Showing 93001 words to 96000 words out of 171073 words

Chapter 32 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7860

ta fita tayi gida ta kwashe duk abinda ya faru a gidan ta sanar dasu, cikin mamaki Yaya babba yace, "Yanzu kenan Zaid yana da wata matar kafin ke? Kuma itace wacce yake so?". Eman tace, "Wallahi kuwa Abba, baka ga yadda yake rawar k'afa a kanta ba." Ajiyar ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????zuciya yayi ya kalli Hajiya Batula yace, "yanzu meye abinyi? Dan baza mu bar yarinyar nan ba itama dan in muka barta Amina tana da tudu biyu kenan, ni tsoro na ma kar yayiwa yarinyar ciki magada su k'aru". Hajiya Batula tace, "Ai ko hakan zata kasance sai dai akan Eman, d'azu munje wajan wani malami nida Luba na karb'o masu magunguna amma fa dole sai dai itama yarinyar a kashe ta."

Eman tace, "A kashe ta mana Mama dan indai har tana raye wallahi bazai tab'a kallo na a matsayin matar sa dan baki ga yadda yake son ta ba". "To amma kashe su da magani guda d'aya zai saka ayi saurin gane mu fa" ta fad'a tana kallon Yaya babba.

"Babu wannan batun abinda muke a akan gawar zamu kasa mu tsare wajan ganin babu wani bincke da akayi akan hakan" ya fad'a yana kallon Hajiya Batula. "A'a mu fara kashe yarinyar in yaso komai ya biyo baya daga baya" ta sake fad'a tana kallon su.

Eman tace, "ita a kashe ta amma shi kar a kashe shi wallahi ina son sa" ta fad'a kamar zatayi kuka, Yaya babba ya kalli Hajiya Batula suka kiftawa juna ido kafin yace, "Ai ita za'a kashe ba shi ba baki ji shi neman maganin da zai soki ma ake yi ba?" Murmushi tayi tace, "Yauwa Umma na, yanzu meye abin yi?."

Tashi Hajiya Batula tayi ta shiga d'aki bata jima ba ta fito da leda a hannun ta tace, "Amma fa ki kula da kyau Eman maganin yana da kyau amma yana da hatsari, kinga wannan koran wanda yafi turuwa shine wanda zaki zubawa yarinyar abinci ko abin sha tasha, bazai bi jikin? ta lokaci d'aya ba sai kamar awa biyar da bata sannan zai kashe ta, shi kuma wanda baiyi koran sosai ba ki zuba a lemo ki tabbatar Zaid yasha sannan kema kisha, sai kin tabbatar yasha zaki sha kar kisha in bai sha ba, daga nan ki zauna inda yake? kada kiyi nesa dashi ko na minti d'aya ne kinji ko?".

Cikin gamsuwa tace, "Insha Allahu Umma zanyi yadda kika ce." "Yauwa to gasu nan ki rik'e dakyau Eman ki kuma kula". A jaka ta saka suka cigaba da hirar yadda za'a kawar da Ibteesam.

******

Bayan sallar i'sha Ibteesam tana zaune kusa da Anty Amina gefe kuma Jidda ce da Zahra suna kallon labari na kasancewar juma'a ce, Daddy ne ya shigo falon yana fad'in, "Amina baki ga maganin Zaid ba?". Kallon Daddy tayi sannan tace, "ban gansu ba wallahi, a ina aka ajjiye?". "A d'aki na, kin san ba wani son magani yake ba shiyasa nake ajjiyewa a inda nake dan shi zubarwa yake yi." Tace, "lafiya dai ko?". Daddy yace, "Ciwon kan ne wallahi yake k'okarin tashi dan daga office ma sai dawo dashi Hameed yayi, to nemi maganin na rasa, amma bara na kira Dr Auwal ya kawo wasu" ya fad'a yana fito da waya tare da fita daga falon.

