Showing 36001 words to 39000 words out of 171073 words

Chapter 13 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7848

Ibteesam yake amma sam ya kasa, tabbas yasan yana jin ta a ransa sosai yana kuma so yaji maganar ta koda rashin kunya zatayi masa, baya so ya ganta da wani ko kad'an yana jin zafi sosai a ransa, "kenan hakan yana nufin ina son tane?" Yayi maganar a fili yana tambayar kanshi.

Tunowa da auren Eman a kansa ya saka shi jan dogon tsaki a fili ya furta, "kawai dan su cika burin su na na kashe ni shiyasa suka aikata hakan". Kawar da tunanin yayi a ransa ya mik'e ya shiga band'aki.

Washe gari.

Cikin k'asaita yake shigowa cikin falon hankalin sa na kan wayar sa kawai yaji yayi karo da mutum wayar hannun sa ta subuce ta fad'i akan tiles, a fusace ya d'ago kai suka had'a ido da Anty Amina da take kallan sa itama, har zaiyi magana sai kawai ya fasa ya tsaya k'ikam yana jiran ta mik'o masa wayar sa.

Kamar ta fahimci me yake nufi ta duk'a ta d'auko masa wayar ta mik'a masa, ba kunya ya saka hannu ya karb'a da niyar barin wajan, "Zaid!" Ta fad'a cikin taushin murya, cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba dan yadda ta kira sunan nashi ya shige shi sosai.

"Baka tunanin wata rana zakayi dana sanin abinda kake yi min?" Ta tambaye shi tana hard'e hannun ta a k'irji. In slowly ya juyo ya zuba mata idanun sa yace, "Dana sani? Ni Zaid nayi dana sani? Ban san ta ba,bana fatan kuma na santa ko a nan gaba, rik'e wannan a ranki" yana fad'ar hakan ya cigaba da tafiyar sa.

Murmushi tayi tana kallan sa har ya b'ace ta girgiza kai ta bar wajan itama.

Tunda ya hau saman yake k'are masa kallo ganin anyi komai yadda yace, komai an canja hatta a.c da tv an canja, k'arewa falon kallo yake kafin ya shiga d'akin, nan ma babu abinda ba'a canja ba, sosai d'akin ya burge shi ya zauna a gefen gado yana juya wayar dake hannun sa tare da kafawa hoton mahaifiyar ido.

Ajiyar zuciya yayi kawai gabad'aya ya rasa abinda yake masa dad'i a ranar ji yake kamar ya rasa wani abun a b'angaren jikin sa dalilin da ya saka yazo yana kallan Maman sa amma sai yaji kewar bata wannan b'angaren bace to me yake ji? Abinda yake tambayar kansa kenan amma ya rasa amsar.

Ganin Daddy yana masa waya ya saka bai d'auka ba ya mik'e ya fito daga d'akin ya sakko k'asa, direct falon Daddy ya nufo ya shiga da sallama a hankali, Daddy da yake zaune ya amsa yana kallan sa har ya k'araso ya zauna a akan kujera ya kalli Daddyn da ya zuba masa ido yace, "Daddy ina kwana" ya fad'a shima idon sa a cikin idon Daddyn.

"Lafiya lau son, sai naga ka saka an canja komai na part d'in ka lfy dai ko?". "Lafiya Daddy kawai ban amince da yarinyar da ta zauna a d'akin bane that's why." "Hmmm Zaid kenan koma dai meye matar kace, yauwa ya batun yarinyar da ka sace?." "Tana gidan su" ya bashi amsa a tak'aice.

"Zaid meyasa ka d'auke yarinyar mutane?". "Bata da kunya." "To dan bata da kunya sai ka sace musu y'a?". "Hukunci na mata kuma na dawo da ita ai". "Ina fatan baka mata abinda kace ba?" d'ago ido yayi ya d'an saci kallan Daddyn nasa yace, "Banyi ba." Ajiyar Zuciya Daddy yayi yace, "Me yasa ka fasa?" Ya fad'a yana kafe shi da ido.

