Showing 63001 words to 66000 words out of 171073 words

Chapter 22 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7842

take gefen ka itace madam d'in tamu?" Ya fad'a cikin sigar tsokana.

Banza yayi masa kamar baiji me yace ba sai Daddy ne ya amsa da fad'in, "Dr jeka kayi aikin ka indai Zaid ne ba amsa zai baka ba". Itama Ibteesam mamaki take ya rik'e mata hannu amma yak'i ya kula ta kuma gashi yana ta magana abin sa, "Washhh" ya furta yana dafe k'irjin sa da hannu d'aya, "Sannu ciwon ne?" Daddy ya tambaya. "Zai daina yi masa ciwon sai a hankali amma, damuwa ce dole ya rage saka kansa silar da ya jawo masa ciwon ma dole ya nisance shi indai zai dinga saka shi a cikin yanayin baya in ba haka ba kuma za'a zo ana da an sani" Dr Auwal ya fad'a lokacin da yake fita daga d'akin.

D'akin yayi shiru babu mai magana a cikin su Daddy ya mayar da hankalin sa kan wayar sa haka ma Jidda Ibteesam ce a zaune cikin takura ta zubawa waje d'aya ido tana tunani, kenan daman Zaid yana da ciwon zuciya? Ganin ta da Khalid ya saka ciwon nasa ya tashi kenan,? Lallai ya zama dole na san abinda zanyi a kan hakan tun kafin na kashe dan mutane da ransa, ashe son da yake min har ya kai haka ban sani ba, maganar Zaid ta katse mata tunani lokacin da yake cewa, "Daddy gida nake so" ya fad'a a shagwa6e kamar zaiyi kuka hannun sa d'aya yana dafe da kansa, "to son baka ji abinda Dr ya fad'a bane ba?" Daddy ya tambaye shi yana mayar da hankalin sa kansa. "Daddy ina so na canja kayan nan sun dame ni sosai." "Sai dai na kira Antyn ka ta hau saman ka a d'auko maka kaya" ya fad'a yana niyar kiran wayar Amina, "Noo Dad sai dai in kai zaka je". "Banda abinka Zaid ina ni ina tafiya na barka a nan?".? Kawar da kai gefe yayi kana yace, "Hameed, ina waya ta?". Daddy ya d'auki wayar Zaid da take kusa dashi ya bawa Jidda ta mik'a masa, karb'a yayi ya bud'e ido ya kira wayar Hameed, shiru yayi alamun Hameed d'in magana yake masa kafin yace, "Kaje ka gida ka tawo min da kaya" yana gama fad'ar hakan ya datse kiran, Daddy ya kalle shi cikin tausayawa yace, "Zaid ya kamata kaci wani abun". "No Dad I'm okay" ya fad'a bayan ya kulle idon sa, "kana buk'atar abinci Zaid, ko tea ne kasha ko kasha fruits". Shiru yayi bai amsa ba sai dafe kansa da yayi, "Zaid" Daddy ya sake kiran sunan sa, "Pls Dad" ya fad'a cikin k'osawa.

Ibteesam da Jidda sudai suna kallon ikon Allah sunyi shiru kamar babu su a d'akin, "Jidda mu tafi ko?" Ibteesam ta fad'a tana mik'ewa tsaye har lokacin hannun sa yana cikin nata, Jidda ma mik'ewa tayi itama tace, "Daddy zamu tafi Allah ya k'ara lafiya". "Amin Jidda, bara Musa ya ajjiye ku a gida" Daddy ya fad'a yana kiran wayar Musa ya sanar dashi fitowar su Ibteesam d'in, Daddy ya kalli Zaid yace, "Zaid ka sakar mata hannu su tafi gida" sake damke hannun nata yayi a cikin nasa yace, "Daddy kace kada ta tafi" ya fad'a kamar mai shirin yin kuka, "meyasa baka so ta tafi?". "Tunda tazo na daina jin ciwo a cheat d'ina sosai, pls Dad beg her to stay with me" ya fad'a yana wani jan numfashi k'irjin sa na d'agawa.

