Showing 66001 words to 69000 words out of 171073 words

Chapter 23 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7811

ya tafi sai Jidda kawai da take tsaye, Daddy ya kalle su yace, "yanzu ya ake ciki ya dai?". "To numfashin nasa dai ya dawo dai-dai yanzu, a barshi ya huta zuwa anjima sabida baya son hayaniya ita matar tasa a bar ta a wajan sa" wanda suke tare da Dr Auwal ya fad'a dan ya d'auka Ibteesam matar Zaid ce.

Daddy baice komai ba ya koma ya zauna a inda aka tanada ya kalli Jidda da take tsaye yace, "Hauwa'u zo ki zauna ki bar tsayuwa haka". Ba musu tazo ta zauna a d'aya kujerar da take kusa da Daddy d'in, "Jidda wanda ya kawo ku yanzu shine Khalid?" Ya tambaya yana kallon ta. D'aga kai alamun eh, ajiyar zuciya yayi bai sake cewa komai ba dan ya san labarin Khalid a bakin Abban su Ibteesam d'in.

A d'akin kuwa Ibteesam tana? zaune kusa dashi tana ta aikin kuka bata san lokacin da ta saka hannun ta a cikin nasa ba yana murza yatsun hannun sa a hankali tana share hawaye, "Kayi hak'uri ka tashi bazan sake yin abinda baka so ba, na tuba ka yafe min bazan sake ba" ta fad'a cikin kuka tana kifa kanta a hannun sa hawayen ta yana zuba a fatar hannun sa. "Bazan kuma ba kayi hak'uri ka tashi" ta kuma fad'a dan jijjiga hannun sa har lokacin kanta yana kife a a hannun sa tana cigaba da kuka.

"Precious Ibteey!" Taji ya kira sunan ta cikin rauni da rawar murya, kana jin yadda maganar ta fita kasan bashi da lafiya numfashin sa kuma ba dai-dai yake ba, da sauri ta d'ago ido ta kalle shi shima kuma ita yake kallo idanun sa sun koma ja sosai jan har yafi na kullum, "Na'am" ta fad'a itama cikin murya irin ta wacce tasha kuka.

"Kina so na mutu ko?" Ya fad'a yana kallon cikin idon ta itama kuma idon ta yana cikin nasa, "A'aaaaaa" ta fad'a hawaye na sake zubowa daga idon ta, sai da ya sauke numfashi dak'yar yana runtse ido sabida yadda k'irjin sa ya amsa sosai yace, "Why kike yin abinda bana so,? Meyasa zaki d'auko shi kuzo tare,? Kin san ya nake ji a nan?" Ya fad'a yana jan hannun ta yana d'orawa a saitin zuciyar sa, so take ta janye hannun ta sabida yadda wajan yayi zafi duk da da riga a jikin sa amma hakan bai hana ta taji zafin da wajan yake fitarwa ba, sake danne hannun ta yayi a wajan tana jin yadda zuciyar sa na bugawa da k'arfi kamar zata fito waje sabida yadda take dukan k'irjin sa, "I'm sorry banyi da niya ba, nayi abinda baka so ne dan gudun abinda baka so d'in, kace na daina hawa napep shiyasa ban hau ba da yazo yace zai zo ya buda ka shine muka tawo tare badan na b'ata maka rai nayi ba sai dan nayi gudun hawa napep amma kayi hak'uri" ta fad'a tana sunkuyar da kai k'asa hawaye yana zuba a idon ta har lokacin.

"Meyasa baki kira ni na turo miki driver ya d'auko ki ba?" Ya fad'a yana cize baki sabida ciwon da k'irjin sa yake masa, "baka da lafiya shiyasa ban kira ka ba" ta sake fad'a muryar ta na rawa sosai, zuba mata ido kawai yayi hawayen na sakkowa daga idon ta wani na bin wani, hannu ya saka ya share mata hawayen fuskar ta yace, "Is okay, stop crying pls".

