Showing 87001 words to 90000 words out of 171073 words

Chapter 30 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7845

sannan ne kuma asirin kiyayyar da take yiwa yarinyar zai karye dan tawa kiyayyar babu ita a ranta sai dai kawai ta share, tana kuka tana mu yafe mata Safiyya tace ta fad'i sunan gidaan marayun daa ta kaita amma kafin ta kai ga fad'a rai yayi halin sa."

"Safiyya ta sake gigicewa a lokacin ta dinga kuka Hajiya ta ta dinga mata hak'uri tana rarrashin ta ita kuma tana cewa tana jin tsoron ranar da Amina zata dawo hankalin ta tace mata ina Baby ita kuma tace mana neme,? Gashi a lokacin tana goyon Zahra ne sai Zahra ta koma a bar tausayi dan gabad'aya Safiyya damuwar da take ciki bata barin ta kula da Zahra."

"Tunda muka bar Gombe ta dage a kan sai mun fara tsayawa a Kano haka akayi muka dawo Kano dinga yawon gidan marayu amma babu Baby babu labarin ta a haka muka hak'ura muka koma Abuja aka cigaba da addu'a, tun daga lokacin kullum cikin damuwa Safiyya take a akan b'atan Baby tun ina rarrashin ta har ya kai ga fara mata fad'a a kan rashin yadda da k'addara."

"Zuwan nan namu Kano take cemin taga wata a asibiti kamar ta santa amma ta rasa a inda ta santa, sai d'azu take min magana hankali a tashe a kan Zahra taga wata yarinya a shagon mai d'inki mai kama dani dan haka ita neman ta zata je, nak'i bada damar hakan sabida ni ban amince da abinda tace ba shiyasa nasan yadda zanyi na hana fitar k'arshe nace su tawo muzo mu duba Zaid a gidan nan ashe sanadin bayyanar gaskiyar komai ne" Abban Zahra ya k'arasa fad'a yana kallon jama'ar falon da suke sauraron sa.

Anty Amina da tame kuka sosai ta goge hawaye ta cikin muryar kuka tace, "Bayan Hajiya ta dawo take tambaya abinda ya faru nake sanar da ita mun rabu da kai kuma Baby ta rasu kace baza'a fad'a musu ba, na had'a k'arya da gaskiya wacce ta saka dole Hajiya ta bar maganar ka ni kuma hakan nake so a lokacin, Baba kuwa bai yadda da maganar sakin ba sai da ya kira ka ka tabbatar masa da hakan shi kuma bai tambaya ina Maryam ba dan a tunanin sa zaka fada masa jikar sa ta rasu amma sai yaji shiru zai maka maganar a lokacin sai wayar ta yanke daga lokacin bai sake neman ka ba, tun daga lokacin nake jina kamar na rasa wani abu daga cikin rayuwa ta amma duk tunani na sai na kasa gane meye shi, nayi kuka a kan hakan amma a banza dan babu abinda nake tunawa sai fuskar Baby itama kuma tunani nake a ina na san yarinyar, hankali na bai fara dawowa kanta ba sai da naga wannan yarinyar taje duba Zaid asibiti gaba na yyi ta fad'uwa in na kalli yarinyar ina ji kamar na tab'a ganin mai irin fuskar ta amma na kasa tunawa, tundaa na dawo gida hankali na ya tashi matuk'a na dinga mafarkai da yarinya budurwa tana yi min murmushi ashe lokacin had'uwa ta da baby ne yazo," sai ta fashe da kuka tana fad'in, "Amma gaskiya Allah sai ya saka min abinda Rabi tayi min, ban santa ba ban tab'a ganin ta amma ta zab'i cutar dani da kuma cutar da yarinyar da bata ji ba bata gani ba, meye ribar ta dan ta raba mu?" ta k'arasa fad'a tana kuka sosai.