"Haka kawai Dad" ya bashi amsa yana d'an gyara zama, "ka kyauta, let me tell you something happiness, ka kusa samun sibling" Daddy ya fad'a da murmushi a fuskar sa yana kallan sa.? "Sibling from who?" Zaid ya tambaya da alamun mamaki yana kallan Daddy. "From your step mother". D'an zaro ido kad'an yayi kana ya tab'e baki yace, "Dad da girman ku zaku wani haihu yanzu? A gani na ai kun wuce haihuwa" ya fad'a kansa tsaye da iyakar gaskiyar sa.

Murmushi Daddy yayi yace, "Akwai wanda yake wuce kyautar Allah ne Zaid?". "Okay Allah raya ake cewa ko? To Allah ya raya, zance wani waje" ya fad'a yana mik'ewa tsaye. "Ina zaka?". Kallan Daddyn yayi kamar baya son fad'a masa kafin ya daure yace, "yanzu zan dawo" daga haka ya fice kawai bai sake waiwayen Daddyn ba.

Kicib'is sukayi da Eman tana k'okarin shiga waja Daddy, ko kallo bata ishe shi ba kamar bai ganta ba yayi ficewar sa.

Fasa shig wajan daddy d'in tayi kawai tayi cikin gidan, d'akin da Anty Amina ta saka ta dawo nan ta shiga ta d'auko waya ta kira mahifin ta, "Abba mun had'u yanzu amma ban ga wani canjin komai ba a tare dashi dan ko kallo na baiyi ba" ta fad'a kamar zatayi kuka. Daga can b'angaren Yaya Babba yace, "kuma kin tabbata kinyi amfani dashi yadda ya dace kuwa Eman? An bani tabbacin indai ya shak'i khamshin turaren nan bazai sake miki musu ba har abada." "Wallahi Abba na saka amma ko kallo na ma baiyi ba yayi ficewar sa kamar ma ya manta dani a matsayin matar sa." "Shikenan kiyi amfani da d'ayan ki tabbatar farar jikin ki ta gogi tasa ko yaya ne". Shiru tayi tana tunani kafin tace, "Amma Abba wannan kamar yafi wahala." Hajiya Batula da take a zaune kusa dashi ta amshe da fad'in, "Haba Eman kamar ba mace ba ki san yadda zakiyi ko hannun ki ne ya had'u da nasa mana". "To Ummi zan gwada anjima" ta fad'a a sanyaye da ita fa lamarin ya fara bata tsoro ta yaya jikin su zai had'u dana Zaid,? "yauwa ko kefa, ai bazai dake ki a banza b wallahi duk sai mun fashe abinda yayi miki" Ummi ta fad'a cikin sigar lallashi, da haka sukayi sallama ta kashe wayar tana tunanin mafita.

Zaid kuwa tund???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a ya d'auki mota kawai tafiya yake ba tare da yasan inda zashi ba bai tsinci kansa a ko ina ba sai a k'ofar gidan su Ibteesam, k'arewa gate d'in gidan su kallo yake yana jin wani irin sanyi yana ratsa shi b'acin ran da yake tare dashi yana gushewa a hankali, kewar da yake ji a jikin sa a hankali yake ji tana gushewa, ajiyar zuciya yayi ya kifa kansa a kan sitiyarin motar yana sauke nufamshi kamar wanda yayi gudu, daga daren jiya zuwa lokacin ya amince da son Ibteesam yake so me tsanani wanda bai san iyakar sa ba,? iska ya fesar ya kwantar da kansa jikin kujerar yana tuna fuskar ta lokacin da ya shaida mata za'a maida ita gida tayi murmushi, murmushin gefen baki yayi zuciyar sa na wani irin bugu kamar ganga dan tuno ta d'in da yayi wani abu yake ji yana masa yawo a jikin sa.

Bud'e k'ofar motar yayi ya fito yana kallan gabas da yamma na unguwar, da yake layin nasu babu wani mutane sosai sai wanda ba'a rasa ba, kallo ya gani ya dawo kansa kamar wanda suka ga wani d'an film ya tsaya, tsaki kawai yaja direct ya nufi gate d'in gidan su Ibteesam ba tare da fargabar komai ba.