Ibteesam da take zaune jikin ta yayi lak'was ta fara raba ido jikin ta yayi mata sanyi lokaci d'aya, Anty Amina ta Mik'e tana fad'in, "bara naje naga jikin nasa" bata jira mai zasu ce ba ta fice daga falon. Jidda ta kalli Ibteesam da jikin ta yayi sanyi sosai tace, "Anty Ibteesam kema kije kiga yanayin jikin nasa mana". Zahra ta amsa da, "Gaskiya dai kuwa ke ya kamata ma ace kina gefen sa a halin yanzu." Ajiyar zuciya kawai tayi bata ce komai ba ta kwantar da kanta jikin kujerar tana hasashen halin da yake a ranta, ganin hakan ya saka suka k'yale ta suna gulmar ta k'asa-k'asa.

Anty Amina ta jima sannan ta dawo ta kalli Ibteesam tace, "Baby kuje ku duba shi amma kar kuyi hayaniya". Kamar jira Ibteesam take ta mik'e suma suka mik'e suka nufi saman nasa a hankali kamar masu tausayin k'asa, a hankali suka tura falon suka shiga babu kowa a falon sai k'arar a.c da ake ji a falon, burki Jidda da Zahra suka ja Zahra tace, "Ki fara duba yanayin da yake ciki kafin mu shi" ta fad'a tana kallon Ibteesam da itama su take kallo.

A hankali take takawa har cikin bedroom d'in ta tura suma suka biyo bayan ta suka shiga, yana kwance cikin bargo d'akin yayi d'umi sosai sai khamshi da yake tashi mai kwantar da hankali, cak suka tsaya suna kallon yadda yake sauke numfashi a hankali idon sa kulle kamar mai yin bacci, "mu koma bacci yake" Ibteesam ta fad'a a hankali tana niyar fita daga d'akin.

"Precious sake tafiya zakiyi ki barni?" Ya fad'a idon sa a kulle ba tare da ya bud'e ba, cak ta tsaya daga tafiyar da take niyar yi ta juyo ta kalle shi kamar ba shine yayi maganar ba dan idon sa a kulle yake, Zahra tace, "sannu ya Zaid ya jikin naka?". Maimakon ya amsa sai yace, "Zahra why sister d'in ki bata sona? Akwai wani abu da nake dashi wanda yake mara kyau?" Ya tambaya har lokacin yana kwance idon sa a kulle.

Zahra tayi shiru tana tausyain cousin d'in nata ta kalli Ibteesam da take tsaye a waje d'aya tace, "Baka dashi Yaya Zaid." Bud'e idon sa yayi ya mik'e zaune dak'yar ya jingina da gadon yace, "Meyasa bata sona Jidda?" Ya fad'a yana kallon Jidda da jajayen idon sa.

Tausayi ya bawa Jidda ta kasa magana sai kallon Ibteesam da take yi, dan tunda tasan Zaid bata tab'a jin sa cikin rauni kamar yanzu ba, "ya salam" ya furta yana dafe jijiyoyin kansa da suke bala'in harbawa a lokacin, "kun gani tak'i ma tayi min magana, shikenan kuje sai da safe" ya fad'a yana mayar da idon sa ya kulle har lokacin hannun sa na dafe da kansa.

Cikin sanyin jiki suka fice suka bar Ibteesam a tsaye a inda take ta kasa ko motsi, "u can go Precious tunda kina so na mutu ne" ya fad'a bayan ya Bud'e yana kallon ta. "Bana so ka mutu" ta fad'a a hankali muryar ta a sanyaye. Da hannu yayi mata alama da tazo inda yake ta taka a hankali taje kusa dashi ta zauna ya rik'e hannun ta yana kallon fuskar ta, "Subahanallahi, kaji yadda hannun ka yayi zafi? Ka kwanta ka huta ko zaka samu sauk'i" ta fad'a tana kallon sa dan jikin sa yayi zafi sosai.

"Bazan samu sauk'i ba indai baki ce kina so na ba Precious, na rasa Mama na wacce take kula dani kema kuma ina neman rasa ki, why kike so na mutu?" Ya fad'a yana runtse ido dan Allah kad'ai yasan azabar da yake ji in yana magana, "ni bance bana son ka ba" ta fad'a a hankali. "To me kika ce?". Ibteesam tace, "bazan amince kana yiwa Mama na rashin kunya a gaba na bazan jure ba shiyasa". Girgiza kai yayi kawai tare da cewa, "Is okay, sai da safe" ya fad'a yana kwanciya? ba tare da ya sake cewa komai ba.

