Showing 108001 words to 111000 words out of 171073 words

Chapter 37 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7834

"are u deef? I said precious want to see you" ya fad'a a d'an fusace yana hararar wayar. Kitt ta kashe wayar ba tare da tace komai ba yabi wayar da kallo yana sake jin takaici na binne masa zuciya, babu jimawa yaji knocking sai da ya harari k'ofar sannan yace, "Come in". Daddy ne ya bud'e k'ofar ya shiga bayan sa Anty Amina ce, Daddy ya kalli inda suke a zaune yace, "har yanzu jikin ne?". Kasa bashi amsa yayi sai kallon Ibteesam da har lokacin kuka take, Anty Amina ta kalle ta sai taji duk kunya ta kama ta ganin rigar Zaid d'in ce ma a jikin ta duk sai taji wani iri ta kawar da kanta daga kallon Ibteesam d'in tana murmushi a zuciyar ta.

"Mama!" Ibteesam ta furta cikin murya mara sauti, k'arasawa wajan ta tayi tace, "Baby ya jikin?". Dak'yar Ibteesam ta mik'e tsaye ta tsaya duk da tana jin jiri sosai, "Sannu daughter, ki kamata" Dady ya fad'a yana kallon Amina. Rik'e ta tayi ta kwantar da ita a kafad'ar ta, runtse ido Zaid yayj ganin duk da jallabiyar da ya bata tana da kauri amma ana hango jikiin ta ko shi kad'ai yake gani dai bai sani ba, "Dad a fara kawo mata kaya ta saka before ta fita haka" ya fad'a yana kallon Daddy.

Motsawa tayi alamun su tafi dole Anty Amina ta fara takawa a hankali itama tana daurewa tana tafiyar sabida bata so tayi ihu a gaban Daddy, da kallo ya bisu har suka fita daga d'akin suka fito falo ya tsaya kallon yadda za'a sauka daga saman, tsaki yayi wanda har Daddy sai da ya kalle shi shima ya kalle shi yace, "Daddy yau kad'ai naji takaicin rashin escalator or elevator a gidan na, ka duba kaga yadda take shan wahala" ya fad'a yana cize baki kamar yaje ya d'auke ta.

Kawar da kai Daddy yayi yana murmushi yana mamakin halayyar Zaid shi bai san wani abu kunya ba, kafin su fara sauka a hankali, Allah yaso babu mutane a falon haka ya saka har suka wuce falon Anty Amina basu ga mutane ba kuma kasancewar dare ne, sai a lokacin Zaid yayi ajiyar zuciya ya rik'e ciki yace, "Washhh". Daddy ya kalle shi yace, "Jikin ne?". "Yunwa". Daddy yace, "baka ci abincin ba?". Yace, "bana son ci". Cikin tausayawa Daddy yace, "meyasa?". Yace, "sai precious ta samu lafiya, Daddy ina son magana dakai gobe" daga haka ya juya yana dafe bayan sa ya koma d'akin sa.

A can k'asa kuwa suna shiga d'akin Anty Amina Ibteesam ta fashe da kuka bata kula ta ba sai ta had'a mata abinda zai taimaka mata sannan ta dawo ta umarce ta da ta tashi taje ta shiga ruwan, ita ta taimaka mata ta shiga ta barta a band'aki ta koma d'akin da yake matsayin na Ibteesam d'in ta d'auko mata kaya ta dawo ta ajjiye mata a kan gado, tana fitowa tana bata nan ta saka kayan ta zauna a gefen gado tana sauke numfashi babu laifi ta d'an ji dad'in jikin ta.

Anty Amina ta shigo da abinci ta bata taci sannan tasha magani ta kwanta duk da ba baccin take ji ba, Anty Amina ta kalle ta tace, "Baby Eman ta rasu fa". Zaro ido Ibteesam tayi tare da dafe k'irji tace, "Wacce Eman d'in Mama?". Tace, "wacce kika sani ta gidan nan, jiya da daddare wajan 11 na dare."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Allah ya gafarta mata". Anty Amina tace, "Amin ya Allah, ki kwanta ki huta" tana fad'ar hakan ta fita daga d'akin tare da kullo mata k'ofar.

