Showing 162001 words to 165000 words out of 171073 words

Chapter 55 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7867

musu suka shiga wajan a lokacin har an fara show d'in, yadda suka shiga cikin turawa sai ka d'auka suma sune sabida yadda suka saje suka yi bala'in kyau a cikin su, popcorn d'in sane ya zube yace, "Precious bara na samo wani". Kai ta d'aga masa sabida wak'ar da Kizz yake rairawa mai suna Boys are bad ta d'auki hankalin ta, yana barin wajan ta mayar da hankali ga kallon Kizz sai kawai taji an kama k'ugun ta an rik'e an jawo ta, kallon wajan tayi taga wani bature yana ta yi mata murmushi alamun suyi rawa.

Da sauri ta juya sai kuwa suka had'a ido da Zaid dake bayan ta ta fincike jikin ta tayi wajan sa a guje amma ina ya riga ta barin wajan domin kuwa kafin ta har ya samu taxi ya shiga.

Taxi itama ta tsayar Allah ya saka tasan sunan hotel d'in ta fad'awa mai taxi d'in suka tafi, a zaune ta same shi ya cire kaya daga shi sai singlet da boxer a zaune yana wuci, d'urkusawa tayi a gaban sa tace, "Kayi hak'uri dan Allah wallahi ban san mutumin ba kawai naji an rik'o ni ne unexpected dan Allah ka yafe min". D'ago jajayen idon sa yayi ya watsa mata dole taja bakin tayi shiru ta koma gefe tana kuka.

Bai ko kalle ta ba ya shiga wanka bayan ya fito ya tsaya gaban mudubi sai yake hango lokacin da ya rik'e nata k'ugu ya kuma jata jikin sa bai san lokacin da ya d'auki turaren dake kan mudubin ya doki mudubin ya fashe a wajan kafin ya zauna ya dafe kai yana wuci,? ta k'ara sautin kukan ta amma kamar bai san da ita ba, jin kukan yayi yawa ya saka shi yace, "Wallahi in baki yi min shiru ba sai na mare ki." A yadda yayi maganar dole taja bakin tayi shiru ta mik'e jiki a sanyaye ta shiga band'aki tayi wanka ita, tasan tayi masa laifi amma ai ya kamata ya fahimce ta tunda yasan bature ne ba sanin sa tayi ba a wajan sa kuma ba wani abun bane.

Haka ta fito daga wankan ta saka kayan baccin tana ta kallon sa amma bai ko kalle ta ba, bata sani ba kawai ta taka mudubin da ya fasa sai kuwa ta saki k'ara jini ya fara fita daga k'afar tata, da sauri ya diro daga kan gadon ya rik'o ta ya zaunar da ita a gefen gadon ya fara kalle-kalle dan yasan ba'a rasa first-aid box a dakunan su, a can gefe ya hango shi ya d'auko ya zauna kusa da ita ya rik'e k'afar ya fara k'okarin cire nata glass d'in.

Kuka take tana rik'e hannun sa amma bai daina ba sai da ya cire ya saka mata magani ya d'aure wajan har lokacin fuskar nan tasa a had'e kamar bai tab'a dariya ba, magani ya bata tasha ya kwantar da ita shi ma ya kwanta a gefen ta yana cigaba da danna wayar sa, "I'm sorry baby ka daina fushi dani dan Allah wallahi ba laifi na bane ba" ta fad'a cikin kuka sosai, maimakon yace wani abu sai kawai ya mik'e ya jawo sweeping machine ya share glasses d'in? ya tabbatar babu ko d'aya sannan ya koma ya kwanta tare da juya mata baya, kukan take har lokacin ta rungume bayan sa amma ko gezau baiyi ba har tayi bacci.

Jin tayi bacci ya saka shi ya juyo yayi mata kiss a goshi har lokacin yana jin zafin abinda ya gani amma shima yasan ba laifin nata bane kamar yadda tace, haka suka tashi ko magana yak'i yayi mata sai fama bin gefe take kamar k'adangaruwa.

