Showing 141001 words to 144000 words out of 171073 words

Chapter 48 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7858

nasan size d'in ki ba?" Ita dai bata ce komai ba dan tasan tunda yace ya sani d'in ya sani, tunda kuma bazai tambaya ba ta godewa Allah dan kunya yake ji, "naga kina son abaya sosai wacce kike so dubai ko turkey ko saudia?". Tace, "ko wacce ma ina so."

D'ago da ita daga jikin sa yayi yace, "Zan tafi Precious tunda har an fara hana ki magana dani". Kallon sa tayi kafin ta d'auke kai tace, "to ka gaida Mama." "Shikenan abinda zaki cemin?".
"To me kake so nace?".
"Komai ma kice."
"I love you".
"Show me."
"What?".
"Love" ya fad'a bayan ya dawo da fuskar sa wuyan ta. Cak ya tsayar da fuskar ta dai-dai tasa yana kallon idon ta itama tana kallon nasa, baiyi tsammani ba yaji ta masa kiss a lips d'in sa ta d'auki d'ankwalin ta ta bud'e motar ta fita tana dariya.

Shima murmushin yayi ya shafa lips d'in nasa ya lumshe ido sannan ya fita shima ya koma gaban motar jiki a sanyaye ya kunna ya tafi.

Bayan wasu kwanaki.

Shirya-shirye ya kankama sosai an gama gidan gabad'aya an zuba kayan ciki, duk wani abu da ya shafi dangin amarya Umma da Abba ake samu akan maganar sosai sunji dad'in karamcin da aka nuna musu an basu matsayin iyayen Ibteesam.

B'angaren amarya ana ta shan gyara ta ko wanne b'angare, Umma nayi Mummy nayi takanas aka d'auko mai gyara daga sudan tazo tana gyara Ibteesam shiyasa ta zama ko waje ta zauna ta tashi khamshi yake yi, y'an uwan Anty Amina ana ta shirye-shirye haka mahaifiyar ta duka ba'a barsu a baya ba wajan taka rawar gani a wajan diyar y'ar uwar tasu, Ango kam an ko kusa Mummy ta hana shi ganin Ibteesam koda wasa sai dai suyi waya ko video call amma ya ganta an dai ya jima sai dai yayi ta mitar yaje gidan ya gama zaman sa amma ko kyallin ta baya gani.

Yau ta kama saura sati d'aya biki a yau kuma yaci alwashin kota halin k'ak'a sai yaga Ibteesam hakan ya saka shi sakkowa da wuri ya shiga kitchen kamar yadda yayi kuduri, kamar yadda yayi tunanin Anty Amina tana ta aikin ta yace, "Sannu da aiki Anty" ya fad'a fuskar sa tayi kalar tausayi.

"Yauwa Zaid, lafiya dai ko na ganka haka." Sai kuwa ya shagwa6e kamar zai mata kuka yace, "Ina so naga Precious amma Mummy ta hana ni ganin ta, ko gidan naje fa sai na neme ta na rasa zuciya ta tana yi min zafi a kan hakan, ki taikama min ki saka na ganta please" ya fad'a kamar zai mata kuka. Anty Amina tace, "a kan wanne dalili kai da matar ka a hana ka ganin ta,? Kar ka damu yanzu daman na kira ta tazo akwai sak'on da Hajiya ta kawo mata sai ka ganta ka kwantar da hankalin ka kaji ko". Murmushi yayi mai kyau wanda zata iya cewa bata tab'a ganin sa a fuskar sa ba yace, "Thanks you Anty, and kizo muje falo kiga wani abu" ya fad'a yana niyar fita.

"To bara na kammala abinda nake yi" ta fad'a tana cigaba da suyar dankalin da take yi, dawowa yayi ya kashe wutar gas d'in yana fad'in, "yanzu zaki dawo" yana fad'a bai jira mai zata ce ba ya fito dole itama ta biyo bayan sa tana mamakin sakewar da yayi ds ita duk da bawai sosai ba amma babu laifi kuma baya sirika da ita sam sai ma matsayin matar baban sa da ya bata, tunda ta fito take kallon akwatunan da suke falon ta kamar hauka a ajjiye ko wacce cike da kaya, "Zaid meye wannan?" Ta tambaya bayan ta k'arasa wajan.

