Showing 81001 words to 84000 words out of 171073 words

Chapter 28 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7853

kuwa sanyin hannun ta da yake shiga cikin sa ba k'aramin dad'in hakan yake ji ba sai lumshe ido yake yana jin wani irin yanayi mai dad'i yana shigar sa, amai yaji yana taso masa gashi a kan hanya, bud'e k'ofar motar yayi ya d'an zura kansa yana shak'ar fresh air da take kad'awa, hanyar da yake babu motoci da mutane sosai sai ya tsaya a haka yana jiran yayi aman amma yak'i zuwa, ciwon cikin yake ji yana k'aruwa sosai haka aman ma, jikin sane ya soma rawa kar-kar hakan ya bata tsoro ta motsa hannun ta da yake cikin sa tana fad'in, "Sannu, muje asibiti kawai dan Allah".

Dawo da kansa yayi cikin motar ya kwantar da kujerar da yake kai jikin sa har lokacin rawa yake, "ki danna min ciki na zai daina" ta fad'a a hankali yana hakki, bata san lokacin da ta fara abinda yace ba ta fara danna masa ciki a hankali yana fitar da numfashi alamun yana jin ciwo sosai, kusan mintina uku a haka yayi saurin mik'ewa ya bud'e motar ya amayar da abinda yake damun sa a cikin, kamar an zare masa ciwon cikin haka yaji ya dawo cikin motar yana ajiyar zuciya, ruwan da yake motar ya d'auka ya wanke bakin sa ya juye ragowar akan aman wajan ya koma kamar babu komai sai ruwa sannan ya kulle k'ofar motar, "thanks you" ya furta murya a sanyaye yana kallon ta.

D'auke kai tayi bata amsa ba taji ya sake rik'o hannun ta yana kalla, "abinda aka zana miki yanzu babu saura kad'an" ya tambaya yana sake zubawa hannun nata ido yana kallon zanen henna da ya goge, kallon ta yayi yaga bashi take kallo ba sai yace, "Yaushe zaki kuma yi?". "Sai na samu time" ta bashi amsa ba tare da ta kalle shi ba.

"Precious" ya furta cikin murya mai dad'i yana kallon ta, kallon sa tayi ta kawar da kai tace, "wacece?". Da ido ya nuna ta alamun ita, girgiza masa kai tayi alamun a'a tana tab'e baki, d'an murmushi yayi kad'an ya mik'e zaune sosai yana kallon titi yace, "To wace in ba ke ba?". "Your wife" ta fad'a k'asan mak'oshi tana hararar sa k'asa-k'asa.

"Kece ai". Kallon sa tayi shima ita yake kalko a lokacin tace, "Ba ni ba, wacce muka had'u a asibiti." D'an tab'e baki yayi ya yatsine fuska yace, "Ohh Eman?". "Whatever" ta bashi amsa a d'an fusace tana hararar sa. "Meyasa ranki ya b'aci?" Ya fad'a yana rik'o hannun ta yana matsawa a hankali.

"Meyasa baka tab'a fad'a min kana da mata ba?". "Nayi tunanin Daddy ya fad'a miki cos ni ban d'auki auren matsayin aure ba, but are you jealous?" Ya tambaya yana d'aga mata gira guda d'aya.

"For what reason zanyi kishi? Kawai na tambaye ka ne" ta fad'a tana tab'e baki tare da kawar da kanta gefe, kallon ta yake dan yanayin ta bai gwada abinda ta fad'a ba sai ya samu kansa da yin y'ar dariya kad'an yace, "kina so kiyi k'arya, i don't know why". Shagala tayi da kallon sa ganin yadda yayi mata bala'in kyau kamar ba shi ba, fuskar sa ta washe haqoran sa sun bayyana sai hakan ya k'arawa fuskar sa kyau da kwarjini, sai ta tsinci kanta da fad'uwar gaba a kan hakan tayi saurin d'auke kanta ba tare da tace komai ba, "Precious!" Ya sake furtawa a lokacin ya katse mata tunanin da ta tafi.

