Showing 78001 words to 81000 words out of 171073 words

Chapter 27 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7830

d'ora mata dutse haka take ji, daurewa tayi tana kuka ta kalli Abban tace, "Su waye suka haife ni?". Girgiza kai Abba yayi tare da fad'in, "Bamu sani ba muma Ibteesam, ziyara ta kaimu gidan marayu a ranar juma'a shekara goma sha tara kenan da suka wuce, a lokacin shekarar ki biyu da haihuwa a duniya muka karb'e ki muka dawo gida."

Ajiyar zuciya take saukewa a hankali idon ta na kan Abba tana kallon sa har ya kai k'arshe, sunkuyar da kai kawai tayi hawaye suka cigaba da zuba a idon ta, ta kasa furta komai balle tace ko zata ji dad'i a ranta, share hawayen ta tayi ta mik'e tsaye ta kalli iyayen nata tayi murmushi tace, "sai da safen ku" daga haka bata sake waiwayowa ba ta fita daga falon da sauri.

Kuka Umma take yi sosai itama batace komai ba ta fita daga falon, aka bar Mama a tsaye tana raba ido Abba kuma yana zaune yana kallon ta, maganar da taga yana son yi ya saka tayi wuf ta fita itama ta bar falon.

A daren wad'an nan mutane hud'u sun kwana zuciya babu dad'i a haka har garin Allah ya waye.

Washe gari kamar koda yaushe Ibteesam ta daure ta tashi tayi duk abinda zatayi wanda ta saba yi kullum tayi wanka ta shirya, d'akin Umma ta shiga da sallama ta same ta a zaune tayi shiru, amsa sallamar tayi ta d'ago tana kallon ta gaban ta na fad'uwa, "Ina kwana Umma, yau na makara sallah da yawa" ta fad'a cikin k'okarin b'oye damuwar ta.

Umma bata amsa ba sai rik'e hannun ta da tayi ta kalli fuskar ta tace, "Kowa ya kalli fuskar ki ya san kina tare da damuwa Ibteesam, kina son ki san asalin jyayen ki ko?". Girgiza mata kai tayi tace, "ko d'aya Umma, nasan na kwana da damuwa amma ba irin wacce kike tunani ba, tunani na bai wuce akan ta yadda aka same ni ba, shin ni y'ar halak ce ko akasin ta, shine abinda yake tsaya min a rai bayan shi babu komai Umma, ki kwantar da hankalin ki Umma na har duniya ta tashi ke zan cigaba da yiwa kallon uwa ta haka Abba shi zan nuna matsayin mahaifi na domin ku na taso na sani, ku kuka raine ni kuka bani tarbiyya mai kyau, bayyanar wannan maganar a gare ni bazai saka na juya baya ba kuna nan kamar yadda kuke a waje na" ta k'arasa fad'a da murmushi a fuskar ta.

Umman ma murmushin tayi tace, "Allah yayi miki albarka Ibteesam". "Amin Umma na, baza'a karb'o miki d'inkin bane?" Ta fad'a tana kallon Umman nata, "za'a karb'o Ibteesam". Mik'ewa tsaye tayi tace, "To bara na d'auki Jafar muje mu dawo kin san halin telan naki da safe anfi samun sa." "Baki breakfast ba zaki fita?". "Kin san breakfast bai wani dame ni ba, bana jin yunwa a yanzu" tana gama fad'ar hakan ta fita Umma ta bita da kallon tausayi.

A falo taga Jafar ya gama karyawa yana k'okarin fita tace, "Jafar tsaya na d'auko mayafi ka raka ni wajan Salim tela" ta fad'a tana shiga d'aki ba jimawa ta fito suka tafi.

Dake basu da nisa titi kawai zaka fito ya saka nan da nan suka k'araso wajan suka shiga da sallama, matshiyar budurwa dake zaune da alama itama jiran sa take ta amsa tana kallon Ibteesam, "Sannun ki" Ibteesam ta fad'a tana zama kusa da ita.

Murmushi Zahra tayi tace, "Yauwa sannu kema". Daga haka babu wacce ta kuma magana sai satar kallon Ibteesam da Zahra take yi tana mamakin wannan kamannin ta, "Hajiya Ibteesam kece da safiyar nan?" Salim ya fad'a yana fitowa daga inda suke ajjiye kaya in sun gama, d'an murmushi tayi kana tace, "Eh nice kasan irin ku sai ana zuwan safiya dan tsaf zan zo naga baka nan, d'auko min kayan Umma sauri nake". Y'ar dariya yayi kawai ya koma d'akin da ya fito.

