Showing 126001 words to 129000 words out of 171073 words

Chapter 43 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7812

need events, babu abinda za'ayi". Da mamaki Mummy tace, "kana nufin haka zaku tare babu events?". D'aga kai yayi kana yace, "yess ni bana da ra'ayin hakan."

Daddy yace, "amma abokan ka babu wanda yasan kayi aure yana dakyau ayi ko walima ce kowa yasan Zaid d'in Daddy ya girma" Daddy ya k'arasa fad'a da murmushin farin ciki a fuskar sa ganin yadda d'an nasa ya ware lokaci d'aya kamar bashi ne yayi kwanaki a sume ba, d'an murmushi yayi kad'an yace, "Wannan reason d'in ya saka nace bana so, Daddy she's my wife, bana son ayi wani walima wani ya ganta har yace tayi kyau, I'm jealous about dis". Sakin baki kawai su Daddy sukayi suna kallon ikon Allah shi kuwa daga zuciyar sa maganar take fitowa, dan shi ba lusari bane da zai bar matar sa wasu banzaye suna kallon ta ba,Mummy tace, "Amma ita kuma friends d'in ta fa? Ai yana dakyau ace sun zo shagalin bikin ta tunda ba bazawara bace ba."

Yatsine fuska alamun ya gaji yayi ya kalli Mummy cikin k'osawa yace, "sazo suna in ta haihu". Girgiza kai kawai Mummy take tana mamakin rashin kunyar Zaid, wato sazo in ta haihu, "in ita tana da ra'ayin events d'in fa?" Daddy ya tambaye shi. "Oh Dad kuna son maimaita abu guda wallahi, abinda nake so shi take so nida ita abu d'aya ne so babu banbancin ra'ayi? a nan" ya fad'a yana kallon Daddy dan shi ya gaji da maganar ma wallahi.

"A'a ban amince ba in dai tana so dole ayi ko baka so" Daddy ya sake bashi amsa, shiru kawai yayi baice komai ba yana kallon wani wajan daban dan ahi a ganin sa an takura masa ne, Anty Amina murmushi kawai take yi tana kallon su da burgewa dan har cikin ranta tana jin dad'in kasancewar Zaid a matsayin mijin Ibteesam sabida tafi kowa sanin bashi da halin banza, Ibteesam ita kam duka kunyar su take ji tunda ta sauke kai k'asa ta kasa d'agowa tana jin barin zancen da Zaid yake yi amma ta lura shi ko a jikin sa.

"Precious ki d'ago kanki kar wuyan ki yayi ciwo" ya fad'a yana kallon ta, ai kuwa sai ta sake sauke kanta k'asa tana kulle fuskar ta da hannun ta, Daddy ya girgiza kai yace, "An fad'a maka ita irin kace mara kunya." Ya kalli Daddy ya kalli Mummy ya kalli Anty Amina yace, "Wa zanji kunya a nan? Itama gulma ce" Ya Fad'a yana tab'e bakin sa. Murmushi kawai Daddy yayi yace, "Shikenan ku tashi kuje, sai ka siyi ticket d'in Gomben, amma ka aske wannan gashin kan naka a kuma rage sajen yayi yawa."

Kamar jira kuwa yake ya mik'e tare da mik'a mata hannu alamun ta bashi hannun ta, ina ma k'asa ta tsage ta shige ciki haka take ji a lokacin sabida abinda Zaid yake mata ba k'aramar kunya yake bata ba, su kansu mutanen falon kallon sa kawai suke cikin mamakin k'arfin hali irin nasa,ganin tak'i ta mik'o masa hannun ya kama shoulders d'in ta ya mik'ar da ita tsaye ya rik'e hannun ta yana fad'in, "I don't like dis kind of gossiping wallahi" ya fad'a yana jan hannun ta suka yi cikin gidan.