Sai da ya gaji dan kansa sannan ya saurare ta suka koma kamar da suka bar England suka dira a Dubai, Ibteesam tayi kyau ga k'ara kiba komai na jikin ta ya sake cika sosai fatar ta har wani shaning take sabida kyau, k'are mata kallo yake tana d'aure towelnta fito daga wanka yace, "Precious kin k'ara k'iba fa anya baki da ciki?" Ya fad'a kansa tsaye yana kallon ta. Turo baki gaba tayi tace, "ni bani da komai, kwata-kwata kwanan mu nawa da zaka ce ina da ciki." "Kika sani ko a ranar farko an samu?". "Nidai A'a." Zaiyi magana kiran Daddy ya shigo dole ya amsa suka gaisa har da Anty kafin ya bawa Ibteesam ma su gaisa, karb'ar wayar yayi yace, "Daddy ina jin fa Precious ciki ne da ita amma sai muje asibiti za'a tabbatar." Daga can b'angaren Daddy yayi murmushi yana girgiza kai yace, "To Allah ya tabbatar Zaid." "Amin Daddy, ka fad'awa Anty ma ta taya mu da addu'a". Ya amsa da to kawai ya kashe wayar.

Kallon sa kawai take cikin mamakin sa ya juya suka had'a ido yace, "Yeah bana jin kunya ni kam" dan yasan abinda zatace masa kenan.
Idon ta har wani cikowa yayi sabida takaicin abinda ya fad'awa Daddy tace, "Yanzu fisabinillah Daddyn ka fad'awa haka? Ni wallahi kana bani kunya a ko ina" ta fad'a kamar tayi masa kuka. Kallon ta yayi sai kuma ya tab'e baki tare da yatsine fuska ya d'auke kansa ya cigaba da danna wayar sa hankalin sa a kwance. Yana kallon ta tana tayi masa k'unk'uni tana turo baki har ta gama shiryawa sai kawai taga ya mik'e yace, "Asibiti zamu je" ya fad'a yana rik'o hannun ta.
Zatayi magana ya d'aga mata hannu dole tayi shiru tana kallon ikon Allah.

Ta dole ya tilasta mata suka je asibiti cikin ikon Allah gwajin farko ya nuna tana d'auke da ciki na sati uku...


Up coming book BAK'AR ANIYA....=؃?

*?ASAITAR SO!*

*89_90*

Not edited>?z?



Tun a asibitin ya kasa b'oye farin cikin sa ya dinga juyi da ita, likitocin suka tsaya suna kallon su cikin burgewa suna taya su murna suma. Kamar kwai haka ya lallab'a ta suka dawo gida ya zaunar da ita shima ya zauna yana kallon cikin nata.

Ita kam harga Allah kunya take ji fisabinillah daga tarewa sai ciki babu hutuwa ko amarcin bata gama mora ba zatayi ciki, ganin ta had'e fuska bata dariya sai ya kalli fuskar ta yace, "Bakya farin ciki?". Turo baki gaba tayi bata ce komai ba tana shirin yi masa kuka, "fad'a min meye?".
"Ni..ni... yanzu kawai sai aji ina da ciki daga tarewa sai ciki ko hutawa banyi ba".
"To sai me? Ba mijin kine yayi miki ba?". Kallon sa tayi taga fuskar sa a washe kana ganin yanayin sa kasan farin cikin da yake ciki ba kad'an bane dan zata iya cewa bata tab'a ganin farin ciki haka akan fuskar sa ba.
"Nidai A'a kunya nake ji" ta fad'a kamar zata yi masa kuka, dariya yayi kad'an yace, "kunyar wa kike ji?".
"Su Daddy mana".
"Tunda har kika yadda kika yi cikin ai zancen kunya ya k'are precious" ya fad'a yana d'aga mata gira duka biyun yana murmushi.

Kallon sa tayi har lokacin fuskar ta babu walwala tace, "Wai yanzu kuma kowa yasan abinda kayi min na samu ciki ko?". Tunda yake bai tab'a jin abinda ya bashi dariya kamar abinda tace ba sai kuwa ya fara dariya babu kakkauwa harda su rik'e ciki, sak tayi tana kallon sa ganin yadda yake dariya kamar ba shine Zaid ba karo na biyu kenan da taga dariyar sa amma wannan har tafi waccan, sai da ya gama dariyar ya kalle ta suka had'a ido yace, "abinda muka yi dai ba nayi miki ba."

