Showing 84001 words to 87000 words out of 171073 words

Chapter 29 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7859

shi...." d'au ya d'auke ta da marin da yasa ta ganin taurari guda hamsin sun wulga ta idon ta lokaci d'aya,? hawaye suka zubo daga idon ta dan ba k'arya marin ya ratsa ta, "Hasbunallah" ya furta yana dafe kai ganin yadda take kuka har ta zauna a akan kujera hannun ta rik'e da kuncin ta, da sauri ya zauna kusa da ita ya jawo ta jikin sa tana fizgewa ya rik'e ta gam ya kwantar da kanta a k'irjin sa tana rera kukan da yake jin sautin sa har cikin zuciyar sa.

Bugun zuciyar sa ya k'aru da jin yasa take ta k'okarin fincikewa ta kasa sabida rik'on da yayi mata, "I'm sorry precious banyi nufin saka ki kuka ba, pls ki daina kuka ina ji har zuciya ta, in ba kina so zuciya ta ta buga ba ki daina wannan kukan pls" ya fad'a dak'yar yana hakki dan ba k'aramar azaba yake ji a zuciyar sa.

Cikin kuka tace, "A haka kake sona kana duka na? Wanda yake son baya k'aunar yaga wani ya tab'a ka balle shi da kansa, a haka zan sokan?" Ta fad'a tana kuka sosai.

"I promise u bazan sake dukan ki ba insha Allah, I'm so sorry ina da kishi ne sosai, ina kishin ki ina jin zafi na ganki da wannan yaron" ya fad'a yana shafa gadon bayan ta alamun rarrashi.

Kukan take bata daina ba tana jin zuciyar ta babu dad'i, "nayi alqawari bazan sake dukan ki ba daga yau har a tashi duniya insha Allah, ki daina kuka kinga na baki hak'uri" ya katse mata tunani da fad'ar hakan. Bata daina kukan ba kuma batayi magana ba, "babu macen da na tab'a bawa hak'uri cikin son raina sai ke, ban tab'a yiwa Mama na laifi ba har ta bar duniya haka Daddy na balle na basu hak'uri, kece ta farko kodan wannan kiyi daure kiyi kinji?" Ya fad'a cikin rauni dan sosai kansa yake sarawa ga zuciyar sa na bugawa da sauri.

Nan ma bata amsa ba bata daina kukan ba kuma sai ya sake ta ya koma gefe ya dafee kansa da saitin zuciyar sa yace, "Nayi magana da yawa kaina na ciwo amma na kasa shiru sai kin daina kuka, zuciya ta precious zata fito indai baki daina ba" ya fad'a yana fitar da numfashi dak'yar dan sosai k'irjin sa yayi nauyi sosai.? Ganin yanayin sa ya saka ta goge hawayen ta k'arasa kusa dashi ta zauna a k'asan carpet tana kallon sa tace, "Shikenan na daina nayi hak'uri, amma kaima duk abinda nace bana so na daina kaji?". Bai iya amsa mata ba sai juya mata kai kawai da yake yi dan baya tunanin zai iya magana sabida kansa.

Hannu ya saka ya jawo ta ta mik'e tsaye ya zaunar da ita a kan kujera ya mayar da kansa kan cinyar ta ya kwanta, hannun ta ya jawo ya dafe zuciyar sa ya d'ora nasa hannun a kan nata, ya d'auki d'ayan ya d'ora a goshin sa ya lumshe ido, lup-dup haka take ji zuciyar na bugawa da sauri ga jijiyoyin kansa na harbawa kamar zasu tsinke, shiru tayi ta kasa koda motsin kirki yana jikin ta a kwance kusan mintina biyar suna a haka kafin taji yana sauke numfashi a hankali alamun yayi bacci.

Kallon fuskar sa take tana jin wani abu mai kama da tausayi da soyayya yana ratsa cikin zuciyar ta lokaci d'aya, a hankali take shafawa goshin sa duk da zuciyar ta tana hana ta amma b'angaren zuciyar ta na dama yana k'arfafa guiwa a kan hakan, murmushi tayi tunawa da yanayin su na d'azu ya bata nishad'i sosai.

