Showing 9001 words to 12000 words out of 171073 words

Chapter 4 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7825

d'an iska, ko wayee ka kira shi da haka baya saurara maka nan take zuciyar sa take harzuk'a yayi maka hukunci ko ya saka yaran sa suyi maka, Zaid abokin sa d'aya takk a duniya shine Hameed wanda companyn sa yake a hannun sa bayan shi bashi da wani aboki a duniya.

Uncle bala, Uncle Sani da Uncle Saifullahi a yanzu basu da burin da ya wuce kashe Zaid shine babban burin su da sun gama dashi su dawo kan Daddy in ya mutu su kuma su mallaki komai nasa wannan dalilin ya saka suka shigo da Amina cikin rayuwar sa, aikin suke amma babu nasara kuma duk da haka Daddy bai fasa kyautata musu ba amma su burin su suga bayan sa duka kud'in su a wajan malamai suke k'arewa wajan karb'o magani.

Zaid duka ya karance su kuma shima yana dagewa wajan taya Daddyn sa da addu'a kuma shima ya kan karb'o maganin tsari wanda aka samo shi daga alkur'ani mai girma a wajan wani malami dake kusa da gidan su Wizzy, kasancewar Daddy ya kasance mai taimakom talakawa koda yaushe gidan sa a cike yake da mabuk'ata addu'ar da suke masa ita take dad'a bashi kariya daga sharrin su Uncle Sani, wannan ya dalilin ya k'arawa Zaid tsanar iyayen nasa ko kad'an baya kaunar ganin su shiyasa koda wasa baya ziyartar ko wanne a cikin su kuma baya sakewa da d'an kowa a cikin su indai ba yaran Mama Asma'u ba, yana raga musu ne ma sabida da Daddy yana nuna masa b'acin ran sa akan hakan, har lokacin kuma Daddy ya kasa gane manufar su a kan sa sabida shi tsakani da Allah yake zaune dasu shi kuma Zaid bai sanar dashi ba sabida gudun shigar sa wani hali dan sosai yana kaunar mahaifin sa.

Had'uwar Zaid da Ibteey ba k'aramin b'atawa Zaid ran yayi ba, ta zagi Maman sa sannan tace masa d'an iska ta kira shi da d'an shaye-shaye mai lalata yaran mutane, wannan kalamai nata suka dasa masa tsanar ta lokaci d'aya gashi sam shi bai iya tsanar abu ba dan in yace bayayi kawai yayi, ba'a tab'a jifan sa da irin kalman ba
shiyasa ya d'auki alwashin koya mata hankali yadda ko nan gaba akace ta yiwa wani abinda tayi masa baza tayi ba dan a kanta yake tunanin fara lalata yaran mutane kamar yadda ta fad'a.

*Note: Dan Allah ku lura cewa nayi duk mai son siya ya nemi wannan number ba ya tura kati a wannan number direct ba.*

_*free pages dai basu da yawa ki biya kud'i k'alilan ki karanta labarin cikin kwanciyar hankali da nishad'i, naira 100 ne kacal ba tsada kamar ruwan pure water, tuntub'i wannan number domin biya but only WhatsApp +2347045242700.*


Comments and share fisabinillah...=?O?d'
*g& ?ASAITAR SO! g&*

? ? ? ? ? ?? ?? *Nana Haleema*

*7?'?8*

"Ibteey kiyi sauri ku tafi kinga rana har ta bud'e bana so kiyi dare" Umma ta fad'a tana fitowa daga d'aki da leda a hannun ta, mik'ewa tsaye Ibteey tayi ta gyara mayafin ta tace, "To Umma ai na shirya". "Ina Jidda?". "Umma kin san jiya anyi ruwa gwara ta huta sabida yanayin jikin ta." D'an jim Umma tayi tana kallan Ibteey kafin tace, "Bana san fitar ki ke kad'ai". D'an murmushi Ibteey tayi tace, "Babu komai Umma ki tayi min addu'a, na tafi kar lokacin sallah yayi" ta fad'a tana niyar ficewa daga falon.

"Ibteesam!" Umma ta kira ta daga baya cikin sanyin murya, juyowa tayi tace, "Na'am Umma na". "In dare yayi ki kwana kya dawo gobe kar ki tawo da daddare kinji ko?". "To Umma insha Allah sai na dawo" ta fad'a tana ficewa Umma ta bita da addu'a.