Falon yayi shiru ba'a jin komai sai kukan Amina da Safiyya, Umma da ta zuba musu ido tana kallon su dukkan su cikin tausayi, Abban Ibteesam ya d'ora da cewa, "A lokacin da muka ziyarci gidan marayu Ibteesam tana da shekara biyu ne a duniya, kenan tayi rabin shekara a gidan muka d'auko ta, yau shekara goma sha tara kenan dan yanzu Ibteesam shekarar ta ashirin d'aya a duniya, sunce mana a k'ofar gidan marayun aka ganta an ajjiye ta an rbta takarda a kusa da ita an saka sunan ta Maryam sannan ba shegiya bace da iyayen ta, aka d'auke ta aka shiga da ita ciki aka cigaba da rainon ta a cikin yara marayu har Allah ya kaimu, Ibteesam bata san ba mune iyayen ta ba sai jiya shima kuma riska tayi ana maganar sai ta tambaya dan taji komai, na sanar da ita komai sabida tunda taji babu amfanin ayi mata k'arya shiyasa muka snaar da ita gaskiyar komai ashe da rabon ya zata had'u da iyayen ta na asali a yau" Abba ya k'arasa fad'a yana murmushi.

Sai a lokacin Umma tace, "Amma wannan Rabi bata kyauwata kanta ba, Allah da ya halicce mu yace baya tausayin jaririn da aka haifa ya karb'i ran mahaifiyar sa sabida daman ba uwar ce mai rayawa ba shine, amma yana jin tausayin uwar da ta sha wahalar haihuwa ya kuma d'auke mata ran abinda ta haifa sabida radad'i da mahaifiyar zataji, waye yake raba uwa da y'a in ba Allah ba?".

Ibteesam da take zaune a wajan ta zuba musu ido kawai tana kallon su dan ita kam babu wani d'igon hawaye a tare da ita kallon su kawai take yi, Abban tane ya juyo ya kalle ta yace, "Zo Baby". A hankali take takawa har taje inda yake zaune ya rik'o hannun ta ya zaunar da ita a kusa dashi yana murmushi, rik'e hannun ta yayi yana kallon fuskar ta yana murmushi, kafin ya kai ga magana Mummy ta taso ta rik'e hannun Ibteesam ta mik'ar da ita tare da rungume ta a jikin ta, sosai ta matse ta ji take kamar za'a kuma raba su da ita, d'ago da ita tayi daga jikin ta tana share hawayen ta tace, "Baby ga mahaifiyar ki itace wacce ta haife ki" ta fad'a tana jan hannun Ibteesam har zuwa kusa da Anty Amina.

Duk inda uwa take uwa ce nan take jikin Ibteesam ya fara wani irin tsuma ta rungume Anty Amina itama ta rungume ta tana kuka, sai a lokacin Ibteey ta samu damar fashewa da kuka wata irin nutsuwa da bata tab'a jin irin ta ba tana shiga ko wanne sashi na jikin ta, "Kiyi hak'uri Baby ba son raina na tafi na barki ba, ban san na aikata ba kiyi hak'uri" shine abinda Anty Amina kawai take fad'a tana sake k'ank'ame Ibteesam a jikin ta tana kuka.

D'ago da ita tayi daga jikin tana share mata hawaye tace, "Ki daina kuka kinji Baby bazan sake rabin ki ba har abadah wancan lokacin ma ban san nayi ba, Anty Safiyya, Abban Baby duk ku yafe min akan abinda ya faru a baya kun fi kowa sanin halayya ta ba'a hayyaci na nake ba, dan Allah ka bawa Hajiyan Gombe hak'uri akan abinda ya faru ban sani ba" ta k'arasa fad'a tana kuka.

Alhaji Khabir yayi murmushi yace, "k'addara ce fa Allah ya rubuta zata faru babu wanda ya isa ya goge ta, Allah ya nufa baza ki rayuwa da yarinyar ki na tsahon wannan shekarun da suka shud'e sai yanzu, babu komai babu wanda yake tsallake k'addarar sa komai ya wuce kuma tunda Allah ya bayyana ta cikin k'oshin lafiya."

