Showing 99001 words to 102000 words out of 171073 words

Chapter 34 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7864

halin da Zaid yake ciki, a haka ta daure ta kwanta badan tana jin bacci ba, koda baccin ya d'auke tayi shi cikin mafarkai marasa dad'i wanda dalilin hakan ya saka ta tashi jikin babu kwari kamar wacce aka yiwa duka,? koda aka fito wajan karyawa y'an uwan sun fahimci tana cikin damuwa sai bayan manyan sun bar wajan sannan Zahra ta kalle ta tace, "Anty Baby me yake damun ki yau?". D'ago kai tayi ta kalle ta kafin tace, "Me kika gani?". Fatima ta amsa da fad'in, "Gashi nan duk kinyi wani iri kamar bake ba, me yake damun ki ko zaman gidan ne baya yi miki dad'i?". Murmushin dole tayi tace, "A'a wallahi ba haka bane, kawai na tashi yau yanayi na babu dad'i ne shiyasa." Amina tace, "In anyi sallar la'asar yau ma ai zamu fita zaki dawo dai-dai in Allah ya amince, dan mu munfi so muga ana walwala." Daga haka suka cigaba da hirar su tana saka musu baki sama-sama.

Kamar yadda suka tsara bayan la'asar suka fita yawon zaga gari, babu laifi ta d'an sake amma da taji k'arar wayar ta zata firgita ta duba ko Zaid ne amma sai taga akasin hakan, Amir yana lura da yanay???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?in ta ya canja amma bai mata magana ba, bayan sun koma gida ya kira Zahra yake tambayar ta abinda yake damun Ibteesam d'in, Zahra tace, "Wallahi ban sani ba, nima haka na ganta yau". "Kin tabbata ba wani ne ya b'ata mata a rai a gidan nan ba?". Tace, "Babu wanda ya b'ata mata rai, sai dai in rashin lafiyar mijin tace take damun ta." Da mamaki Amir ya kalle ta yace, "Mijin ta kuma? Tana da aure ne daman?". Zahra tace, "Eh mana tana da aure, auren bai wani jima sosai ba dan dai kawai anyi shi ne cikin wani irin yanayi". Amir yace, "Wanne irin yanayi kenan?". Tace, "Abba yana ciki kazo muje ka tambaye shi wannan tambayoyin naka sun min yawa" ta fad'ar hakan tayi ciki shima ya biyo bayan ta dan yana so ya gasgata maganar ta.

A falon ya ci burki ya zauna kusa da Hajiya kaka yana fad'in, "Abban Abuja wata magana naji a bakin Zahra shine nazo na tambaya" ya fad'a yana kallon Abba. "Baba na mai ka jiyo?" Abba ya fad'a yana ajjiye kofin furar dake hannun sa.

"Wai Baby tana da miji a Kano?" Ya tambaya yana kallon Abba, murmushi Abba yayi yace, "Eh tana dashi, yanzu ma maganar muke da Kaka dan gobe nake so zamu wuce Kano". Komawa yayi ya jingina da kujera tare da fad'in, "ashe dai da gaske ne, to shi mijin waye shi? Kuma tana son sa?". Hararar sa Hajiya Kaka tayi tare da fad'in , "Ungo nan" ta fad'a tana yi masa dak'uwa, ta cigaba da fad'in, "meye naka kake wannan tambayoyin kamar d'an jarida?" Ta fad'a cikin harshen fulatanci tana kallon sa.

Murmushi Abba yayi shima cikin harshen fulantacin yace, "Hajiya ai yayan tane in ya tambaya babu laifi". Kallon Ameer Abba yayi kafin yace, "Sunan shi Abdallah mahaifin sa shine yake auren mahaifiyar ta a yanzu, yana son ta kuma matuk'a dan na tabbata k'anwar ka baza ta sha wahala ba" Abba ya k'arasa fad'a yana kallon Ameer da murmushi a fuskar sa.

"Nikam Abba da kace mijin mahaifiyar ta sai nake tunanin tunda yanzu komai ya warware a sihirin da yake jikin ta ba matar ka bace ba kuwa?" Ya fad'a cikin mayar da hankali yana kallon Abba, girgiza kai Abba yayi yace, "A'a ni ai lokacin da nayi sakin ina cikin hankali na ba ni asirin ya kama ba ita ya kamata, so babu aure na a kanta hasalima yanzu tana da auren ta."? "Haka ne kuma Abba, amma ya akayi auren babu sanarwa babu komai? Shine ban gane ba ni" ya sake tambaya yana kallon sa.