Fuskar Eman ce take mata yawo a idon ta nan da nan taji hawaye ya cika mata ido, had'uwar su ta k'arshe da ita shine lokacin da ta shiga kitchen ta d'auko 5avile daga nan bata kuma ganin ta ba, "Allah ya gafarta mata, duniya kenan yau gare ka gobe ga wanin ka, Allah kasa mu dace kasa k'arshen mu yafi farkon mu kyau amin" Ibteesam ta fad'a tana goge hawayen idon ta.

Rufe ido tayi kome ta gani tayi saurin bud'ewa tana cusa kanta a pillow kamar a lokacin take ganin abin, tsigar jikin ta ta tashi ta d'ago fuskar ta tana runtse idon ta zuciyar ta na bugawa da sauri, yanayin da suka kasance a daren jiya ne yake dawo mata cikin kanta da yadda komai ya juye musu lokaci d'aya da yadda ta birkice shima ya birkice, "wayyo Allah!" Ta furta tana saka hannyen ta ta kulle fuskar ta tana jin wani irin yanayi sabo yana bin jinin jikin ta yana zaga ko wanne b'angare na magudar jinin dake kai sak'o ga ko wanne sassa na jikin ta, yadda komai ya faru take gani kamar tv aka kunna mata ta sake danna hannun ta a fuskar ta kunyar duniya ta ishe ta kamar Zaid d'in yana gaban ta,? sam bata tab'a kawo hakan zata kasance tsakanin ta dashi da wuri haka ba amma sai gashi a lokacin da bai shiryawa hakan ba itama bata shirya ba komai ya faru.

Yadda yake rarrashin tane da kalaman sa sune suke mata amsa kuwa a kunne sai ta toshe kunne tare da runtse idon ta, "ko ta yaya hakan ta kasance?" Ta tambayi kanta idon ta a kulle hannun ta kuma na cikin kunnen ta, fuskar sa ta gani a idon ta lokacin da yake ta bata hak'uri kamar yayi mata kuka, "wayyo Allah ya zanyi da kunyar Umma, Mummy da Mama, ga kuma Daddy da shi kansa Zaid d'in?". Saliva ta had'd'iye tace, "dukka sun san abinda ya faru kuma, wayyo ni Maryam na shiga uku" ta fad'a kamar zararrriya tana sake tamke idon ta.

A hankali ta bud'e ido ta kalli agogo taga k'arfe goma saura na dare gashi sam bata jin bacci ko kad'an ga wayar ta na saman sa balle ta d'an rage mata zafi, sosai taji dad'in maganin a lokacin? dan bata jin zafin sosai kamar na d'azu sai ciwon jiki da kanta da yayi mata nauyi, bud'e k'ofar da akayi ya saka tayi saurin kulle ido kamar bacci take yi har da d'an juyi kad'an, shiru taji amma kuma tana jin motsi kad'an-kad'an har zata bud'e idon sai taji an kunna switch d'in wutar d'akin blue light mara haske sosai ya kama, k'arasawa yayi gaban ta ya zauna a kan bedside yana kallon fuskar ta da yaga tayi haske sosai, murmushi yayi ya sunkuya ya yiwa forehead d'in ta kiss yana shafa fuskar ta a hankali, tunda ya matso kusa da ita ta shak'i khamshin turaren sa sai ta sake nutsuwa kamar tayi bacci.

"I love you precious, i love you soo much and more, I'm sorry for what happened yesterday I'm loosed my control" ya fad'a yana sake yiwa forehead d'in ta kiss kafin ya sakko bakin ta shima yayi masa sannan ya koma ya sake zama yana kallon ta, hannun sa ya saka a wuyan ta yaji babu zazza6i sai kad'an ya mayar da hannun sa jijiyoyin kanta nan ma taji suna harbawa amma kad'an alamun kanta na ciwo, "ohh headache again" ya fad'a yana dafe kansa dan shi gabad'aya laifin ya d'auka ya d'orawa kansa.

