Showing 39001 words to 42000 words out of 171073 words

Chapter 14 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7814

tasa zata saka wani a cikin tashin hankali, yace min Daddy ni in nayi k'arya ji nake kamar an d'ora min wani abu mai nauyi a k'irji na dana fad'i gaskiya sai naji ya tafi, tunda ya furta baiyi d'in ba amma ita bamu san tata hujjar ba wata k'ila ta fishi gaskiya, nagode Allah ya saka maka da alkhairi Allah ya bar zumunci" Daddy ya fad'a da yanayin farin ciki.

"Babu komai an zama d'aya ai, sai dai zan sake maimaitawa in ya kasance tace bata son auren za'a katse shi dan bana so nayi mata dole dan ba ni na haife ta ba" Abba ya fad'a yana kallan Daddy, "babu komai da gaskiyar ka ai" Daddy ya fad'a shima. Mik'ewa Abba yayi tare da fad'in, "Ni zan wuce sai wani lokacin" shima Daddy Mik'ewa yati sukayi musabaha Daddy ya rako shi har bakin motar sa yana tayi masa godiya ya tafi.

Zaid kuwa saman sa ya nufa ya bud'e wata drower ya d'auko cardboard paper yana so ya zana wani takalimi, kayan zanen sa ya d'auko ya baje su a kusa dashi ya d'ora cardboard d'in a kan wani katako mai kama da kallo ya zauna, lumshe ido yayi yana tunanin ta ina zai d'ora pencil d'in ya fara zanen, maimakon ya hararo abinda zai zana sai dai ya hango fuskar Ibteesam tana masa murmushi, bud'e idon yayi da sauri ya girgiza kai yana d'an dukan kansa yace, "pls ki barni nayi aikin na yarda ina son ki" ya fad'a kamar yana magana da ita yana lumshe idon sa.

A hankali ya fara zanen nasa cikin k'warewa sai dai maimakon ya zana takalmin sai ya tsinci kansa da fara zana Ibteesam, sai da zanen nasa yayi nisa sosai kana ya fahimci abinda yake zanawa, "ohh"? ya furta yana dafe kai tare da kafawa zanen ido ganin ya gama zana fuskar ta gabad'aya ta fito tar kamar hoton ta, murmushi yayi mai kyau wanda haqoran sa suka bayyana ya saka hannu yana shafa fuskar da zana, "tana da kyau" ya furta har lokacin murmushi a fuskar sa yana jin wani irin nishad'i yana zaga ko wanne lungu da sak'o na jikin sa.

Lokaci d'aya ya tsinci kansa a cikin farin cikin da ya jima baiyi ba, maimakon yayi abinda yake gaban sa sai kawai ya cigaba da zana ta yana yi yana murmushi, tsaf ya zana ta ya d'auko color yana shawafa inda ya kamata a sakawa, take zanen Ibteesam ta fito cikin riga ja wacce a gaban ta ya rubuta love da kalar bak'i mai kyau kanta babu d'ankwali, "woww masha Allah" ya furta lokacin da ya gama yana k'arewa hoton kallo.

Bud'e k'ofar da akayi ya saka ya kalli wanda ya shigo fuskar sa har lokacin d'auke da murmushi, ganin wanda ya shigo ya saka ya k'ara fad'ada murmushin sa, "Wow Zaid wacece wannan?". Hameed ya Fad'a yana kallon zanen da Zaid yayi dan sosai yayi kyau.

"She's my favourite" ya fad'a muryar sa can k'asa yana yiwa hannun sa kiss yana shafawa hoton har lokacin murmushi yake, Shi kuwa Hameed ya manta rabon da yaga abokin nasa yana murmushi hakan ya sanya ya shagala da kallon sa har sai da Zaid d'in ya kalle shi yace, "kallon fa?". "Zaid kaga yadda murmushi yake maka kyau kuwa? Allah kana b'oye kyauwun ka in had'e fuska."

"Yanzu dai fad'a min ka yadda kana son nata?" Hameed ya fad'a yana zama a kujerar da take kusa dashi, lumshe ido yayi ya bud'e yace, "Yess i love her, ina losing control a kanta yanzu fa sample din shoe d'in nan na d'auko zan zana sai kawai gani nayi na zana ta" ya fad'a yana sake kallon zanen da yayi.