A hankali take takawa ta fito daga gidan tana D'an kalle-kalle, sunkuyar da kanta tayi tana murmushi ganin wanda take so ta gani sun had'a ido, shima murmushin yayi ya nufo ta yace, "Ibteey na sai ina?" Ya tambaya cikin sanyin murya yana mata murmushi. D'an d'agowa tayi ta kalle shi kafin ta sake sunkuyar da kai tace, "hotoro zanje gidan Dada". Murmushi yake jifan ta dashi yace, "Ina Jidda zaki tafi ke d'aya?". "Kasan anyi ruwa ga yanayin ciwon ta ya saka nace a k'yale ta."
Gyara tsayuwa Khalid yayi yace, "Bana san fitar ki ke kad'ai kin sani ko?". "Na sani yanzu zan dawo ba jimawa zanyi ba" ta fad'a a d'an k'agauce dan ta gaji da maganar.

"To sai kin dawo" ya fad'a har lokacin idon sa a kanta, murmushi tayi kawai ta fara tafiya da d'an sauri dan so take ta isa titi da wuri ta samu mota, kallan ta yake har ta b'acewa ganin sa kafin ya d'auke kai ya kalli wanda ya tsaya a gefen sa yana kallan sa, "Mtswww munafuki meye?". Ya kwashe da dariya yace, "Wannan kallo da kake binta dashi Khalid ai sai ta fad'i." "Hmmm yarinyar ce akwai kyau wallahi" Khalid ya bashi amsa yana lumshe ido tare da bud'ewa.

"Hmmm ai tunda har tana sanka ai zance ya k'are Khalid in nine kai wallahi da yanzu nayi batun aure dan barin irin su Ibteey a k'asa wani minister na zuwa zaiyi wuff da ita." Khalid ya kalli abokin sa kafin yayi murmushi yace, "Kai kana tunanin akwai wanda Ibteey zata so bayan ni? Kai kasan san da take min kuwa?." "Na sani mana kai kuma ba irin wannan san kake mata ba."

D'an yatsine fuska yayi ya saka hannu d'aya yana sosa kansa kafin yace,"Ina santa mana amma gaskiya auren mace mai qiba baya tsari na". "Haba Khalid kasan da hakan kuma kake b'ata mata lokaci?". "Kai yarinyar tana so na ne over in yanzu nace mata ba auren ta zanyi ba tsaf zatayi ciwo, zo muje gida" yana gama fad'ar hakan yayi gaba shima yabi bayan sa.

Ibteesam kuwa tafiya take a hankali cikin nutsuwa har ta fita bakin titi duk da tazarar su babu yawa, a kan titin ta tsaya tana kallan wanda zaiyi hanyar da zata bi tana kuma kallan agogon hannun ta, wani mai napep d'in ta hango babu kowa ta saka masa hannu ya tsaya tace, "Hotoro bos stop". "Hajiya kud'in ki dari biyu". "Zan bada dari uku amma drop". "To hajiya" yana gama fad'ar hakan ta shiga yaja napep d'in.
Tun daga kan gada ana traffic ne har danger state road, "Hajiya ko zamu bi ta baya ne nan traffic yayi yawa wallahi sai mu kusa la'asar a nan wajan". "Eh muje d'in naga wajan a cakud'e." Juya kan Napep d'in yayi yabi k'asan gada suka wuce.
Tafiya suke hankalin ta na kan titi shi kuma yana kallan titi yana tuk'in sa a hankali, parking taji yayi sai a lokacin ta dawo daga duniyar tunanin duniyar da ta tafi dan a zahiri kallan titi take amma a zuciyar ta wani tunanin take daban ta kalle shi tace, "Lafiya ka tsaya?". Juyowa yayi ya kalle ta yayi murmushi, "Hiii" aka fad'a ana kallan ta daga k'ofar Napep d'in, zatayi magana kenan aka fesa mata hoda a fuska ta lumshe ido ta zube akan kujerar, Wizzy ya kalli mai napep d'in yace, "good job" ya fad'a yana yi masa jinjina.