A hankali ya tura k'ofar gidan ya shiga, Asiya da take tsaye tana gyara inda busassun flowers suka zubo ta d'ago ta kalli wanda ya shigo, gaban tane ya fad'i tozali da tayi da kyakykyawan gaye a tsaye yana kallan gidan kamar me nazarin wani abun, "wowwww" ta furta a fili ba tare da ta sani ba tsintsiyar hannun ta ta fad'i k'asa ba tare da ta sani ba, sai a lokacin ya kula da ita da kuma irin kallon da take masa, tsaki yaja a hankali yake nufar inda take sai kuma ya juya kawai ya k'yale ta dan shi fa ya tsani kallo a rayuwar sa, har zaiyi magana sai ga Jidda ta fito, mayar da hankalin sa yayi ga Jidda da bata kula dashi ba yace, "Kee ina....." sai kuma yayi shiru tunawa da yayi bai san sunan ta ba.

Jidda da ta tsaya cak tana kallan sa da mamakin yake shi tace, "Mene?". "I forgot her name ina yayar ki?" Ya fad'a cikin wata irin murya mai dad'i da sanyi wacce ta kusa saka Asiya suman tsaye.

"Anty Ibteey tana ciki" ta fad'a kai tsaye tana cigaba da kallan sa da mamakin waye shi, inda ta nuna da hannun ta ya nufa directly, Asiya da ta k'ame a wajan tunda taji sautin muryar sa ta sake shiga cikin rud'u da shauk'in da bata san dalilin sa ba, har ya b'ace daga ganin ta bata sani ba sai da taji muryar Jidda na fad'in, "Anty Asiya waye wannan ya shigo kai tsaye haka?". Asiya bata iya bata amsa ba sai jingina da bango da tayi wani irin yanayi yana ratsa ko wanne b'angare na jikin ta.

Babu kowa a babban falon hakan ya saka ya tsaya cak yana kalle-kalle dan yaga k'ofa biyu ya rasa wacce zai nufa, Jafar ne ya fito da plate a hannun sa yana cin dankali yana niyar wucewa da alama bai kula da Zaid ba, "Kai ina yayar ka?". A firgice Jafar ya kalli Zaid dan shi har ga Allah tsoro ya bashi dan bai kula da mutum a wajan ba, "Anty Ibteey?" Ya fad'a cikin tambaya.

D'aga masa kai Zaid yayi kawai Jafar ya nuna masa part d'in Umma yana cigaba da kallon sa, baice komai ba kawai ya shiga part d'in Umma, Umma na zaune a akan kujera Ibteesam na kwance a cinyar ta tana share hawaye kawai suka ji sallama tare da shigowa, d'agowa Umma tayi tana kallan sa cikin mamaki da al'ajabi, Ibteesam ma mik'ewa zaune tayi tana kallan Zaid cikin tsoro da al'ajabi halayyar sa, neman waje yayi ya zauna ya kalli Umma yace, "Ina kwana". Umma mamaki ya hana ta amsawa sai kallon sa kawai ta take yi cikin takaici, "Don't worry ba wani abun ya kawo ni ba kawai na tashi ina so na ganta ne" ya fad'a yana nuna Ibteesam da hannu yana kallon fuskar ta da alama itama mamaki ne ya hana ta magana.

"To kuma haka ake shigowa gida kai tsaye babu neman izinin kowa kamar gidan karuwai?" Ta fad'a da takaici tana kallon sa, "oh i forgot ashe fa sai an nemi izini, koda yake ma ai gidan mu ne nima" ya Fad'a bilhakki dan shi har ga Allah ya manta da wani neman izini abinda da wanda ya tashi a turai, "wai meyasa kake bibiya tane dan Allah? Abinda kake so ka samu a tare dani ka samu to meye na takura min?" Ta fad'a hawaye na sakko mata daga? idon ta.