"Finally Zaid in love wow, mu ajjye batun love a gefe yanzu ya batun zana takalmin? Kasan fa gobe zasu so karb'ar sample d'in?". "I will try my best" ya fad'a yana ajjiye zanen fuskar Ibteesam a kan gadon sa ya d'auko wata cardboard paper d'in ya ajjiye da niyar fara zane.

"Kai Zaid gaskiya tana da kyau masha Allah" Hameed ya fad'a yana d'aga zanen yana k'are masa kallo, murmushin da yake kan fuskar sane ya gushe lokaci d'aya ya karb'i zanen ya ajjiye a gefen sa yana sake had'e fuska, "in badan kaine kace haka ba da yanzu na zubar maka da haqora wallahi, ka sani ina son abu ni kad'ai nake yabon sa" ya fad'a yana k'okarin fara zanen.

Murmushi Hameed kawai yayi baya so ya tanka masa ya fasa zanen shiyasa yayi masa shiru yana kallon sa yana zanawa cikin k'warewa.

A b'angaren Abba kuwa koda ya bar gidan su Zaid gidan sa ya nufa, bayan ya shiga ciki ya huta yayiwa Umma waya yace suzo ita da Ibteesam, babu jimawa suka shigo falon nasa da sallama suka zauna, Abba ya kalli Ibteesam yace, "Maryam!". D'ago ido tayi ta kalli Abba tace, "Na'am." "Da gaske yaron can yayi miki fyad'e?". Dammm gaban ta ya fad'i ta dafe k'irji tana rarraba idanu a k'asa ta kasa cewa komai, "wannan wacce irin tambaya ce Abba Jafar? To yaron nan ma har a tsaya ana tambaya yayi fyad'e,? D'azu fa yazo gidan nan kai baka ga shigar sa ba kamar yana niyar tsallake wuta, ba neman izini ba komai ya shiga har tsakiyar falo na ya zauna a akan kujera yana kallon idona yana cemin wai yana son Ibteesam harda wani kafa sharud'an banza da wofi shine kazo kana tambaya a kan sa?" Umma ta fad'a tana kallon Abba da mamaki.

"Halisa ba ke na tambaya ba ki bari wacce na tambaya ta bani amsa, Maryam ina jinki". Sunkuyar da kai k'asa ta kuma shi ta d'aga masa kai alamun eh, "to tunda har ya aikata abinda naga zaifi kawai zan bashi auren kine dan a yanzu shine wanda ya dace da ya aure ki" Abba ya fad'a kansa tsaye yana kallon yanayin Ibteesam.

"Aure Abba?" Ta tambaya a firgice tana kallan sa, "eh aure Ibteesam, tunda har ta kasance yayi raping d'in ki ai shine ya dace ya aure ki a halin yanzu." Muryar tace ta soma rawa kamar zatayi kuka, Umma zatayi magana yayi saurin d'aga mata hannu Ibteesam tace, "Tsakani da Allah Abba baiyi min komai ba na fad'a ne kawai dan a hukunta shi amma wallahi Allah bai min fyad'e ba, dan Allah kar ka aura min shi wallahi bana son sa" ta fad'a tana fashewa da kuka.

Murmushi Abba yayi lokaci na farko da yaji Zaid ya burge shi har cikin ransa, halayyar sa ta rashin yin k'arya ta burge shi sosai, yace, "Amma shine kika ce yayi miki kika saka zamu kai k'arar sa akan laifin da bai aikata ba,? K'ananun mutane zaki mayar damu,? Yanzu da mun kai k'ararda wanne ido zamu kalli yaron da kuma mahaifin sa?". "Kayi hak'uri Abba ni so nake a hukunta shi ne shiyasa na fad'a" ta fad'a cikin kuka.

