Showing 159001 words to 162000 words out of 171073 words

Chapter 54 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7846

murmushi kad'an.

"To wai meyasa baka so a kira ka da wannan kalaman na baya?" Ta fad'a tana kallon sa, "sabida ni bashi bane, Precious na tsani ace min d'an isa ko d'an shaye-shaye, bana shaye-shaye ko kad'an ban san su ba raina ya b'aci over in aka kira ni dasu."

"Amma ai kana shan sigari ko ka daina?".
"Ban daina ba itama bana kula ta sai raina ya b'aci."
"Ka daina sabida lafiyar ka, wallahi ni na tsane ta ko warin ta bana so."

Murmushi yayi kad'an yace, "To zan daina sabida ke kawai". Itama tayi murmushi tace, "Nagode". Hira suka cigaba dayi ciki nishad'i da soyayya har lokacin sallar magariba yayi ya fita ita kuma ta shiga ciki don yin sallar, bayan ta idar ne ta kira Umma a waya suka sha hira tana tambayar Jidda tace mata bata jin dad'i shiyasa bata ganta ba, bayan sun gama wayar ta kira Abban Jidda suka gaisa dashi shima yayi mata nasiha kafin suyi sallama ta kira Abban ta, shima dai nasiha yayi mata da kuma fatan alkhairi sannan ta kira Mummy.

Sai da akayi kiran i'sha sannan ta ajjiye wayar tayi sallah Mama ta aiko musu da abinci ta karb'a ta ajjiye ta hau sama, wanka tayi ta fashe jikin ta da turaruka ta canja kaya zuwa riga da siket na atampa tana sakkowa shi kuma yana shigowa, k'are mata kallo yake yi har ta k'araso cikin falon ganin kallon da yake mata sai ta saka hannu ta kulle fuskar ta tare da zama a akan kujera, a hankali ya taka ya zauna kusa da ita yana cigaba da kakkon ta da shak'ar khamshin dake tashi a jikin ta, "Precious kina so ki haukata Zaid fa" ya fad'a mata in low voice yana kallon fuskar ta da har lokacin take a kulle.

Hannu ya saka ya cire hannayen ta da suke kan fuskar ta tayi saurin kulle idon ta ya cigaba da kallon ko ina na fuskar ta, blowing kisses ya fara aikata dasu a ko ina na fuskar ta da wuyan ta kafin ya had'e face d'in su waje d'aya hancin su na gogar na juna ko wanne yana shak'ar numfashi d'an uwan sa, "abincin ka" ta furta idon ta har lokacin a kulle, khamshin alawar da ya fito daga bakin ta ya shiga cikin kofofin hancin sa ya sake rikita shi ya fara kissing d'in ta.

Itama ba'a barta a baya ba ta fara mayar masa da martanin abinda yake mata hakan ya sake gigita shi ya fara fita a hayyacin sa, tunawa da tayi a falo suke bak'i na iya shigowa ya saka ta zare bakin ta a hankali ta bud'e idon ta tana kallon tasa fuskar, idon sa a lumshe fuskar sa tayi haske sosai kamar ya shafa powder smallest pink lips d'in sa yana ta motsi alamun magana yake so yayi, yana jin yadda take kallon sa a jikin sa amma yak'i bud'e idon nasa sabida yanayin da yake ciki suna had'a ido bai san a ina abin zai tsaya ba.

Mik'ewa tayi tsaye ta zuba masa abincin a plate tazo da spoon tazo ta zauna tana fad'in, "Baby oya eat" ta fad'a tana mik'a masa plate d'in, sai a lokacin ya bud'e ido ya sauke su a tsakiyar nata sai kuwa tayi saurin janye nata dan kallon idon sa na haifar mata da wani irin yanayi mara misaltuwa, ganin bai karb'a sai ta d'iba a spoon d'in ta kai bakin sa ya fara ci kuwa babu musu sai dai baice komai ba, rabin abincin yaci kafin ya karb'i spoon d'in ya fara bata itama kasancewar bata cin abinci in dare yayi bata ci wani sosai ba, drink d'in da yake a glass cup ta d'auka ta mik'a masa, karb'a yayi yasha ya barshi a bakin sa ya matso da ita sosai ya fara zuba mata lemon da yake bakin sa cikin nata.