Kallon ta kawai yake ganin tana kuka duk sai yaji wani iri a jikin sa a hankali yace, "na fad'a miki nazo na ganki". "Meyasa kake so ka ganta? Ko dan kaga kayi laifi an k'yale ka shiyasa kakewa mutane abinda kaga dama,? To wallahi ka jira sammaci dan wallahi sai na kaika kotu, kai baka ji kunya bama ka lalata min yarinya kazo gaba na kana cemin wai kana so ka ganta ne?".

Kallon Umma yake da mamakin abinda take cewa wanda shi sam bai gane ba sai kawai ya tab'e baki yace, "Mama nifa ina son tane kuma auren ta zanyi" ya fad'a kansa tsaye yana d'ora k'afa kan d'aya.

A tare suka kalli juna Umma ta zaro ido tana mamakin jin abinda yace Ibteesam ce tayi k'arfin halin cewa, "Ni kuma bana son ka kuma bazan tab'a son ka ba har abada" ta fad'a cikin masifa tana hararar sa.

Mi?ewa tsaye yayi ya zuba hannun sa a aljihu ya zuba mata ido kana yace, "sona ya zamar miki dole gwara ma ki tattara duk wanda yake cikin zuciyar ki ki saka a dustbin in ba haka ba zaki ja masa bala'in da bai tab'a shiga ba a duniya, Mama ki fad'a mata ta soni bana son ban samu ba, samun kanta da zaman lafiya shine ta saka sona a ranta in ba haka ba kuma......" ya fad'a yana ficewa daga falon da alama mamaki ya hana su sake cewa komai.

A baban falon ya sake had'uwa da Asiya ko kallon ta baiyi ba ya fice daga gidan gabad'aya yana jin wani irin b'acin rai in ya tuno kalaman Ibteesam.

Koda ya koma gida d'in motar sa har zai shiga cikin gida sai kuma ya shiga falon Daddy dan yaga kiran wayar sa lokacin yana tuk'i, da sallama ya shiga ganin su biyu ne ya saka ya juya zai fita Daddy yayi saurin cewa, "K'araso mana ina zaka ga?". Baice komai ba ya k'arasa ciki ya kalli wanda suke tare da Daddy yace, "ina wuni" ya fad'a ba tare da ya kalle shi ba a lokacin.

"Lafiya lau Zaid" Abba ya bashi amsa yana kallan sa da karantar yanayin sa, "Zaid!" Daddy ya kira shi a tausashe yana kallan sa, d'ago idon sa yayi yace, "Na'am Daddy". "Kasan wannan" ya fad'a yana nuna masa Abba.

Kallan Abba yayi kafin ya dawo da kallon sa ga Daddy yace, "A'a". "Shine mahaifin yarinyar da ka d'auke." D'ago kai ya sake yi ya kalli Abba na wasu seconds kafin ya mayar da kansa k'asa baice komai ba, "Zaid sun zo nemawa y'ar su hakkin ta bayan sace ta d'in da kayi ka dake ta bai ishe ka ba sai da kayi mata fyad'e, meyasa kayi min k'arya Zaid?."

Da mamaki ya kalli Daddy ya bud'e ido ya nuna kansa da yatsa yace, "haka tace nayi raping d'in ta?". Daddy ya zuba masa ido yace, "In ba kayi ba zata fad'a ne?". Gefen sa ya kalla ya furzar da iska daga bakin sa yace, "Daddy kasan k'arya bata cikin dabi'a ta ina fad'ar gaskiya ne koda gaskiya zata saka wani ciwon kai, ni ban mata komai ba kawai ta fad'a ne dan tayi min sharri kawai dan nace ina son ta, ohhh wannan ne dalilin da ya saka maman ta take cewana lalata rayuwar ta?" ya fad'a kansa tsaye yana cize lips d'in sa.

Abba ya kalli Daddy shima ya kalle shi Daddy yace, "A ina kuka had'uda maman nata?" Daga gidan nake yanzu" bashi amsa kansa tsaye ba tare da shakka ko wani abun ba, mamaki ya kama Abba da Daddy suka kasa magana ya katse shirun da fad'in, "Na tashi ina so na ganta ne shiyasa naje sabida ina son ta". "Kana son ta fa kace?". "Eh Daddy ina son ta na fad'a maka yanzu ma daga can gidan nake, dan nace ina son ta ba hakan yana nufin ta samu damar da zata yi min abinda taga dama ba, wallahi dan ina sonta bazan fasa yi mata hukunci ba" ya k'arashe fad'a yana k'wafa.

