Showing 165001 words to 168000 words out of 171073 words

Chapter 56 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7852

in yazo yaga yanayin jikin nata sabida sosai take shan wahala.

Kamar kullum yau Umma da Mummy suka zo duba ta tana zaune kanta na kafad'ar Umma tana ta sauke ajiyar zuciya, "Sannu Ibteesam, me kike so kice?" Mummy ta fad'a tana kallon ta cikin tausayi. Ibteesam tace, "shinkafa da manja da yaji da kifi shima kuma a soya shi da manja, a saka kwai shima kuma a soya shi da manjan a matsa min lemon a kai". Mummy tace, "Zahra maza tashi kije ku had'a mata, in babu kifi a gidan a bayar a siyo, Jidda tashi kema". Ba musu suka mik'e suka shiga kitchen wannan tana dafa shinkafa wannan tana gyara kifin nan da nan suka had'a mata abinda tace suka kawo mata.

Lokacin Zaid ya shigo ta fara cin abincin kamar gaske tana ta zabga uban yaji tana ci hankalin ta a kwance, kallon abincin yayi yace, "Precious wannan yajin zai miki illa fa" ya fad'a yana d'auke robar yajin daga wajan, "ni shi nake so naci kawai ka bani" ta fad'a kamar tayi masa kuka, mik'a mata yayi ya zauna yayi tagumi yana kallon ta.

Ana ta murna taci rabin abincin tace ta k'oshi sai ta ware kad'an ana hira da ita, ai ko minti goma abincin baiyi ba ta dawo dashi gashi yajin da tafi ya fito ta hancin ta duk sai ta sake gigicewa, dak'yar aka samu ta nutsu tana sauke ajiyar zuciya tana shan ruwa, idon Zaid har cikowa yayi da hawaye sabida tausayin ta shikam cikin ya fice masa daga kai ganin yadda take shan wahala sai yaji haushin ma abinda zata haifa yake yi, bacci ne ya d'auke ta a akan kujerar su Jidda suna ta kallon ta cikin tausayi, "Mummy" Zaid ya fad'a fuskaa hade yana kallon ta. Ta amsa tana jiran mai zaice, "Umma ina jin shekaru precious bazai wuce 22 ba ko?". Umma ta d'aga kai alamun haka ne, ajiyar zuciya yayi sannan yace, "tayi kankanta da haihuwa a yanzu ni na yanke shawara kawai za'a fitar da cikin nan in a kuma tsayar da haihuwar in ta kai 25yrs sai ta haihu" ya fad'a yana kallon Mummy da ta saki baki da hanci tana kallon sa.

"Ban gane za'a fitar da cikin jikin ta ba" Mummy ta fad'a tana kallon sa cikin mamaki da al'ajabin abinda yace d'in. "Yes Mum, bazan iya jure ganin ta cikin wannan yanayin ba gaskiya i can't, is better a cire cikin nan gaba in ta sake girma sai ta haihu" ya fad'a a sanyaye har da karyar da wuya ko za'a tausaya masa.

Umm da mamaki ya hana ta magana tace, "Wai cikin za'a cire Zaid?". D'aga mata kai yayi kafin yace, "To meye amfanin shi yana wahalar min da ita, look at her ji yadda ta koma kamar ba ita ba".

Mummy ta kalli Umma itama ta kalle ra cikin mamaki Mummy tace, "Kul kaji ka aikata wannan d'anyen aikin da kake furtawa, kyautar da Allah ya baku wacce ba kowa yake bawa ba kake cewa zaka zubar? Ka sani ko wannan ne kad'ai cikin da Allah zai baku a rayuwar ku gabad'aya" ta fad'a cikin gargad'i tana kallon sa. Sai kuwa ya rausayar da kai yace, "Mummy to yanzu haka za'a barta tana shan wahala for god sake? Tayi k'ank'anta da haihuwa gwara a bari sai nan gaba sai ta haihu" ya sake fad'a kamar zaiyi mata kuka.