D'auke idon ta tayi ta turo masa baki ya kama bakin da yatsun sa yace, "Kowa ya sani mana precious ai an san ba'a ruwa kika sha ba." Sai kuwa ta fara yi masa kukan shagwa6a tana dire masa k'afa tana fad'in, "Allah nidai kunya nake ji". Waya taga ya d'auko da sauri tace, "Me zakayi?". Yace, "Zan kira su Daddy ne na fad'a musu I'm gonna be a Daddy" ya fad'a yana fara dannawar alamun kira, sai kuwa ta fincke wayar tace, "Kayi min rai dan Allah kar ka fad'a musu kaji?".

Da mamaki ya kalle ta yace, "Meyasa?". "Nidai A'a ka bari in mun koma ka fad'a musu". Girgiza kai yayi yace, "shikenan, gobe ai zamu wuce daman" ya fad'a yana lakuce mata hanci yana murmushi tare da d'ora hannun sa a cikin ta yana ta murmushi.

"Bakya murna da cikin ko?" Ya tambaye ta ba tare da ya kalle ta ba, sai ta girgiza kai tace, "ina yi mana sosai ma kuwa, miji na kuma abin qauna ta zan haifawa baby fa ai dole nayi murna". Jin abinda tace sai ya sake fad'ad'a fara'ar sa ya kama kanta yayi mata kiss a goshi yana jin wani irin farin ciki wanda bai tab'a tsintar kansa a ciki ba.
"School d'ina fa da kace in mun koma zaka samu min private university?".
"I'm sorry to say, sai kin haihu kuma" ya fad'a yana shafa cikin ta.
"Amma ba haka mukayi da kai ba" ta fad'a tana buga k'afar ta cikin shagwa6a.

"Nima ban san da cikin bane shiyasa nace haka, I'm sorry Precious bazan iya barin ki kina zuwa school da ciki ba." Jin hakan da yace dole tayi shiru dan tasan tunda yace hakan bazai canja ba.

Washe gari da wuri suka fito Airport suka hau jirgin zuwa Nigeria, tunda suka suka jirgin Ibteesam take jin kanta na juya mata sabida sam khamshin jirgin bai mata ba sai ma tayar mata da zuciya da yake tana jin amai, lura da yanayin ta da yayi ya saka yace, "Precious lafiya?". Kai ta girgiza masa alamun a'a kafin tace, "Amai" ta fad'a tana wata shak'uwa alamun aman take so ta fitar, "muje toilet" ya fad'a a rud'e ya mik'ar da ita yana rik'e da hannun ta zuwa band'akin jirgin amma aman yak'i fita sai jin sa da take.

D'aya daga cikin ma'aikatan jirgin ganin yanayin ta ya saka ta k'araso wajan tana tambayar lafiya, zuwan ta wajan yayi dai-dai da aman da Ibteesam ta fara yi sai kuwa ya rik'e ta gam har ta gama ya wanke mata baki da fuskar ta, sai a lokacin ya samu damar kallon ma'akaciyar suka tattauna da English ta tauyasa mata sosai, komawa sukayi suka zauna nan aman ya sake tasowa suka sake komawa ta kuma yi sai da akayi haka har sau uku duk ta galabaita jikin ta yayi sanyi, emergency aka duba ta a jirgin suka bata maganin da bazai cutar da Babyn cikin ta ba.


Facemask aka samu aka fesawa turare mara k'arfi aka bata ta saka sannan taji dad'i tayi bacci a jikin sa, lokacin da suka shigo Nigeria yana rik'e da ita tana jikin sa dan jikin ta yayi zafi gashi kuma bata da kwari, driver yayiwa waya Allah ya taimaka yana kusa da Airport d'in yazo ya d'auke shi suka tafi.