"Kai tafi can ka rufe mana baki ka ishe mu da surutun banza, wannan tambayoyin da kake jera masa kamar kaine mahaifin ta, son ta kake ko me?" Hajiya kaka ta katse shi da fad'ar hakan, kallon ta yayi yace, "Wai ina ruwan kine Hajiya dan na tambaya,? In ma son nata nake tunda tana aure ai zance ya k'are, amma fa indai bata son sa sai sun rabu baza'a takurawa k'anwa ta ba" ya fad'a yana mik'ewa tare da ficewa daga falon.

Murmushi Abba yayi suka cigaba da tattaunawa da Hajiya.

Mummy kuwa tana d'aki tana waya Ibteesam ta shigo bayan ta Zahra ne da Sultana, zama sukayi har Mummy ta gama wayar tayi ajiyar zuciya tana kallon wayar, "Mummy lafiya?" Zahra ta tambaya tana kallon ta, itama kallon ta tayi tace, "Ina fa lafiya Zahra, Zaid ne a asibiti wallahi a can ya kwana ma, amma yanzu dai Daddyn nasa yace anyi discharging d'in su zasu koma gida". "Subahanallahi, Mummy me ya same shi?" Zahra ta fad'a cikin tashin hankali tana kallon ta.

"Wallahi wai jiya da daddare kamar e yanzu abokin sa Hameed ya same shi a d'aki tana ta tari jini na zuba a bakin sa, ciwon dai zuciyar nasa d'in nan ne dai ya tashi har yafi wancan" ta k'arasa fad'a cikin damuwa a kan fuskar ta. Ibteesam da ta k'ame a wajan cikin tashin hankali bata san lokacin da tace, "Yanzu yaji sauk'i?". Kallon ta Mummy tayi tace, "to kin san halin sa da azazzala ya takura sai an sallame shi wai ya gaji da zaman asibitin tunda ya samu sauk'i, baki ji muryar Daddyn saba kamar yayi kuka, ciwon mai d'a d'aya bashi da dad'i" Mummy ta k'arasa fad'a cikin raunin murya. Shiru Ibteesam tayi tana jinm kamar ta jawo gobe tazo su tafi Kano kawai ta ganshi.

Washe gari da wuri suka d'auko mota suka tawo Kano cikin kewar y'an uwan ta da ta baro da alqawarin zasu zo Kano.

Zaid yana zaune yana shan tea a hankali gefen sa Hameed ne da Wizzy, Hameed ya k'are masa kallo yace, "Zaid kaga yadda ka rame lokaci d'aya kamar ba kai ba, dan Allah ka daina saka wannan damuwar a zuciyar ka kaga kana da matsalar zuciyar." Ajjiye kofin hannun sa yayi ya kalli Hameed yace, "Wai me zanyi wanda za'a sha wahala kafin a raba ni da matata koda tace bata so?" Ya fad'a muryar sa a dashe yana kallon su. "Kamar yaya kenan Mai gida?" Wizyy ya tambaya yana kallon sa. "She's my wife but suna so su raba ni da itane" ya fad'a cikin tari kad'an yana dukan k'irjin sa. Wizzy ya gyara zama yace, "Ai kawai ta inda zakayi maganin abun ku samu yarinyar ku zama d'aya kai da ita shine zaka dak'ile duk wani abu da ake so a zagayo maka dashi". Kallon sa Zaid yayi yace, "Mu zama d'aya like how?". Y'ar dariya yayi yace, "Mai gida matsalar ka kai hausa bata ishe ka ba, abinda nake nufi kawai kasan yarinyar a y'a mace".