Murmushi mai napep d'in yayi yace, "Godiya nake Oga". Cak Wizzy ya d'auke ta ya saka ta a mota ya d'auki hanya a guje.

***********

Tsaf ya shirya cikin dogon jeans black mai zanen fari ya saka riga fara mai ma6allai a gaban rigar ya kawo farar picap ya saka a kansa,? wayar sa ya d'auka tare da jakar sa ta tafiya ya fito daga d'akin nasa, a hankali yake sakkowa daga saman yana yi yana kallan agogo dan ganin ya kusa missing flight, cak ya tsaya tare da komawa baya yana kallan Amina da take zuba wani ruwan magani a cikin miyar agusi d'in da take ajjiye a akan dining table d'in, wani irin takaici ne ya kama Zaid tsanar ta ta sake yi masa dirar mikiya lokaci d'aya, a fusace yake sakkowa daga saman yana wani irin wuci kamar zaki, ganin sa ya saka ta firgita tayi baya da sauri tana b'oye maganin a zanin ta, bai jira wani abu ba yana k'arasowa ya d'auki miyar ya watsa mata a jikin ta, ihu Amina tayi sabida miyar da zafi tana zazzage rigar ta, sakin flasks d'in yayi a kan tiles d'in kafin ya juyo a fusace ya nuna ta da yatsa yace, "In kika sake wani abun ya sami mahaifina zan iya kashe ki" ya fad'a yana zaro mata manyan idon sa wanda suka koma jajaye sabida b'acin rai da k'unar zuciya.

Daddy da ya jiyo ihun Amina ya fito da sauri ya sakko k'asan, cak ya tsaya yana kallan ta jikin ta duka miya ga Zaid ya saka ta a gaba yana nuna ta da yatsa, "Zaid!" Daddy ya kira shi a fusace yana kallan sa da b'acin rai a bayyane a fuskar sa. "Zaid meyesa baka da kirki ne? Me yake damun ka? Uban me Amina ta tare maka ne a gidan nan ka sako ta a gaba haka eyeee,? Inda mahaifiyar ka tana raye wani yake mata irin abinda kake mata zaka ji dad'i?" Daddy ya fad'a cikin fad'a yana nuna shi da yatsa. Kallon sa Zaid yayi yana jin wani irin b'acin rai yana taso masa daga k'asan zuciyar sa tsanar Amina kuwa dad'a nitso cikin zuciyar sa, a kanta kad'ai Daddy yake masa fad'a har haka ya za'ayi bazai tsane ta ba, "Bata hak'uri" maganar Daddy ta katse masa tunani.

Da sauri ya d'ago kai ya kalli Daddyn nasa jikin sa ya soma wani irin rawa dan shi a rayuwar sa sam bai san wani abu wai shi hak'uri ba, bai tab'a bawa wani hak'uri ba sai dai shi a bashi koda shine bashi da gaskiya k'arfin ikon sa yana sakawa a bashi hak'uri, "Kayi abinda nace Zaid" Daddy ya sake fad'a cikin murya mai amo yana kallan Zaid, Saurin dafe kan sa yayi yana jin wani irin jiri yana neman d'aukar sa, jikin sane ya soma wani irin rawa kamar an jona masa wutar lantarki, "Ka bata hak'uri Zaid in ba haka ba zaka had'u da b'acin raina wanda baka tab'a gani ba."

Bakin sane yake rawa yana so yayi abinda Daddy yace amma ya kasa bakin sa yayi masa wani irin nauyi wanda bai tab'a yin irin sa ba, "baza kayi abinda nace bane Zaid?" Daddy ya sake fad'a a tsawace yana kallan sa da b'acin rai.

"I'm....so..rr...y" ya fad'a a rarrabe cikin rawar murya, yana fad'ar hakan ya wani runtse ido kamar wanda ya aikata babban sab'o yana yana girgiza kai, "Abuja" abinda ya iya fad'a kenan sanyayeya juya a fusace ya fita daga falon.