Abban Ibteesam ya kalli Umma da take kallon Ibteesam da Anty Amina tana murmushi shima yayi murmushi yace, "To Alhaji Khabir da kuma Maman Ibteesam guda biyu munyi muku laifi akan wani abu". Abban Zahra ya kalli Abban Ibteesam yace, "babu wani laifin da zakuyi mana har abada, bamu da abinda zamu biya ku har abada sai dai mu dinga yi muku addu'a Allah ya saka muku da alkhairi." Murmushi Abba yayi yace, "A kwanakin baya wata y'ar hatsaniya ta shiga tsakanin Ibteesam da kuma Zaid, to sai mukayi gudun wani abu nida mahaifin sa, ni tsoro na bai wuce kar ace dan bani ba haife ta ba na barta wani abu ya same ta shine abinda ya saka na amince da abinda mahaifin Zaid d'in, a tak'aice dai Ibteesam matar Zaid ce ba tare da ya sani ba itama kuma bata sani ba, bana tunanin dukkan su sun sani d'in in ba yanzu ba" Abba ya k'arasa fad'a yana kallon Ibteesam da kuma Zaid da ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon su d'aya bayan d'aya.

"Haba dai wannan ai ba wani abu bane, mu muma matsayin iyayen baby ne wanda suka haife ta amma kune iyayen ta sabida ku ne kuka raine ta, kuka bata ci, sha, suttura, ilimi, uwa uba tarbiyya mai kyau, bata da wani iyaye har gobe in ba ku ba domin duk wani nauyi da ya rataya a kan mu kune kuka sauke mata shi na tsahon shekara goma sha tara, mu kuwa kwata-kwata shekarar ta d'aya da wani abun a hannun mu, har gobe kuna da iko da Baby baza kuma ku daina amsa sunan iyayen ta ba dan kun yanke hukuncin aurar da ita kunyi dai-dai matsayin ku na iyayen ta" Abban Zahra ya fad'a yana kallon su Umma da murmushi a fuskar sa.

Sosai Abba yaji dad'in kalaman Abban Zahra hakan ya saka shi yayi murmushi kafin yayi magana Daddy yace, "Ibteesam har yanzu kina da damar da zaki ce baza ki zauna da Zaid ba ba dole akayi miki ba, in kina so shikenan in bakya so ki fad'a kar ki cuci kanki" Daddy ya fad'a yana kallon ta.

Shiru tayi ta kasa cewa komai tana mamakin wai ita matar aure ce matar Zaid kuma, Umma tace, "A barta tayi tunani a kan hakan ko Ibteesam?". D'aga kai tayi alamun eh kawai dan bata san me zata ce ba. Daddy ya kalli Zaid da yake kallon su yace, "Zaid ka taya Ibteesam murna ga iyayen ta na asali" Daddy ya fad'a da murmushi yana kallon Zaid d'in.

Tab'e baki yayi ya kalli Anty Amina da take rik'e da Ibteesam har lokacin kafin yace, "Wai dukkan ku kun amince wannan itace mahaifiyar matata? in kun amince ku ni ban amince ba sai anyi DNA na gani da ido na sannan zan amince da abinda kuke fad'a, ta yaya za'a ce itace mahaifiyar ta bayan ga iyayen ta a zaune?" Ya fad'a yana kallon Daddy da shima shi yake kallo yana nuna su Umma.

Wani murmushi Anty Amina tayi mai d'auke da ma'anoni da yawa ta kalli Zaid tace, "Ai jini ba wasa bane Zaid ita kanta taji hakan a jikin ta". D'an tsaki yaja kad'an yace, "To na tambaye ki ne? Bana son in banyi magana da mutum ba ya saka min baki kin sani" ya katse ta da fad'ar hakan ransa a b'ace dan shi bai amince Anty Amina itace mahaifiyar matar sa ba.

"Kai Zaid kana da hankali kuwa? Amina ba babar ka bace?"Mummy ta fad'a tana kallon sa cikin fad'a, d'an tsaki yaja kawai ya bar falon ya koma sama dan shirin tarwatsa masa kai suke yi da maganganun su masu kama da tatsuniya. Anty Amina tayi murmushi mai kyau tace, "k'yale shi Mummy". Shi kam Daddy kunya ce ta kama shi haka ma Abban Jidda dan sai suke ganin kamar Abban Ibteesam zai ga basu yiwa y'ar sa zab'in miji na gari ba tunda gashi a gaban idon kowa yana mayarwa da babar ta magana.