Dafe kai yayi kafin yace, "Ka fad'a yadda zan gane bana son magana cikin magana". Hameed ya kalli abokin nasa cikin tausayin halin da yake ciki yace, "Abinda Wizzy yake nufi sex ya shiga tsakanin ka da ita." D'ago kai yayi ya zubawa Hameed ido jin abinda yace kafin yace, "Kana ganin zata amince ita?". Wizzy ya cafke maganar yace, "Sai ta yadda kai ba mijin ta bane? Ai kana da damar yin duk abinda kake so". Tab'e baki yayi ya koma jikin kujerar ya kwanta tare da fad'in, "Nop bana son mata abinda bata so, sai nayi tunani" ya fad'a tare da mik'awa ya shiga d'akin sa.

"Mai gida Hameed ina tausayin mai gida wallahi, budi yadda soyayya ta mayar dashi kamar bashi ba duk ha rame yayi bak'i kullum cikin ciwo" Wizyy ya fad'a tana kallon Hameed,? "addu'a zamu taya shi da ita Wizzy Allah ya bashi lafiya ya kuma daidaita su, dan matuk'ar ya rasa wannan yarinyar zai iya rasa rayuwar sa da ba k'aramin so yake maya ba" Hameed ya fad'a yana kallon k'ofar da Zaid ya shiga.

Ibteesam basu shigo Kano ba sai bayan azahar hakan ya saka suka wuce gida direct suka yi wanka aka kwanta kowa a gajiye yake.

Sai bayan la'asar Ibteesam ta farka ta tashi tayi sallah suka ci abinci, bayan sun gama cin abincin Abba ya kalli Ibteesam da take kallon Tv yace, "Baby an gaji ko?" Ta fad'a tana murmushi, "Eh wallahi Abba, amma yanzu ai na dawo dai-dai" ta bashi amsa yana murmushi. Yace, "zaki je kiga Maman ki ko?". D'aga masa kai tayi alamun eh, "kafin ki je ina so na tambaye ki?" Ya fad'a yana mayar da hankalin sa kanta, itama hankalin ta ta tara masa tana jiran taji me zaice, "Akan batun mijin ki ne Maryam" Abba ya fad'a yana kallon ta, gaban ta ya fad'i haka kawai taji tsoro ya kamata amma sai ta daure tana jiran taji me zaice, Abba yace, "Maryam ki sanar dani gaskiyar abinda yake ranki kar ki b'oye min komai, kina son zama da Zaid a matsayin miji ko bakya so?" Ya fad'a dai-dai lokacin da Mummy ta fito ta zauna.

Gaban ta ya fad'i matuk'a ta kasa furta komai sai bakin ta da yake rawa dan ita kam bata san me zata ce ba, ganin shirun yayi yawa ya saka yace, "ke nake jira Baby." Muryar tace ta soma rawa tace, "Abbaaaa" sai kuma tayi shiru tana kallon k'asa, ganin hakan ya saka Mummy tace, "ka barta zamuyi maganar a kai yadda mukayi zan sanar dakai". Abba yace, "Shikenan". Mummy tace, "Yauwa zamu tafi duba Zaid d'in tunda mun huta" ta fad'a tana kallon Abba.

"Hakan yana da kyau" ya fad'a yana mik'ewa ya shiga ciki Mummy ma ta mik'e suka fito tare gabad'ayan su suka shiga mota sai gidan su Zaid.

Da sallama suka shiga Falon Anty Amina da take zaune ganin su ya saka ta mik'e tana fad'in, "Sannun ku da zuwa mutanen Gombe" ta fad'a da murmushi tana rarar su cikin murna da farin ciki, Ibteesam ta rungume Anty Amina tace, "nayi kewar ki Mama na". Shafa kanta tayi tace, "Sannun ku da zuwa". Zama sukayi kafin mai aiki ta cika musu waje su da abin sha, Anty Amina tace, "ya kuka baro mutanen Gombe, su Hajiya suna lafiya?". Mummy tace, "Lafiya lau suke, Hajiya tana gaishe ki". Murmushi Anty Amina tayi tace, "Ina amsawa da kyau, kunsha hanya yau kam". Mumny tace, "Wallahi kuwa, ya jikin Zaid d'in?". Tace, "Zaid da sauk'i duk da banga ya sakko bama gabad'aya, yana sama ai". Mummy ta mik'e tace, "bara muje na duba shi naga yanayin jikin nasa". Zahra ma ta mik'e tabi bayan Mummy suka nufi saman da Zaid d'in yake.