"Tunda tazo baka kula ta bafa Abdallah kuma kake cewa ta zauna bayan ko magana baka yi mata ba?" Daddy ya bashi amsa yana kallon yanayin sa cikin tsoro da tashin hankali, amma hakan bazai saka ya takura y'ar mutane ba. "Daddy please kace ta zauna". Ibteesam ta kalli Jidda itama ita take kallo dukkan su sun rasa abinda zasu ce, "Ka sakar mata hannu anjima zata dawo yanzu Maman ta ke kiran ta" Daddy fad'a cikin sigar lallashi, "promise zata dawo?" Ya tambaya yana murza yatsun ta. Kallon ta Daddy yayi hakan ya saka tace, "Promise, i will come back insha Allah" ta fad'a muryar ta a sanyaye. A hankali ya sakar mata hannu suka fara tafiya da niyar fita daga d'akin bayan sun yiwa Daddy sallama, "Ibteesam" ya kira sunan ta da wata irin murya da ta kusa saka Ibteesam zubewa a wajan, "Na'am" ta fad'a tana juyowa tana kallon sa, "Byee" ya furta yana mayar da idon sa ya kulle tare da juyawa k'ofar baya, murmushi tayi kad'an ta fita daga d'akin.

A harabar asibitin suka ga Musan suka shiga motar suka tafi a lokacin Mummy ta bud'e k'ofar motar da suka zo da ita ta fito cikin tashin hankali suka nufi inda akace musu Zaid d'in yana kwance.

Da sallama Mummy ta shigo d'akin, amsawa Daddy yayi yana juyowa don ganin wacece, "Yaya Safiyya barka da zuwa" ya fad'a yana mik'ewa tsaye, "yauwa Daddyn Zaid, barka da rana". "Barka dai, Sannu da zuwa". K'arasawa inda Zaid yake tayi kana tace, "Yauwa, ya me jikin? Bamu jima da sauka ba muka je can gidan naku muna zuwa ake sanar damu rashin lafiyar tasa, badai ciwon sa bane ba ko?". Daddy ya d'an shiru kafin yace, "Eh ba ciwon sa bane, sannun ku lallai kun sha hanya".

"Zaid ya jikin?" Ta fad'a tana shafa kansa, "Mummy da sauk'i ai na warke". "Sannu Zaid Allah ya baka lafiya." "Yauwa yanzu da kika zo ki saka shi yaci wani abun yak'i cin komai" Daddy ya fad'a yana kallon Mummy, "Shikenan fad'uwa tazo dai-dai da zama na tawo masa da zob'o da meatpie, mun je masa dashi can gidan akace kuna nan, yanzu Zahra zata shigo dasu". Zahra ta bud'e kofar ta shigo hannun ta rik'e da leda mai d'an girma, suka gaisa da Daddy kafin ta k'arasa inda Zaid yake tace, "Sannu Yaya Zaid". Kai kawai ya d'aga mata.

"Kaga Zaid tashi kaci kar kace min A'a kasan bazan yadda ba." "Mummy baki na babu dad'i ban wanke ba kuma." "Ai baza'a rasa sabon brush da toothpaste a toilet ba tunda private hospital ne, Zahra shiga ki duba" ba musu Zahra ta shiga aka duba akwai, Mummy da kanta ta shiga ta d'auko ta dawo ta taimaka masa ya tashi ya k'arasa wajan sink d'in da ke d'akin ya wanke bakin nasa ta rik'o shi suka dawo ta fara bashi yana ci a hankali yana korawa da zob'o mara sanyi sosai, a haka har ya ci meatpie biyu ya sanye cup d'aya na zob'on.

Daddy dai yana kallon su cikin burgewa yana sake tabbatarwa a zuciyar sa tabbas Zaid rasa wanda zai kula dashi yana d'aya daga cikin abinda ya saka halayyar sa take baud'ewa.

A haka Hameed ya shigo ya kawo masa jallabiya mai k'aramin hannu da duk abinda yasan zai buk'ata, Ya shiga band'akin yayi wanka ya shirya ya fito fess dashi kamar bashi ba, Mummy na zaune kusa dashi da yace wash zata ce sannu, Sai a lokacin Daddy ya samu damar fita daga d'akin dan zuciyar sa da Mummy kawai ya amince ya bar Zaid.