"Musa! Musa!! Musa!!!". A guje ya Musa ya tawo jikin sa na rawa dan yadda yaji muryar Zaid d'in ba k'aramin rud'a shi yayi ba, "Na'am gani" ya fad'a yana dan rank'wafawa, bai magana ba sai bud'e motar da yayi kawai ya shiga ganin hakan shima Musa ya shiga suka nufi hanyar airport, tunda suka shiga yake jan tsaki fuskar sa a tamke kamar koda yaushe sai wuci yake yana girgiza kai, in ya tuna ya bawa Amina hak'uri sai yaji kamar yayi hauka sabida takaici da bak'in ciki.
Koda suka k'arasa baiyi magana ba ya bud'e motar ne kawai ya fice ya shiga ciki, da kallo Musa ya bishi kafin yace, "Oh albasa batayi halin ruwa ba".

Daddy kuwa yana fita ya matsa kusa da Amina ya rik'e hannayen ta duka biyun yace, "Kiyi hak'uri dan Allah insha Allah hakan baza ta kuma kasancewa ba, na rasa abinda yake damun Zaid a kanki amma zan kamo bakin zaren kada ki bari abinda ya faru ya dame ki dan Allah badan ni ba". Share hawayen da suka ciko mata ido tayi ta d'an yi murmushi tace, "Babu komai kar ka damu, da ka sani baka yi masa tsawa ba kasan yanayin jikin sa yanzu sai hakan ya tayar masa da ciwon sa." Ajiyar zuciya Daddy yayi dan shima tunda yayi masa tsawar yaga yadda yanayin sa ya canja jikin sa yayi yake tsoron Allah yasa kada hakan ya zama silar tashin ciwon Zaid, "dole ne na tsawatar masa sabida kar ya sake kuskuren aikatawa nan gaba? in yaga yayi ba'a yi masa tsawa ba gobe ma kuma yi zaiyi, babu abinda zai same shi ki kwantar da hankalin ki."
"Duk da haka sabida yanayin ciwon sa ka daina masa irin wannan tsawar." "Amina kowa fa yana da fushin nan, kowa yana da zuciya amma mu muna sarrafa ta yadda ya kamata shi waye da bazai sarrafa zuciyar shi ba? Komai fushi haka rayuwa zatayi,? Dole a dinga tsawatar masa yasan ba komai ake samu ta fushi da zafin zuciya ba, kiyi hak'uri dan Allah. " "Haka ne, bara naje nayi wanka na canja kaya na" ta fad'a tana zame hannun ta daga rik'on da yayi mata ta wuce d'akin ta tana wani irin murmushi mai kama da murmushin nasara.

Wayar sa da tayi k'ara ya saka ya ciro ta daga aljihu ganin mai kiran ya sanya gaban sa fad'uwa dan indai kaga kiran sa to ba alkhairi bane ba, "Hello Yaya" ya fad'a a sanyaye. "Ka rik'e hello d'in ka Abubakar, ashe d'an ka bashi da mutunci? Ashe bayan shaye-shaye har da daban ci yake yi bamu sani ba? Tsabar tsinancewa irin ta Zaidu mu zai saka y'an daba su yiwa dukan tsiya dan kawai munzo gidan su,? Sun fasa min baki shi kuwa Bala ma sun targad'a shi a hannu kaga kenan nan gaba kashe mu zai saka ayi". Shiru Daddy yayi yana sauraran sa jikin sa duk yayi sanyi, "To sai ka aiko da kud'in magani tunda d'an iskan d'anka ne yayi mana wulaqanci." Ajiyar zuciya Daddy yayi yace, "Allah ya baku hak'uri insha Allah zan kawo shi ya baku hak'uri." "Ku rik'e hak'urin ku bama so amma dole ka aiko da kud'in magani". "To zan turo insha Allah". "Ka kyautawa kanka" ya Fad'a yana katse kiran.

Ajiyar zuciya Daddy yayi jiki a sanyaye ya koma sama yana tunanin halayyar Zaid, ya rasa a ina ya d'auko wannan halayyar tasa.

Saukar sa a airport na Abuja bai jira driver ba kawai ya d'auki drop d'in taxi ya tafi gidan su da yake mai tama, a k'ofar gidan ya sauka ya bawa mai taxi d'in kud'in sa shi kuma ya nufi gate d'in gidan yayi knocking, dake mai gadin gidan yasan da zuwa sa yayi sauri yazo ya bud'e yana yi masa sannu da zuwa, a ciki ya amsa kafin ya shige cikin gidan yana wata irin tafiya cikin k'asaita, direct inda yake mallakin sa a gidan ya nufa ya bud'e ya shiga, falon yana nan tsaf a gare sai k'ura kad'an, d'akin ya wuce ya ajjiye jakar hannun sa ya fad'a band'aki, wanka yayi tare da alwala ya fito ya shirya cikin jallabiya kofi colour mai hula a baya, sallah ya tayar bayan ya idar ne ya fito ya shiga kitchen.