Ibteesam kuwa sosai taji haushin Zaid ganin an fad'a masa itace babar ta amma shine yake mata magana haka kamar wata sa'ar sa, Daddy dai shiru kawai yayi yana tunanin yadda za'a kwashe tsakanin Amina da Zaid a matsayin Sirikar sa babar matar da yake so sama da kowa a duniya.

"Lokacin Sallar i'sha har ya wuce" Daddy ya fad'a yana mik'ewa tsaye, duk tare suka mik'e mazan sukayi alwala a falon matan suka shiga ciki, bayan an idar da sallar Umma da Abba suka Mik'e tare da fad'in, "To mu kam zamu wuce yanzu" Abba ya fad'a yana kallon jama'ar falon. Umma ta kalli Ibteesam da itama ita take kallo tace, "Ibteesam zamu tafi" ta fad'a da murmushi tana kallon ta.

"Yau Ibteesam tana tare da Maman ta ko?" Abba ya fad'a yana kallon ta da murmushi a fuskar sa, "Umma na zauna?" Ta fad'a a hankali tana kallon Umman ta, sai ta bawa Umma dariya ta d'an yi dariya kad'an tace, "Ki zauna mana Ibteesam gobe ma zan aiko Jidda sai ta kawo miki kayan ki." Murmushi ta kuma Ibteesam tace, "To Umma". Daga haka su Umma sukayi sallama suka tafi cike da kewar Ibteesam.

Abban Zahra ya kalli Ibteesam yace, "Baby zance ko Ibteesam?" Sai tayi murmushi itama tana wasa da mayafin ta, "Anty Ibteesam nice Zahra k'anwar ki" Zahra ta fad'a tana dawowa kusa da ita ta zauna tana rungume ta, d'agowa tayi ta kalli Zahra itama tana murmushi cikiin jin dad'in ganin y'ar uwar tata, "akwai Yaya Khalipha yana can madina yana karatu, sai kuma Sultan da Sultana our twins suna Gombe wajan Hajiya sunje hutu" ta fad'a tana kallon Ibteesam da murmushin farin ciki.

Mummy ta kalli Ibteesam da take ta aikin murmushi tace, "Baby zo nan". Ba musu ta mik'e ta koma kusa da ita ta zauna tace, "Baby wacce school kike yi yanzu?". "Ina level 300 a Yusuf mai tama sule" ta fad'a tana kallon Mummyn. "Masha Allah, kice Babyn tamu ta kusa kammala digree d'in ta" Abban ta ya bada amsa yana kallon ta cikin so da k'auna da kuma kewar ta da ta jima a ransa, murmushi kawai tayi batace komai ba tana jin soyayyar Abban ta na shiga ranta fiye da yadda take tunani.

"To Mummyn Baby muma sai mu wuce ko? Nasan yau Baby tana tare da Maman ta ko?" Abba ya fad'a yana kallon Ibteesam dan yasan a wajan mahaifiyar ta zata kwana, bata ce komai ba sai murmushi kawai dan tasan shima zai so ace ta bishi ta kwana a gidan sa. "Abba nima bazan tafi ba a nan zan kwana" Zahra ta fad'a tana sake rik'e hannun Ibteesam.

Mummy ta mik'e tace, "To shikenan ai, Baby sai kinzo" a haka dai sukayi sallama ba son ransu ba suka tafi cikin kewar Baby da ta cika musu zuciya dukkan su.

Falon ya rage daga Anty Amina sai Daddy da Ibteesam da take kusa da Anty Amina a zaune, "Baby bakya jin yunwa?" Anty Amina ta fad'a tana shafa kanta da murmushi a fuskar ta.

"Ganin ki ya saka na daina jin yunwa" ta fad'a a nutse tana kallon ta, murmushi tayi tace, "Ai kuwa haka zaki ci". Daddy da yake kallo su cikin burgewa yace, "ya dai kamata kuci abincin dukkan ku kar farin ciki hana ku cin abinci" ya fad'a lokacin da yake mik'ewa tsaye ya hau saman sa.

