku kyau yayi? Kiga fa su Hamma Ameer yadda suke ai har sun fishi." Amina tace, "Haba Anty wane mutum, ai wallahi yafi su had'uwa ga wani class magana ma wahala take masa, kamar fa irin labarawan dubai d'in nan wallahi". Lokacin Zahra ta fito taji suna maganar ta amshe da fad'in, "To ai haka halin sa yake dan ma ganin ku bak'in fuska ya saka shi yayi muku magana amma wajan aji kam k'arshe ne."

Aysha tace, "ai mun gani kam wallahi, na taya ki murna Yaya ta dan ni daman ina son miji mai nutsuwa har ga Allah" ita dai banza tayi musu ta shiga wanka, har ta fito suna ta aikin hira ta kalli Jidda da bata wani sake ba tace, "Jidda baza kiyi wankan ba?". Sai Fateema tace, "Duk ta wani takure tak'i sakin jikin ta, kinga mu nan y'an hira ne munfi so muga an zage ana kwasar dariya". Dariyar kawai tayi ta tashi ta shiga band'aki.

Suna gama shiryawa akayi azahar suka yi sallah sannan suka fito cin abinci, suna zama Hajiya tace, "to maza d'auki ki kaiwa mijin ki sai ki dawo kici" ba musu ta mik'e ta d'auki abinda zata d'auka ta tafi d'akin da yake ciki, da sallama ta shiga yana zaune daga shi sai k'aramar riga mara nauyi sai wando iya guiwa yana amsa waya, ajjiye abincin tayi zata fita ya rik'e hannun ta har ya gama wayar sannan ya jawo ta ya zaunar da ita kusa da ita yace, "Ina zaki je?". Tab'e baki tayi tace, "Zanje inda ake son magana dani mana". "Ni bana son magana dake?". Ta kalle shi sannan tace, "Eh mana sai share ni kake tunda muka tawo baka cemin komai ba shiyasa na k'yale ka".

Kallon ta yayi na wasu seconds kafin yace, "nida ke wa ya kamata ya fara yiwa wani magana? Na sakko amma ko kallo na bakiyi ba balle ki gaishe ni kuma kice na share ki,? Precious bazan tab'a iya share ki ba har na bar duniya, duk maganar da zata fito daga bakin ki kamar sinadarin da yake k'aramin k'arfin zuciya ne, kin sani ba lafiya ce dani ba ina daurewa ne cos bana son zaman asibiti amma har yanzu ban dawo dai-dai ba, u know kuma ban cika son magana ba dake kad'ai nake iya doguwar magana haka amma kice na share ki,? Is okay jeki" ya fad'a yana cika mata hannu ya jawo abincin da ta ajjiye masa yace, "tunda bai kai matsayin a yi serving d'ina ba let me serve my self" ya fad'a yana bud'e abincin har zai zuba sai yaga fura da nono sai ya fasa ci ya zuba furar da cofi ya fara sha.

Duk sai ya d'aure ta da jijiyoyin jikin ta, tabbas haka ne ita ya kamata ta fara gaishe shi koda bazai amsa ba tunda ko babu matsayin miji yayan tane kuma gashi bashi da lafiya, kallon sa tayi taga yana shan furar sa fuskar sa duk tayi wani iri sai taji mugun tausayin sa a ranta har ta bud'e baki zatayi magana taga ya d'aga hannu alamun tayi shiru ya nuna mata k'ofa, jiki a mace ta mik'e ta fita ya bita da kallo yana lumshe ido tare da sauke numfashi.

Haka ta koma can sukuku babu wani kuzari a tare da ita suka fara cin abinci dan daman wuya take ji taci abincin sosai kafin su cigaba da hira amma ita hankalin ta yana wajan sa, suna wannan zaman Hamma Ameer da Hamma Sagir suka dawo nan aka fara sabuwar hira cikin walwala har taso manta damuwar da take ciki, sallar la'asar ya tashe su aka je akayi sallah a lokacin gari ya rufe alamun hadari iska ta kad'awa mai dad'i babu rana ko kad'an, lokacin duka iyalan gidan suka dawo aka baje a wajan Hajiya nan akace Ibteesam ta kira Zaid.

A hankali ta k'arasa inda yake gaban ta na fad'uwa dan bata san a yanayin da yake ciki ba, yana tsaye yana kallon taga da alama yanayin yayi masa dad'i, kallon sa tayi ya canja kaya zuwa bak'in yadi mai shara-shara ya saka hula kalar aikin jikin yadin sosai yayi bala'in kyau kasancewar sa fari bak'in yadin ya haska shi over, "masha Allah Baby kaga yadda kayi kyau?" Ta fad'a ba tare da tasan ta fad'a ba tana kallon sa da murmushi.