Da kallo Mummy ta bisu tana dariya tace, "Amina aiki ya same ki" ta fad'a tana dariya sosai. Dariyar itama tayi kad'an bata ce komai ba dan in tace zatayi siriki da Zaid tabbas itace zata sha wahala bashi ba, Daddy ma dariyar yayi ya mik'e ya fita dan ana jiran sa, Mummy ta mayar da hankalin ta ga Anty Amina tace, "ya kike ganin za'ayi dan dai bazan bar masa Ibteesam a hannun sa har su tare ba dole ya daina ganin ta". Anty Amina tayi dariya tace, "Wannan ai aikin kune dan ma Umma nata ta tafi." "Da sun dawo daga Gomben zan b'oye ta bazai sake ganin ta sai zasu tare d'in."

Murmushi Anty Amina tayi tace, "Duk yadda kukayi". Itama murmushin tayi suka cigaba da hira cikin nishad'i.

Tunda suka hau saman ya kasa cewa komai sai kallon ta da yake yi fuskar sa a sake, tallafar hab'ar sa yayi ya sake zuba mata ido ko kiftawa bayayi, turo baki gaba tayi ganin irin kallon kurillar da yake msta tace, "Nifa bana son wannan kallon ka daina". Sai da ya lumshe ido ya bud'e sannan yace, "Ni kuma ina so". Kusa da ita ya dawo ya kama hannun ta ya rik'e gam ya d'urkusa guiwowin sa a k'asa ya kalli cikin idon ta yace, "For the third time, do u love me precious?" Ya fad'a cikin wata murya da take so special wacce bai san yaya take ba.

D'aga masa kai tayi alamun eh, ya girgiza mata kai yace, "kiyi magana pls". Kallon sa tayi ta mayar da idon sa k'asa tace, "I love you". Dab'as ya zauna a wajan yana rik'e da hannun ta har lokacin yace, "Repeat it again please". Kallon cikin idon sa tayi da ya tara wani irin ruwa mai haske yana wani narai-narai ta cilla nata idon cikin nasa duk da abinda yake fuzgar ta akan hakan tace, "i love you so much my Husband".

Lumshe ido yayi jikin sa yayi wani irin bala'in sanyi yana ji kamar ana tsintsinka kuzarin? jikin sa haka yake ji, mik'ewa tsaye yayi ya mik'ar da ita ya rungume ta tsam a jikin sa jikin sa har rawa yake, "just call me baby" ya fad'a cikin wata irin murya mai dad'in fad'a gumi yakiji yana keto masa? ya sake rik'e ta tsam kamar zai b'alla mata k'ashin bayan ta, d'ago ta yayi daga jikin sa ya fara blowing kisses a ko ina a fuskar ta da wuyan ta kamar wanda ya zauce haka yake yi, ai kafin tace wani ya cilla bakin sa cikin nata yana kissing d'inta gently,? lumshe ido tayi tana jin sabon yanayin da yake kawo mata ziyara dan babu k'arya tana enjoying abinda yake yi.

K'afar suce ta gagara d'aukar su ya fad'a kan gado ya jawo ta jikin sa ya zaunar da ita a cinyar sa har lokacin bai bar abinda yake yi ba, yanayin jikin ta taji yana canjawa zuwa wanda b'ata tab'a tsintar kanta a ciki ba sai a lokacin, tun daga kanta har legs thumbs d'in ta take jin wani abu kamar zare yana bin jikin ta, sai da ya kwashe sama da minti biyar a haka kafin ya zame bakin sa idon sa a kulle yana lumshe ya koma da baya ya kwanta a kan gadon yana numfarfashi, jawo ta yayi ya kwantar da ita a k'irjin sa ta saka kunnen ta a dai-dai inda zuciyar sa take, yadda take jin zuciyar sa na bugawa sai abin ya kuma saka ta a cikin sabon yanayi mai wuyar fad'a, mik'ewa tayi tana kallon fuskar sa tana lumshe ido tana sake bud'e su a kan fuskar sa, shima bud'e idon yayi tayi saurin janye nata ganin yadda suka canja kala suka koma ja kamar ba farare wands ta gama kallon cikin su d'azu ba, mik'ewa zaune yayi ya jawo fuskar sa ya had'e da tata hancin su na gogur na juna yana lumshe ido, "i love you soo much Precious kece bugun zuciya ta".