"Uhum" ta samu kanta da amsawa ba tare da ta sani ba, bud'e idanu yayi waje da mamaki ya kalle ta sai kuma ya sake yin murmushi yace, "Wowww". Itama sai ta samu kanta da sakin murmushi ta saka hannu d'aya ta kulle fuskar ta tana dariya kad'an, "Shyer girl, i like it" ya fad'a yana kallon ta cikin yanayin da bai san irin sa ba.

"For the second time, do you love me?" Ya fad'a yana sake murza hannun ta da yake cikin nasa har lokacin,? damm gaban ta ya fad'i ta runtse ido jikin ta yayi sanyi ta bud'e fuskar ta tace, "Ban sani ba nima" ta fad'a a hankali tana kallon gefe d'aya. "Okay, still you love him right?". Kallon sa tayi sai taga yanayin sa ya canja lokaci d'aya fuskar ta koma kamar koda yaushe babu murmushi ko kad'an a kanta, "Who?" Ta tambaya cikin rainin hankali.

Sake tamke fuska yayi ya juya k'wayar idon sa ya kalle ta yace, "Ban sani ba" ya fad'a yana mata kallon da ya kusa saka ta fitsari a wando.

Shiru tayi masa bata bashi amsa ba duk da ta tsorata da kallon da yake mata, "no answer?" Ya fad'a cikin muryar da take nuna ransa ya fara b'aci, "shima ban sani ba ko ina son sa har yanzu" ta fad'a kamar tayi kuka. Ajiyar Zuciya yayi ya kalle ta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya kunna motar suka fara tafiya, "meyasa kike so kiyi k'arya?" Taji ya fad'a ba tare da ya kalle ta ba.

"Ba k'arya nake ba" ta bashi amsa itama ba tare da ta kalle shi ba, "another one" ya furta yana tab'e baki, "i love him more than you" ta furta cikin d'aure fuska tana kallon gefen titi. Wani murmushi yayi mai bayyanar da zallar takaicin sa ya kulle idon sa yana tuk'a motar, kallon sa tayi ta kalli titi taga yana nufar inda wata mota take gashi ya kulle idon sa, "zaka daki wata mota fa, ka bud'e ka zaka kashe mu" ta fad'a tana zare ido tana kallon titi, har lokacin bai bud'e ido ba sake nufar wajan yake tunda baya ganin abinda yake yi, gab da zai daki motar ta saka hannu ta juya sitiyarin motar sukayi gefe ya taka burki motar ta tsaya ta fad'a kansa gabad'aya, gam ya rik'e ta ya bud'e idon sa yana kallon cikin nata idon, itama shi take kallo cikin firgice da tsoro dan har lokacin tsoron bai barta ba k'irjin ta sai dukan biyar-biyar, take yi, kallon ta yake sosai dan yanayin da ta shiga na tsoro ba k'aramin burge shi tayi ba dan idon ta yyi wani irin kyau kamar ba nata ba, sajen fuskar sa ya goga mata a kumatun ta tayi saurin rufee ido tana jin wani iri a jikin ta, ganin ta kulle ido ya bashi damar sake k'arewa fuskar ta kallo yana jin kamar ya mayar da ita cikin sa sabida son da ta da yake karuwa kullum a zuciyar sa, idon sa ya dire a kan d'an smallest lips d'in ta da bushe, lumshe ido yayi ya bud'e a kan lips d'in nata, a hankali yake kai bakin sa zuwa kusa da nata har lokacin idon ta a rufe yake taji saukar lips d'in sa masu laushin gaske a kan nata, yunk'urawa tayi da niyar barin jikin sa taji ya rik'e ta sosai ya fara kissing d'in lips d'inta in slowly.

Ido ta bud'e a hankali akayi sa'a shima ya bud'e nasa suka had'a ido tayi saurin kulle nata tana jin yadda yake wa bakin ta kamar ya samu alawa, kusan minti biyu suna a haka zuwa lokacin yanayin sa ya soma canjawa hakan ya saka shi dole ya zare bakin sa daga cikin nata ya mayar da kansa kafad'ar ta idon sa a kulle, "ka barni na koma na zauna, bana son irin haka" ta fad'a muryar ta rawa sosai.