"Mtswwe tunda har tayi cikin ai ta wuce yarinya meyasa bakayi tunanin yarinya bace ka yi mata cikin? Kaga bana son shirme wannan maganar ka ajjiye ta kar na sake ji kayi ta, kai yanzu in aka barka sai ka zubar da cikin dan rashin hankali, in kuma shine? kad'ai wanda Allah ya nufa zaku samu fa?" Ta sake fad'a cikin fad'a tana kallon sa. Sai kuwa yace, "Shikenan sai mu hak'ura muje gidan marayu mu samo yara biyu mu rik'e su har su girma babu kuma wanda zai san ba mune muka haife su ba, nifa Mummy ita kad'ai ta ishe ni zaman duniya ba lallai sai mun samu yara ba indai tana tare dani bani da damuwar komai, so kawai za'a cire cikin" ya fad'a bilhakki yana kallon ta.

"Kar ka kuskura Zaid ko wacce mace da ka gani da haka take shan wahala in tana da ciki sai dai na wannan yafi na wannan, itama haka Maman ta tasha wahala kafin ta haife ta kuma laulayi da kake gani na d'an lokaci ne da cikin yayi kwari shikenan zata daina, zubar da ciki kuskure ne babba cikin ma kuma na halak dai-dai yake da kisan kai, kayi hak'uri ka kwantar da hankalin ka zata daina nan da y'an kwanaki kad'an" Umma ta fad'a cikin taushin murya tana kallon sa. Mummy tace, "Wahalar ma da Amina tasha a lokacin haihuwar ta ko rabin ta ai batayi ba". Ajiyar zuciya yayi badan wai ya yadda ba ya kalli Ibteesam d'in da take bacci sai ya mik'e ya fita Mummy ta bishi da kallo. Zahra tayi dariya bayan fitar sa haka ma Jidda.

Shi kuwa yana fita b'angaren Daddy ya shiga ya tarar da Anty Amina a tsaye ita da Daddy da alama fita zasuyi, Daddy yace, "A'a Zaid muna shirin shigowa mu duba Daughter sai gaka." Baice komai ba kawai ya zauna a kan kujera fuskar nan a had'e Daddy ya kalle shi yace, "Lafiya dai?". "Daddy babu lafiya" ya fad'a yana kallon sa. "To meye ya faru?" Daddy ya tambaya yana kallon sa.

"Daddy Precious tana shan wahala kullum bata da lafiya shine na yanke hukuncin za'a fitar da cikin nan da 3years sai ta haihu shine Mummy take ta fad'a wai kar na sake fad'ar hakan, su basa ganin wahalar da take sha ne? Kowa ya daina sonta ya koma son abinda yake cikin ta" ya fad'a kamar zaiyi kuka fuskar nan a had'e tamau. Daddy ya kalli Anty Amina da ita ata kalle shi da mamaki da kuma al'ajabi Daddy yace, "kar ka kuskura ka aikata wannan d'anyen aikin na fad'a, wannan ai shirme kake k'okarin aikatawa kuma ba soyayya kake nuna mata ba indai zaka iya kashe abinda yake cikin ta". Kallon Anty Amina Zaid yayi yace, "Anty kinji ko, duka yanzu basa son ta kowa ta abinda yake cikin ta yake yi bata ita ba, nikam zan iya hak'ura da haihuwa akan samuwar lafiyar ta". Anty Amina da ta kasa magana tace, "Abinda ake fad'a maka ai shine gaskiya Zaid, in ka zubar da cikin jikin ta kai kanka sai kazo kana dana sani a nan gaba kayi hak'uri na d'an lokaci ne komai zai wuce nan da y'an kwanaki kad'an, amma kar na sake jin maganar abortion a bakin ka."

Baice musu komai ba kawai ya wuce ya hau saman sa, Daddy ya bishi da kallo sannan yace, "na rasa ranar da Zaid zaiyi hankali Wallahi, in banda shirme wannan wacce irin magana ce haka?". Dariya tayi kad'an tace, "Gaskiya dai". Baice komai ba kawai suka wuce suka fita.