"I love you more my dear Baby" ta fad'a itama idon ta a lumshe kamar nasa, "can i?" Ya fad'a muryar sa a can k'asan mak'oshi, tace, "What?". "Just romance pls" ya fad'a yana sake goga hancin sa a kan nata "Allow me pls" ya fad'a yana zura hannun sa bayan ta, zip d'in rigar ta ya sauke k'asa ta bud'e gabad'aya rigar ta gaba ya sauka k'asa, "Oh god" ya furta lokacin da rigar tayi k'asa ya sake shiga sabon yanayi.

Dukkan su sun rud'e cikin k'aramin lokaci duk sun fita a hankalin su zaman kansa gagarar su yayi har sai da ta kaisu ga kwanciya, jikin Zaid rawa yake sosai yana yamutsa ta ta ko wanne b'angare yana fad'a mata kalaman da suke sake antaya ta cikin chakwakiyar k'aunar sa, kiran sallar da ya fasa ta tagar d'akin ya shigo har cikin d'akin ya ratsa kwakwalwar su ita kuna ta turowa kunnen su, tsayawa yayi da abinda yake yi ya rik'e ta gam gam yana sauke numfashi da sauri da sauri, almost 10mints suka d'auka suna sauke numfashi kafin su dawo hankalin su, da sauri ta mik'e daga jikin sa ta kifa kanta a guiwowin ta tana jin wata irin kunya mai muguwar nauyi tana bin jikin ta.

Mik'ewa zaunen yayi shima yana murmushi sosai kafin ya kifa fuskar sa a bayan ta da yake bud'e ya fara goga fuskar sa a bayan ta yana lumshe ido yace, "babu wata kunya gulma ce bayan kin gama enjoying hot romancing zaki wani kulle fuska".? Sake k'asa tayi da kanta tana murmushi bata san lokacin da tace, "ashe baka da kunya?". Sai ta bashi dariya ya fara dariya sosai kamar bashi ba, d'ago kai tayi ta shagala da kallon sa ganin yadda yake dariya sosai har da kwanciya kamar ba Zaid d'in da ta sani ba, ko dariyar tarko ya d'ana mata tabbas tarkon ya kamo ta sosai dan ta fita a hankalin ta ta shagala da kallon kyakykyawar fuskar da da take dariya cikin annuri da walwala.

Sai da ya gaji dan kansa kana ya tsagaita dariyar yana kallon ta da alama bata san ma ya tsaya da dariyar ba tayi nisa wajan kallon sa, gira d'aya ya d'aga mata yana rausayar da kai yana kallon cikin idon ta, "dama kana dariya haka?" Ta fad'a har lokacin tana kallon sa. Mayar da fuskar sa yayi kamar koda yaushe kadaran kadahan yace, "In ina tare dake precious meye bazan yi ba". "Amma dariya tana yi maka kyau, ka dinga yi." Hancin ta ya lakuce yace, "zanyi amma fa just for u only, mema kika ce ashe bani da kunya ko,? Precious ban san wani abu kunya ba bamu had'a hanya va ko mafarki, make sure kema ki anjiye ta a wajan Mummy before kizo gida na, dan sai kin koma mara kunya kamar Zaid d'in ki".

"Nidai bazan iya komawa ba" ta fad'a tana turo baki.
"Really?". Ta bashi amsa da, "Yes". "Ni kuma nace zaki koma, mu zuba?" ya fad'a yana mik'a mata hannu alamun su k'ulla, itama hannu ta mik'a masa suka k'ulla yace, "Zan baki mamaki, Precious na tabbata wata rana da kanki zaki ce Baby Wanka zaka yi min" ya fad'a yana kashe mata ido d'aya, runtse idon ta tayi sosai ta d'ora hannun ta akan fuskar ta, tab'e baki yayi yana d'an murmushi kad'an, tayar da sallah suka ji anyi a masallaci dole ya mik'e yace, "Ki fad'i gaskiya sai kinyi wanka zakiyi sallah? Dan naga u enjoyed it better than me". Sai kuwa ta mik'e a guje ta fita daga d'akin bata jira ta kulle zip d'in bama, murmushi yayi mai sauti yana jin zuciyar sa wasai kamar an wanke masa ita da ruwa babu sauran daud'a a tare da ita ya shiga band'aki. Sai da ta gyara rigar sannan ta sauka k'asa Allah ya taimake ta babu kowa a falon ta fad'a d'aki a guje.