Sai da ya juye mata tass ya sauke zuba wani a bakin nasa ya kuma zuba mata a nata bakin kafin ya zarce da yin abinda yake so, k'arar wayar sa da ta cika musu kunne ya saka shi ya dawo hayyacin sa ya sake ta ya juya yana kallon wayar ita kuma ta samu damar mik'ewa da sauri tana kwashe plate da cup d'in, kitchen ta kai ta ajjiye tana sauke ajiyar zuciya dan gabad'aya jikin ta ya mutu.

A tsaye ta same shi ya gama wayar tace, "ahmmmm wannan abincin a kaiwa mai gadi kar ya lalace" ta fad'a tana nuna masa ragowar abincin da yake kan dining a ajjiye, baice komai ba sai idon ta da yake kallo tayi saurin yin k'asa da idon nata ya k'araso wajan kamar zai d'auki abincin sai ya kamo k'ugun ta ya rungume ta baya kansa na kafad'ar ta, hannun sa ya saka cikin rigar ta k'asa yana shafa cikin ta da ya d'an tasa kad'an yana hura mata iska a kunne yace, "Me kika tanadar min yau?".

Ya kashe mata jiki gabad'aya idon ta a lumshe tace, "abinda kake so" ta fad'a cikin muryar da take nuna shauk'i da zallar soyayyar sa, "zan je na dawo zan fad'a miki sai ki bani kin yadda?". Ta d'aga masa kai alamun eh dan ya fara zautar da ita abinda yake mata yana neman sagar mata da k'afa. Sai da yayi mata kiss a wuyan ta sannan ya d'auki abincin ya fita dashi.

Yana fita tayi sama da sauri ta shiga d'akin ta tana sauke numfashi da sauri kafin ta shiga band'aki tayi brush ta fito, rigar bacci mara nauyi ta d'auka wacce take tsahon ta har guiwa mai d'an kauri, zama tayi a kan gado tana kallon kanta a mudubi tana tuna wahalar da tasha jiya a hannun sa sai kuma fad'uwar gaba ta kawo mata ziyara jikin ta yayi sanyi.

Shima koda ya dawo kitchen ya ajjiye mata flaks d'in ya kashe komai na k'asan sannan ya hau saman, wanka shima yayi ya saka nashi kayan baccin riga da kuma trouser mara tsaho sosai, d'akin nata ya nufa ya same ta a zaune tana kallon kanta a mudubi, mik'ar da ita tsaye yayi yace, "tunanin me kike yi haka?". Girgiza masa kai tayi tace, "babu komai". "Muje mu kwanta" ya fad'a yana jan hannun ta. Tirjewa tayi tace, "Ni a nan zan kwana" ta fad'a kamar tayi kuka.

"Okay, mu kwana a nan d'in."
"A'a kai ka tafi naka d'akin."
"Why?".
"Babu komai."
"Precious duk zafi duk sanyi, duk tsananin duk farin ciki, duk wuya duk dad'i, baza mu tab'a raba shinfid'a dake ba indai ina tare dake, in ma kina wannan tunanin a rainki ki daina ni Zaid na zamar miki chew gom ko ina kike ina tare dake, so muje". Babu yadda ta iya haka yaja hannun ta suka fita daga d'akin zuwa nasa d'akin.

Waje ta samu ta zauna kamar mara lafiya tayi shiru banda fad'uwar gaba babu abinda take ji, cup d'in tea ya mik'a mata shima yana rik'e da nasa yana sha ya kalle ta yace, "Tsoron me kike ji?". Da sauri ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido tayi saurin saukar da idon ta k'asa tace, "babu komai". Murmushi yayi kad'an yana cize lips d'in sa tsaf ya karanci abinda take jin tsoro share ta kawai yake sai yace, "to kisha tea d'in ki".