Anty Amina ce ta bud'e d'akin ta shigo ganin hasken fitila ta kasan k'ofar sai take tunanin jikin Ibteesam d'in ne babu dad'i, turus taja ta tsaya ganin wanda yake zaune ya zubawa Ibteesam ido hannun sa na kan fuskar ta yana shafawa a hankali.

D'ago kai yayi ya kalli wacce ta shigo sai ya mik'e tsaye yana runtse ido ya fara tafiya, har ya gota Anty Amina sai yaja ya tsaya yace, "Pls take care of her" yana fad'ar hakan ya fita daga d'akin ta bishi da kallon mamaki, wai yau Zaid? ne a d'akin ta wanda bai tab'a shigowa ba koda wasa kuma shine yake ce mata pls yau, lallai ta amince soyayyar da yake yiwa Ibteesam ba k'arama bace ba.

Hasken d'akin ta kashe kafin ta ja mata k'ofar ta fita.

Washe gari da saffafiya gidan ya kuma cika dank'am maza da mata kasancewar sunce a nan za'ayi zaman makoki, Hajiya Batula da bataliyar ta dukka sun tawo gidan kowa ya samu waje ya zauna ana karb'ar gaisuwa.

Zaid da wuri ya tashi dan gajiya yayi da kwanciyar yayi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya kamar kullum,babu laifi yaji dad'in jikin sa sosai sai abinda ba'a rasa ba kamar rashin k'arfi da yake ji da kuma ciwon kai, wayar Ibteesam ya d'auka da take ajjiye ya saka aljihu ya fito falon sa, kamar jiya k'ofar da zata kaishi k'asa ta waje ya bud'e har zai sauka sai ya fasa ya sakko daga steps uku sai ya tsaya a jikin wata taga dake steps d'in, magana ya jiyo kamar jiya sai ya mayar da hankalin sa ga abinda yake ji, muryar maza yake ji guda biyu daya mata ma biyu amma dake k'asa-k'asa ake maganar ya kasa banbance muryoyin su waye.

"Sai yanzu kuka gano bana tare daku kenan? Kun maraka ai kun bari d'an zaki ya girma yafi k'arfin ku domin kuwa ya zama muku kadangaren bakin tulu wallah". Hajiya Batula tace, "Wallahi Amina baki isa ba kin shiga cikin mu kin gama jin sirrin ka mu kuma mu barki? Kema kin san k'arya kike". Yaya babba yace, "muna miki gargad'i ne akan ki fita sabgar mu kafin kema mu juyo kanki ki tafi inda y'ar mu Eman ta tafi ta sanadin ki". Yaya Bala ma yace, "ai ni Amina ta bani mamaki wai ashe duk wannan abubuwan da ake yi ita kariya take bawa Abubakar da d'an sa shiyasa kullum aikin mu baya gaba sai baya, to bara kiji wallahi sai kin bar gidan nan wannan alqawari ne in kuma ba haka ba wallahi kema zaki bi Eman inda ta tafi" ya fad'a a fusace yana nuna ta da yatsa.

Murmushi takaici tayi tace, "baku isa kuyi min abinda Allah bai min ba, mutuwa ta da rayuwa ta ba'a hannun d'ayan ku take ba ko yanzu na mutu lokaci nane yayi dan haka babu abinda kuka isa kuyi min kariya kuma yanzu na fara bawa Zaid da mahaifin sa kuma nasan Allah yana bayana sabida ban nufi kowa da sharri ba".

Kwafa yaya Babba yayi yace, "Haka kika cee?". Tace, "Haka nace haka kuma zan ta cewa, ni na d'auka mutuwar y'ar ku zata saka ku saduda ku gane cewa kaikayi ne ya koma kan mashek'iya? Kun so kashe Baby sai sharrin ku ya fad'a kan y'ar ku amma duk da haka baku gane sakkaya Allah ya fara nuna muku ba".

"Mutuwar Eman babu abinda zata hana amma ki sani wallahi sai mun d'auki fansa domin ran y'ar mu bazai tafi a banza a wofi ba, sai mun d'auki fansa akan taki y'ar kuma sannan mu idda nufin mu akan Zaid in kin isa ki hana" Yaya babba ya fad'a kamar zai make ta. Tace, "Zan hana kuwa sabida ni da Allah nake tak'ama ba boka ko malam ba, shine zai bani kariya ya kuma kare bayin sa da kuke son cutar dasu akan son zuciyar ku".