Bata daina kukan ba har lokacin yayi murmushi yace, "Ki daina kukan bana so" ya fad'a yana kallon, hannu ta saka tana share hawayen nata, kallon ta yake kamar ya rungume ta haka yake ji ya zuba mata ido kamar ya lashe ta sabida so da k'auna,? "smile pls" ya fad'a cikin wata irin murya da ta haddasa mata kasala har ta lumshe ido ba tare da ta sani ba, murmushi tayi tana sake yin k'asa da kanta dan sai a lokacin take jin nauyin abinda tayi, "cry cry baby" ya fad'a fuskar sa a sake.
Mik'ewa zaune yayi yana lumshe ido yace, "Washhh" ya fad'a yana dafa k'irjin sa da har lokacin yake masa zafi, "sorry" ta fad'a a hankali tana kallon sa da tausayawa.

"Ruwa" ya furta idon sa a kanta, kalle-kalle take ko zata ga ruwa nan ta hango katon d'in swan da ba'a bud'e ba tayi sauri ta fasa ta d'auko d'aya ta bud'e masa ta kawo masa inda yake, karb'ar ruwan yayi ya had'a da hannun ta ya jawo ta ta fad'a jikin sa ya mayar da hannun sa zagayo dashi a k'ugun ta ya rungume ta a k'irjin sa, lumshe ido yayi yana jin wani irin sanyi da farin jiki yana ratsa ko jikin sa, ya kasa tantance wanne kalar so yake yiwa Ibteesam, yana jin ta a ko ina na jikin sa, ko wacce jijiya ta jikin sa indai zata harba zata harba da soyayyar Ibteesam a ransa,b'angaren Ibteesam d'in ma hakan taji bugun zuciyar sa ya d'auki hankalin ta ta lumshe ido khamshin jikin sa yana shiga jikin ta sosai tana kuma sauraron yadda zuciyar sa take bugawa, idon sa a lumshe tana kwance a k'irjin sa ya fara hura mata iska daga kumatun ta zuwa bayan kunnen ta a hankali kafin yace, "i love you soo much and more, i don't wanna lose you in my whole life" ya fad'a yana mayar da hannun sa bayan ta ya rik'e ta gam-gam.

Su Ibteesam an shiga sabuwar duniya nan take ta kasa gane a wacce duniyar take dan ji take kamar an d'auke ta an kaita sama ana wayo da ita a sararin samayi, kamar wacce aka tunawa wani abu tayi saurin bud'e ido ta yanje jikin ta daga jikin sa, bai hana ta ba ya mayar da kansa ya kwanta idon sa har lokacin a kulle, inda take zaune ta koma ta ya kamo hannun ta ya rik'e gam dan ji yake kamar ya d'auke ta ya saka ta a cikin jikin sa rik'e mata hannu baya gamsar dashi.

Bud'e k'ofar da akayi bai saka ya sake ta ba sai ma sake rik'e ta da yayi yana lumshe idon sa, "Maryam ya farka?" Daddy ya fad'a a hankali yana kallon Ibteesam, kafin tayi magana yace, "Dad I'm awake" ya fad'a idon sa a kulle har lokacin.

"Ya jikin naka Zaid? Kana jin ciwon k'irjin?". "Na warke, Dad suzo su sallame ni I'm tired" ya fad'a yana dan yatsine fuska.

"Zasu sallame ka sai anjima" Daddy ya fad'a yana kallon sa, Jidda ta da ta shigo ta nemi waje ta zauna tana kallon Zaid tana mamakin so da kishin Ibteesam da yake yi.

Anty Amina da Eman ne suka shigo d'akin da sallama a bakin su aka amsa, Jidda ta gaida su Anty Amina ta amsa fuska a sake, juyowa Ibteesam tayi zata gaida Anty Amina suka had'a ido Anty Amina ta zuba mata ido tana kallon fuskar ta kamar tasan mai irin ta amma abin ya kwanta mata a rai, "Ina wuni". Ibteesam ta fad'a tana kallon Anty Amina, amsawa tayi cikin sakin fuska.

"Maryam ga Antyn Zaid Amina" Daddy ya fad'a yana nuna mata Amina, murmushi tayi tana sunkuyar da kanta k'asa, "Amina Maryam kenan wacce na baki labarin ta". D'an murmushi Anty Amina ta k'ak'alo tana kallon Ibteesam bata ce komai ba haka nan taji gaban ta na fad'uwa.