"Lefen precious ne" ya fad'a kai tsaye yana bude d'aya daga cikin akwatinan, zaro ido waje tayi sanann tace, "wannan kayan ne lefe Zaid?". Ya kalli kayan sannan ya kalle ta yace, "ko sunyi kad'an ne Anty?". "Zaid akwatuna talatin da shida set uku fa kenan, ina za'a kai wannan kayan haka?". Yace, "Anty kar kice sunyi yawa please". Kafin tayi magana Daddy ya shigo ta juya tana fad'in, "Daddyn Zaid kalli kayan nan fa wai kayan lefe ne kamar za'a bud'e kanti?" Ta fad'a yana nuna masa kayan.

Maimakon taga ya fara yi masa fad'a sai taga ya biye masa suna ta duba kayan tare da yabon kayan, sai ta saki baki tace, "Au wai baza kayi masa fad'a ba biye masa na kayi?". Ya d'ago ya kalle ta yace, "Meye abin fad'a a nan Amina? Dama ce Allah ya bashi ya kuma yi amfani da ita, in kika ga mutum yayi abu lokacin sane in ya wuce bazai yi ba, dan haka ni banga laifin sa ba kaya sunyi masha Allah."

Akwatin da Zaid ya bud'e Daddy ya yake kalla ganin kawai gold ne a ciki duk da bata da girma amma kud'in dake cikin ta yafi k'arfin kan mutum, itadai Anty Amina daskarewa kawai tayi tana kallon su ganin suna ta yabon kaya kamar ba da wahala suke neman kud'in ba. "Kuzo muje babban falo gasu Yaya Babba can sun dawo daga Egypt" Daddy ya Fad'a yana kallon su, har Zaid zai musa Daddy ya girgiza masa kai dole yayi shiru suks bar kayan a falon Anty Amina suka fito.

Tunda suka fito Zaid bai kalli kowa a cikin y'an uwan mahaifin nasa ba kansa na k'asa k'arshe ma kujerar dining yaja ya zauna bai k'arasa falon ba, "Sannun ku da zuwa" Anty Amina ta fad'a fuskar ta ba yabo babu fallasa, Yaya babba yace, "Yauwa Amina mun same ku lafiya? Ya Zaid da jikin?". Ta amsa da lafiya tana kawar da kanta gefe, Daddy yace, "Yaya Babba lafiya ta samu" ya Fad'a da murmushi yana kallon sa. Shima murmushin yayi haka sauran y'an uwan yace, "Alhamdulillah yanzu bana jin komai, ai mu Nigeria an barmu a baya akan komai su sabida kayan aiki ma bazai barka ka zauna jinya ba." "Gaskiya dai kam kalli fa har ka taka k'afar ka kamar ba kai ba" Yaya Bala ya fad'a da murmushi yana kallon sa.

Zaid Yaya babba ya kalla yace, "Abdullahi ya jikin naka?". D'ago ido yayi daga kan wayar sa ya watsa masa su kafin yace, "Abdallah nake". Murmushi yayi yace, "to Abdallah ya jikin?". Tab'e baki yayi kafin yace, "Da sauk'i na samu sauk'i, duk da ba haka kuka so ba". Sai jikin su yayi sanyi Yaya Babba ya kuma cewa, "Zaid ka dubi darajar Allah ka yafe mana dukkan abinda ya faru, tabbas mun so cutar da kai nida y'an uwan na amma Allah ya kare ku duk abinda nayi nufin aikata muku ya dawo kaina, kayi hak'uri ka yafe min dukkan abinda nayi maka wanda ka sani da wanda ma baka sani ba" ya k'arasa fad'a murya a sanyaye.

Banza Zaid yayi masa Daddy ya kalle shi cikin fushi yace, "Zaid ba magana ake maka bane?". Yaya babba yace, "K'yale shi Abubakar barshi ya yanke hukunci da kansa, Amina kema ki yafe mana daga baya da muka gano bakya tare damu mun so mu cutar dake da y'ar ki kema." Itama bata amsa ba ta d'auke kanta, muryar Zaid suka ji yace, "ni me nayi muku kuke so ku kashe ni?". "Son dukiya, dukiyar mahaifin ka muke kwadayi" Yaya babba ya bashi amsa kai tsaye.