"Hmmm kedai ki jira badai muna gidan nan ba yanzu y'ar taki ma tana nan sai kinyi dana sanin yaudarar mu wallahi" Yaya babba ya fad'a yana jan k'wafa tare da barin wajan da sauri suma suka rufa masa baya.

Anty Amina tayi ajiyar zuciya tace, "Ya Allah ga bayin ka ya hayyu ya qayyum ka basu kariya daga sharrin wad'an nan bayin naka da suke nufin cutar dasu, Allah ka kare su da karewar ka, Allah ka cigaba da bani ikon taimaaka musu a koda yaushe kar ka bani ikon gazawa" ta fad'a tana lumshe ido tare da barin wajan itama.

Zaid da yake tsaye kansa yayi bala'in kullewa ya gane maganar Yaya babba da Hajiya batula da kuma Yaya Bala, muryar Amina ce take masa gizo ya rasa maganar wacece gashi kuma? ya rasa gane wacece Amina, barin wajan yayi ya koma sama dan yana buk'atar magana da Daddy.


*Ayi hak'uri nayi fama da rashin caji yau kuma ga ciwon kai da nake fama dashi.*>?y?

*?ASAITAR SO!*

*62_63*

Not edited>?'?




K'asan ya sakko tun kafin ya k'araso yake hango mata a zaune a falon ya tamke fuska ya zuba hannu aljihu babu wanda ya kula ya nufi falon Anty Amina.

Yana shiga Anty Amina tana fitowa daga d'akin Ibteesam d'in hannun ta rik'e da plate d'in abinci, kallon sa tayi shima ya kalle ta kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa kawai ya murd'a handle d'in k'ofar ya shiga d'akin, ta juya baya ta fito daga wanka d'aure da k'aramin towel jikin ta na d'igar da ruwa alamun fitowar ta kenan, taji an bud'e k'ofar amma bata juyo ba dan duk tunanin ta Anty Amina ce ta shigo, a hankali yake takawa har ya isa inda take yayi hugging d'inta ta baya ya zagayo da hannun sa ya rik'e k'ugun ta yana shafar ruwan dake fuskar ta, d'aga ta yayi cak ya juyo da ita suna kallon mirror d'in dake jiki katuwar wardrobe d'in d'akin.

Kallon fuskar ta yake ta cikin mudubin ita kuma tayi saurin k'asa da idon ta tana jin muguwar kunyar sa da ta kawo mata ziyara lokaci d'aya, k'ashin wuyan ta ya d'an tab'a kafin yace, "ya jikin naki?". Batayi magana ba sai k'asa da tayi da kanta idon ta a rufe, "answer me" ya sake fad'a cikin wata irin murya mai kashe jiki yana shinshinar wuyan ta idon a lumshe, nan ma shiru bata ce komai ba sai k'okarin kwace jikin ta da take yi, kasa kwacewa tayi dan daman ba wani k'arfi gare ta ba sannam kuma ba rik'on wasa yayi mata ba, had'a cheek d'in sa yayi da nata kamar wanda zasuyi hoto yana kallon fuskar ta ta cikin mudubin yana murmushi da shi kasan yasan na nishad'i ne, haske yaga tayi sosai fuskar ta rame idon ta ya sake fitowa waje hancin ta ya kuma tsaho, "Precious how do u feel now?" Ya fad'a mata yana kallon ta ta mudubin.

"Better, pls ka sake ni" ta fad'a murya a can k'asa har lokacin idon ta na k'asa, "can i check?" Ya fad'a a hankali, d'ago ido tayi ta kalle shi ta mudubin suka had'a ido tayi saurin sauke idon ta zuciyar ta na bugawa da sauri, murmushi shi kuma yayi ya lakuce mata hanci yana sake rik'e ta gam, haske taga yayi mata sosai kamar ya shafa powder fuskar sa ta tsuke sai sajen ya kuma yin bak'i sai ya haska farar fuskar tasa, "where?" Ta tambaya idon ta na k'asa.