A haka itama tayi bacci ba tare da ta sani ba har lokacin hannun ta na kan k'irjin sa da goshin sa, sai k'arfe shida sannan ya bud'e idon sa tare da mik'ewa tsaye, kallon ta yayi yaga tana bacci wuyan ta ya karkace ya saka shi yayi saurin mik'ewa ya kwantar da ita akan kujerar sosai yadda zatayi balance ta sake sosai, murmushi yayi tare da yi mata kiss a goshi ya shiga cikin d'aki.

Wanka yayi tare da alwala ya saka jallabiya yana fitowa tana bud'e idon ta, d'an sakin fuska yayi kad'an amma baiyi murmushi ba yace, "barka da tashi, time d'in sallah ya kusa" ya fad'a yana nuna mata agogon d'akin.

Da sauri ta mik'e ta lalubo wayar ta ta kunna tana fad'in, "Wayyo Allah nasan Umma nata kira na, kazo ka mayar dani gida dan Allah, ni bana son irin haka". "Calm down Umma baza ta nemi ki ba kinji? Relax" ya fad'a yana k'arasowa falon. "Meyasa kace haka?" Ta tambaya tana mik'ewa tana k'okarin mayar da d'ankwalin ta da ya zame, "Cos tasan kina tare da mijin ki, wow yayi kyau" ya fad'a yana rik'e d'ankwalin yana d'an shafa kiston kanta.

Kwace d'ankwalin tayi ta d'aura tare da fad'in, "Babu kyau, haramun kake tab'awa fa." "Who told you?" Kallon sa tayi kafin tace, "Ai kaima kasan haka ne basai an fad'a ba." D'aga gira sama yayi yace, "Nidai nasan ba haramun nake tab'awa ba, ko a gaban Umma zanyi baza tace komai ba." Kallon sa tayi tace, "Baka son k'arya amma yau kayi." Yatsine fuska yayi yace, "Ba k'arya nake ba ina fad'a miki gaskiya ne, amma zan tabbatar miki da hakan" ya fad'a yana mik'ewa tare da shiga small cafe d'in sa.

Ita kam alwala take so tayi ga fitsari da take ji amma tana kunyar shiga d'akin sa kai tsaye ba tare da yace ba, ta kasa zama sai juyi take domin fitsarin ya kamata sosai, a lokacin ya dawo hannun sa d'auke da coffe cup biyu ya ajjiye mata d'aya yana kallon ta, zama yayi ya kurb'i coffen kafin yace, "ki shiga bedroom d'in mana ba fitsari kike ji ba?" Ya fad'a yana d'aga mata gira d'aya.

Da sauri ta Mik'e ta shiga ya bita da kallo yana murmushi a zuciyar sa, bata jima sosai ba ta fito har d'ankwali ta d'aura ta kalle shi tace, "Mu tafi gida dan Allah." "Tab ai in mukayi sallah ma 355 restaurant zamu je ko bakya jin yunwa?". Girgiza kai tayi tace, "Bana ji ni muje gida kawai." Baice komai ba ya nuna mata coffee da hannun sa.

Dole ta zauna ta d'an sha kad'an akayi kira yaje masallaci ya dawo itama tayi sallah sannan ya dawo, wayar sace tayi k'ara ya duba yaga sunan Mummy hakan ya saka ya d'auka tare da sakawa a kunne, "okay ganin nan" ya fad'a bayan ya saurari abinda akace, kallon ta yayi har zai magana sai ya fasa ya d'auki key d'in motar sa ya bud'e ta inda zata sada su da babban falo suka fara sauka ba tare da tasan ta inda zasu fita ba.

A can falon kuwa Abban su Zahra ne da Daddy da Mummy a zaune ana jiran sakkowar Zaid d'in Anty Amina ta shiga falon da sallama tana k'okarin ganin tayi murmushi, "Sannun ku da zuwa, kuyi hak'uri ban fito da wuri ba ina sallah ne" ta k'arasa fad'a tana shigowa falon.