Zahra da mamaki ya kusa sumar da ita jin sautin maganar Ibteesam kamar ta Abban su ya sanya ta sake kallon ta a lokacin Ibteesam ta sunkuyar da kai tana danna waya, waya ta d'auko da niyar yiwa fuskar Ibteesam hoto Salim ya fito yana fad'in, "Hajiya Ibteesam ga kayan naki" ya fad'a yana mik'a mata ledar kayan Jafar ya karb'a, mik'ewa tsaye tayi tace, "Daman an biya gabad'aya ko?". D'aga kai yayi alamun eh tare da fad'in, "casss ma kuwa." Dariya tayi tace, "to sai anjima, ki gaida gida" ta fad'a tana kallon Zahra da take binta da ido.

Salim ya kalli Ibteesam da ta fita ya kalli Zahra yace, "tab, banda nasan Ibteesam haifaffiyar unguwar nan ce ba da nace y'ar uwar kice Zahra, wannan kamar taku har ta b'aci fa" ya fad'a da mamaki a fuskar sa.
"Ashe bani kad'ai na gani ba" ta fad'a tana kallon Salim, "wallahi kunyi mugun kama kamar yaya da k'anwa". "Allah kenan" Zahra ta fad'a cikin mamakin da ya kasa barin ta, "ga kayan ki, ki gaida Mummyn dan Allah." Da to kawai ta amsa ta karb'i kayan ta fito ta shiga mota ta bar wajan cikin al'ajabi.

Koda suka koma gida bayan Ibteesam ta bawa Umma kayan ana dubawa Jafar yace, "Umma muka had'u da wata a wajan me d'inki kamar su d'aya da Anty Ibteey wallahi." Umma ta kalli Ibteesam tace, "Wai haka?". K'aramin tsaki tayi tace, "Oho masa nikam ban kula bama". Umma tayi dariya kawai aka shiga da kallon d'inkin.

**

A hankali yake takawa zuwa saman yana jiyo muryar Daddy da take tashi a hankali da alama waya yake yi, har zai tura d'akin ya shiga sai ya tsaya jin abinda Daddy d'in yake cewa, daga cikin falon Daddy ne yake fad'in, "Eha
gaskiya maganar haka take, amma ni gaskiya bana so Zaid yasan Ibteesam matar sace yanzu nafi so ya k'ara yin hankali tukunna sai a sanar dashi, amma yanzu abinda zai faru a tuntub'i Ibteesam d'in aji in wanda yake neman auren nata ne a ranta cikin ruwan sanyi za'a raba auren su da Zaid ba tare da ta sani ba shima ya sani ba". Shiru yayi alamun yana sauraron abinda ake fad'a masa a waya kafin ya cigaba da fad'in, "Hakan shine dai-dai ai, Allah ya zab'a abinda yafi alkhairi" daga haka suka yi sallama Daddy ya kashe wayar.

Zaid da yaji komai ya saki murmushin da ya jima baiyi irin sa ba yana jin sa fess dashi kamar wanda aka tsamo daga cikin wuta aka saka shi a waje mai sanyi, daidaita kansa yayi kafin yayi sallama ya shiga cikin falon, "Daddy lafiya kake kuwa?" Ya tambaya yana k'arasawa cikin falon yana kallon mahaifin nasa.

Kallon sa shima yayi tare da fad'in, "Me ka gani?". "Haba Dad kalle kafa duk kayi wani iri kamar ba kai ba, me yake damun ka?'". Ajiyar zuciya Daddy yayi kafin yace, "Ciwon kane yake damu na Zaid, rashin lafiyar ce take tab'a na rasa wanne kalarr tunani ma zanyi."

Kallon Daddyn nasa yake yana karantar yanayin sa kafin ya zauna yace, "Daddy ni na ji sauk'i na warke beside yanzu ma fita zanyi, amma bayan ciwo na akwai wani abun kana k'okarin b'oye min ne kawai". Kallon Zaid d'in Daddy yayi kafin ya d'auke kai yace, "ina zaka je bayan ba lafiya ce dakai ba?" Ya kawar da waccan maganar dan baya son sanar da Zaid asalin abinda yake faruwa a gidan, "zanje wajan Hameed, Daddy baka amsa min ba" ya sake dawo da tambayar.