Ajiyar zuciya Abba yayi yace, "babu komai tunda kin gano kuskuren ki na fasa baki auren sa,? kina so ya rabu dake ya bar cikin rayuwar ki?". Ai da sauri ta d'aga kai alamun eh tana kallan Abban nata, gyara zama Abba yayi yace, "Maryam yaron yace yana sonki wannan dalilin mahaifin sa ya nemi alfarmar ki akan yana so ku zama abokai dake dashi duk wani abu da kika ga yayi ba dai-dai ba ki fad'a masa zai amince tunda yana sonki, Maryam yaron maraya ne ashe mahaifiyar ta rasu tun bai kai haka ba rashin mahaifiya wacce zata nuna masa dai-dai da ba dai-dai ba ya saka ya koma haka yake yin komai da zuciyar sa ba tare da yayi aiki da kwakwalwar sa, dangin mahaifin sa basu da burin da ya wuce su kashe shi su kashe mahaifin sa su gaje dukka dukiyar da ya mallaka a duniya,?tun mahaifiyar sa na raye suke nuna mata k'iyayya k'iri-k'iri wannan abubuwan ne suka yiwa kansa yawa shine suka kaishi ga wannan zafin zuciyar da yake da ita, ya nemi alfarma ta akan na saka ki ki d'ora masa tarbiyyar yaro a kan dai-dai ni kuma nace sai naji ta bakin ki, yanzu ya kina ganin zaki iya?" Abba ya k'arasa fad'a da wata irin murya mai nuna zallar tausayi.

Duk tana jin me Abba yake cewa amma itama kam bata ji wani abu wai shi tausayi a ranta ba sai dai kawai zata yi alfarmar kamar yadda Abban ta ya buk'ata, "To Abba kace abota kuma bayan bada kowa kake barin mu muyi abota ba" ta fad'a muryar ta a can k'asa.

"Na amince miki kiyi abota dashi Ibteesam dan na yadda da tarbiyyar ki dana baki, in kika yi haka zaki ceci rayuwar sa ki kuma ceci yaran da zai haifa nan gaba Allah ke kuma zai baki lada".

"To Abba, amma gaskiya duk da haka ina jin tsanar sa a raina". "Kiyi k'okari ki kawar da tsanar a lokacin da kuke tare dashi" Abba ya fad'a yana kallon ta.

"To Abba Allah ya bani iko" ta fad'a tana goge idon ta, "Amin, Allah yayi miki albarka tashi kije" ya fad'a da murmushi a fuskar sa ta mik'e ta fita jikin ta a sanyaye.

Kallan Umma yayi da tayi shiru yace, "Halisa ya kikayi shiru?". Ajiyar zuciya tayi ta rausayar da kai tace, "To me zance Abban Jafar? Daman yaron maraya ne bashi da uwa?". "Eh mahaifiyar ta ta jima da rasuwa". "Allah sarki dole yanayin tarbiyyar sa ta banbanta da ta mutane rashin uwa ai ba wasa bane ba, balle shi da yake cikin irin wannan k'alubalen da k'arancin shekarun sa, amma meye ribar ka na saka Ibteesam tayi abinda kace?". "Babu komai kawai dan ta saita masa rayuwa."

"Meyasa baka fad'a mata da auren sa a kanta ba?". "Ba yanzu ba sai lokacin hakan yazo." "Amma baka gudun ta cigaba da son Khalid tana d'aukarwa kanta zunibi?." Kallan Umma yayi kana yace, "Baza ta shiga da son sa ba." Da mamaki Umma tace, "Ya akayi ka sani?". Murmushi Abba yayi yace, "ki jira mu gani" yana gama fad'ar hakan ya tashi ya shiga d'aki.

Zaid kuwa bayan ya gama zanawa Hameed ya karb'a ya tafi ya tashi daga wajan yana bank'arewa sabida yadda bayan sa ya rik'e, runtse ido yayi ya d'auki zanen Ibteesam ya d'auka ya k'arasa drower ya bud'e ya d'auko case d'in da ake saka iirin zanen ya saka ya gyara nan take ya koma kamar babban hoto ya k'arasa nesa da hoton Maman sa ya kafa hoton Ibteesam.

Murmushi yake yana kallan wanda hoton ya haska wajan, barin wajan yayi ya shiga band'aki yayi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya ya fito falon sa, k'asa ya sakko ya shiga kitchen, fridge ya bud'e ya d'auki apple ya k'arasa inda wuk'a take ya raba ta biyu ya wanke ya fara ci, yana fitowa kawai ba tare da tsammani ba kawai yaji an fad'o jikin sa apple d'in hannun nasa ta fad'i k'asa.