Abban Zahra ya d'ago kai da niyar su gaisa suka had'a ido? da ita ya Mik'e a firgice yana nuna ta da yatsa yace, "Amina!". Jin maganar wanda baza ta tab'awa mantawa dashi a duniya ba ya saka ta d'aga kai a fircgice ta kalle shi, zaro ido tayi da ta tabbatar shine tace, "Khabir!".

Mik'ewa Mummy tayi ta kalle shi tace, "Kaima ka santa ko? Itace wacce na fad'a maka a asibiti na ganta kamar na santa.". "Safiyya Amina ce fa, Amina matata ta shekarun da suka shud'e."

Da mamaki da tsoro da fargaba tace, "Amina dai?". D'aga mata kai yayi yace, "Amina mahaifiyar Maryam". Zaro ido waje Mummy tayi ta juya ya kalli Anty Amina da itama ita take kallo ta dawo da kallon ta ga Abban Zahra sai kawai ta fashe da kuka, a lokacin Zaid ya k'araso falon Ibteesam tana daga can baya a tsaye ba wanda ya lura da ita, "Mummy meya saka ki kuka? Wannan matar ce ko,?" Ya tambaya a fusace yana nuna Anty Amina da ta daskare a wajan.

A fusace yayi kan Anty Amina kamar zai kame ta yace, " wai ke wacce irin mata ce ne? Mummy me tayi miki ki fad'a min kafin na shak'e ta" ya fad'a yana juyowa ya kalli Mummy wacce ba tashi take yi ba.

"Khabeer ina y'ata Maryam?" Anty Amina ta fad'a tana kallan Abban Zahra da Mummy.

"Ina wunin ku" muryar Ibteesam ta shiga cikin kunnen su dukkan su suka juyo suna kallon ta, firgita tayi da kallon da suke mata dan kowa ya zuba mata ido kamar zasu cinye ta, a hankali Mummy take k'arasowa kusa da ita tace, "Daddyn Zaid wacece wannan?". Daddy da ya shiga rud'ani yace, "Maryam kenan matar Zaid, ina nufin wacce Zaid yake so zai aura."

Jawo hannun ta tayi ta k'araso da ita falon ta tsayar da ita a gaban Abban Zahra, kallon sa take tana zare ido shima kuma kallon ta yake yana ganin kamar fuskar saa aka cire aka sakawa Ibteesam, Zahra da ta shigo falon a lokacin bayan ta idar da sallah tace, "Mummy Ibteesam, wacce mukaa had'u a wajan Salim" ta fad'a tana nuna Ibteesam da yatsan ta.

Kallon Daddy Mummy tayi tace, "Ina iyayen ta?". Daddy yace, "A unguwar yakasai suke, lafiya dai ko?". Mummy tace, "Sune suka haife ta?". Daddy ya d'an jimm yana kallon fuskar Ibteesam kafin ya girgiza kai alamun a'a yace, "Abban ta ya sanarr dani a gidan marayu suka same ta."

Zubewa Mummy tayi tare da yin sujudul shukur kafin ta d'ago tana kuka sosai tace, "Ko tantama bana yi itace Baby, Khabeer itace Babyn mu da muka jima muna nema" ta fad'a tana fashewa da kuka. Juyawa Mummy tayi ta kalli Anty Amina tace, "Maryam d'in ki wacce kika haifa itace wannan, ko tantama banayi itace y'ar da kika haifa kika tafi kika barta a hannu na" ta fad'a tana nuna Ibteesam da ta kasa motsin kirki a wajan.



_fans, bara na sauke numfashi kafin nace komai dan lamarin ya bani tsoro nima....>?/? Amina as Ibteesam mother=?F? @&?=?1?=?(?_

*?ASAITAR SO!*

*51_52*

Not edited>??


Kallon Ibteesam Anty Amina tayi ta mayar da kallon ta ga Abban Zahra ta kalli Mummy tace, "Kuna so kuce wannan ce Maryam wacce na tafi na barta a lokacin tana da kwana arba'in a duniya?". Mummy ta kalli Abban Zahra kafin ta mayar da kallon ta ga Anty Amina tace, "Ko tantama bana yi wannan d'iyar kice Maryam." "To ya akayi ta bar hannun ku?" Ta tambaya tana kallon su cikin tuhuma.