"Jeka ka dawo mayi maganar" Daddy ya fad'a yana mik'ewa daga falon ya shiga d'aki, ganin hakan ya saka dole shima ya Mik'e ya sauka ya fita daga gidan.

*****
"Mummy! Mummy!!" Zahra take kwala mata kira tun daga k'ofar shiga falon har cikin d'akin ta, "kee lafiya wannan kira kamar makauniya?" Mummy ta fad'a tana kallon ta.

"Mummy yau naga abin mamaki a wajan Salim tela wanda tunda kika haife ni ban tab'a ganin irin sa ba." Gyara tsayuwa Mummy tayi tace, "Me kika gani?". "Wata yarinya Mummy mai kama da Abba sak kamar an tsaga kara, wallahi koni da Yaya Khalipha bamuyi kama da Abba kamar ta ba, Mummy har maganar ta irin ta Abba wallahi." Gaban Mummy ya fad'i ta dafe k'irji tace, "Zatayi kamar shekara nawa a duniya?". D'aga kai Zahra tayi kamar mai tunani kafin tace, "Eh baza ta wuce kamar 20yrs ba ko sama da haka." Mummy ta kuma rud'ewa tace, "Meye sunan ta?". Zahra tace, "Ibteesam naji Salim ya kira ta dashi, Mummy har irin d'an d'igon bak'in nan na gefe fuskar Abba tana dashi. "

Da sauri Mummy ta bud'e drawer ta d'auko hoto ta nunawa Zahra tace, "Kalli dakyau tayi kama da wannan?". Kallon hoton Zahra take tana tuno fuskar Ibteesam kafin tace, "To ai kinga wannan yarinya ce Mummy ita kuma babba ce, yanayin fuskar su dai yayi kama da na juna sosai ma kuwa, kai itace ma wannan" Zahra ta fad'a cikin tabbatarwa.

Cikin rawar murya Mumny tace, "Indai wannan kika gani yayar ki Maryam ce Zahra, itace yayar ku" ta fad'a jikin ta har rawa yake.

Zaro ido Zahra tayi tace, "Itace Mummy wallahi itace, sabida Salim ma sai da yace badan yasan a unguwar take ba da yace nida ita yaya da k'anwa ne, Mummy bara na koma wajan Salim ya bani address d'in ta" ta fad'a tana niyar fita, tare suka fito falon ita da Mummy suka tarar da bak'i suna sallama.

Dukkan su tsayawa sukayi suna kallon bak'in dan ya zamar musu dole su d'aga zuwa wajan Salim a lokacin sabida zuwan bak'in.

********

Zaid tunda ya shiga mota maimakon ya bi hanyar gidan su Hameed kamar yadda yayi niya sai ya tsinci kansa a k'ofar gidan su Ibteesam, kamar koda yaushe bayan yayi parking cikin gidan ya shiga ba tare da neman izini ba.

Kusan karo sukayi da Asiya tana niyar fitowa tayi saurin bashi hanya, har ya gota ta ta tsayar dashi ta hanyar fad'in, "Gaka mai kyau, mai ilimi, d'an asali, amma ka tsaya kana son wacce bata da asali bata da dangi wata k'ila ma zina akayi aka samar da ita". Juyowa yayi dan yaga da wa take magana sai yaga shi take kallo alamu yana nuna dashi yake kenan, "ina magana ne akan Ibteesam, bata dace dakai ba domin ita ba y'ar gidan nan bace tsinto ta aka yi a gidan marayu iyayen ta sun cillar da ita, kasan irin yaran na wanda aka haifa ta hanyar zina haka iyayen su suke musu" ta k'arasa fad'a da murmushi ganin ya tsaya yana sauraron ta.

Kamal ne k'anin ta yazo wuce Zaid ya rik'o shi ya nuna masa Asiya yace, "Tana da hankali ko mahaukaciya ce?". Kamal ya zaro ido yace, "Ba mahaukaciya bace yaya tace fa." Girgizq kai Zaid yayi tare da sakin yaron yace, "Good" ya furta yana kallon ta da itama shi take kallo, ba zato babu tsanmani taji saukar zafafan maruka a kuncin ta har guda hud'u.