Goga masa jikin ta take a jikin sa khamshin turaren ya bugi hancin sa kansa ya fara juyawa lokaci d'aya yanayin sa ya fara sauyawa, fatar hannun ta da take goga masa a fatar jikin sa ya saka shi ya runtse ido sabida yadda yake jin khamshin turaren yana ratsa ko wanne b'angaren na jikin sa, wani irin numfashi ya fara lokaci d'aya yana jin komai yana canja masa a lokacin....




*Kar a fitar min da littafi dan Allah......*

*?ASAITAR SO!*

*29_30*


Tankad'a ta yayi tayi taga-taga zata fad'i Allah ya taimake ta tayi saurin dafa bango tana zare ido, dafa kai yayi da hannayen sa duka biyun sabida yadda kan nasa yake wani irin juyawa jiri yana d'aukar sa, dafa bango yayi idon sa a rufe yake lalube da hannu har ya k'arasa inda step d'in suke, hawa saman yake yana wani irin numfashi kamar wanda ake zarewa rai.

Band'aki ya shiga jikin sa na wani irin rawa yayi sauri ya watsa ruwa mai zafi a jikin sa ya fito ya zura jallabiya ya kwanta a kan gadon, juyi kawai yake hannun sa d'aya a kansa hannu d'aya dafe da marar sa da take wani irin ciwo kamar me nak'uda, juyi yakee sosai yana wani irin numfashi a fili idon sa a runtse jikin sa na rawa.

Daddy da suka shigo a lokacin da hanzari ya k'ara wajan sa ya rik'e masa hannu yana fad'in, "Zaid lafiya? Meya same ka?" ya tambaya a rud'e. Ina Zaid baya jin ma me Daddy yake cewa sabida yana cikin azaba, ji yake kamar ana san saka gatari ana daddatsa masa marar sa kansaa kuwa kamar ana rasar sa haka yake ji, "Ka kira likita kawai" Anty Amina ta fad'a a rud'e tana kallan da Daddy da ya kasa zama.

Da hanzari Daddy ya rik'e likita yana fad'a masa emergency ake neman sa, aka yi sa'a bashi da aiki yace gashi nan zuwa, "Sannu Zaid" shine kawai abinda Daddy yake fad'a yana kallon Zaid, a hankali ciwon ya fara raguwa ya daina juye-juyen sai idon sa da yake a kulle har lokacin, gumi ya jik'a masa jikin sa sosai kamar babu a.c a d'akin, "Eman jeki ki shigo da Dr" Daddy ya fad'a yana kallan ta lokacin da yaga shigowar kiran Dr.

Bata jima ba suka dawo tare da Dr a bayan ta yana shigowa ganin halin da Zaid yake ciki ko gaisawa da Daddy basu yi ba ya k'arasa inda yake, kula yayi da yanayin sa yaga yana gumi hakan ya tabbatar masa da babu zazza6i kenan sai hannun sa da ya gani a kansa da kuma marar sa, allura ya b'alla wacce zata cire masa radad'in da yake ji yayi masa, allurar na fara ratsa naman jikin sa bacci ya soma d'aukar sa kafin wani lokaci yayi bacci.

Sai a lokacin Daddy suka gaisa da Dr Daddy yace, "Likita me yake damun sa haka? Ban tab'a ganin sa cikin irin wannan yanayin ba, kodai ciwon sane?". "Ba ciwon sa bane Alhaji in ka lura in ciwon sane ai baya motsawa sosai balle ya samu damar juyi irin haka, a yadda na fahimta ciwon mara ne da ciwon kai."

Daddy ya kalli likita da mamaki yace, "Ciwon mara kuma sai kace mai haihuwa?". "Ai maza suna ciwon mara Alhaji musamman samari wanda suka jima babu aure kuma basu tab'a zina ba, amma shi nasa gaskiya ban san musabbabin ta ba tunda bashi ne yayi min bayanin yadda yake ji ba nine na fahimci haka, sai ya tashi zan dawo anjima muji nashi a wanne b'angaren yake."