Kusan 30mints sannan Daddy ya dawo da alama gida yaje ya dawo, Amina ce ta bud'e d'akin ta shigo da sallama a bakin ta, su Mummy suka amsa ba tare da Mummy ta kalle ta ba, "Sannu Zaid ya jikin?" Ta tambaya tana kallon sa. Kamar da dutse tayi magana dan ko motsi baiyi ba balle ta saka ran zai amsa mata, waje ta samu ta zauna ta kalli Mummy tace, "ina wuni". Sai a lokacin Mummy ta juyo suka had'a ido, gaban Mummy ya fad'i ta sake ware ido tana kallon fuskar Amina tana so ta tuna inda ta santa, "Lafiya lau" ta amsa a sanyeye tana kallon ta.

Daddy ne yace, "Amina Yaya Safiyya kenan yayar Maman Zaid, Yaya Safiyya ga Amina matata". Murmushi Mummy tayi sosai tace, "Allah sarki, ai da muka je gidan bamu ganta ba sai wata yarinya budurwa muka gani ita take sanar damu rashin lafiyar tasa, ai gwara da ka fad'a min da anyi abin kunya wata rana". Itama Amina murmushi kawai tayi tana ji kamar tasan Mummy a wani waje.

Daga haka d'akin yayi shiru babu mai magana kafin a kira wayar Daddy ya mik'e ya fita.

B'angaren bayan sun koma gida Jidda ta shiga d'aki ta sami Ibteesam tsaye tana d'auko abu a wardrobe tace, "Anty Ibteesam". "Na'am" ta fad'a ba tare da ta kalle ta ba, "Wai meyasa kika shiga damuwa ne akan rashin lafiyar Zaid daga jiya zuwa yau? Baki dawo dai-dai ba sai da kika je kika ganshi?."

Kallon Jidda tayi ta tsayar da abinda take yi tace, "Meyasa kika tambaya?". Zama Jidda tayi a kan gado tace, "Kawai ina so na sani ne, gani nayi ko breakfast kasa yi kikayi har sai da Abba yaje ya dawo yace muje tare sannan kika ware."

"Jidda ba dole na shiga damuwa ba, ta sanadi na fa ya shiga wannan halin da yake ciki" ta bata amsa tana cigaba da aikin ta, "Nikam sai nake gani kamar kin fara son sane" Jidda ta bata amsa kai tsaye. Juyowa tayi ta rufe wardrobe d'in ta dawo ta zauna akan stool d'in mudubi ta kalli Jidda tace, "Sam ba haka bane babu so a tsakani na dashi sai tausayi, Khalid shi nake so ba Zaid ba kin ji ko?". "Duk tausayin ne ya saka kika dinga k'arewa fuskar sa kallo a asibiti? Anty Ibteey anya.." Jidda ta fad'a tana sake fuskantar Ibteey din sosai.

"Jidda babu so tausayin sa kawai nake ji har ga Allah, yanzu da naji yana da ciwon zuciya ya sake bani tausayi matuk'a shiyasa nayi alqawarin komawa ma amma banda haka babu abinda zai saka na koma." "To ai shikenan, amma kam son da yake miki yafi wanda Khalid yake miki yawa, da nice ke da Zaid d'auka na bar Khalid badan yafi Khalid kyau da kud'i ba sai dan Zaid yafi Khalid k'aunar ki" ta fad'a tana mik'ewa tsaye.

Banza Ibteey tayi mata har ta fice daga d'akin, juyawa tayi tana kallon fuskar ta a mudubi tana tuno fuskar Zaid d'in, _ina jin wani iri a jiki na akan Zaid, ina jin tausayin sa sosai, amma ba hakan yana nufin ina son sa bane Khalid nake so, to amma meyasa yanzu nafi tunanin sa akan Khalid? Ai bashi da lafiya dole nafi tunanin sa,_ hira take da zuciyar ta dan bata son maganar Jidda ta zama gaskiya a kanta.

Shigowar Umma d'akin ya katse mata tunani ta kalli Ibteesam tace, "Ke kuma tunanin me kike yi haka?". Kallon Umma tayi tace, "Babu komai". "K'arfe nawa zaki koma asibitin?". "Sai zuwa bayan la'asar in Allah ya kaimu". Umma ta zauna akan bedside tace, "To me zaki siya ki tafi dashi na dubiya?". Turo baki tare tace, "Umma ni basai na kai komai ba zuwan ai yafi". "A'a baza ayi haka ba, in zaku tafi ki tsaya ku siyi fruits sai ku kai musu."