Haka ta daure ta shaye tea d'in tass ta ajjiye cup d'in ganin kallo yake a falon ya saka ta mik'e tace, "Sai ka shigo na kwanta" tana fad'a ta shiga d'akin ya bi bayan ta da kallo har ta b'ace, ya jima zaune kafin ya mik'e shima ya kashe komai ya shiga d'akin, tana jin sa dan ta kasa baccin amma tayi saurin rufe idon ta kamar mai bacci har ya kashe wutar d'akin ya k'arasa inda take ya kwanta shima a bayan ta, binkito ta yayi ya juyo da ita suna kallon juna duk da idon ta a kulle yace, "don't pretend like sleepiest, i know ba bacci kike yi ba". Ai kafin tace wani abu ya fara aika mata da sak'on da dole ya saka taja bakin ta tayi shiru tana karb'ar sak'on nasa.

Sai da ya tabbatar ya fitar da ita daga hayyacin ta kamar shi sannan ya cimma burin sa.

Kamar jiya yau ma kukan take amma ba kamar na jiya ba kana kallon wannan kasan na raki ne bana zafi ba amma ya rikice sai aikin rarrashi yake suka yi wanka suka kwanta tana masa kukan shagwa6a shi kuka yana ta rarrashin ta.

Washe gari fess ta tashi ba ciwo sai kuzari da take ji a jikin ta lokacin da ta farka kamar jiya baya nan ta fara had'a d'akin ta gyara komai na d'akin sannan ta fita zuwa nata tayi wanka ta shirya ta sannan ta sauka, k'ofa ta bud'e kamar tasan kuwa jira ake aka mik'o mata breakfast ta ajjiye ita kuma ta dafa tea.

Tana tsaye a kitchen d'in kawai ta tafi duniyar tunanin abinda ya faru a tsakanin su jiya, murmushi tayi in ta tuna wani abun a cikin kalaman sa sai taji kamar k'asa ta tsage ta shige ciki sabida kunya, murmushi take ita kad'ai wani abun in ta tuna sai ta rufe fuskar ta kamar yana gaban ta a haka har ya shigo bata sani ba, hard'e hannu yayi a kirji yana kallon yadda take ta murmushi ita kad'ai sai ya lumshe ido, shi kam ya rasa adadin soyayyar da yake yiwa precious d'in sa, yana jin ta a ko wanne waje na zuciyar sa da kuma gangar jikin sa yadda jini yake zagaya ko ina na jikin sa haka yake jin sonta na zagaya ko ina na jikin sa hakan ya saka ta zama babban b'angare a cikin rayuwar sa.

"Our yesterday movement!" ya furta yana kallon ta, sai kuwa ta juyo inda taji maganar tayi saurin kulle fuskar ta tana murmushi, k'arasowa yayi ya jawobta jikin sa k'irjin su na gugar na juna ya rik'e k'ugun ta yana kallon fuskar ta yace, "yeah yesterday it's special day". K'asa tayi da kanta tana murmushi ya d'ago da kan nata yace, "you smiled, that's means u enjoy it too?". Sai kuwa ta kifa kanta a k'irjin sa tana d'an dukan sa kad'an-kad'an.

Yar dariya yayi kad'an kafin yace, "gossip". "Good morning" ta furta tana jikin sa, "morning my sugercane, I'm sorry yau ma na barki ko? Ina can ina had'a miki big surprise". D'ago kai tayi suka had'a ido ya d'aga mata gira d'aya yace, "but ba haka ake gaida miji ba". Da ido tayi masa alamu? to yaya akeyi, "Allow me to show you". D'aga masa kai tayi alamun ya nuna mata.

Pink lips d'in ta da suke d'auka hankalin sa a koda yaushe yayi kissing ya had'a da cheek d'in ta yace, "that's". Sunkuyar da kai kasa tayi sai ya sake cewa, "you know precious har kin fi sugarcane d'in ma". Hannu ta saka ta kulle fuskar ta tana dariya shima yayi murmushi kad'an yana mamakin yadda yake mata magana haka.