Bai hana ta ba ya sake ta ta koma ta zauna tana gyara zaman mayafin jikin ta ranta a b'ace, hawaye ne suka fara sakkowa daga idon ta take haushin? ya sake cika mata zuciya tana mai jin takaicin kanta da har ta sakar masa fuska haka, kallon ta yake da kyau bayan ya dawo dai-dai ya d'aga burkin motar suka cigaba da tafiya, muryar ta ya tsinta tana fad'in, "Ka mayar dani gidan mu" ta fad'a? cikin kuka tana goge hawayen ta.

"Meyasa kike kuka?" Kallon sa tayi ta zuba masa harara tace, "Baka san ma dalilin da ya saka nake kukan ba?". "Inda na sani ai bazan tambye ki ba" ya sake fad'a hankalin sa yana kan titi. Sai kuwa ta sake fashewa da kuka dan ganin rainin hankalin da yake mata, "tunda muke da Khalid bai tab'a rik'e koda hannu na ba sabida shi sona yake amma kai da yake ba sona kake ba ga irin abinda kake yi min, ni ka mayar dani gida dan Allah" ta fad'a tana kuka sosai kamar wacce aka yiwa mutuwa.

Jin abinda tace ya saka shi yayi murmushi mai sauti yace, "Ya kyautawa kansa, dan wallahi da sai na saka an cire masa hannun da bazai sake tab'a wata mace a duniya ba" ya k'arasa fad'a yana d'auke fuska.? Kallon sa tayi dan ita ta fad'a ne fa dan yaji haushi amma sai taga akasin hakan, "look, wai dan nayi kissing lips din ki kike kuka?." Sai ta sake fashewa da kuka tace, "Bana so to, ai kasan haramun ne zunubi Allah yake rubuta mana ka saka nayi abinda ban tab'a yi ba tunda nazo duniya, yau na sake tabbatarwa da ba sona kake ba."

"Tab ai kam sai ki shirya dan zaki yi abinda yafi kuka ma ba kuka ba, even kiss kina min kuka ina ga...." saurin kallon sa da tayi ya saka shi ya fasa fad'ar abinda zai ce ya saki murmushi mai sauti yana kallon idon nata, d'auke kai tayi ta cigaba da kukan ta yace, "kina so kice ba son ki nake ba ina sha'awar kine right?".? Kallon sa tayi da sauri jin ya fad'i abinda yake ranta, har lokacin fuskar sa a sake kamar bashi ba, ta gefen ido ya kalle ta yace, "Kar ki mamakin ya akayi nasan abinda yake ranki, Allah ya bani baiwar hakan."

D'an runtse ido yayi jin jijiyar kansa ta harba ya d'an yatsine fuska dan shi kansa yasan yayi magana da yawa da kansa zaiyi ciwo, "Precious kenan, kin manta kwana nawa kika yi a hannu a Kaduna ban miki komai ba sai yanzu?" Ya fad'a yana d'an dafe jijiyar kansa.

"To meyasa kake so ka tab'a ni bayan ba haka ake soyayya ba?" Ta fad'a bayan ta gama kukan ta share hawayen ta.

"Na kira ki nace kinci abinci, wanne kaya kika saka, kinyi aiki yau, kin gaji, shine love a wajan ki? Wannan shashancin ba dai-dai yake dani ba, cos bana son yawan magana u know."

"Okay da baka san yawan mgana sai akace ka dinga tab'a ni any how?" Ta fad'a a fusace tana kallon sa, kallon ta yayi kafin ya mayar da hankalin sa ga tuk'i yace, "Imagine ni mijin kine ya zaki yi?" Ya fad'a yana kallon titi yana tafiya a hankali kamar wanda baya so suje inda zasu.