Eman ce ta fito falon ta kalli Anty Amina tace, "Anty abinci fa?" Ta fad'a tana wani yatsine fuska kamar tana magana da sa'ar ta, had'a ido sukayi da Ibteesam Eman tace, "Anty wannan fa?" Ta fad'a tana nuna mata Ibteesam. Anty Amina ta kalli Eman tace, "Ibteesam kenan d'iya ta" ta fad'a tana mik'ewa tsaye tare da rik'e hannun Ibteesam d'in.

Basu sake ce mata komai ba suka wuce ta ta bisu da kallo tana k'wafa dan babu abinda bata ji ba rainin hankali ya saka ta tambaya,? d'aki Anty Amina ta shiga da Ibteesam ta zaunar da ita a bakin gado itama ta zauna tace, "Yanzu me kike so kici?". Murmushi tayi tace, "Kece zaki zauna Mama, ki fad'a min duk abinda kike so na dafa miki da kaina" ta fad'a tana mik'ewa tsaye.

"A'a, shekara nawa bana tare dake? Ban tab'a dafa abinci kinci ba, ban tab'a baki abinci a baki ba, dan haka ki fad'a min abinda kike so yanzu na dafa miki da kaina na kuma baki a bakin ki" ta fad'a tana mayar da ita ta zaunar tana kallon ta da zallar qauna irin ta uwa da y'a. "Ni Mama babu abinda nake so naci dan bana jin yunwa" ta fad'a a shagwa6e tana kallon ta.

Maimakon tace wani abu sai ta zauna kusa da ita tare da kwantar da kanta a kafad'ar ta tana buga bayan tace, "Baby ina son ki son da ko wacce uwa take yiwa y'ar ta, shekara da shekaru inaa fama da kewar ki yau kin dawo gare ni ki fad'a min abinda kike so kawai". "Mama coffee kawai zansha bana cin abinci da daddare" ta fad'a cikin soyayyar Maman nata da take sake bin ko wanne lungu na jikin ta.

"Ki zauna bara na kawo miki coffee yanzu" ta fad'a tana mik'ewa, rik'o hannun ta Ibteesam tayi ta mik'e ta ajjiye mayafin jikin ta tace, "Mama muje tare" murmushi tayi suka fita tare har zuwa kitchen, ko wanne zuciyar sa cikin farin ciki suka gama had'a coffee suka dawo falon Anty Amina suka zauna, kamar yadda ake bawa yara abinci haka Anty Amina takee bawa Ibteesam coffee har sai ds ta shaye kafin ta kwantar da ita a cinyar ta, Cikin takun sa na isa da k'asaita ya shigo falon yana kallon Ibteesam a kwance a cinyar wacce yafi jin haushi sama da komai a duniya.

Kama k'ugu yayi yana kallon su ta yaya za'a ce itace Maman Ibteesam in banda kawai ana so a raina masa hankali, da wannan tunanin ya shigo falon ba tare da yace k'ala ba ya zauna a kan kujera, babu wacce bata gan shi ba a cikin su suka d'auke kai kamar basu ganshi ba, "Precious" ya fad'a a hankali yana kallon tv.

Banza tayi masa dan har yanzu haushin sa take ji akan abinda yayiwa Maman ta d'azu, janye ta Anty Amina tayi daga jikin ta tare da fad'in, "Na bar cake a oven ina zuwa" ta fad'a tana mik'ewa tsaye tayi kitchen da sauri, da mugun kallo Zaid ya bita kafin yaja dogon tsaki, tana hankalce dashi ranta ya sake b'aci ganin irin kallon da yake jifan mahaifiyar ta dashi, "Precious". Ya sake fad'a yana kallon ta.

Idon sa ta kalla ta buga masa harara tare da tsaki itama tana kallon gefe, a lokacin Anty Amina ta dawo da cake a hannun ta tana fad'in, "Baby karb'i wannan kici" ta fad'a da murmushi tana niyar sakawa Ibteesam cake d'in a baki, tankwab'e hannun Anty Amina yayi cake d'in ya fad'i k'asa dukkan su suka kalle shi da mamaki a fuskar Ibteesam.

"In kowa zai amince da kece mahaifiyar ta ni bazan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login