Bata sake bari sun had'u ba har dare shima lokacin ta fito cin abinci ne yazo wucewa ta wajan dining room d'in ya ganta a tsaye tana ajjiye abinci a kan dining d'in, har ya gota ta ya dawo ya kama k'ugu yana kallon ta yace, "kin gama b'uyar?". Kallon fuskar sa tayi sai taga ya rage gashin ba kamar da safe ba wannan zanen na kansa ya cike babu shi sai yayi kyau zatin kyaun sa ya fito sosai, d'auke kai tayi bata ce komai ba tana niyar wucewa ta koma kitchen, hanya ya tare mata fuskar sa babu? walwala yace, "Ina miki magana kinyi shiru, zamuyi fad'a dake a kan hakan". Cikin shagwa6a tace, "to me zance maka?". "Hakan ma da kika ce is okay" ya fad'a yana zagayowa ta bayan ta ya rugume ta suna kallon mudubin jikin counsell, sosai taga fuskar sa tayi kyau a mudubin har haske ya k'ara sabida zaman asibiti ga rama, "ka cika ni Mama zata iya fitowa fa ko Daddy" ta fad'a cikin yanayin tsoro tana k'okarin cinfike jikin ta.

Sake rik'e ta yayi sosai har lokaci? fuskar sa ba'a sake take ba yace, "So what in sun fito? Sun san ai ke matata ce." "Eh na sani amma dai ina jin kunya dan Allah ka sake ni?". "Saki! Kar na sake ji kince na sake ki sai dai kice na cika miki jiki ko na sakar miki jiki but not saki only kinji ko?". "Eh naji, to sakar min jiki na dan Allah". Kwantar da kansa yayi a kan kafad'ar ta yace, "who told you jiki kine? Bayan abinda na sani a jikin naki koke baki sani ba, kinga nawa ne kenan."

"Na shiga uku, nidai ka cika ni dan Allah" ta fad'a kamar tayi kuka tana k'okarin kwace kanta amma ya sake rik'e ta gam, "nida abuna kice na cika? Baki isa ba sai naga dama dan kaina". Zatayi magana yace, "Shiiiiii bana son yawan magana pls" ya fad'a yana lumshe ido yana sake kama k'ugun ta sosai. Motsin da ta jiyo ne ya saka ta sake tsorota kamar tayi kuka ta kalle shi ta mudubin taga idon sa lumshe ya kwantar da kansa a kafad'ar ta kamar mai bacci, "Ibteesam baki gama jera....." Maganar Anty Amina ta mak'ale lokacin da ta fito ganin abinda yake wakana a wajan, komawa da baya tayi Ibteesam kuwa kamar tayi kuka sabida takaici ta daddage ta ja jikin ta amma ko gezau baiyi ba sai ma sake rik'e ta Da yayi, mamaki ya saka take kallon sa ganin ko k'okarin sakin ta baiyi ba bayan tana da tabbacin yaji shigowar Mama kuma yaji maganar ta amma baiyi wani yunk'uri na sakin ta ba, Anty Amina da ta koma ciki sai kawai ta samu kanta da fashewa da dariya sosai, tana cikin dariyar Daddy ya shigo ta k'ofar kitchen ya k'araso falon da yake jiyo dariyar Amina haka, kallon ta yayi da mamaki yace, "Hala wani abun farin cikin ne ya samu ko?". Tsagaita dariyar tayi tace, "Babu komai." "Kuma kike wannan dariyar haka?". Dariyar ta kuma yi kad'an tace, "Eh". Daddy yace, "Ai shikenan" ya fad'a yana bud'e k'ofar da zata sada shi da babban falon, cak shima ya tsaya ganin su a tsaye a wajan Ibteesam ta runtse idon ta, jin motsin bud'e k'ofa ya saka ta bud'e ido da sauri ganin Daddy ya saka ta sake jin sabuwar kunya ta mayar da idon ta ta kulle tana jin yadda hawaye suka taru a idon ta, Zaid da shima yaji motsin sai ya bud'e ido suma had'a ido da Daddy sai ya d'auke idon sa yayi kissing d'in neck d'in ta ya sake ta ya hau sama.