"It can't be possible, wannan ba abinda za'ayi imagine bane dan bazai faru ba" ta fad'a cikin tsiwa da rashin kunya, tab'e baki yayi ya cigaba da abinda yake yi yaji muryar ta tana fad'in, "Bana so naga ka saka English wears d'in nan amma dake bani da mahimmaci a wajan ka kasa dainawa kodan ni d'in, i told you bana son wannan zanen na kanka amma still kak'i kayi yadda nake so" ta fad'a muryar ta a sanyaye tana wasa da gefen mayafin ta.

Ajiyar zuciya yayi yace, "bana iya saka kaya manya suna damu na over, but zan gwada ko dan ke d'in". Bata ce komai shima kuma yaja bakin sa yayi shiru zuwa lokacin an fara kiran sallar la'asar.

Kallon titi yake dan shi kansa bai san inda zasu je ba kawai yana jin dad'in tafiyar ne shiyasa kawai yake gaba, "ina zamu je ne wai?" Ta tambaya tana kallon sa.

Kansa ya nuna mata da hannu dole tayi shiru dan ta fahimci kansa na ciwo kenan, hanyar gidan su kawai ya d'auka direct bai sake kula ta ba har suka je k'ofar gidan su ya danna horn aka bud'e gate d'in ya shiga da motar ciki, kallon sa take tana so ta tambaye shi ina suka zo amma ya tamke fuska ya k'i bata damar hakan, parking ya gama ya kashe motar ya kalle ta yace, "Bana son wata magana kawai muje ko na d'auke ki" yana fad'a ya bud'e motar ya fita dole itama ta bud'e tabi bayan sa, kallon gidan take tana mamakin girman gidan dan a yanayin da suka shigo gidan ya bata tabbacin gidan su ne, k'ofar da zata sada shi da saman sa suka bi ya bud'e k'ofar suka fara hawa saman, falon take k'arewa kallo babu wani tarkace amma yayi kyau sosai, bai kalle ta ba shiga bedroom ita kuma ta ja burki a wajan tana kallon mulkin mallaka irin na Zaid, shi komai sai abinda yake so za'ayi, bata jima ba ta ganshi ya fito da alama alwala yayi ya kalle ta yace, "Baza kiyi sallah bane?". Hararar sa tayi tace, "zanyi." "Okay, ni kike jira na zama ruwa kiyi alwala?". "Ni ina da alwala" ta bashi amsa tana d'auke kanta daga kansa.

"Oh wannan alwalar ai ta jima da lalacewa, shyer girl u have to change it oh ready waccan tayi damage, ko kina so kice u did not feel anything when we kissed each other?" ya fad'a yana d'auko sallaya ya shinfid'a.

Kamar k'asa ta tsage ta shiga haka taji sabida kunyar da ya bata, ta kalle shi ta gefen ido taga harkar sa shi yake bilhakki ya fad'a mata har zuciyar sa, "A ina bathroom d'in?" Ta fad'a tana kallon d'akin.

Da hannu ya nuna mata bedroom d'in ta nufi ciki jikin ta a sanyaye, d'akin ne ya d'auki hankalin ta ganin girman sa kamar falo gashi tsaf dashi sai khamshi yake kamar d'akin mace, k'arewa d'akin kallo take kafin ta nufi k'ofar da ta gani dan tasan nan ne band'akin ta saka slippers d'in da yake bakin band'aki ta shiga, da sauri tayi alwala ta fito tana mayar da d'ankwalin ta idon ta ya sauka a kan zanen hoton ta da yake manne a d'akin, hoton ya ja hankalin ta ta nufi wajan a hankali idon ta akan hoton har taje inda hoton yake, "wowwwww" ta furta ganin yadda tayi bala'in kyau a zanen kamar zama tayi yana kwafar ta yana zanawa sabida kyauwun da tayi, kallon na kusa da hoton ta tayi tace, "Wannan itace Maman nasa kenan, Allah sarki ga kama nan suna yi sosai, Allah ya jik'an ta". "Amin, in kin gama kallon kizo muyi sallah" ya Fad'a yana rik'e da handle k'ofar yana kallon ta.