Hannun ta yaja zuwa kan dining d'in dan yasan bata ci komai ba ya bata abinci taci shima yaci kad'an sannan ya sake jan hannun ta zuwa sama, d'akin sa suka shiga ya jawo trolly yace, "zamu d'an yi tafiya zuwa Abuja flight d'in ya kusa tashi" ya fad'a yana d'auko kaya yana zubawa a jakar. Sai da ya zuba komai nasa a ciki wanda yasan zaiyi amfani dasu sannan suka fito aka kulle d'akin aka je d'akin ta, a falo ya tsayar da ita yace shi zai had'a mata kayan ta barshi kuwa.

Ya d'an jima a d'akin sannan ya fito ita kuma ta shiga ta yafa mayafi ta d'auki abinda yake sirri a wajan ta ta zuba a hand bag.

Kasa suka sakko ya kashe komai ya wutar gidan aka bayar da abincin sannan suka fito zuwa part d'in su Daddy, gaisawa sukayi sannan sukayi musu sallama dan su Daddy jirgin k'arfe biyu na rana zasu hau, yaso suje gidan Umma da Mummy amma lokaci ya k'ure dole suka tafi.

Tun da suka shiga Airport suka fita daga motar taga sun nufi International section a maimakon domestic tunda yace Abuja zasu ce, kallon sa kawai take tana so ta tambaye shi amma sai ta share suka shiga ciki, dake babu komai a jakar tasu nan da nan aka auna ta su kuma shiga shiga screening, sai a lokacin taga passport guda biyu a hannun sa, suna zama kafin ta tambaye shi aka sanar da jirgin su ya zama ready ya rik'e hannun ta suka fita daga wajan.

Jirgin Qatar suka hau sai bayan sun zauna yaga sai kallon sa take alamun magana take so tayi sai ya d'aga gira d'aya yace, "Ya dai?". "Ban gane ba ina zamu je haka?". Murmushi ya d'an yi ya d'auko wayar sa yayi musu selfie mai kyau sannan yace, "Saudia zamu je precious" ya fad'a yana kallo idon ta da itama shi take kallo.

Baki ta bud'e kawai farin ciki da mamaki ya hana ta magana ganin hakan ya saka shi yace, "Jidda na tambaya take sanar dani kuna da International passport wai last year Abba yayi muku zaku je umra baku samu visa ba, shiyasa nayi surprising d'in ki a kan hakan, daga Saudi zamu England sai muje dubai" ya fad'a har lokacin idon sa yana cikin nata.
Baki ta bud'e zatayi magana yace, "shiiiii, just say i love you Zaid". Muryar ta har rawa take tace, " i love you my husband" ta fad'a tana kwanciya a jikin sa shima ya rik'e ta.

A jidda suka sauka suka hau mota zuwa makka dan shi yafi ya fara umra sai ya dawo madina, a ranar da suka shiga sukayi umra Ibteesam sai farin ciki take ganin yau gata ga ka'aba bata san lokacin da ta fara kuka ba, a gajiye suka koma As_safwa hotel Allah ya saka babu nisa da masallaci, suna shiga d'akin Ibteesam ta baje a kan gado sabida a gajiye take ga gajiyar tafiya gata umra, shi kam wanka ya shiga yayi da ruwa mai zafin gaske yana fito ta mik'e dak'yar itama tayi wanka ta fito kawai ta saka doguwar riga sai bacci.

Tun daga ranar suka fara ibada da addu'a dan babu ranar da zata fito ta koma basu yi d'ayafi ba, shaquwa da k'aunar juna ta sake shiga tsakanin su sosai, kwanan su biyar suka hau mota sai Madina.