Bata gama dawowa dai-dai ba ya cafki wuyan ta ransa a b'ace yace, "ido na kike kalla kike cemin Ibteesam da zina aka haife ta,? Ni kike fad'awa haka?" Ya fad'a yana sake d'auke ta da marin da ya kusa saka ta suma ta kwalla k'ara tana ihu.

Jiyo ihun ta da mutunen gidan sukayi ya saka ya fito a guje kowa yana so ya riga d'an uwan sa zuwa inda aka jiyo ihun nata, dai-dai lokacin da ya tsuguna a inda ta fad'i yana nuna ta da yatsa yace, "in kika sake kika k'ara kiran Ibteesam da makamancin wannan sunan sai na canja miki kamanin wannan banzar fuskar taki mai kama da monkey." "Waye kai da zaka zo har cikin gidan su ka dake ta,? Mai hankali ko mara hankali?" Mama ta fad'a daga baya dan bata hango fuskar Zaid bayan sa take gani, mik'ewa tsaye yayi ya karkad'e hannun sa kamar wanda yayi aikin k'asa ya juyo a hankali ya watsa mata idon sa yana takawa a hankali har yazo inda take yace, "da me nayi miki kama a idon ki?." Muryar Mama ta fara rawwa tace, "A'a ai ban san kai bane ba." "Sai kin bani amsa dame nayi miki kama?" Ya fad'a a tsawace yana kallon ta.

"Mai hankali" ta fad'a jikin ta har rawa yake yi, "good" ya furta yana bin mutanen da suka fito da kallo, Umma ce kawai da Jidda babu Ibteesam a wajan sai kawai ya wuce su ya nufi b'angaren Umma kai tsaye.

A falo ya tarar da Ibteesam tana kuka bata ma san ya shigo ba sai maganar sa taji yana fad'in, "Umma meya sata kuka?". Umma daa ta shigo a lokacin tace, "Abinda waccan ta fad'a maka shine ya saka ta kuka." Numfashi ya fesar ya nufi k'ofa da niyar fita Umma tayi sauri tace, "Ina zaka je kuma?". Juyowa yayi ya kalli Umma yace, "Yadda ta saka ta kuka ni kuma zanje na saka jini ya fita daga jikin ta, zan mata tabon da baza ta tab'a manyawa da ni a duniya ba." "A'a kar kaje" Ibteesam ta fad'a cikin muryar kuka tana kallon sa.

Dawowa baya yayi ya kalle ta yace, "Kina so ta saka ki kuka a banza a wofi ne,? Bata isa ba sai tasan ta tab'a ki". "Yaya tace fa" ta bashi amsa tana goge hawayen ta, "ita ta haife ki?" Ya fad'a yana kallon ta. Girgiza kai tayi tace, "Ba ita ta haife ni ba, amma kuma itace gaba dani." Girgiza k'afa yake yana daga tsaye hannun sa na cikin aljihu yace, "ita kuma wacce take goyan bayan ta wacece?". "Mahaifiyar tace" ta bashi amsa, "okay, zan had'a su dukkan su nayi musu hukunci dai-dai dasu".

Ibteesam tace, "Dan Allah kar kaje". A fusace ya kalle ta yace, "kina so su zage ki a banza ne,? Ko kina so su saka ki kuka a banza?." "Nidai nace ka k'yale su kawai" ta fad'a tana kawar da kanta daga kansa.

Kallon Umma yayi da take tsaye tana kallon su sai a lokacin ya tuna bama su gaisa ba yace, "Ina kwana". "Lafiya lau, ya jiki?". "Da sauk'i" ya furta yana zama kusa da Ibteesam, "meyasa baki zo kin duba ni ba jiya da yau?" Ya tambaye ta ba tare da ya kalle ta ba.

"Babu komai" ta bashi amsa a tak'aice, kallon ta yayi kafin ya tab'e baki yace, "K'arya kike yi, na fad'a miki bana zama inuwa d'aya da mak'aryaci sabida bana son k'arya ki sanar dani dalili." "Ni shine dalili na bayan shi babu komai." Gyara zama yayi ya kalle ta sosai yace, "ina so ki jawa wannan saurayin naki kunne naji yana maganar wai auren ki zaiyi ko? Ina so ki fad'a masa fita daga sabgar ki in ba so yake yayi dana sani ba." Bata amsa ba ba kuma ta kalle shi ba tana jin sa yana maganar sa wacce take sake b'ata mata rai.