Duk sai taji wani iri a jikin ta amma wani b'angaren na zuciyar ta na fad'a mata dai-dai tayi, wani abu ne yake fizgar ta ji take kamar ta kwanta a gefen sa kodan ya samu sauk'i, mik'ewa tayi tsaye ta fara takawa cikin blue light d'in da yake d'akin yake kallon ta yana jin kamar yayi kuka dan ji yake duk taku d'aya da take yi tana yine da kuzarin sa yana sake fita a jikin sa, "I love you soo much Precious, ban sani ba ko bazan kai gobe a raye ba shiyasa na fad'a miki, sweet dreams" ya fad'a muryar sa na rawa kamar wanda yake kuka yana jan bargo ya kulle fuskar sa.

Kamar an saka igiya an d'aure nata k'afa haka taji ta kasa cigaba da tafiyar jikin ta yayi bala'in sanyi, a hankali ta cigaba da takawa har ta fice daga d'akin ta kulle masa ta sauka gabad'aya hankalin ta baya tare da ita, kacibus sukayi da Eman ta kalle ta itama ta kalle ta Eman tayi tsaki ta wuce itama ta wuce.

Niyar shiga d'aki take taji maganar Anty Amina na fad'in, "Baby lafiya na ganki haka? Kodai jikin nasa ne ya sake tashi?". Maimakon ta bata amsa sai ta fara hawaye tayi saurin gogewa ta juya ta kalli Maman nata tace, "A'a Mama kaina ne yake min ciwo nima". "Ayya sannu, shiga ciki akwai paracetamol sai ki d'auka kisha" daga haka ta barta a wajan ta shiga d'aki tana murmushi da ta fahimci Ibteesam d'in.

D'akin ta shiga ta zauna a bakin gado duk a tunanin ta sunyi bacci sai taga sun mik'e sun kalle ta Zahra tace, "Anty Ibteesam mun d'auka a wajan sa zaki kwana". Jidda ta amshe da fad'in, "Gaskiya Anty Ibteey yana son ki sosai dan Allah ki amince masa mana, kinga fa mijin kine baiyi amfani da wannan power da yake da ita ba akanki yake miki magana cikin taushi."

Ajiyar zuciya tayi kawai bata ce musu komai ba ta mik'e ta shiga band'aki..

Koda ta fito bata kula su ba ta shiirya ta cikin kayan da Jidda ta kawo mata ta kwanta, juyi kawai take yi amma ta kasa baccin da ta kulle ido Zaid take gani a yanayin rashin lafiyar da ta barshi, duk da fitar da sukayi d'azu Anty Amina ta sanar da ita komai akan dalilin da ya saka yake mata haka dan taga ta damu da yawa amma ai ba hujja bace tunda matar baban sace kuma tana gaba dashi, ita kam tayi alqawarin sai ranar da yayi nadamar abinda yake yiwa maman ta ya d'urkusa ya bata hak'uri sannan zatayi tunani akan zama dashi a matsayin miji.

Da wannan dogon tunanin nata bacci ya d'auke ta.




*Dan Allah kar a fitar min da labari.*


*?ASAITAR SO!*

*54_55*

Not edited>??



Washe gari haka Ibteesam ta tashi sukuku kamar wacce aka zarewa kuzarin ta haka ta koma, a haka ta karya zuciyar ta cike da tunanin halin da yake ciki duk da tayi ci alwashin baza taje duba shi ba.

Har suka gama karyawa suka shirya bata saka Zaid a idon ta ba bata ji kuma wanda yayi maganar sa ba, har suka gama shiryawa aka tafi gidan Mummy ita da Zahra Jidda ma tayi gida bata ganshi ba.

Sun jima da tafiya ya sakko babu kowa a falon dan yaji fitar Daddy, falon Anty Amina ya shiga nan ma tsit babu motsin kowa har zai wuce yaga Anty Amina ta fito daga d'aki tana waya ya kalle ta itama ta kalle shi ta wuce shi ba tare da tace komai ba, tsaki yaja kawai ya fita daga falon ya koma sama dan a yanayin da yake ciki baya tunanin zai iya tuk'a mota, waya ya d'auka ya kira layin Zahra nan take sanar dashi suna gidan Mummy dole haka ya sakko ya hau mota ya nufi gidan Mummyn.