Anty Amina ta kalli Ibteesam tace, "Ke baza kije ki duba jikin nasa ba? Yayi rashin lafiya fa sosai kamar bazai rai ba" ya fad'a tana kallon Ibteesam da itama take kallon ta, d'an tab'e baki tayi tace, "Mama na gaji anjima naje na duba shi" ta fad'a tana mik'ewa ta shiga d'akin da ta take lokacin da tazo.

Eman kuwa tunda taga dawowar su tayi nufin aiwatar da aikin ta akan Zaid da Ibteesam, kanta ya kulle ta rasa a inda zata zubawa Ibteesam abinda zata sha, a guje ya shiga kitchen ta d'auki lemon kwali guda biyu ta jik'a magungunan ko wanne ya jashi a sirinji ta yiwa Lemukan allura, wanda akace ita da Zaid zasu sha ta d'auke d'ayan kuma ta ajjiye a inda tasan Ibteesam zata d'auka in ta shigo kitchen d'in, tana niyar fitowa Ibteesam ta shigo ta nufi fridge ta bud'e hannun ta ya kai kan lemon ta d'auka ta fito ba da ta kula Eman.

Eman kamar ta sume dan farin ciki ta fito cikin nishad'i ta zauna a falo tana jiran su Mummy su sakko daga saman ta hau ta kaiwa Zaid, babu jimawa su Mummy suka sakko lokacin ana kiran sallah magariba sukayi sallah suka cigaba da hira har i'sha sannan suka tafi tare da sallama suka tafi uta da Zahra, d'akin da Ibteesam Anty Amina ta shiga ta ganta a zaune tana shan lemo tace, "Baby tashi kije sama ki duba Zaid yanzun nan." Babu yadda zatayi dole ta mik'e hannun ta rik'e da kofin lemon ta fita daga d'akin ta hau saman sa, tana shiga taga Eman ta fito daga falon nasa, kallon kallo akayi Eman ta buga mata harara tare da tsaki ta fita ita kuma ta shiga.

A zaune yake ya had'a kai da guiwa a k'asan tiles ya zubawa hoton Ibteesam ido, jikin sa taga yana wani irin rawa kamar an jona masa shocking haqoran sa na had'uwa dana juna amma idon sa yana kan zanen hoton Ibteesam dake cikin d'akin.

A hankali ya juyo ya zuba mata ido yana kallon ta tana tsaye tana kallon sa cikin wani irin yanayi, maimakon ya tashi yaje inda takee kamar yadda zuciyar sa da gangar jikin sa takee ingiza shi sai ya mayar da kansa ka guiwar sa yana sauke numfashi, a hankali take takawa har lokacin glass cup d'in yana hannun ta ta k'arasa inda yake ta ajjiye lemon a nesa dashi ta tsuguna kusa dashi tace, "Sannu ya jikin naka?".

Furta hakan da tayi ya wani firgita ya d'ago kansa ya rik'e hannun ta ya k'ank'ame a jikin sa na rawa sosai, wuci taji daga jikin sa kamar tazo kusa da k'aramar wuta haka take ji jikin sa na fitar da wucin sabida zafin zazza6in da yake jikin sa, lemon bayan ta ta d'auka jin har lokacin akwai sanyi ta kafa masa kofin a bakin sa wai ko zai d'an ji sanyi, kamar jira yake ya shanye lemon ya kawar da kansa har lokacin baice komai ba.

Zama tayi kusa dashi kamar yadda yayi ta kwantar da kanta a kafad'ar sa tana jin yadda yake sauke numfashi a hankali a hankali, kanta ne taji ya sara tayi saurin dafe kai tare da furta, "Washhhh" tana cigaba da juya kanta, cikin ta taji yayi wani irin damk'a kamar an saka igiya an d'aure mata ciki ana tamkewa haka take ji, "ciki na" ta fad'a cikin muryar marasa lafiya tana sake kwanciya a jikin sa tana juya kai a kafad'ar sa.

A haukace ya d'ago ya rik'e fuskar ta yana kallon idon ta yana jijjiga ta dan ciwon kan da yake ji baya tunanin zai iya magana, ciwon cikin nata ne yake k'aruwa ta fara fitar da wani irin numfashi tana shigewa jikin sa tana juya kanta a k'irjin sa, lokaci d'aya yaji shima cikin nasa ya rik'e ya fara fitar da numfashi kamar ita amma hankalin sa yana kanta ganin yadda jikin ta yake rawa sosai numfashin ta na fita da saurin gaske kamar wanda zai bar gangar jikin ta.