"Zauna na baki labarin dukkan abinda ya faru bayan barin ki gidan" Mummy ta fad'a tana nuna mata waja? zama alamun ta zauna, sallamar Umma da Abba ya saka kowa ya mayar da hankalin sa gare su da sauri Ibteesam ta k'arasa wajan Umma tana fad'in, "Umma gwara da kika zo suna so su tarwatsa min kwakwalwa ta na gaza gane abinda yake faruwa a nan" ta fad'a kamar zatayi kuka.

Daddy yace, "Ku shigo mana, ni na kira su nace in suna da dama suzo dan suna daga cikin wanda zasu warware abinda yake faruwa a nan" ya fad'a yana nunawa su Umma wajen zama.

Abban Zahra ya gyara zama yace, "Kamar yadda kuka ji sunana Khabir Umar ni d'an garin Gombe ne iyaye na dangi na duka suna can har kawo gobe, aiki yake kaini garuruwa da dama amma a Abuja nake da zama gabad'aya, Safiyya itace mata ta farko mun jima bamu samu haihuwa ba har Allah ya had'u mu da Amina a lokacin da nazo ganin nan aiki, mun had'u da Amina a kasuwar kanti kwari taje siyayya nima kuma naje muka had'u a shago guda."

"Tun daga lokacin Allah ya k'ulla soyayyaa tsakani na da ita, Amina ta kasance y'ar ce wajan Babban malami a garin nan babu wanda bai san mahaifin ta ba a unguwar su wannan ya sake bani sha'awar auren ta, cikin ikon Allah komai ya tabbata har ya kai ga manya sun shiga tsakani, lokacin dana auri Amina Safiyya tana can Finland wajan mahaifiyar Zaid a lokacin bata fama da rashin lafiya to a lokacin bata ga Amina ba, bayan ta dawo tana Abuja ni kuma mun tawo Kano wani aikin tare a haka suka fara laulayi dukkan su."

"Nayi farin ciki sosai a lokacin sai nake jin tsoron d'auko d'aya daga wani gari na kawo ta inda d'aya take dan a gani na za'a iya rasa cikin jikin ta, akwai wata budurwa ta tun ta makaranta a Gombe mai suna Rabi da farko naso na aure ta amma sai naga bata da dabi'u masu kyau a tak'aice dai ita ba mata ta gari bace ba, sai na fasa wannan fasawar da nayi sai ta rik'e ni a ranta tasha alwashin raba ni da duk abinda nake so a duniya, tun samun cikin su dukkan su Amina tafi Safiyya wahala sosai sai hankali na yafi karkata akan ita Aminan sai take ganin kamar nafi son Amina ne a kan Safiyya, Safiyya ce ta fara haihuwa a lokacin na lallab'a aka hau jirgi muka je Abuja dan kullum ina tunanin rashin sanin junan su nake kwana, sun gaisa duk da bak'i sunyi yawa a lokacin duba da gidan barka ne, a haka har akayi sunan Usman Khalipha kenan amma Amina da Safiyya basu yiwa juna kallon tsaf kasacewar cikin taro ne sai washe garin suna, a nan suka gaisa ko wacce tasan y'ar uwar ta a lokacin ne ma zaman Amina ma ya koma Abuja."

"Bayan haihuwar Khaleepha da wata biyu Amina ta haifi Baby wacce aka saka mata Maryam sunan Hajiyar su Aminan kenan, tun daga haihuwar nan sai Amina ta canja sam bata k'aunar ko kad'an nazo inda take tun ina d'aukar abin wasa sai naga kullum k'ara gaba yake yi, bayan kwana arba'in da haihuwa lokacin wacce tazo daga gida kula da ita ta koma sai ta daina d'aukar Baby ko kuka zai shid'ar da yarinyar baza ta kula ta ba, nayi fad'an nayi masifar amma a banza sai dai na d'auke ta na kaiwa Safiyya ta shayar da ita."