Tun zuwan su gidan Mummy ta rude ta rasa inda zata saka Ibteesam sabida farin ciki, ta kawo mata wannan ta kawo mata wancan har Ibteesam ta gaji da cin abinci, a nan falo suka baje ana kallon hotunan sunan Ibteesam d'in ana hira da nishad'i, bud'e k'ofar da akayi ya saka suka d'ago kai suna kallon wanda ya shigo, "A'a Zaid lafiya kake kuwa?" Mummy ta fad'a tana kallon sa tare da mik'ewa ta isa inda yake dan gani tayi kamar yana juwa, kujera ya samu ya zauna yana lumshe idon sa ba tare da ya furta komai ba har lokacin, "Zahra bani ruwa" Mummy ta fad'a tana zaune kusa dashi tana kallon Zahra, da sauri Zahra ta mik'e ta kawo ruwa Mummy ta bud'e masa ta mik'a masa, d'an kawar da ruwan yayi yace, "Mummy bana so" ya fad'a cikin muryar da take nuna zallar rauni a tare dashi.

"Me yake damun ka haka Zaid? Kaga yadda ka rame kuwa?" Ta fad'a bayan ta ajjiye ruwan a gefe tana kallon sa, ajiyar zuciya yayi ya dafe kansa ya bud'e ido ya kalli Mumny yace, "Ciwon kaine sai chest pain". "Subahanallahi, Zaid amma ka zauna a gida baka je asibiti ba? Kasan yanayin ciwon kan nan naka fa?" Ta fad'a cikin rud'ani tana kallon sa.

"Mummy indai ban samu abinda nake so ba bazan warke ba" ya fad'a yana runtse ido sabida ciwon da yake ji a kansa da k'irjin sa, kallon su Ibteesam tayi kafin ta dawo da kallon ta ga Zaid d'in tace, "Me kake so Zaid? Fad'a min ko meye zan taya ka nemo indai zaka samu lafiya, kai kad'ai nake kalla na tuna y'an uwa na kai kad'ai ka rage min kowa namu ya rasu ka sanar dani abinda kake so kaji".

Kallon ta yayi sai ya d'an saki fuska ganin ta shiga damuwa sosai ya d'an rik'e hannun ta yace, "kar ki damu Mummy zanji sauk'i" ya fad'a yana mik'ewa tsaye, "ina kuma zaka je Zaid? A wannan yanayin da kake ciki bazan barka ka tafi kai kad'ai ba" ta fad'a itama tana mik'ewa tana kallon sa. "Kar ki damu Mummy babu abinda zai faru" ya fad'a yana sakin hannun ta bai kuma kallon kowa ba ya fita daga falon tabi bayan sa har sai da ya tashi motar ya bar gidan sannan ta dawo jikin ta a sanyaye ta zauna.

B'angaren Ibteesam d'in ma hakan take jikin ta yyi bala'in sanyi har tana jin kamar ta tashi ta bishi amma alwashin da ta d'auka a kansa ya hana ta ko kallon sa, Mummy da take cikin tunani tace, "Ko me yake damun sa kuma Allah ne ya sani, Allah ya sassautawa yaron nan abubuwan da suke damun sa, har yanzu ya kasa samun jin dad'in rayuwa tun bayan rasuwar Maryam" Mummy ta fad'a a sanyaye tana kallon wani wajan daban.

"Amin Mummy, Yaya Zaid ai yana cikin wani yanayi a kwanakin nan, daman shi bame yawan shiga mutane da magana ba sai hakan ya saka ya sake zama so silent" Zahra ta fad'a tana satar kallon Ibteesam da tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta a wajan.

Haka dai suka cigaba da hira sama-sama har yamma tayi lokacin dawowar Abba yayi, lokacin da Daddy ya dawo sai da ya shirya yayi sallar magariba ya dawo sannan su Ibteesam suka fito, kasa rufe baki Abba yayi har suka k'araso Ibteesam ta tsuguna tace, "Abba barka da dare" ta fad'a da murmushi a fuskar ta tana kallon k'asa. Maimakon ya amsa sai ya d'ago ta ya zaunar da ita a kusa dashi yace, "Baby yaushe kuka zo?". "Tun safe nazo Abba lokacin ka fita" ta bashi amsa cikin girmamawa.