"Ni kuma Eman matar Zaid" ta katse musu tunani lokacin da tace haka tana jifan Ibteesam da wani kallo dan haka kawai take jin kishin Ibteesam a ranta, gaban Ibteesam ne yayi mummunar fad'uwa jin ta ambaci matar Zaid sai ta samu kanta da kallon Zaid d'in taga idon sa a kulle kamar yadda yake sai murza hannun ta da yake yi a hankali, ta kalli Daddy ko zata ji ya k'aryata amma sai taji shiru baice komai ba, "Sannun ki" Ibteesam ta fad'a dak'yar tana jin wani irin zafi a ranta wanda bata san dalilin sa ba, Zaid yana jin su bai amsa ba dan in ya bud'e ido tsaf zai iya shak'e wuyan Eman shiyasa ya mayar da idon sa ya kulle.

Duk sai jikin Ibteesam ya saki ta rasa me yake damun ta lokaci d'aya asibitin ya fice mata a rai ta saka d'aya hannun nata ta b'amb'are hannun ta daga cikin nasa tare da mik'awa tsaye tace, "Daddy zamu tafi magariba ta kusa" ta fad'a bayan ta baro inda Zaid yake, "ku jira Musa ya dawo ya kai ku" Daddy ya fad'a cikin kulawa. Baza ta iya yiwa Daddy musu ba dole ta koma ta zauna nesa dashi tana jin kanta duk a takure.

"Meyasa kike so ki tafi ki barni?" Ya fad'a idon sa a kulle, banza tayi masa dan har ga Allah lokaci d'aya taji tana jin haushin sa sosai ba tare da ta san dalilin hakan ba, "Daddy kaji tayi min shiru ko?" Ya fad'a a shagwa6e yana daga kwancen. "To Zaid me zata ce maka? Wannan tsakanin ku ne babu ruwa na". Knocking d'in k'ofar akayi tare da shigowa, Musa ne ya shigo ya bawa Daddy sak'o Ibteesam da Jidda sukayi masa sallama suka tafi ba tare da ta sake kallon inda Zaid yake ba.

Shigowar likitan d'azu ya saka su Daddy suka kalle shi ya kalli inda Ibteesam take yaga bata nan yace, "Alhaji zamu bashi sallama yanzu yaji sauk'i, amma tsakanin shi da matar sa akwai k'auna sosai dan tunda tazo inda yake a d'azu bugun zuciyar sa ya fara dai-dai, i swear ban? tab'a ganin soyayya irin wannan a gaske ba dan haka ta daina yin nisa dashi a yanzu duk inda yake ta kasance a kusa dashi ciwon nasa zai zo da sauk'i insha Allah" ya fad'a yana mik'awa Daddy takardar sallamar ya k'arasa inda Zaid yake ya had'a allura yayi masa a jijiya kana ya fita daga d'akin.

Tunda Dr ya gama bayani Daddy yake murmushin farin ciki yana ji a jikin sa lokacin da za'a bayyanawa Zaid Ibteesam matar sace ya kusa, lokacin da wacce zata saita masa Zaid yazo ya kusa, farin ciki sosai Daddy yayi da kalaman Dr sab'anin Amina da Eman da suke kallon sa da mamakin gaske.

"U see Daddy, na Fad'a maka bana so tayi nisa dani ina jin wani iri amma ka barta ta tafi" ya fad'a yana dafe k'irjin sa da yake masa zafi sosai.? "Kar ka damu ta kusa dawowa inda kake ma gabad'aya, yanzu zaka iya tashi ko na taimaka maka?". "I can" ya fad'a yana mik'ewa dak'yar ya tsaya a tsaye cikin sa na wani irin kamar an d'aure masa haka k'irjin sa yayi masa nauyi sosai, Amina kuwa mamaki take kawai take ganin yadda ya warke kamar bashi a sume d'azu ba, k'wafa tayi tana girgiza kai tana tunanin ya kamata su canja plan.