Lokacin da suka koma gidan yana rik'e da ita har lokacin suka shiga part d'in Anty Amina, suna zaune kamar koda yaushe suka ga shigowar su kwatsam babu zato, Daddy ne yace, "Zaid yanzu kuke tafe?". "Uhum" shine kawai abinda yace sabida baya cikin nutsuwar sa jin yadda jikin ta yayi zafi, k'okarin barin jikin sa take ganin Daddy da Maman ta amma ya hana hakan sai dad'a rik'e ta yake gam suna k'arasawa cikin falon, "Bata da lafiya?" Daddy ya tambaya a rud'e yana kallon Zaid d'in.

D'aga kai yayi yana zaunar da ita yace, "Eh Daddy tun a flight take ta amai jikin ta yayi weak sosai ga fever ma." Daddy yace, "Subahanallahi, bara a kira Dr Auwal yazo ya duba ta" Daddy ya fad'a yana ciro waya da niyar kiran Dr, kusa da ita ya zauna yana ta yi mata sannu dan shi ya manta ma fa basu gaisa da Daddy ba.

Ita kam Anty Amina kallon sa kawai take ganin yadda ya rud'e akan aman da tayi tun kuma jirgi tana mamakin girman soyayyar da yake yiwa d'iyar tata, "Sannu" itama ta furta tana kallon Ibteesam d'in da take jingine a kan kujera. Jin muryar ta ya saka shi kallon ta yace, "I'm sorry bamu gaisa ba ko? A rud'e nake ne" ya fad'a yana d'an dafe kansa cikin yanayi na damuwa.

"Daddy ina wuni, Anty ina wuni" ya fad'a duka lokaci d'aya yana mayar da kallon sa ga Ibteesam d'in, suka amsa a tare kafin yace, "kun dawo lafiya?". Nan ma suka amsa da lafiya lau suma hankalin su na kan Ibteesam d'in, shigowar Dr ya saka suka amsa sallamar sa tare da yi masa izinin shigowa, gaisawa sukayi sannan aka nuna masa Ibteesam d'in, k'arasawa yayi inda take ya kai hannu zai tab'a wuyan ta yaji temperature d'in jikin ta yayi saurin rik'e hannun sa yace, "ask me first before you going to touch her, akwai fever" ya fad'a fuskar nan a d'aure yana kallon Dr.

Daddy ya dafe kai yace, "Zaid ka barshi yayi aikin sa mana". Dr yayi murmushi sosai dan shi kam dariya Zaid ya bashi yace, "No Alhaji k'yale shi". Dr ya kalli Zaid yace, "me yake damun ta?". Zaid yace, "Amai take sai fever naji kanta ma ya fara ciwo" ya fad'a yana rik'e jijiyoyin kanta. Girgiza kai Dr yayi yace, "Maybe ko malaria ce amma ayi test mu gani" ya fad'a yana kallon Zaid d'in.

Sai da ya watsa masa wani kallo jin abinda yace sai yace, "Ciki ne da ita na 3weeks, a can dubai lafiya lau take amma muna shiga flight ta fara amai, inda nasan abinda zai faru kenan da bamu dawo ba" ya fad'a yana yatsine fuska yana kuma kallon Dr. Kyakykyawan murmushi Dr yayi yace, "Masha Allah, congratulations Zaid ashe ma rashi? lafiyar irin wacce ake so ce" ya fad'a ciki? murmushi yana mik'a masa hannu alamun su gaisa.

Kallon sa yake jin rainin hankali irin nasa yace, "Dr bata da lafiya jikin ta yayi zafi sosai kace min irin rashin lafiyar da ake so ce? Okay kenan taita rashin lafiyar ko?". Sai da Dr ya dara sosai hakan ya sake kular da Zaid ya buga kwafa yana sake yi mata sannu, "I'm sorry Zaid, daman ai ciki ya gaji haka tunda kaga haka cikin jikin ta mai laulayi ne sosai zan iya ce mata wannan ba komai bane akan rashin lafiyar da zata fara nan gaba." Kallon Daddy yayi yace, "Daddy kaji abinda yake cewa fa? Yana nufin baza ta samu sauk'i ba,? Daddy wannan wanne irin Dr ne?" Ya fad'a cikin fad'a yana aikawa da Dr banzan kallo.

Daddy kallon sa kawai yake yi amma farin cikin samun jikoki daga jinin Zaid ya cika masa zuciya sosai da sosai, daman babban burin sa bai wuce yaga yaran Zaid zagaye dashi ba.