Ai a guje ta kwasa ta fita daga falon ko waiwaye batayi, Daddy ya kalli Amina da take bayan sa tana dariya yace, "Wai daman abinda kika gani kenan kike dariya?". Ta d'aga masa kai alamun eh, murmushi yayi yace, "Tab ai indai ba bashi matar sa akayi suka bar gidan nan ba kin ta ganin irin haka kenan, Zaid ne fa" ya fad'a yana k'arasowa falon tare da zama a kan kujerar dining d'in. Anty Amina tayi y'ar dariya kad'an tace, "Ai naga alamar hakan a tare dashi. " Daddy yace, "kuma shi a tunanin sa dai-dai yake yi tunda ba kunya ce dashi ba."? Anty Amina bata ce komai ba ta fara zuba masa abinci.

Har suka kusa cinyewa Ibteesam bata dawo ba tana can bakin k'ofa? sai sauke numfashi take jin shiru bata jin motsin su ya saka ta dawowa kamar munafuka, a zaune ta tarar dasu har lokacin ta juya zata koma Dadd yace, "Zo kici abinci daughter".

Sum-sum ta dawo kanta a k'asa taja kujera ta zauna ta zuba abincin badan zata iya ci ba, bata jima da zama ba a hankali ya sakko yana waya har zai wuce sai kuma ya dawo ya kashe wayar tare da zama a kujerar da take kallon ta Ibteesam, da mamaki Daddy yake kallon sa kafin yace, "ikon Allah, yau Zaid ne a dining?". D'an rausayar da kai yayi yace, "A bani abincin." Anty Amina taja plate da niyar zuba masa ya d'an kalle ta kad'an yace, "No ba aikin ki bane, ki barta ta zuba ta min" ya fad'a a shagwa6e yana cigaba da danna wayar sa.

Kallon ta Anty Amina tayi hakan ya saka ta jawo plate ta bud'e abincin ta zuba masa ta tura masa gaban sa, spoon ya d'auka ya fara cagula abincin yana kallon ta ta k'asan ido, Daddy da ya cika da farin cikin ganin gudan jinin sa yana walwala har ya zauna a kan dining ana cin abinci dashi abinda bai tab'a yi ba kenan tunda Amina tazo gidan yace, "Zaid tunda ka samu lafiya gobe kafin ka wuce kaje gidan Yaya Babba kayi musu gaisuwa matar sa fa ta rasu". Bai kalli Daddy ba yace, "Allah ya jik'an ta" ya fad'a yana kai spoon d'aya na abincin bakin sa.

"Amin, kaje dai kayi musu gaisuwa accident suka samu dan yanzu ma haka Yaya Babba yana Egypt ana duba k'afar sa" Daddy ya sake fad'a yana kallon Zaid d'in, "kaine ka kaishi Egypt d'in?" Zaid ya fad'a yana kallon Daddyn. Daddy yace, "uhum, amma meyasa ka tambaya ma?". Zaid yace, "Nasan halin wannan yayan naka ai da son kud'in tsiya bazai barshi ya kai kanki Cairo ba" ya fad'a hankalin sa a kwance yana cin abincin sa.

"Yayan nawa kake cewa yana da son kud'i?" Daddy ya fad'a yana rik'e hab'a, d'an d'agowa daga danna wayar yayi ya kalli Daddy yace, "nayi k'arya ne? Ai halin sane". Daddy yayi murmushi kad'an yace, "Kafin ta rasu tace a fad'a maka ka yafe mata tayi maka laifi da dama". Glass cup ya d'auka yasha lemon ciki kafin yace, "Na yafe". "Masha Allah, Allah yayi maka albarka kayi abinda ake so, yanzu dai kaje kayi musu gaisuwar". Yatsine fuska yayi yace, "please Dad nayi magana da yawa" ya fad'a yana d'an yatsine fuska

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login