"Daddy na fa?" Ya sake tambayar sa yana kallon sa, "ai sai ya mutu sannan zamu sami gadon shiyasa muka so mu fara kashe ka sannan shi, da taimakon Allah da kuma taimakon matar Baban ka kuke raye dukkan ku, ka yafe min". Yaya Bala yace, "hakika mun so cutar da kai mun so mu kashe ka kamar yadda mukayi sanadin kashe mahaifiy........" ai Daddy bai bari ya k'arasa ba yayi saurin katse shi cikin wata irin murya mai amo yace, "Zaid ka yafe musu mana". Kallon Daddy Zaid yayi ya kuma kalli Yaya Bala ya mik'e tsaye ya k'araso wajan yace, "maimaita abinda akace, kamar yadda kukayi sanadin mutuwar mahaifiya ta?".

"Zaid ka koma ka zauna nace maka" Daddy ya fad'a cikin tsawa yana kallon sa, "A kan me zan zauna Daddy baka ji me yace bane? Sune suka kashe min Mama na" shima ya fad'a a fusace yana kallon mahaifin nasa. "Haka kaji yace? Ka jira yayi maka bayani mana" Daddy ya kuma katse shi da fad'ar hakan.

"Abubakar ka k'yale shi abinda yaji ai ba k'arya bane, tabbas mune sanadin ciwon Maryam har ta bar duniya mune muka saka mata wannn ciwon da muna ganin itave take hana mahaifin ka saka mu akan komai da ya shafi dukiyar sa" Yaya Babba ya fad'a yana kallon Zaid da yake kallon sa shima.

"Kune kuka kashe min uwa? Kune kuka mayar dani mayara? Kune kuka saka naji d'aci da kuma radad'in rasa mahaifiya ta,?" Sai kuma ya dafe kansa da hannu biyu d'akin na juya masa ya rasa abinda ma zaice, Daddy ya dafe kai yana jin ciwo a zuciyar sa sam baiso Zaid yaji maganar nan ba dan yasan bazai tab'a jurewa hakan ba, in shi yayi hak'uri ya jure yasan Halin d'an sa bazai jure ba shiyasa yaso ya hana maganar amma ina.

"Daddy kaji sune suka kashe min mama na akan wani banzan dalilin su, Daddy ka fad'a musu daga one million to one billion su fad'i abinda suke so zan basu su dawo min da mahaifiya ta" ya fad'a yana wani irin rawa. Girgiza masa kai Daddy yayi yace, "ka tab'a ganin wanda ya mutu ya dawo Zaid?." "Amma sun san da haka meyasa suka kashe ta? Meyasa basu san rai yafi komai a duniya ba,? Kud'i duniya ake samun su a nan kuma za'a tafi a barsu amma rai fa? Guda d'aya ne tal in aka rasa shi baya kuma dawowa, sun san da hakan suka zama silar mutuwar ta? Meyasa basu tunanin yadda zan kasance in bata nan ba, kansu suka sani da abinda zasu samu ko? Meyasa basu tambaye ni tun a lokacin na basu duk abinda suke so sun barmin mahaifiya ta ba? Daddy meyasa?" Ya fad'a cikin tsawa yana kallon su dukkan su, kana ganin yadda jikin yake rawa kasan cewa baya cikin hankalin sa.

Shima Daddy ji yake mutuwar ta dawo ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  masa sabuwa fil a lokacin amma haka ya daure ya kama Zaid amma ya fizge yana girgiza masa kai, kukan kura yayi ya cafki wuyan Yaya Babba ya shak'e da k'arfin gaske, dukkan su kansa sukayi ana b'anb'are shi amma ina kamar mayan k'arfe sake mannewa yake a jikin sa, ganin idanun yaya Babba sun fara fitowa sunyi ja ya saka su dagewa da k'arfi suka janye shi Daddy ya bashi kyakykyawan mari a fuskar sa, "kashe shi zakayi Zaid? Yayan nawa zaka kashe?" Ya fad'a cikin fad'a sosai.