Kallon ta yayi ya d'an yi murmushi kad'an yace, "aiko ki akayi ko?". D'aga kai tayi tace, "eh su Abba sun dawo ance kazo a gaisa." Girgiza kai yayi yace, "Nasan daman baza ki haka kawai ba sai da dalili, muje" ya fad'a yana barin jikin window d'in. Sai taji wani iri zatayi magana ya riga ficewa ta biyo bayan sa har cikin falon Hajiya.

Da sallama suka shiga suka amsa cikin sakin fuska suna kallon sa, har zai zauna a kan kujera sai kuma ya tuna maganar Daddy ya zauna a k'asa tare da fad'in, "Barkan ku da yamma" ya fad'a cikin sakin fuska kad'an yana kallon dan Daddy ya gargad'e akan irin gaisuwar da zai musu kenan, A tare suka amsa kafin Abba yace, "Ya ka baro mutanen gidan?". "Suna nan lafiya, suna gaishe ku" ya fad'a yana d'an kallon k'asa.

"Masha Allah, ya sunan sirikin namu?" Ya tambaya yana kallon sa da murmushi, Zaid ya amsa da fad'in, "Abdallah Abubakar" ya fad'a muryar sa a sanyaye a kamar koda yaushe, "Masha Allah, aiki fa malam Abdallah?" Abbie ya tambaya yana kallon sa, "zane-zane shine aiki na, ina zana samples kamar na takalimi etc company dake out of country suna zuwa su siya" ya fad'a a hankali yana d'an cize baki dan shi baya so a saka shi a gaba haka ana masa magana.

"Kai masha Allah wannan ai aiki ne mai kyauwun gaske, Allah ya taimaka Abdallah". Ya amsa da amin daga nan kuma sai aka fara hira shi kam duk hirar ta ishe shi ya k'agu ya bar wajan, duk da sun burge shi ganin yadda kowa yake bashi kulawa, a hankali manyan mazan suka fara barin wajan ko wanne yana yaba nutsuwar Zaid, samarin ne suma suka fita kafin su Ibteesam d'in ma su fita ganin hakan ya saka shi ya mik'e shima a lokacin aka fara kiran sa a waya, fitowa yayi daga falon yana d'aukar wayar yana magana a hankali, a kusa da Ameer da Sagir ya hango Ibteesam tana ta dariya? suna haka Ameer ya dungure mata kai ita kuma tana cigaba da dariyar ta, daina fahimtar abinda ake fad'a masa a wayar yayi ya tsaya cak yana kallon ta har da taji hakan a jikin ta ta kalli inda yake, suna had'a ido ya d'auke kai ya nufi inda yake matsayin d'akin sa, Fateema ta kalle shi ta kalli Ibteesam da ta tsayar da dariyar tace, "wai shi baya dariya ne?". Ibteesam tace, "haka fuskar sa take bashi da fara'a gaskiya a hakan ma fa wai ya saki fuskar sabida ku". Amina tace, "Naga alama ma ko magana ma bashi da ita sosai bashi kuma da saurin sabo". Ameer ya kalle shi ya kalle ta yace, "gaskiya k'anwa ta kinyi dacen miji mai kyau ga nutsuwa, irin wannan bazai baki kunya a gaban y'an mata ba sabida kamewar sa." Murmushi jin dad'i tayi ta kalli inda yake har ya b'ace ya shiga d'aki tace, "gaskiya dai ba kowa yake sakarwa fuska ba." "Shiyasa nace miki kinyi dace wallahi, yanzu kije ki kira shi ko zai zo a fita dashi yaga gari" Ameer ya sake fad'a yana kallon ta.

"Anya kuwa zashi?" Ta fad'a cikin tunani, "kije dai ki tambaya d'in" Fateema ta fad'a yana kallon ta, a hankali take tafiya har ta kai d'akin ta barsu a wajan suna jiran ta, da sallama ta shiga ta ganshi a zaune ya dafe kai da duka hannayen sa ya ajjiye hular a gefe sai gumi yake kamar babu a.c a falon ga kuma sanyi da garin yayi, zama tayi d'an nesa dashi tace, "lafiya dai ko?". Bai amsa mata ba bai kuma d'ago ba a yadda yake jin zuciyar sa in ya d'ago babu abinda zai hana ya make ta.

"Zaiddd" ta fad'a a hankali tana kallon sa, kamar wanda abu ya soka haka ya d'an gantsare ya koma dai-dai jin yadda ta kira sunan sa abinda bai tab'a ji tace ba, sosai yaji dad'in yadda ta kira shi sai yake ji kamar tafi kowa iya kiran sunan sa duk da ransa a b'ace yake, "ina magana kayi shiru" ta sake fad'a a sanyaye.