Dr yace, "okay kana so ka rasa babyn dake cikin ta kenan?". Had'a ido sukayi dashi yace, "Yess indai zaka ce dole sai taji sauk'i gabad'aya to zaka rasa babyn ne dan zaku wani wajan ayi mata allurar da zata fitar dashi, relax Zaid haka ciki yake ba'a samun baby da sauk'i, yanzu zan bata magani dai-dai da condition d'in ta bayan wannan maganin da zan bayar kar kuje ko ina a baka magani indai ba irin saba ka bata tasha, magani indai yana da k'arfi koda na ciwon kaine zai saka cikin ya fita tunda baiyi kwari ba ko one month baiyi ba" Dr ya fad'a yana kallon Zaid tare da rubuta mata magani.

Ajiyar zuciya yayi yana kallon ta cikin tausayi duk zumud'in cikin da yake yi sai yaji ya fita akan sa jin wai haka zataita shan wahala, Dr Auwal ya rbta mata paracetamol da folid asid da kuma vitamin c da kuma wanda yasan zai taimaka mata, Daddy ya bawa takardar dan yaga Zaid ba'a nitse yake ba, Harira mai aikin Anty Amina ta shigo da sallama ta d'urkusa kusa da Anty Amina ta mik'o mata wani plate tace, "Hajiya gashi an gama". Shak'ar khmashin abincin Ibteesam tayi sai kuwa amai ya tawo ta mik'e a guje tayi wajan sink d'in dining sai amai.

Da sauri yabi bayan ta ya rik'e ta har ta gama ta wanke fuskar ta ya sake rik'o ta suka dawo, hanci ta toshe sabida yadda khamshin yake tayar mata da hankali, Anty Amina ce ta lura da hakan sai tace, "Harira jeki khamshin abincin ne bata so". Mik'ewa tayi da sauri bisa tsautsayi tazo wuce ta kusa da Ibteesam d'in tayi tuntub'e da carpet abincin ya zube a inda Ibteesam take kuwa aman yak'i ruk'uwa ta sake barin wajan a da sauri sai amai.

"Ke wacce irin mahaukaciya ce baki da hankali? Ance miki bata son khamshin sa shine ki zubar a kusa da ita" ya fad'a a fusace kamar zai mare ta, cikin rawar murya tace, "kayi hak'uri tuntu6e nayi wallahi bada sani....." "shut up Stupid! get out before nayi ball dake!" Ya fad'a cikin muryar sa mara amo sosai amma kana ji kasan fad'a yake ransa a kuma b'ace yake. Da sauri ta bar wajan jikin ta na rawa dan magana ma zata iya irga sau nawa Zaid yayi nata tun zuwan ta gidan balle yayi mata fad'a.

Kamar munafuka ta dawo ta kwashe abincin ta goge wajan ta fita, a kan dining take ta kifa kanta a kan table d'in jiri na d'aukar ta, Daddy dai kallon ikon Allah kawai suke yi ganin yadda ya fita hayyacin sa lokaci d'aya, sallama Dr yayi ya fita bayan an bawa driver ya siyo maganin.

Jikin ta ya tab'a jin yadda zazza6i ya rufe ta sosai sai ya juyo kamar maraya yace, "Daddy fever yayi yawa a jikin ta, ni ina ma bamu dawo k'asar nan ba kalli yadda take shan wahala" ya fad'a kamar zaiyi kuka, Anty Amina tace, "kar ka damu zata ji sauk'i, kuje ta huta in an kawo maganin sai a aiko muku dashi" ta fad'a cikin tausayin Ibteesam d'in dan da gani zata sha wahalat laulayi.

Kamar zaiyi kuka haka ya kamata suka fita aka bisu da kayan su.

Tun daga ranar Ibteesam ta fara laulayi mai wahala kullum babu lafiya komai taci sai ya dawo babu abinda yake zama a cikin ta sai apple shima in taci d'aya shikenan, cikin kwanakin duk ta rame sabida wahalar da take sha dan sai Jidda ce da Zahra ne suka dawo wajan ta da zama sabida bata iya komai.

Babu wanda bai tausaya mata ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login