Zaid bai koma part d'in su ba sai dare dan baya jure ganin Ibteesam a halin da take ciki ba hankalin sa tashi yake ba kad'an ba, sanin da mutane a tare da ita bai koma ba sai bayan sallar i'sha ya shiga ya samu Zahra da Jidda a k'asa suna kallo ko kallon ma baiyi ba ya wuce zuwa sama, Zahra ta kalli Jidda tace, "ohhh kinga bawan Allah nan da gaske fushi yake akan an hana shi zubar ea cikin Anty Ibteey, ni kam Allah ya sani ban tab'a ganin soyayya zalla irin wannan ba". Jidda tace, "nima dai haka Zahra, sak ya dawo Zaid d'in sa na baya fuska babu walwala babu yawan magana sai kallo kawai, ai koni ina tausayawa Anty Ibteey tana shan wahala sosai wallahi."

Zahra tace, "nima haka wallahi, Allah dai ya raba su lafiya" Jidda ta amsa da amin suka cigaba da kallon su.

A kwance ya same ta a kan gadon sa da alama ma tayi bacci ya k'arasa inda take ya tab'a jikin ta yaji da zafi amma ba sosai ba, ajiyar zuciya yayi kawai ya shiga wanka bayan ya fito ya shirya yayi duk abinda zaiyi kafin ya kwanta sai ya koma falo ya zauna, bud'e ido tayi dan daman ba baccin take yi ba tana so taga abinda yake yi cikin kwanakin nan baya kwanciya da wuri koda sun kwanta da tayi bacci zai zare ta daga jikin sa ya fita, kusan tunda suka dawo daga Dubai ya fito da wannan dabi'ar hakan ya saka ta ci alwashin ganin abinda yake yi shiyasa batayi bacci ba.

Sakkowa tayi daga kan gadon ta fito zuwa falon ta k'arasa inda yake tana kallon sa, yana zaune akan kujera ya d'aga kansa sama ya jingina da kujerar ya kulle fuskar sa hannayen sa k'afar sa na kan center table, zama tayi kusa dashi ta saka hannu ta zare hannayen sa da yake saman fuskar sa ta rik'e hannun nasa tace, "Baby me yake damun ka?". Bai d'ago ba bai kuma yi mata magana ba sai rik'e hannun nata da yayi shima yana matsawa a hankali.

"Ka sanar dani abinda yake damun ka mana pls, na lura kwana biyu baka cikin walwala da nayi bacci zaka tashi ka dawo falo ban sani na ko wani laifin nayi maka". Ajiyar zuciya yayi har lokacin? bai d'ago kansa ba yace, "Babu komai Precious, kawai bana son kwanciyar ne yanzu". Ibteesam ta matsa sosai jikin sa tace, "baka b'oye min duk abinda ya fashe ka haka kuma baka min k'arya meyasa yau kake so ka fara?."? Jin abinda tace ya saka ya d'ago ido ya kalle ta sai kuwa gaban ta ya fad'i ganin yadda yanayin fuskar sa ta koma ga idanun sa? yayi ja ta kasa d'auke idon ta daga cikin nasa tana karantar abinda take ganowa a ciki, "Precious bana so naga kina shan wahalar nan kullum baki da lafiya sai naga kamar laifi nane da na bari kika yi ciki yanzu, da na yanke hukunci cire cikin nan da 3years sai ki haihu lokacin kin kai 25year su Daddy sun hana, gabad'aya cikin ya fita daga raina sabida wahalar da kike sha" ya fad'a yana murza yatsun ta dake cikin hannun sa.

"Indai wannan ne kar ka damu Baby nima haka Mama na tasha wahala kafin nazo duniya, wannan ya ai ba komai bane a haka nawa da sauk'i a kan na wasu dan haka ka daina damun kanka kaji" ta fad'a masa cikin sigar lallashi tana kallon sa.