"Safiyya taje har part d'in Amina tayi mata fad'a a kan hakan amma sai take ce mata ita a yanzu babu abinda ta tsana sama dani da kuma Baby, abu yayi gaba a cikin kwanakin ta dinga fito da halayye mara kyau kullum cikin zagi da cin mutunci da ambaton sunan iyaye na tana na sake ta, abinda ya tunzura ni har na sake ta shine zuwan Hajiya ta Abuja daga Gombe Amina tayi mata rashin kunya har tana zagin ta tana cewa in ta isa ta saka na sake ta a take a wajan na saki Amina a ranar ta kwaso kayan ta ta dawo Kano a lokacin Hajiyar su taje umara."

"Safiyya ta dage a kan sai na kawo mata Baby kasancewar a can ta barta hakan ya saka ni dole d'auko Safiyya muka tawo Kano gidan su Amina, mukayi- mukayi ta karb'i Baby amma tak'iya k'arshe ma sai cewa tayi in har ni d'an halak ne kar na sake zuwa inda take ta barwa Safiyya Baby, haka muka dawo raina a b'ace nayi alqawarin bazan sake zuwa inda Amina take ba."

"A lokacin na samu canjin wajan aiki muka koma Lagos da zama Safiyya na kula da yaran ta biyu kamar itace ta haife Baby sabida son da take mata yafi wanda takewa Khalipha sabida ta kasancee tana son yarinya mace, arzuqi yana ta k'ara gaba muka sake dawowa Abuja a lokacin ne na samar mata y'ar aiki me taya ta kula da yaran kasancewar Baby ta kasance yarinya mai rigima."

"Shekarar Baby d'aya da rabi a duniya wata ranar asabar Safiyya ta shiga wanka ta barwa y'an aikin yaran ta kula dasu ni kuma bana nan aka nemi Baby ko sama ko k'asa aka rasa, hankalin Safiyya ya tashi ta dinga kuka tana cewa in y'ar aikin bata fad'a mata inda ta kai mata y'a ba sai tayi k'arar ta, itama tana kuka tana cewa wallahi kitchen ta shiga ta d'auko musu ruwa shine da ta dawo bata ga Baby ba sai Khalipha ita kuma ta d'auka Safiyya ce ta fito ta d'auke ta shiyasa bata tambaya ba."

"Hankali ya tashi aka tambayi mai gadi a nan yake bamu tabbacin yaga fitar wata mata da yarinya a hannu amma baiga shigar ta gidan ba bai kuma ga yarinyar hannun ta, aka baza neman Maryam a garin Abuja ranar babu wanda ya iya bacci a cikin mu sabida tashin hankali, duk inda muke tunanin ganin Baby bamu ganta ba ta b'ace har hakan yayi sanadiyar Safiyya ta kamu da ciwon hawan jini."

"Ana yiwa Safiyya saukar alkur'ani da rubutu tana sha dan dawowa tayi kamar mai tab'in hankali sabida rashin Baby, a haka rayuwa ta fara tafiya tun muna neman ta har muka barwa Allah komai muka cigaba da addu'a har lokacin kuma babu wanda ya nemi Baby daga dangin Amina."

"Bayan wasu shekaru ne munje Gombe sai muka had'u da Rabi aka gaisa cikin sak???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?in fuska take tambayar Amina da yarinyar sai Safiyya tace suna Kano, bayan komawar mu ne Abuja ba jima mahifina ya rasu muka sake dawowa Gombe, bayan an share makoki ne muka samu labarin rashin lafiyar Rabi kuma tunda ta kwanta ciwo babu wanda take kira sai ni dole Hajiya ta ta saka muka je duba ta nida Safiyya. "

"Tunda muka shiga take kiran suna na tana na yafe mata nace ni bata yi min komai ba tace tayi kawai na yafe mata, nan Allah ya bata iko take fad'a mana itace tayi amfani da rashin tsarki da Amina take tare dashi a lokacin da take jego ta saka aka jefa mata kiyayya ta da ta y'ar da ta haifa a zuciyar ta, tace bata tsaya iya nan ba bayan ta raba mu sai taga kamar hankali na bai wani tashi ba shine ta d'auki k'afa har Abuja taje ta shiga gida na ta d'auke Baby ta kawo ta Kano gidan marayu, bata tsaya iya nan ba ta saka Amina ta manta fuskar Safiyya haka itama ta manta ta Amina sai an tuna musu dukkan su zasu gane juna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login