"Amma ni ya kashe min mahaifiya ta ko ka san da hakan kuma bakayi komai a kai ba, rai yafi rai ne? Ko kuwa d'an uwa yafi uwa ne? Wallahi bazan barsu ba sai na d'auki mataki a kansu baza su kashe min uwa su zauna lafiya ba" shima ya fad'a cikin fad'a sosai kamar ba Daddy yake magana ba, Yaya babba kuka yake yi sosai haka y'an uwan nasa ma, Anty Amina da Ibteesam da Zahra da babu wanda ya kula da zuwan su tun lokacin kuka suma sukeyi sosai.

"Wai sun kashe min uwa amma suke zaune a gaba haka lafiya lau, oh god!" Ya sake fad'a yana dafe kansa da yake juyawa over ya saka hannu ya jawo tv falon ta fad'i k'asa, Daddy yace, "Zaid zauna muyi maganar." Girgiza kai yayi baice komai ba ya juya da sauri ya hau saman sa yana tafiya yana had'a hanya kamar zai kifa. Hankalin Daddy yayi bala'in tashi suka fara jiyo sautin fashe-fashe a saman daman kuma yasan hakan zata kasance sai a lokacin ya kula da Ibteesam yace, "Yauwa daughter maza jeki wajan sa duk yadda zakiyi ki tabbatar yayi bacci a wannan lokacin, yin baccin sa shine kwanciyar hankalin kowa da kuma nasa hankalin, in baiyi bacci ba ciwon sa zai tashi, kar ki barshi idon sa biyu maza jeki". Kamar jira take ta nufi saman da saurin ta?tun a falon take ganin d'igo-d'igon jini a kan tiles d'in falon.


*Jiya bana nan ne wallahi shiyasa aka jini shiru fatan za'a min afuwa.*=?O?>??
*?ASAITAR SO!*

*78_79*

Not edited >?'?




Da sauri ta k'arasa ciki ta fara karo da tv a k'asa screen d'in ta ya tsage ta tsallake ta shiga d'akin, d'akin take kallo tana k'arewa masa kallo ganin komai na hargitsa shi ga mirror a fashe, duba ta kai kan gadon ta hangon shi a zaune ya dafe kansa jini na d'iga daga hannun sa.

Da sauri ta k'arasa inda yake ta zauna kusa dashi tana k'okarin rik'e hannun sa da yake fitar da jinin, janyewa yayi sai kawai ta jawo shi k'irjin ta ta rungume shi ai kamar jira yake ya rik'e ya tsam ya fashe da kuka kamar k'aramin yaro, kuka yake sosai a jikin ta itama tana yi tana kuka babbuga bayan sa tana shafa kansa da yake jikin ta, cikin kuka take cewa, "addu'a zaka yiwa Mama ita take so a yanzu ba wannan b'acin ran naka ba, na san an b'ata maka an maka ba dai-dai ba amma ka tuna daman Allah ya rubuta lokacin shine lokacin barin ta duniya, ko sun zama sila ko basu zama ba dole zata bar duniya, lokacin ta ya riga yayi dole ta amsa kiran mahaliccin ta, kaita maimaita Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un zaka samu sauk'i a ranka".

Yana jin ta amma babu damar magana sabida kukan da yake yi hankalin sa gabad'aya baya tare dashi gani yake ya aikata babban sab'o a duniya, a ganin sa barin wanda suka kashe masa uwa a duniya suna walwala babban laifi ne shiyasa gabad'aya ya tayar da hankalin sa, sun d'auki mintina a haka yana kuka tana kuka bata hana shi ba dan tasan zai samu sauk'in zafin da yake ji a ransa, a hankali taji kukan yana raguwa numfashin sa na fita a hankali tana cigaba da shafa kansa da kuma bayan sa taji jikin sa ya saki alamun yayi bacci.