Da sauri ta bar wajan ta fito taga har ya shinfid'a sallaya suka tayar da sallah, a nutse sukayi sallar babu tsawaitawa kuma ba'a yita Shape-shape ba, lokacin da suka idar ta kalle shi tana mamaki daman ya iya sallah haka ita ai kallon d'an iska take masa wanda baya sallah, batayi aune ba taji yace, "Sai akace miki y'an iskan basa sallah ne?" Ya fad'a yana mik'ewa tsaye tare da ninke sallayar ya mayar mazaunin ta.

"Na shiga uku" ta furta a fili ba tare da ta sani ba dan ya koma bata tsoro ba mamaki ba, kallon ta yayi ya tab'e baki ya zauna a kan kujera tare da d'ora k'afa kan d'aya, bata tashi daga kan sallayar ba ta zauna tana kallon tv ba tare da tasan abinda zatayi ba, k'arar wayar ta ya katse mata tunani ta kalli wayar ta saci kallon Zaid ganin kamar baya kallon ta ya saka tayi niyar d'aga wayar, kafin tayi receiving call d'in taji yace, "Kika d'aga wayar sa a gaba na zaki saka ni a cikin bad condition, pls ki shiga bedroom ko Gym room abeg" ya fad'a yana had'e hannayen sa ba tare da ya kalle ta ba.

Kallon sa tayi sai taga jikin sa ya saki lokaci d'aya kamar bashi ba sai ya bata tausayi matuk'a sai ta samu kanta da kasa d'aukar wayar tana kallo har ta katse, kiran ya sake shigowa ta kalla taga sunan Khalid d'in ne again sai ta samu kanta da kashe k'arar wayar, "you can pickup, let me give u some space" ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya bud'e velconcy ya tsaya yana shak'ar iska yana maida numfashi dan sosai sa ta fara wani irin bugu kamar zata fito.

Kashe wayar tayi gabad'aya take jikin ta yayi sanyi take jin takaicin Khalid da ya kita a lokacin, mik'ewa tayi ta ninke sallayar ta ajjiye inda ya ajjiye waccan ta nufi inda yake tsaye tana kallon sa ya dafe saitin zuciyar sa yana sauke numfashi da sauri, motsin da yaji ya saka shi ya juyo ya fito daga velconcy d'in ya kulle k'ofar ya kalle ta yace, "Kin gama?". Sunkuyar da kai k'asa tayi tace, "I'm sorry ban san zai kira ba dana kashe wayar".

Fuskar ta ya rik'e da hannayen sa duka biyun ya d'ago da ita ya kalli idon ta yace, "bana so na ganki da wani precious, zuciya ta kamar ta buga haka nake ji, i love you morethan anything, in kika cire Mama na da Daddy babu wanda nake so sai ke." Sosai kalaman suke ratsa jijiya da tsoka da k'ashi da b'argon dake cikin k'ashin ta, nan take taji wani irin yanayi na musamman yana jin jinin jikin ta yana zaga ko wanne b'angare na jikin ta, magana take so tayi masa amma ta kasa hakan ya saka shi ya cigaba da cewa,

"In na kuma ganin ki tare dashi zan saka a kashe ni, bana son sa bana son ganin sa, ki rabu dashi in kina son zaman lafiya a duniya" ya fad'a cikin kakkausar murya har lokacin yana rik'e da fuskar ta.

"Ka daina cewa komai zakayi kisa a kaina, ba ta haka ake samun soyayya ba" ta furta a hankali tana jiran abinda zaice, lumshe ido yayi ya bud'e a cikin idon ta yace, "Ni a haka zan nemi tawa soyayyar, indai ina da rai bazan baza ki tab'a zama da wani matsayin miji ba bayan ni, nine mijin ki precious, wallahi nine mijin ki tun daga nan duniya har a aljanna" ya fad'a cikin tsawa yana kallon ta cikin masifa.

Kamar zatayi kuka tace, "Ka gani ko, komai cikin fad'a kake yin sa baka min komai a hankali, dole nafi son wancan a kanka sabida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login