"Umma wai meyasa kuke damuwa da lamarin sa ne bayan ba alkhairi ne ya had'a mu ba,? Da sace ni ya fara ya kuma dinga duka na amma a yanzu sai naga kuna nuna damuwar ku a kansa sosai har bakwa nuna damuwar ku in naje inda yake kamar wani yaya na ko miji na" ta fad'a tana kallon Umma da itama ita take kallo. Murmushi Umma tayi ta Mik'e tsaye tace, "Ibteesam kenan, in zaku tafi ki d'auki kud'i zan ajjiye miki a cikin bedside sai kuyi siya, ni fita zamuyi yanzu nida Jafar wata k'ila mu biyo mu duba shi" tana gama fad'a mata haka ta fita daga d'akin Ibteesam ta bita da kallo.

A can d'akin Mama kuwa Asiya ce take kwance a cinyar ta take kuka sosai gefen ta yayar Rukayya da take zaune a kusa Mama, "ki daina kuka Asiya insha Allahu sai ya zama mijin ki bazan zuba ido komai ace Ibteesam ba." Share hawayen ta Asiya tayi tace, "Mama komai ace ita kina ganin lokacin da Ambassador yazo har ya santa fa baki ga kallon da Zaid d'in yake mata ba alamun sun san juna, wallahi Mama ina son sa sosai ban san meyasa Abba yafi son ta". Rukayya taja tsaki tace, "Dallah malama ki yiwa mutane shiru ba dole afi son ta ba bata fiki mutunci ba, waye baki raina a gidan nan ba,? Allah yasa bazai aure ki ba naga ta tsiya" ta fad'a tana mik'ewa ta shige d'aki.

"Kin gani ko Mama? Wacce muke ciki d'aya ma tafi son ta dani, nidai na shiga uku anya ni y'ar gidan nan ce?" Ta fad'a tana rushewa da kuka. "Kar na sake ji kin fad'i haka, ke y'ar gidan nan ce itace ma ba y'ar gidan ba". Mik'ewa tayi daga cinyar Maman ta kalle ta tace, "Mama Ibteesam ba y'ar gidan nan bace?". Dan diriricewa tayi alamun bata san tayi maganar ba tace, "Ina nufin in ma akwai wacce batayi kama da y'ar gidan nan ba ai itace, ki kwantar da hankali Asiya duk abinda kike so shi zan miki, tunda yaron nan kike so zan san yadda zanyi ki aure shi insha Allah, tashi kije kici abinci" mik'ewa tayi cikin farin ciki ta shiga kitchen.

Shiru Mama tayi tana tunanin ta yadda za'ayi ta raba auren Ibteesam da Zaid.

Bayan la'asar Ibteesam ta shirya cikin doguwar riga ta abaya mai fad'i kalar maroon ta yi rolling da mayafin abayar ta d'an zame shi baya bak'in gashin ta ya fito a gaban goshin ta kad'an, "Jidda tawo mu tafi mana" ta fad'a bayan ta d'auko kud'in da Umma tace ta d'auka, fitowa tayi cikin doguwar riga ta atampa tace, "Muje" kulle k'ofar sukayi sannan suka fito.

Titi suka fita akwai mai fruits a wajan sa ta siyi apple da banana suka fito kan titi dan su hau Napep, motar ce ta tsaya a gaban su aka sauke glass, "Kuzo na sauke ku" Khalid ya fad'a daga cikin motar yana kallon Ibteesam dan sosai shigar ta amshe ta, Jidda ta shiga baya Ibteesam ta shiga gaba suka fara tafiya, "Ina wuni" Jidda ta fad'a daga baya, "Lafiya lau Jidda ya gida dasu Umma?." "Suna nan lafiya lau" ta bashi amsa, "ina wuni" Ibteesam ta fad'a a hankali tana wasa da zaren jikin rigar ta fuskar ta a d'an had'e, "Lafiya lau love, ina zamu je?". "Nan al_ihsan hospital na cikin GRA" ta bashi amsa ba tare da ta kalle shi ba, "to waye babu lafiya?" Ya tambaya cikin kulawa.