Hannun sa ya janye xaga fuskar sa ya juyo ya zuba mata idanun sa da suka juye zuwa jar kala, zaro ido tayi gaban ta ya fad'i har ta dafe k'irji bata sani ba sabida yadda idon sa yayi ja take hango zallar b'acin rai a cikin su, "what?" Ya furta a d'an fusace yana kallon ta. Itama kallon sa tayi tace, "me yake damun ka haka?". Komawa jikin kujera yayi ya kwanta kana yace, "Waye wancan yake tab'a ki?". Kallon sa tayi da mamaki tace, "Yake tab'a ni kuma? A ina?". A fusace ya d'ago ya kalle ta sai da taji tsoro ganin yadda idon sa ya sake komawa gashi ya zaro su waje har wani ruwa ya tara a ciki yace, "tambaya ta kike ma? Okay baki sani ba kenan ko?."

A tsorace tace, "Ban gane abinda kake nufi bane?". Runtse ido yayi ya bud'e yace, "baza ki gane ba" ya fad'a yana mayar da kansa jikin kujerar, duk sai taji wani iri tana tunanin wanda ya tab'a ta har ya gani, tunowa tayi da Ameer ya dungure mata kai a lokacin da ya fito kuma tana da tabbacin ya gani sai tace, "He's my cousin brother kuma ba tab'a yi yayi ba tsokanar sa muke akan yace yana so a bashi Jidda shine yayi haka" ta fad'a murya a sanyaye tana kallon yanayin sa a tsorace, d'agowa yayi kawai yayi tagumi yana kallon ta yace, "ya tab'a miki kai kice bai tab'a ki ba precious? Sai yayi hugging d'inki sannan ya tab'a ki?" Ya fad'a kawai yana kallon ta da alama takaicin maganar ta yake.

"He's my cousin fa" ta fad'a muryar ta na d'an rawa, cikin fad'a yace, "He's is your biological brother? Or mijin kine,?" Ya fad'a mata yana zaro mata ido ciki fad'a, girgiza kai tayi alamun a'a tana sake sunkuyar da kanta, "cousin brother ba maharramin ki bane ba akan me zaki bari yana tab'a miki kai,? Bakya kishin kanki ne?" Ya sake fad'a kamar zai make ta, "in bakya yi ni ina yi ba kuma zanyi taking dis rubbish ba, ina da kishi akan abinda nake so ki kiyaye in ba haka ba zaki ga fushi na wanda baki tab'a gani" ya fad'a cikin kakkausar murya yana kallon ta.

Ta bud'e baki zatayi magana ya riga ta da fad'in, "don't say anything, tashi kije" ya fad'a idon sa a kulle ba tare da ya kalle ta ba, niyar magana ta kuma yi cikin tsawa yace, "get lost!" Ya fad'a cikin wata irin murya mai amo da ta kusa haukata Ibteesam ta mik'e da sauri kamar zata kifa a tsorace ta fita.

*na yau da gobe ne eyeee*>??>?t?

*?ASAITAR SO!*

*74_75*

Not edited >?u?



A firgice ta fito ta kalli inda suke tsaye suna jiran ta ganin basu ganta ba ya saka ta daidaita nutsuwar ta duk da bata cikin hayyacin ta ta fara takawa inda suke tsaye, tana isowa suka kalle ta sukace, "Yana ina d'in?".

D'an yatsine fuska tayi kad'an tace, "baya jin dad'i yace bazai iya fita" ta samu kanta da zuba musu k'arya dan bata san me zatace, "Ayya Allah ya bada lafiya, muje ko" Ameer ya fad'a yana d'an yin gaba, tsayaww tayi tare da fad'in, "kuje kawai zan zauna wajan Hajiya". Suka juyo a tare Fateema tace, "Sabida me?". "Kawai" ta fad'a tana niyar juyawa. Basu ce komai ba kawai suka shiga mota suka fita.

Kallon k'ofar tayi kamar zata shiga sai kuma ta fasa ta nufi b'angaren Hajiya, a zaune ta same ta ita kad'ai tana jan carbi kamar koda yaushe ta zauna a gefen ta tana fad'in, "Hajiya me ake rok'o mana ne?". Hajiya ta kalle ta tayi murmushi tace, "Gamawa da duniya lafiya, baki bisu ba?". D'an yatsine fuska tayi tace, "Bana son fitar ne shiyasa". "Kodai mijin kine ya hana ki?" Hajiya ta fad'a cikin wasa. Ibteesam tace, "A'a kawai bana so naje ne yau." Hajiya tace, "to sai kije ki taya mijin naki hira ai". Ibteesam ta shagwa6e fuska tace, "Ni wajan ki nake son zama". Ta rik'e baki tana fad'in, "Kaji min jari'ar yarinya, kamar ba jinin Amina ba wacce tasha nonon Safiyya? Tunda suke da mahaifin ki bai tab'a cemin ga abinda sukayi masa mara dad'i ba kullum cikin kyautata masa suke amma ke tun ba'a je ko ina ba har kin fara haka,? Maza maza tashi kije ki taya shi hira mayi tamu anjima".