Daddy yace, "banda abinda ka a yadda ka bani labarin ciwon ai shima yaci ace yayi irin sa shekara talatin da wani abun fa babu aure." "Eh haka ne Alhaji amma baza mu yanke hukunci ba sai munji abinda yace, anjima zan tawo masa da magani ina sauri yanzu ban samu na had'o magani ba, yanzu dai a barshi ya huta ko k'arfe nawa zai kai yana bacci kar a tashe shi". "To shikenan Dr Auwal nagode" daga haka sukayi sallama suka fito gabad'ayan su suka sauka.

Eman kuwa d'aki ta fad'a bayan sun sauko ta bud'e wardrobe ta d'auko turaren da Abban nata ya bata ta bud'e ko wanne tana karantawa, na farko ta bud'e takardar jikin sa taga an saka _wannan za'a fara amfani dashi indai ya shak'i khamshin sai abinda kika ce masa,_ d'ayan ta bud'e wanda tayi amfani dashi d'in, _kar ayi amfani da wannan sai anyi amfani da na farko in akayi amfani da wannan ba tare da an fara da wancan ba ko anyi wancan d'in bazai yi aiki ba, amfanin wannan shine za'a saka masa sha'awar da dole sai ya neme ki._ dafe kai tayi cike da takaici haukan da ta tafka tace, "Na shiga uku me ya shiga kaina haka?" Ta fad'a cikin takaici.

"Yanzu in Abba yasan nayi wannan shirmen ai ba k'aramin fad'a zan sha ba gwara kawai kar na sanar dashi nayi zai fi min sauk'i" ta fad'a a hankali cikin rashin mafita.

Bud'e k'ofar da akayi ya saka tayi saurin b'oyewa tana kallan wanda zai shigo mata d'aki, ganin Anty Amina ya saka ta sake b'oyewa dan an ja mata kunne a akan ba komai zata bari Amina tana gani ba, "ya na ganki wata iri kamar mara gaskiya?" Anty Amina ta fad'a tana yi mata kallan tuhuma.

"Miji na bashi da lafiya ba dole ki ganni haka ba" ta fad'a mata kanta tsaye ba tare da ta kuma kallan inda take ba, "Haka ne, yanzu a kan wanne plan ake ne? Kwana biyu Abban ki baya nema na." "Nima dai kwana biyu bai min maganar komai ba inajin shiri yake yi" ta fad'a tana d'an tab'e baki.

Bata mata komai ba kawai ta juya ta fita dan taga alama sun ci moriyar ta tunda yanzu y'ar su ta shigo gidan an ajjiye ta gefe, k'wafa tayi tana aiyana abinda zata musu itama dan basu isa ba.

Da harara Eman ta bita tare da tsaki tace, "Kema k'iris ya rage mu aika ki waje dan bama so ki gaji komai, yanzu ya zanyi ne ni?" Ta fad'a lokacin da ta sake tuno shirmen da ta tafka, kome ta tuna sai ta mik'e ta d'auki wayar ta ta fita daga d'akin.

Zaid bai farka ba sai bayan sallar i'sha, a hankali ya bud'e idon sa yana kallon d'akin abinda ya faru ya fad'o masa ya mik'e zaune, runtse ido yayi dan har lokacin yana jin ciwon marar ciwon kan ne dai babu, kallan agogo yayi ganin lokaci ya wuce da ya yawa ya sanya shi mik'ewa a hankali ya shiga band'aki, ya d'an jima sosai ya fito yana goge jikin sa da towel, da sauri ya shirya ya saka jallabiya ya tayar da sallah, bayan ya idar da I'sha ya zauna yana lazumi idon sa lumshe yana jin jikin sa wani iri kamar wanda yayi wani aiki ya gaji.

Bud'e ido yayi tuno ta yadda ya fara jin ciwon a fili yace, "Na shiga kitchen na d'auko apple na fito yarinyar nan ta fad'o jiki na, a jikin ta naji wani khamshi mara dad'i da y saka min ciwon kai" shiru yayi alamun tunani, gyara zama yayi yana tuna komai daki-daki, yadda take goga masa jikin ta ya tuna sai kuwa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login