Haka suka isa a gajiye sai da suka huta gab da asuba sannan sukayi wanka suka shirya zuwa masallaci, kasancewar madina ba kamar makka ba ko ba'a cakud'uwa mata da maza ko wanne wajan ziyarar su da daman hakan ya saka shi dole suka rabu bayan ya nuna mata inda zata jira shi in ta riga shi fitowa, bayan an idar da asuba suka ahiga ziyarar kabarin Annabi Muhammad S.A.W, mai Ibteesam zatayi in ba kuka ba farin ciki ya cika zuciyar ta soyayyar mijin ta na sake ninkuwa a ranta, bayan ta kammala ta fito ta tsaya a inda ya nuna mata duk da taso ta b'ata.

Bata jima ba taga fitowar sa ya rik'e hannun ta suka koma ????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
masaukin su, tunda suka shiga d'aki Ibteesam take murmushi har ya cire kayan sa tana zaune tana ta aikin murmushi yace, "Any gist?". "Na rasa da wacce kalma zanyi amfani wajan gode maka miji na, ka kawo ni inda ba kowa yake zuwa ba sai mai rabo, ka kawo ni inda Annabin Allah yake kwance, naje naga d'akin Allah na ziyarci Annabi nikam dame zan biya ka miji na?" Ta fad'a hawaye na fara zubo mata daha idon ta.

Rungume ta yayi tsam tsam yace, "Soyayyar ki ita kad'ai nake so a tare dake matata, in kika bani kin gama yi min komai a rayuwa ta." Cikin kuka tace, "ka samu, indai Soyayya na ma mallaka maka kaina kayi yadda kake so dani." Daga nan dai suka fad'a kogin masoya.

Kwanan su uku a madina duk wani waje na ziyara ya kai ta haka kasuwanni na madina masu kyau duk? sunje yana ta yi mata siyayya kamar baya son kud'in duk da tsadar kayan madina amma hakan bai hana shi jibgar mata kaya ba, kamar a mafarki bayan asuba tazo shiga ziyara suka had'u da Umma da Jidda, dole ta b'oye mamakin ta sai bayan sun fito Ibteesam take cewa, "Umma yaushe kuka zo? Shine ko ku nemi ni?". Umma tayi murmushi tace, "Mijin kine ya biya mana har da Abban ku, shine kuma yace kar mu fad'a miki a bari a baki mamaki." Sakk tayi ta kasa cewa komai sai kallon su kawai da take yi Jidda tace, "Ai tun kafin ku tare yazo ya karb'i passport d'in mu yace kar na fad'a miki, wallahi Anty Ibteey Zaid yana sonki tunda yake son abinda kike so." Ita dai ta kasa magana har suka je masaukin su Umma ana ta hira da sakawa Zaid albarka kafin ta koma nasu masaukin.

Shi kam tunda yaga bai ganta ba yasan sun had'u sai ya koma yana zaman jiran ta, ai kuwa da kuka ta shiga ya taso a gigice yana tambayar ta lafiya, sai ta rungume shi sosai a jikin sa tana tayi masa godiya shi kuma yana murmushi.

Washe gari jirgin su ya d'aga zuwa birnin london suka bar su Umma a Madina, a london a nan aka baje hajar soyayya mai tsayawa a rai dan tsukewa Ibteesam ta koma yi fita yawon zaga gari yau suna nan gobe suna can, zaman su ya sake yin dad'i Soyayya ta sake shiga tsakanin su sosai da kuma shaquwa mai k'arfin gaske ta sake tabbatarwa ita kad'ai ce a zuciyar Zaid duk da har kawo gobe in miskilancin sa ya motsa baya kula ta sai dai da ido.

Kamar kullum yau sun shirya zasu je kallon mawaki Kizz Daniel da yazo zaiyi show a d'aya daga cikin stadium d'in dake garin, Ibteesam tayi kyau cikin blue d'in jeans da blue d'in riga ta saka bak'in glass kanta saka hula sai riga da ta sake d'orawa a kan riga da wandon mai budaddan gaba wacce tazo mata har guiwa, shima shigar tasa haka take kasancewar ba lokacin snow bane basu saka kayan sanyi ba.

Yana rik'e da hannun ta suka hau taxi suna wajan, popcorn ya shiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login