Kallon ta yayi yaga bama shi take kallo ba sai yayi k'wafa yace, "Tashi ki raka ni wani waje" ya fad'a yana mik'awa tsaye, "bazan je ba" ta bashi amsa kai tsaye. "Sai kinje, tun muna shaida juna ki tashi in kuma so kike na d'auke ki ta k'arfi shikenan" ya fad'a yana fara tattare hannun rigar sa.

Mik'ewa tsaye tayi ta kalle shi tace, "Umma baza ta barni ba." "Baza ta hana ba, shiga ki fad'a mata ina jiran ki, wallahi kika ki fitowa sai na shigo d'akin na d'auko ki kinji nace wallahi" ya k'arasa fad'a yana girgiza kai.

Shiga tayi ta sanar da Umma kamar yadda ta zata Umman bata hana ba ta fito, yana ganin fitowar ta yayi gaba ta biyo shi a baya har mota suka bar unguwar.


*Afuwa yau bani da caji ne shiyasa..*

*Kar a fitar min da littafi dan ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Allah.*


*?ASAITAR SO!*

*49_50*

Not edited>??


*Page d'in yau ku gyara zama kawai* >?#?=؃?


Tunda suka fara tafiya bata ce komai ba shima kuma haka tuk'i yake a hankali kamar baya son tafiyar, tana lura dashi sai rufe ido yake ya bud'e kamar wanda yake jin bacci, inda babu mutane sosai ya samu ya tsayar da motar tare da kansa a kan sitiyarin motar kamar mai bacci.

Kallon sa tayi da d'an mamaki kafin ta d'auke kanta ta mayar kan titi, shirun taji yayi yawa hakan ya saka ta sake jiyowa sai taga hannun sa akan cikin sa yana jan numfashi dak'yar, "lafiya?" Ta tambaya idon ta a kansa. Bai d'ago ba kai kuma ce komai ba hakan ya saka ta sake cewa, "jikin naka ne ya tashi?". Nan ma shiru babu amsa sai motsi kawai da yake yi, "Ina magana kayi shiru, in baka da lafiya ka sanar sai muje asibiti" ta fad'a kamar zatayi masa kuka.

Sai a lokacin ya d'ago kansa ya mayar jikin kujera ya kwanta har lokacin idon sa a kulle yake yace, "ciwo nake ji a ciki kad'an". "Innalillahi, to ai gwara muje asibiti kafin abin yayi nisa" ta fad'a a rud'e tana kallon sa. Bud'e ido yayi ya kalle ta yace, "ko munje asibitin baza su iya min maganin sa ba" ya fad'a muryar sa na fita dak'yar dan da gaske ciwon yake ji.

"To a ina za'a samu maganin sa in ba asibiti ba?" Ta tambaya har lokacin a rud'e take, "wajan ki" ya fad'a can k'asan mak'oshi yana lumshe ido ya bud'e a fuskar ta, d'an zaro ido tayi kad'an tace, "Waje na kuma?." "Uhum" ya furta yana mayar da idon sa ya kulle. "Like how?" Ta tambaya tana rik'e hab'a cikin mamakin abinda yace.

Bud'e idon sa yayi ya kalli cikin idon ta yace, "hannun ki" ya fad'a a hankali kamar wanda baya so wani yaji abinda yake son fad'a mata, da ido tayi masa alama da bata gane ba, ajiyar zuciya yayi ya mayar da idon sa ya kulle ya jawo hannun ta guda d'aya ya d'ora a kan cikin sa, kallon sa take da mamaki da fad'uwar gaba zatayi magana taji hannun ta ya sauka a akan fatar cikin sa, niyar kwace hannun ta tayi yayi saurin matse shi yace, "Pls shine zai saka na samu relief". Runtse ido tayi cikin kunyar da tazo mata lokaci d'aya tana jin yadda zafin da cikin sa yayi yana shiga cikin tafin hannun ta ga gashi-gashi da take ji hannun ta yana tab'awa.

Shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login