Ajiyar zuciya yayi kawai baice komai ba ta sake cewa, "Bayan wannan akwai abinda yake damun ka fad'a min" ta fad'a tana kallon idon sa, janye idon sa yayi ita kuma ta kwanta a jikin sa yace, "bana son takura ki ga rashin lafiya ga kuma ni shiyasa nake daurewa na k'yale ki, but ina tsananin buk'atar ki Preciousssss". Murmushi tayi dan ta karanci hakan a idon sa kuma yayi k'okari sosai dan tunda ta fara rashin lafiyar nan bai neme ta ba duk da yana so itama kuma tana so, "Baby ko ina cikin numfashin k'arshe ne zan mallaka maka jiki na balle kuma ina ji ina gani ina tafiya ina magana" zaiyi magana tayi saurin had'e bakin ta da nasa.

Abinka da wanda yake jiran kiris nan da nan ya manta da mara lafiya yake tare.

Bayan wasu watanni.

Zaid ne a zaune yana ta aikin danna laptop Ibteesam tana zaune a kusa dashi cikin ta ya fito sosai kamar wacce cikin ya kai watannin haihuwa, tayi kib'a fuskar ta ta d'an tasa kad'an.

"Magana fa nake maka Baby" ta fad'a cikin shagwa6a tana kallon sa da yake aikin sa kamar ba dashi take ba, sai da ya gama aikin sa kusan mintina ashirin sannan ya kalle ta yace, "ina jinki". Ranta ya b'aci amma da yake ita take nema sai tace, "kaga Zahra k'anwa tace haka Jidda, ga kuma Asiya ita kuma kasan wanda zai auri Zahra cousin d'in na ne haka wanda zai auri Jidda, ga Fateema can ita ma kuma auren gida ne, kaga in aka gama na Zahra da Jidda a nan Gomben za'a tayi nasu Fateema dan Allah ka barni naje Gomben nan dan matsayin annabi" ta fad'a kamar tayi kuka tana kallon sa da shima ita yake kallo fuskar nan a d'aure tamau yana.

"Precious kina so aita maimaita magana guda d'aya bayan kin san ni bana so, ba'a nan za'ayi bikin Jidda da Zahran bane?" Ya fad'a yana kallon ta. "Eh a nan ne, amma ai akwai wanda za'ayi nasun dai a can tunda kaga a can zasu zauna mazajen su kuma duka y'an can ne" ta fad'a cikin rausayar da kai a dole sai yaji tausayin ta. K'asa ya sakko kusa da k'afar ta ya d'aga k'afar ta ya d'ora a kan table d'in da laptop d'in sa taje kai ya fara matsa mata kamar yadda ya saba kullum yace, "In akayi a nan d'in kika je ai is okay basai kinje can ba, ki bari Aman da Amani su zo duniya da kaina zan kaiki Gomben amma banda yanzu".

"Amma k'anne na ne fa ai bai kamata ace ban je ba nice fa babba a cikin su, dan Allah kayi hak'uri naje kar kace A'a" ta fad'a sosai muryar ta take rawa sabida kuka take so tayi. Sai kuwa ya sake tamke fuskar sa ya d'ago ya kalle ta yace, "Baza kije ba, na nan zaki je shima kuma kika b'ata min rai a kai wallahi shima baza ki ba, bani da hankali zan barki kije har Gombe da wannan cikin a jikin ki ko an fad'a miki ban san abinda nake yi ba,? Kar na sake ji kinyi min maganar zuwa Gombe in ba haka ba ranki ne zai b'aci, kije wanda za'ayi a nan shima ban yadda da kwanan gidan biki ba" ya fad'a cikin kakkausar murya yana cigaba da matsa mata k'afar tata.

Hawaye take kawai bata ce komai ba dan tasan shikenan ta k'are tunda har ya ce baza taje ba, kiran sallar da akayi ya saka shi ya mik'e yayi alwala ya fita ko kallon ta baiyi na dan baya so ma yaji tausayin ta, mik'ewa tayi tayi sallah itama sannan ta sakko ta fita zuwa part d'in Mama, da kuka ta shiga falon Anty Amina, a zaune take ita da bakuwa taga shigowar ta tana kuka hankalin ta ya tashi ta rik'o ta tace, "Ke lafiya kika shigowa mutane babu sallama sai kuka?". "Mama wai bazan je Gombe ba yanzu tsakani da Allah an kyauta ace banje ba,? Na fad'a masa a jirgi zamu je ba mota ba amma yak'i wai sai na haihu naje" ta fad'a taba kuka tare da kwanciya a jikin Mama.