Kettle ya kunna ya dafa ruwan zafi ya had'a tea ya dawo falo ya d'an kad'e inda zai zauna kafin ya zauna ya fara shan tea d'in a hankali, sai da ya kammala sannan ya d'auki key d'in mota ya sauko dan ya bawa Mai gadi umarnin a wanke masa motar sa da take gidan, yana fitowa ya shiga motar aka bud'e masa gate ya fita ya nufi unguwar Zone 6.
A dai-dai wani d'an gida plat mai kyau ya tsaya tare da danna horn d'in motar tasa, mai gadin gidan lek'o yaga motar da bai sani ba sai ya kulle k'ofar ya fito, sauke glass d'in Zaid yayi ya kalli mai gadin tun kafin yayi magana yace, "Kace mata Zaid ne" ya fad'a a dak'ile yana Kawar da kansa gefe.

Cike da mamaki mai gadin yake kallan sa ganin ko irin sallamar nan ma babu sai wata magana da yake yi a gadarance kamar gidan sa, bai musu ba ya juya ya shiga cikin gidan jim kad'an ya dawo ya bud'e masa gate d'in ya shiga cikin gidan, parking yayi ya kashe motar ya fito ya nufi k'ofar da zata sada ka da falon gidan, da sallama ya tura k'ofar ya shiga yana kallan falon, da fara'a ta amsa ta mik'e tana fad'in, "Ga Zaid sannu da zuwa" ta fad'a cikin nuna zallar farin cikin ta da nishad'i.
Sakin fuska yayi kad'an ba tare da yayi murmushi ba ya zauna a kan kujera tare da d'ora k'afa kan d'aya yace, "Ina wuni". "Lafiya lau Zaid ya gida ya Daddyn naka?". "Lafiya" amsa yana kallan tv dake gaban sa. "Masha Allah, Zahra kawo masa ruwa da abinci" ta d'an d'aga murya ta fad'a. "No Mom ruwan dai but abinci kam I'm okay." "Aikam baka isa ba abinci kam sai kaci shi, kai ka isa ma kazo ka tafi baka ci komai ba."

Shiru yayi baice komai ba wacce aka kira da Zahra ta fito cikin nutsuwa ta ajjiye abincin a gaban sa tace, "Ina wuni Yaya Zaid". D'ago kai yayi ya kalle ta kafin ya d'auke kai yace, "Ya karatu?."? "Alhamdulillah" daga nan sukayi shiru babu wanda ya sake magana. Mom ta bud'e abincin ta zuba masa tace, "To bismillah". Kallan abincin yayi jellop d'in pasta da nama a cikin ta tayi masa kyau a ido sosai hakan ya saka ya d'auki spoon ya dibi kad'an ya kai bakin sa, a hankali yake taunawa ya sake d'iba ya ci sai ya ajjiye spoon d'in jin wayar sa na vibrating, d'aukar wayar yayi tare da cewa, "okay in ta farka ku bata abinci naje gidan Mom sai zuwa gobe zan shigo" ya fad'a bayan ya saka wayar a kunnen sa.
Bayan ya kashe wayar Mom ta kalli d'an k'anwar tata tace, "ina kazo a garin namu?". "Nan kawai" ya bata amsa a takaice. "Lah aikam naji dad'i takanas ka tawo Abuja sabida ni? Kai Allah yayi maka albarka ya nuna nuna min auren ka." Murmushin gefen baki yayi kad'an baice komai ba, "yaushe zaka kawo min sirikar tawa?". Kallan ta yayi kafin ya d'auke kai yace, "hmm Mom kenan."

Murmushi tayi tace, "Ina zaka je goben kuma?" Ta fad'a tana kallan sa cikin kulawa, ajiyar zuciya yayi kafin yace, "Kaduna". "Allah ya kiyaye"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login