"Inda kike jin zafin" ya bata amsa yana sake rik'e ta, girgiza kai tayi tace, "A'a na daina ji." D'age gira yayi yace, "ohh really? Thanks god ashe zamu iya sakewa." Runtse ido tayi tana jin kunya kamar ta nutse a wajan, ta lura shi sam bashi da kunya hakan ya saka ta daddage ta fincike jikin ta sai kuma ta tsaya sabida zafin da taji tace, "Wayyo!" Ta fad'a tana yarfe hannu tare da saurin zama a kan gadon.

Rud'ewa yayi lokaci d'aya ya zauna kusa da ita yana fad'in, "Sorry, ko muje asibiti?". Girgiza kai tayi alamun a'a idon ta na cikowa da hawaye, d'ago fuskar tata yayi dai-dai lokacin da hawayen suka zubo sai kuwa ya sake rud'ewa hankalin sa ya tashi yana fad'in, "Precious why the cry know,? Dan Allah ki daina, i don't like it wallahi" ya fad'a yana jan hannun ta zuwa chest d'in sa.

Sosai ta jin bugun zuciyar sa ta d'auke hannun ta shi kuma ya share mata hawayen ta sakko k'asa ya d'urkusa ya rik'e mata hannu yace, "Ki daina kuka dan Allah, nasan nayi miki laifi amma kiyi hak'uri ba laifi na bane kema kin sani, I'm sorry, I'm sorry" ya fad'a yana kifa kansa a kan hannun ta.? Shiru tayi tana kallon sa itama tasan bashi da laifi yadda ya rasa control d'in sa haka itama haka ta rasa dukkan su ba'a hayyacin suke ba, a hankali tace, "zan saka kaya na". Mik'ewa yayi yana rik'e bayan sa ya isa inda wardrobe d'in take ya bud'e, kallon kayan yake basu da yawa sosai kasancewar har lokacin kayan ta suna gidan Umma, hannun sa ya kai kan wata atampa kawai ya jawo ta ya mik'o mata, karb'a tayi tana cigaba da kallon k'asa shi kuma ya koma kan stool ya zauna yana kallon ta.

Shagwa6e fuska tayi ba tare da ta kalle shi ba tace, "To ka tashi ka fita". Murmushi yayi mai kyau kafin yace, "Naje ina?". Ta d'an d'ago kansa kad'an tace, "Waje kaya zan saka".

K'afa ya d'ora kan d'aya ya tallafe cheek d'in sa da hannu biyu ya zuba mata ido yace, "Precious there's nothing da zaki b'oye min by now kawai ki shirya" ya fad'a yana d'age mata gira gida d'aya.

Cikin shagwa6ar da bata san tana da ita ba tace, "nidai bazan iya shiryawa kana nan ba". Yace, " wannan shagwa6ar da kika yi ma baza ta barni na fita ba, okay lemme close my eyes" ya fad'a yana kulle idon sa yana jin sabon nishad'i yana ratsa shi, shagwa6ar da take yi tana saukar masa kasala da wani irin yanayi dashi kad'ai yasan ya yake ji, ganin ya kulle ido ya saka ta mik'e dak'yar ta saka kayan tana yi idon ta a kasa har ta gama ta koma ta zauna nan tace, "Na gama". Bud'e idon nasa yayi ya kalle ta yace, "Wow kinyi kyau Precious" ya fad'a yana lumshe ido ya bud'e su fess a kanta yana yi mata wani irin kallo na k'asan ido

Wasa take da d'ankwalin hannun ta dan jin kallon da yake mata take yana jin cikin ta kamar tafiyar kiyashi haka yake ji yana ratsa ko wanne sassaa na jikin ta yana saukar mata da kasala, shi kuma yana kallon ta kafin ya dawo kusa da ita ya tsuguna yace, "i love you soo much Precious, i love u, i love u with all my heart, duk da bama cikin hayyacin mu a jiya but i enjoyed it, Precious u are the one and only in town, you're so sweet and taste like honey kai better than honey ma, I'm so

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login