"Sannun ki da zuwa, lallai yau ina da babbar bak'uwa a gidan nan, ya kika baro mutanen gidan?". "Suna lafiya Abba". Yace, "Masha Allah, ina fatan kina jin dad'in zaman gidan ko?" Ya fad'a da murmushi a fuskar sa. Itama murmushi tayi tace, "Sosai wallahi Abba". "Zahra yanzu kawo mana abinci ki zuba a tray yau gabad'ayan mu zamu ci tare" ya fad'a yana kallon Zahra.

Babu b'ata lokaci aka kawo abinci a k'aton tray suka had'u har Mummy aka ci cikin zallar nishad'i da walwala, sun jima suna hira har sha biyu saura na dare kafin Abba yace kowa yaje ya kwanta dan da wuri zasu wuce Gombe.

Kamar yadda aka tsara k'arfe goma na safe suka d'auki hanyar Gombe.

A b'angaren Zaid haka ya kwana cikin yanayin da bai tab'a shiga irin sa ba, haka ya daure bai sakko ba sai gab da azahar ya tarar da Daddy tare da bak'i hakan ya saka kawai ya fita ya hau mota ya nufi gidan Mummy, tun a gate mai gadi ya sanar dashi basa nan sun tafi Gombe haka ya juyo kamar zaiyi kuka ya dawo gida.

A parking space d'in gidan ya tsaya ya d'auki wayar sa ya kira layin Ibteesam har ta tsinke ba'a d'auka ba, ya sake kira amma ba'a d'auka ba dole ya hak'ura ya fito yana jin zafi a ransa sosai, a falon ya tarar da Daddy da Anty Amina bak'in sun tafi har zai wuce Daddy yace, "Zaid zo nan". Baice komai ba ya dawo ya zauna kansa a k'asa kana kallon sa zaka ga zallan rauni a tare dashi.

"Zaid har yanzu jikin ne?" Daddy ya fad'a yana kallon sa da kulawa, d'an d'ago kai yayi ya kalli Daddyn kafin yace, "naji sauk'i". Daddy yace, "Baka min k'arya me yasa yau zaka fara? Kalle ka fa kowa ya ganka yasan baka cikin hayyacin ka, ji yadda ka rame maganar ka ma ba dai-dai take ba." Numfashi ya fesar kafin yace, "Daddy na jima banji zafin rashin mahaifiya a kusa dani ba sai cikin kwanakin nan, Daddy ina buk'atar mai kulawa da lamari na amma na rasa, hatta kai d'in da nake samun kula daga wajan ka kwana biyu ka watsar dani, Daddy in banyi rashin lafiya ba lafiya zan k'ara?" Ya k'arasa k'arasa fad'a kamar zaiyi kuka muryar sa har rawa take yi.

Kallon sa kawai Daddy yake yi dan bazai iya tuna rabon da yaga rauni kamar haka a tare da Zaid ba, sosai ya bashi tausayi ya tausasa murya yace, "Zaid ya za'ayi na watsar da kai? Kai fa kad'ai na mallaka a duniya in ba kula da kai ba dawa zan kula?". Cize lips d'in sa yayi ya kalli Daddyn yace, "Daddy dan Allah dan Annabi ka cire min son precious a raina ko zan daina jin abinda nake ji a kanta, Daddy in na kai wani lokacin a irin wannan yanayin da nake ciki tsaf zaka zo kaga gawa ta na mutu, ni kad'ai nasan me nake ji a zuciya ta, jiya ta bar gidan nan without my permission bayan tasan bani da lafiya amma bata damu ba ta tafi sabida bata sona, naje gidan Mummyn nan ma ko kallo na batayi ba sai Mummy ce tamin magana, yau na koma wai sun tafi Gombe dangin Abban ta, na kira ta tak'i picking call d'ina, Daddy me na aikata Allah ya jarrabe ni da abinda yafi k'arfi na,?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login