Wani irin sanyi ne mai dad'in gaske ya ratsa zuciyar Daddy har ya kasa b'oyewa ya bayyana a akan fuskar sa yace, "kana so kace min kana sonta da aure Zaid?". "Oh dad sau nawa zan fad'a maka ne wai? Ina son ta ina sonta ina sonta, dole kuma ta soni babu wanda zata so bayan ni na fad'a mata wannan" ya k'arasa fad'a a fusace yana kallan wani wajan daban.

"Dad ka fad'awa Maman ta in naje gidan ta daina cewa ban nemi izini na na shiga a gani na nima gidan mu ne right" ya fad'a yana kallan Abba da yake kallan sa kawai, murmushi yayi yace, "Gidan kune". "To ta daina fad'a bana so" ya sake fad'a yana kallan wani wajan daban........



K'asaita so d'in kenan fa =??=??=?? '




*Kada a fitar min da littafi dan Allah don annabin rahama.*

*?ASAITAR SO!*

*27_28*

Murmushi Abba yayi mai sauti ya kalli yadda Daddy ya zubawa Zaid ido yace, "Shikenan Zaid tashi kaje". Jin muryar Abba ya saka shi ya kalli Abban dan shi har zaice wani abun sai kawai ya fasa ya mik'e ya fita.

Daddy ya kalli Abba yace, "ni na rasa ma abinda zance wannan wacce irin soyayya ce? Daman ana so dole ne?." "Yanayin sane shi kawai a haka ai" Abba ya fad'a muryar sa a sake. "Tunda naji hakan sai naji ina so na sake neman wata alfarmar a wajan ka a karo na biyu" Daddy ya fad'a yana kallan Abba.

Gyara zama Abba yayi yace, "To ina jinka." "Batu ne dai a kan Zaid d'in, kar kaga kamar na cika son kaina da yawa ba haka bane ba wallahi ina dubawa ne yau in na fad'i na mutu na bar duniya wa na bari wanda zai kula da lamari na,? Dan dai a haka ni gani nake da Zaid da babu duka d'aya ne tunda shi abu kad'an ne yake tunzura shi baya kauda kai a akan fushi ko kad'an, tunda ya furta yana son Maryam tabbas yana son ta shine nake neman alfarma dan Allah tayi amfani da son da yake mata ta gyara shi ta dawo dashi hanya madaidaiciya ta nuna masa abu mai kyau da mara kyau."

Abba da yayi shiru yana sauraren sa yace, "Ta wacce hanya kenan? Ko kana so a bayyana musu zancen auren ne?." "A'a ba haka nake nufi ba, mace na canja mutum da halayyar sa lokaci koda shi baya son ta balle kuma yana so, so nake dan Allah kayi mata dabara ta saki jiki da Zaid koda a matsayin abokin tane duk wani motsi nasa in yayi ba dai-dai ba ta gyara masa, nasan tabbas bazai yi saurin karb'ar gyaran ba amma tunda har yana sonta zai gyara d'in, wannan shine alfarmar da nake nema a wajan ku da kai da ita."

Ajiyar zuciya Abba yayi yace, "to a yanzu gaskiya bana ce zata yi ba dan ita tace yayi mata fyad'e shi kuma yace baiyi ba kaga kenan akwai wannan zafin a ranta, amma yanzu in na koma zan tabbatar da abinda yake wakana, insha Allah zan lallashe ta ta amince da buk'atar ka duk da daman mijin tane nauyin hakan a wuyan ta yake, auren nasu kuma ni bana so su san dashi a yanzu d'in zamuyi saurin datse shi ba bamu san mai Allah ya tanadar a cikin sa ba zamu jira mu gani na zuwa wani lokaci. "

"Kayi hak'uri dai bawai ina so na sake kare Zaid bane amma tunda nake da Zaid baya min k'arya shi yana fad'ar gaskiya ne koda fad'ar gaskiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login