A haka su Hameed tare dasu Wizzy suka zo aka tattara aka tafi gida.


******

A b'angaren gidan Mummy bayan magariba Abban su Zahra ya dawo bayan ya ci abinci ya huta take ce masa, "Nikam yau naga wata a asibiti wallahi kamar na santa amma na rasa a inda na santa" ta fad'a cikin mamaki da al'ajabi.

"Too a ina kika santa?" Ya tambaya yana kallon ta, "to ai shine na rasa, amma wallahi na santa duk da ita batai min kallon sani kamar yadda nayi mata ba." Yayi murmushi yace, "To ita d'in wacece?". "Matar Daddyn Zaid ce fa, kuma ni dai nasan yayi aure amma ban san matar sa ba balle nace a gidan na santa kuma kasan na jima rabo na da garin nan sai dai shi Zaid d'in yaje" ta bashi amsa tana canja cannel d'in tv.

"Wata k'ila a wani wajan kika santa, yanzu ya me jikin?". "Me jiki da sauk'i yanzu mukayi waya ma suna gida yaji sauk'i, ya kamata kaje kaima ka dubo shi" ta fad'a tana kallon sa. "Zanje insha Allah." Gyara zama Mummy tayi tace, "na samu wani gidan marayun a cikin nasarawa wanda bamu je ba? wancan lokacin, mu jarraba muje muji can d'in ko za'a dace" ta fad'a murya a sanyaye tana kallon sa.

Juyowa yayi ya mayar da hankalin sa kanta yace, "Safiyya! sau nawa kike so muje gidan marayu neman Baby ne? Babu gidan marayun da bamu je ba a indai a Kano yake amma ba'a dace ba kuma yanzu kike so mu koma?". "Labarin sa naji ne kuma wancan lokacin bamu je shi ba." "Sabo ne shiyasa bamu je ba, tunda ya kasance sabo kuwa baza mu same ta a can ba tunda ita yanzu batun shekara goma sha ake ko ashirin ma, ki cigaba da addu'a kawai in muna da rabon sake ganin ta zamu ganta insha Allah."

Ajiyar zuciya tayi tace, "Shikenan Allah ya mu dace" ta fad'a cikin sanyin murya, "Amin, abinda zaki ce kenan tun farko". "Hmmm amma sai Allah tsayar damu a ranar alqiyama nida Rabi yayi masa hisabi, ta cuce ni ta cutar min da y'a, yarinya bata ji ba ba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ta gani ba ta....." kukan ya taci k'arfin ta ya saka ta yin shiru bata k'arasa fad'ar abinda take so tace ba, shiru yayi kawai yana kallon ta baice komai ba dan yasan baza ta ji rarrashi ba a halin da take ciki a yanzu, sai da tayi kukan ta gashi sannan ta share hawayen ta tace, "Ko har yanzu Baby tana nan da kamanin ka ko kamanin sun canja Allah ne ya sani" ta fad'a da d'an murmushi kamar ba ita ta gama kuka ba.


"Mudai cigaba da addu'a kinji" ya fad'a yana kallon ta cikin tausayi da raunin zuciya, Mik'ewa tayi ta shiga d'aki ya bita da kallo tausayi.

******

B'angaren Ibteesam tunda suka bar asibitin batayi magana ba har suka je gida a lokacin an fara kiran sallah hakan ya saka ta shiga d'aki kai tsaya tayi alwala ta tayar da sallah.