Dole Ibteesam ta mik'e? ta fita tana tunanin yadda zata tunkare shi sabida tasan a yadda ta barshi, a inda ta barshi a nan ta same shi sai dai yanzu idon sa a b'ude yake yana kallon sama ba kamar d'azu ba, tana zama a kusa dashi sai kawai ta fashe da kuka tana fad'in, "kayi hak'uri ka daina fushi dani kaji" ta fad'a cikin kuka tana kallon sa hawaye na bin fuskar ta, fuskar sa a cunkushe ya kalle ta yana jin kukan ta har kansa ya mayar da idon sa ya kulle baice komai ba, ganin hakan ya saka ta k'ara sautin kukan ta ta kwantar da kanta a k'irjin sa tana kukan, runtse ido yayi tare ds sauke ajiyar zuciya ya sani bazai tab'a iya fushi da ita ba kawai dauriya yake amma badan yana jin dad'in hakan ba, hannu ya saka yana bubbuga bayan ta a hankali kafin yace, "is okay ya wuce, ki daina wannan kukan". Sake shiga jikin sa tayi tana kuma fashewa da sbon kuka.

"Ya Allah! Nace miki ya wuce ki daina pls" ya fad'a yana d'ago fuskar ta, tsayar da hawayen tayi tana kallon k'asa ta turo baki gaba, kallon bakin nata yayi ya lumshe ido ya bud'e su a kanta yace, "Kina bawa zuciyar Zaid wahala ban san me zan miki wanda zai tabbatar miki da ina son ki ba Precious" ya fad'a yana share mata hawaye da hannun sa. "To ba kaine kak'i kula ni ba tun safe" ta fad'a a shagwa6e tana niyar sake zubo da wani hawayen, "kar kiyi kuka pls, I'm sorry kinji?".

D'aga masa kai tayi kafin yace, "Precious ina da kishi sosai, ina kishin ki yife da komai a duniya, nasan y'an uwan kine ba kuma zan hana ki mu'amala dasu ba amma ki san wacce zakiyi sabida ni, wallahi d'azu ji nayi kamar an saka wuk'a aka soka min a zuciya ta sabida kishin ki, in kika cigaba da haka wata rana zaki zo ki tarar da gawa ta na mutu" ya k'arasa fad'a a sanyaye yana kallon idon ta. Wani dad'i ne ya lullube ta a rayuwar ta tana so taga ana nuna zallar kishin ta haka sai ta jita a sama kanta ya fashe sabida murna, "I'm sorry bazan sake ba insha Allah, ka yafe min" ta fad'a tana kallon sa cikin karyar da murya.

Murmushi yayi kad'an yayi kissing d'in lips dinta kad'an kafin ya d'ago yana kallon fuskar ta, "dawa kukayi waya d'azu a Kano lokacin da zamu Airport?". Had'e fuskar su yayi kafin yace, "She's my secteria" ya fad'a yana goga hancin sa a kan nata, "shine take maka magana tana iyayi? Nidai gaskiya gwara ka canja zuwa namiji" ta fad'a tana turo masa baki kamar tayi kuka. Kallon fuskar ta yayi kafin yace, "Why zan canja?". "Because I'm jealous".

Sakin fuskar ta yayi har lokacin yana kallon ta yace, "kamar kin san she's my ex". Dafe k'irji tayi tare da zaro ido waje tace, "what?". Shima zaro nasa idon yayi da har lokacin suke jajaye yace, "yeah". Baiyi tsanmani ba kawai yaga ta fara kuka sosai, sai kuwa ya rud'e ya gigice ya jawo ta jikin sa yana fad'in, "I'm joking my precious, ki daina kuka wasa nake miki i swear" ya fad'a bayan ya kwantar da ita a jikin sa. D'ago fuskar ta tayi tace, "Really?". Yace, "of course, I'm sorry bazan sake ba" ya fad'a yana kama kunnen sa.

"Nidai a canja ta daga inda kake ta daina maka waya tana iyayi" ta kuma fad'a tana niyar sake sabon kuka, "is okay za'a canja ta, but u have to know babu wata mace da tayi saura a duniya da zata burge Abdallah in ba precious ba, bana tunanin zan so wata d'iya mace kamar yadda nake son ki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login