Sai da ta bari baccin yayi nisa sannan ta zame shi daga jikin ta ya kwanta ta mik'e ta d'auko mai me laushi tazo ta fasha masa a hannun da ya yanke da mirror sannan ta kunna masa a.c ganin yana gumi ta rage hasken d'akin ta koma gefe kawai tana kallon sa, tausayin sa take ji yana sake shiga jikin ta ganin yadda ya firgice lokaci d'aya kamar bashi ba kuma daman tasan dole ya fita a hayyacin sa uwa ai ba abar wasa bace, yau wani ya tsaya a gaban ka yace shine ya zama silar mutuwar mahaifiyar ka ai dole ka fita daga hankalin ka balle shi y'an uwan mahaifin sane suke son ganin bayan sa, hawaye ta share ta k'arasa inda yake tayi kissing d'in sa forehead sannan ta fito daga d'akin.

A can k'asa kuwa tun bayan barin Ibteesam waja? Daddy ya kalli y'an uwan nasa da idanun sa wanda suka koma ja yace, "Yaya me yasa zaku fad'awa Zaid wannan maganar? In ni ka fad'a min na jure na shaye shi bazan iya ba, ni matata ce shi kuma mahaifiyar sace itace ta kawo shi duniya ta raine shi, bashi da abinda yake so a duniya sama da Maman sa, yau ka tsaya a gaban sa kace kune kuka zama silar mutuwar ta kana ganin zai k'yale ku ne,? Babu wanda bai san halayyar Zaid a cikin ku ba yana da zafin zuciya especially akan abinda yake so, kun tabo masa inda ya jima yana masa zafii yau kun fama shi kowa kuma yasan fami yafi sabon ciwo, koda Zaid ya k'yale ku har abada bazai tab'a daina ganin bak'in ku ba domin kun shafawa kanku bak'in fanti a fuskar ku wanda goge shi a idon sa sai dai mutuwa, koma meye kuka aikata a kaina da Maryam da kuma Zaid d'in kanku kuka yiwa kuma gashi kuna ganin sakayya tun daga duniya, Allah yana bani kariya nida shi ta ko wanne b'angare kun kasa nasara a kan mu sai kuma Allah ya sake azurta ni da matar da tafi k'arfin ku take bani kariya a koda yaushe, ni bazan ce komai ba na yafe muku amma ku sani ni kaina bazan tab'a daina ganin bak'in ku a kan zama silar rasuwar Maryam ba" Daddy na gama fad'ar hakan ya hau saman sa da sauri.

Zahra da Anty Amina suka yi ciki aka bar su a zaune a wajan suna zuba hawaye dukkan su, kasa magana sukayi gabad'ayan su haka suka mik'e jiki babu kwari suka fita daga falon.

Ibteesam duk tana tsaye tana ji ta goge idon ta ta shiga falon Anty Amina tayi tagumi, tana ganin shigowar ta tace, "yayi baccin?". D'aga mata kai kawai tayi alamun eh tana bin kayan da suke zube a falon da kallo, mata ce komai ba Antyn ta mik'e ta hau saman Daddy dan shima yana buk'atar ya samu yayi baccin sabida kwakwalwar sa ta samu hutu.

Haka gidan ya kasance ranar babu walwala ko kad'an su kansu su Ibteesam d'in suna zaune ne amma babu wani abu da suke yi sai tunani a haka har Daddy ya sakko lokacin azahar har ta gota.

Daddy ya kalli Ibteesam da murmushi yace, "Daughter taga lefen ta tun ba'a kai ba" ya fad'a cikin son kawar da b'acin ran da yake zuciyar sa. Murmushi tayi kawai ta sunkuyar da kai tana mamakin wannan uban kayan duka na lefe ne, "Da kika sakko yayi baccin?" Ya tambaya cikin kulawa.

"Eh Daddy yayi, amma sai an gyara saman sabida ya fasa komai hannun sama a yanke yake" ta fad'a kanta a k'asa ba tare da ta d'ago ba. Ajiyar zuciya Daddy yayi yace, "In ya tashi sai a kira cleaner d'in sa ya gyara wajan, amma dan Allah kar ku sanar Mummyn ku abinda ya faru itama zata shiga wani hali in taji". Zahra ta d'aga kai tace, "insha Allah Daddy baza mu fad'a mata ba". Murmushi yayi kad'an yace, "Allah yayi albarka" daga haka ya wuce ya fita.

Anty Amina da take bayan sa tace, "Tashi kije ki gano ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login