Shiru tayi bata amsa ba sai Jidda ce tace, "Zaid ne". "Subahanallahi, wai Zaid dai da muka had'u jiya dashi?". "Eh shi" Jidda ta bashi amsa, "Ya salam, nima ya kamata na shiga na duba shi ko babu komai zan samu lada" ya fad'a yana satar kallon Ibteesam.

Sai a lokacin tace, "A'a basai ka shiga ba bana son wani abun ya kuma faruwa, yanzu sai yazo yana fad'a maka wata maganar mara d'adi tunda kai kaje inda yake gwara ka barshi kawai" ta fad'a dan bata so ya shiga Zaid ya gansu tare.

Murmushin jin dad'i yayi jin dan kar a fad'a masa magana mara dad'i ya saka tace kar ya shiga yace, "Babu komai zanje ai ni dubiya zanyi." Daga haka taja bakin ta tayi shiru basu kuma cewa komai ba har aka je asibitin, fad'uwar gaban ta ta tsananta lokacin da suke tunkarar d'akin ba tare da tasan dalilin hakan ba, Gab da zasu shiga d'akin Mummy ta fito da saurin ta ta wuce su Ibteesam ba tare da ta lura dasu ba tayi hanyar waje, a hankali suka murd'a handle d'in k'ofar suka shiga da sallama.

"Shikenan ma gata ta dawo" Daddy ya fad'a yana kallon Zaid da ya dame su da zancen Ibteesam, kallon k'ofar yayi ganin itace d'in ya saka ya kasa d'auke idon sa daga kan k'ofar yana kallon ta tana takowa a hankali, cak numfashi sa ya tsaya ganin wanda ya shigo d'akin da sallama, kallon Ibteesam yayi da kanta yake a sunkuye ya kalli Khalid sannan ya kalli Daddy da suke gaisawa da Khalid cikin mutunci da sakin fuska, "Dad!" Ya kira sunan sa da wata irin murya mai nuni da tsantsar rauni idon sa a kulle yace, "Kace su fita bana so na gansu" ya fad'a yana sake kulle idon sa sosai.

"Zaid Maryam ce fa" Daddy ya fad'a da mamaki yana kallon sa, "Dad su tafi bana so na gansu, su tafi...." sai kuma ya kasa k'arasawa ya fara wani irin numfashi kamar mai shak'uwa, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Zaid lafiya?" Daddy yayi kansa da sauri yana rik'e shi. Magana yake so yayi amma k'irjin sa yayi mugun rik'ewa sai juya kai da yake yi yana wani irin numfashi da yake fita dak'yar, hawayen wahala ne suke biyo gefen idon sa a yadda ya dage dole sai yayi magana shine ya sanya idon sa ya tara ruwa suke zubowa nunfashin nasa ya tsaya cakkk.




*Kar a fitar min da labari dan Allah.*
*?ASAITAR SO!*

*41_42*

Not edited>??




Jijjiga shi Daddy yake ganin kamar baya numfashi, "Zaid wake up" ya fad'a yana sake jijjiga shi, shigowar Dr ya saka Daddy ya bar wajan ya tsaya daga nesa yana kallon yadda ake k'okarin ganin an dawo masa da numfashin sa dai-dai, juyowa likitan da suka shigo tare da Dr Auwal yayi yace, "Alhaji ku d'an bamu waje kad'an". Dukkan su jiki a sanyaye suka fita, k'ememe Ibteesam tak'i barin inda take tsaye sai kuka da take hawaye na zuba a idon ta sosai, Dr ya kalle ta ya kalli Dr Auwal kawai suka cigaba da aikin su.

Bashi numfashi sukayi da gaggawa aka samu numfashin nasa ya dawo dai-dai, Dr Auwal ya kalli Ibteesam da take ta kuka yace, "Ki daina kuka an samu numfashi nasa ya dawo dai-dai zai warke insha Allah, zo ki zauna kusa dashi" ya fad'a yana bata kujerar dake kusa da gadon. A hankali ta taka taje ta zauna tana cigaba da kuka su suka suka fita suka bar ta a d'akin.

Da sauri Daddy ya k'araso inda suke yace, "Ya jikin nasa Dr?". "Alhaji akan issue d'in heart attack d'in sane, meye ya tayar masa da hankali a yanzu?". Shiru Daddy yayi ya juya dan ganin ko Khalid yana nan sai yaga wayam alamun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login