A b'angaren Eman nata lemon da ta tsiyaya daga wanda ta kai masa tasha dan tana da tabbacin yasha wanda ta kai masa, zama tayi a kan kujerar dining tana jiran sakkowar Ibteesam ita kuma ta hau.

*Ayi hak'uri yau bana gida ne.*

*?ASAITAR SO!*

*58_59*

Not edited>??



Gawa ce a shinfid'e a tsakiyar falon an gama shirya ta ana jiran maza su shigo su d'auka, falon dank'am yake da mata ko wacce taci dogon hijjabi wasu sun rik'e carbi ana ja wasu kuma suna magana k'asa-k'asa, falon yayi tsittt baka jin komai sai sautin kukan mata da yake tashi kad'an-kad'an.

Anty Amina ce a zaune a gefe idon ta yayi ja sosai sabida kukan da tasha tayi tagumi da hannu d'aya tana jan jarbi tana kallon gawar da take kwance a wajan tana tuna maganar da sukayi a daren jiya, wata mata ce ta dafa ta daga bayan ta tace, "Haba Amina ki daina wannan kukan mana addu'a take buk'ata a yanzu ba kuka". Share hawayen ta kawai tayi tana kallon gawar ba tare da tace komai ba.

A guje Hajiya Batula ta shigo falon bayan ta farfad'o daga suman da tayi ta fad'a kan gawar tana fad'in, "Eman d'ina baza ta mutu ba, kuce mata ta tashi dan Allah, ke Eman tashi kar ki tafi ki barni kinji ki daure ki tashi" ta fad'a cikin fitar hayyaci tana jijjiga gawar Eman da aka rufe ta ruf baka ganin komai na jikin ta sai farin likkafanin da aka mata suttura dashi, Mama Asma'u ce ta ta shigo ta kama ta tana fad'in, "Ku taimaka min mu rarrashe ta" ta fad'a tana kallon matan Hajiya Luba ta tashi suka mik'ar da ita dak'yar daga kan gawar Eman, "Ni ku k'yale ni na tashi y'ata yarinya ta bata mutu ba, ku bari na tashe ta nasan bacci take" ta fad'a tana k'okarin fincikewa daga rik'on da suka yi mata tana sake nufar inda Eman take.

A lokacin maza suka shigo d'aukar gawar Hajiya Batula tayi kukan kura ta kwace jikin ta ta isa inda mazan suke ta fad'a kan gawar tana fad'in, "Babu wanda zai tafi da y'ar ta ku barmin ita ko a haka ne na dinga kallon ta kunji" ta fad'a kamar mai tab'in hankali tana kallon maza, Daddy ya kalli Anty Amina da Mama Asma'u yace, "Kuzo ku kama ta". Mik'ewa sukayi suka kama ta aka d'auki gawar Eman aka fita da ita daga falon Hajiya Batula ta fad'i a wajan a sume.

Mata suka yo kanta a guje aka janye ta daga hanya akayi gefe da ita ana yayyafa mata ruwa, dogon numfashi taja ta bud'e idon ta tana sauke numfashi a hankali, "ko wanne mai rai mamaci ne Batula muma duk y'an haka ne wata rana duka zamu bar duniyar mu koma ga mahaliccin mu, a yanzu Eman babu abinda take buk'ata a wajan ki sai addu'a wannan kukan da kike mata ba gata kike nuna mata ba addu'a ita kad'ai ce abinda zaki mata wacce zata isa har inda take, mun san da ciwo da radad'i da kuma zafi amma haka zaki jure ki daure ki ta karanta Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un zaki ji dad'i a zuciyar ki, bamu san me kike ji ba amma in kika mik'awa Allah lamuran ki zai miki maganin komai, kiyi mata fatan rahamar Allah da fatan Allah ya bata ikon amsa tambayoyin ta" Anty Amina ta fad'a tana rik'e da Hajiya Batula da take tsiyayyar da hawaye.

"To meyasa mutuwar bata d'auke wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login