Yayar Anty Amina da take zaune a wajan tace, "gaskiya dai babu dad'i ace bikin kannen ki guda da y'an uwan ki ace baki je ba dole baza kiji dad'i ba, amma fa ta wani b'angaren yana da gaskiya lafiyar ki ai tafi komai, ki duba fa cikin ki kwata-kwata wata bakwai amma kalli yadda ya girma kamar wata tara, ai bakin mutane ma a bin gudu ne dan yanzu anta tanka cikin kenan in wani kasan shi wani ai baka sanshi ba." Sai kuwa ta sake fashewa da kuka tana fad'in, "Yanzu? Anty haka zan zauna banje bikin ba? Duka shagalin fa acan za'ayi amma yace bazani ba."

Anty Amina tace, "kwarai kuwa haka zaki zauna a gida, ai yayi miki ma da ya barki zuwa na nan d'in sai kiyi hak'uri kinfi kowa sanin halin mijin ki, ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki da kansa zaki ga ya kaiki".

Daddy da yake shigowa falon dan su gaisa da Yayar Anty Amina yaji maganar bayan sun gaisa ne yake tambayar abinda ya faru Mama ta fad'a masa, "Tunda a jirgi zasu je banga amfanin hanta d'in da zaiyi ba, bara na kira shi" Daddy ya fad'a yana fitowa da waya tare da fita daga falon. Ba'a jima ba Daddy yayi Anty Amina waya ta turo Ibteesam ta tura ta ta fita falon a hankali, a zaune ta ganshi tunda yaga fitowar ta ya girgiza kai dan ya fahimci k'ara ta kawo kenan, sai da ta zauna sannan Daddy yace, "Daughter yaushe ne tafiyar Gomben?". Kanta a k'asa tace, "ranar lahadi ne". "Kai Zaid ka barta taje tunda a jirgi zasu je ba kuma musu nake nema a nan ba umarni na baka" Daddy ya fad'a yana kallon sa shi kuma yana kallon ?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
ta. "Toh" shine abinda ya furta kawai ya mik'e ya fita.

Tun daga ranar ta fara fuskantar fushin sa wanda tunda suke dashi bai tab'a yin irin sa ba, kallon ta sai yaga dama yake yi balle magana sai yaga tana son wani abun in yaga dama ya kawo mata in baiga dama ba ya share ta, a haka aka fara bikin su Jidda da Zahra da kuma Asiya amma duka bata da walwala, ranar alhamis aka yi musu kamu juma'a akayi dinner asabar aka d'aura aure aka kai Asiya gidan ta, sai a d'aurin auren Ibteesam taga Khalid wanda rabon da ta ganshi tun rabuwar su ta k'arshe.

Haka Ibteesam take sukuku gashi an gama komai gobe da safe jirgin su xai d'aga zuwa Gombe amma duk sai taji tafiyar ta bar kanta? sabida mugun fushin da yake yi da ita ta d'auka na d'an lokaci ne amma sai taga anfi kwana biyar bai daina ba, kashe wayar ta tayi dan kar ma wani ya neme ta akan tafi Gombe ta kwanta tana ta kuka har tayi bacci, tana cikin bacci da safe taji ana jan k'afar ta tana bud'e ido ta ganshi a kanta fuskar nan a had'e kawai ya saka mata waya a kunne, muryar Mummy taji tana fad'in, "Baby baza ki je bane?". Kallon sa tayi taga yana kallon ta sai ta sunkuyar da kai tace, "Mummy kuje kawai bazan je ba bana jin dad'i gabad'aya." Mummy tace, "kodai Zaid ne ya hana ki?". Girgiza kai tayi kamar tana gaban ta tace, "A'a Mummy kawai gajiyar biki ce bayana kamar zai b'alle". "Ai kinsha hidima, babu wanda baice ki zauna ki huta ba amma kika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login