Ko bayan ta idar ta d'auko alkur'ani ta fara karantawa kamar kullum har ta kammala karanta suratul Yunus A.S ta ajjiye alkur'anin, komawa tayi ta zauna tana tunani Jidda ta shigo d'akin da sallama, kallon ta tayi bata ce komai ba tayi murmushi ta zauna kusa da ita tace, "Anty Ibteesam ke yaya tace dole na fad'a miki gaskiya koda baza ki so hakan ba, kina so Zaid naga soyayar sa a idon ki a lokacin da muka shiga tare da Khalid ya fara wannan numfashin, hankalin ya tashi hakan ya bayyana a fuskar ki, naga soyayyar sa a idon ki a lokacin da muka dawo d'akin bayan an barku ku kad'ai, naga nishad'i a lokacin da farin ciki a kan fuskar ki a lokacin, naga soyayyar sa a idon ki a lokacin da wannan yarinyar tace itace matar sa, naga kishi k'arara a cikin idon ki wallahi dan tun lokacin kika kasa zama a d'akin sai da muka fito hankalin ki ya kwanta, yanzu yafi Khalid matsayi a zuciyar ki Anty ki amince da magana ta kawai" ta k'arasa fad'a tana dafa ta.
Cire hannun Jidda daga bayan ta tace, "Na fad'a miki ni bana son sa iina tausayin sane kawai amma ni bai kai na so shi ba, jin da nayi yanzu ma yana da aure na k'ara jin tsanar a raina bana son sa bana son matar sa dan Allah ki k'yale ni" ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka.

Jidda tayi dariya tace, "To meye na kukan kuma?". "Ki daina ambatar sa shi da matar sa bana son ji gabad'aya" ta fad'a tana had'e hannayen ta waje d'aya. "To ina ruwan ki in na ambaci matar sa,? Wai tsaya ma, meye najin haushin sa keda bakya son sa" Jidda ta tambaya cikin shak'iyanci.

Kallon da ta watsa mata ya saka ta mik'e a guje tana dariya ta fita daga d'akin, Jafar ne ya lek'o dakin yace, "Anty kizo inji Umma" yana gama fad'ar hakan ya juya ya fita a guje, mik'ewa tayi ta wanke fuskar ta jin Umma ta dawo ya saka ta fito falon.

"Sannu da zuwa Umma" ta fad'a tana zama a akan kujera, "Yauwa sannu, ku bani abinci yunwa nake ji" ta fad'a tana ajjiye mayafin ta akan kujera, kallon Jidda Ibteesam tayi itama ta kalle ta kafin ta kalli Umma tace, "Umma wallahi na manta shaf ni ban dafa abinci ba, bara na d'ora yanzu" ta fad'a da niyar mik'ewa Jidda tace, "Sha zaman ki daman kina d'aki kina kuka ba dole ki manta ba, na dafa bara na kawo miki".

Sai bayan ta zubowa Umma farin couscous da miya Umma ta karb'a tace, "Kuka kuma? Kukan me to?". "Wai kuka take dan Khalid ya kaimu asibiti shima yace bara ya shiga ya duba Zaid yana ganin su tare Zaid ya fara wani irin numfashi kamar zai mutu k'arshe ya suma shine duka ta tayar da hankalin? ta tun a can take kuka" Jidda ta fad'a tana zama kusa da Umman ta.

Umma da ta zuba abinci a baki ta cinye kana tace, "Too! Shi kuma daga ganin ku da Khalid sai suma? Kishin ki yake har haka?". "Wallahi kuwa Umma babu jimawa kuma da suna tare ya dawo dai-dai dan likitan ma ya d'auka natar sace, ni kaina in ba a film ba ban tab'a ganin irin haka ba" Jidda ta sake fad'a. "To tunda ya warke kuma meye na kukan?" Umma ta fad'a tana kallon Ibteesam.? "Umma nifa ba wannan ne ya saka ni kuka ba, kawai haushi naji da ya b'oye min yana da mata sai yau na sani".

Dariya Umma tayi ta ajjiye abincin hannun ta tace, "To meye na damuwa dan yana da mata keda ba son sa kike ba,? Meye naki da zai fad'a miki?". "To an san yana da matar meyasa ita ba'a ce ta dinga nuna masa dai-dai da ba dai-dai ba sai ni?" Ta fad'a a d'an fusace. "Sabida ke aikin ki kenan ita kuma matar sace ko Umma?" Jidda ta bata amsa tana kallon Umma.

"Haka ne batun ki Jidda, to ni abinda ya bani mamaki meye na jin haushi dan yana da aure? Ina ruwan ki da matar sa banda abinda Maryamu ta" Umma ta bata amsa tana cigaba da cin abincin ta.

"To an san yana da mata meye za'a takura min sai na dinga kula shi Ba sai a saka matar tasa ba lallai sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login