Showing 105001 words to 108000 words out of 171073 words

Chapter 36 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7855

normal amma kasancewar ta yarinya ya saka nayi mata, gaskiya maganar Dr akwai abinda ya gusar da hankalin su ya saka musu k'arfin sha'awa har suka riski kansu a haka."

Dukkan su sunyi shiru babu wanda ya iya magana kafin Dr ya katse shirun da fad'in, "in Allah ya saka suka farka dan anyi musu allurar bacci ko k'arfe nawa zasu kai kar a tashe su dan allurar ita zata saka ga6o6in su suyi dai-dai su kuma dawo hankalin su, in sun farka sai a tambaya aji ko akwai abinda suka sha wanda ya kaisu ga gushewar hankali, dan Zaid d'in yafi macen shan wahala duba da shi ne namiji kuma daman ba lafiyar kirki gare shi ba."

Mummy ta katse shi da fad'in, "kana ji ana anyi mata d'inki amma kace yafi ta shan wahala? Kawai dan ba kai ka duba ta bane yasa kace haka, shi yana magana amma ita ko tari ta kasa yi" ta fad'a cikin tausayin su duka biyu. Murmushi kawai Dr yayi sukayi sallama ya bawa Daddy takardar maganin da za'a siyo musu suka fita ta baya.

Yaya Babba da ya hayo saman ba tare da dukkan su sun lura dashi ba yaji duk abinda likita ya fad'a ya shiga tunani, kenan maganin da aka bata ta zubawa Ibteesam a abinci ita taci, wanda aka bata ta zuba musu ita da Zaid a abinci dan su samu kusanci da juna shi Ibteesam da Zaid suka ci, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ya akayi hakan ta faru? Meyasa baki duba da kyau ba Eman kika zuba,? Yanzu gashi kin kashe kanki, wayyo Allah kaico na na rasa y'ar da nake so sabida son zuciya ta" ya fad'a a fili ba tare da ya sani ba.

Daddy, Anty Amina, Umma, Mummy duk suka zuba masa ido suna kallon sa da mamakin abinda suka ji yana fitowa daga bakin sa da alama bai san a fili yake fad'a ba.


*in nace muku nayi busy ina nufin serious busy d'in nan, ayi hak'uri kqana biyu ana ta samu miskila.*>?'?
*?ASAITAR SO!*

*60_61*

Not edited>?'?




Ganin irin kallon da dukkan su suke masa ya saka shi ya dawo hankalin sa a rud'e yace, "Ya jikin Zaid d'in?" Ya tambaya cikin borin kunya yana kallon su cikin rashin gaskiya. Daddy ne ya iya cewa, "Da sauk'i, muje k'asan mu barsu suyi bacci" ya fad'a yana yin gaba suma suka biyo bayan ?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? shi suka sauko.
Iya rud'ewa Yaya Babba ya rud'e ya kasa zama sai zagaye yake a cikin gidan duk da da mutane sosai a compound d'in gidan an kafa runfuna ana zaune ana cin abinci mai rai da lafiya kamar ba gidan mutuwa ba, Burin Yaya babba bai wuce su keb'e da Hajiya Batula ba su tattauna akan maganar amma yasan babu dama gashi hankalin sa yak'i kwanciya gabad'aya.

Sai gefen magariba Zaid ya farka ya kalli agogo ganin lokacin Sallar la'asar har ya wuce na magariba ya kusa ya saka shi ya mik'e zaune yana runtse ido, har yanzu shi kam bai koma dai-dai ba jikin sa na ciwo haka kansa, komai nasa a sage yake jin sa, kallon inda take kwance yayi yaga bacci take hankalin ta a kwance da alama baccin yana yi mata dad'i, murmushi yayi yana kallon yadda take bacci cikin kwanciyar hankali sai yaji nutsuwa na ratsa shi ya kafa mata ido yana kallon ta hankalin sa na sake kwanciya.

Tunawa da yayi baiyi sallah ba ya shi ya mik'e yana rik'e bayan sa ya shiga band'aki, sai da yayi wanka ya sake gasa jikin sa sosai da ruwan zafi sannan yayi alwala ya fito, yana shiryawa yana kallon ta har ya gama ya tayar da sallah yana yi yana runtse ido sabida ciwon da k'ugun sa da bayan sa suke masa in ya duk'a dak'yar yake d'agowa, a haka ya idar lokacin anyo kiran magariba ya bi jam'i, bayan an idar ne yaji cikin sa kamar an kwashe komai a ciki sabida yunwar da yake yi ba kad'an bace, mik'ewa yayi yana takawa a hankali ya fito falon yana kallon sa kamar wanda yake neman wani abu, small cafe d'in sa ya nufa amma sai yaja ya tsaya yaji baya sha'awar coffee ko tea kawai indomie yake son ci.

K'ofar da zata sada shi da waje ya bud'e kasancewar babu haske baya gano wad'an da suke tsaye a jikin steps d'in suma kuma baza su gano shi ba, har zai danna switch d'in wutar wajan sai ya tsaya abinda yaji ana tattaunawa ya d'auki hankalin sa, muryar Yaya Babba yaji yana fad'in, "Batula kin kashe mana y'ar mu da kanki, maganin da ya kamata ace waccan yarinyar da take matsayin matar sa tasha shi tasha ita Eman d'in, wanda ya kamata ace Zaid da ita sun sha shi da yarinyar suka sha, yanzu alhakin kisan Eman yana kanki" ya fad'a kamar zaiyi kuka sabida bak'in cikin da yake ji a zuciyar sa.

Dafe k'irji tayi tace, "Na shiga uku na, a ina kaji wannan labarin?". Hararar ta yayi yace, "zan miki k'arya ne? Ko kuma duk zaman da ake kinga Zaid ko ita yarinyar? Nace kin gansu?" Ya fad'a a fusace yana jifan ta da banzan kallo. Shiru tayi alamun tunani kafin tace, "Ban gansu ba." Yaja dogon tsaki sannan yace, "To maganin da kika bata ta zuba susha ita da shi wannan yarinyar ce tasha dan yanzu dukkan su suna kwance abinda muke gudu ya faru" ya fad'a yana tafa hannu.

"Na shiga uku na lalace na kashe y'a ta da kaina, meyasa Eman bata kula dakyau ba ta sha wanda ya kamata ace matar tasa tasha,? Sai da na jaddada mata ta kula, Wayyo Allah kaico na ni Batula" ta Fad'a cikin kuka. "Duk ke kika ja ai tun farko nace miki ayi aikin da zai lalatawa yaron nan kuzarin sa na d'a namiji amma kika ce ba haka ba kina so wani abun ya shiga tsakanin su da Eman, gashi nan bai shiga ba Eman ta mutu shi kuma ya kwana ya wuni tare da wacce muke son ta mutun, na tsani yarinyar wallahi" ya fad'a kamar ya zabga mata mari sabida yadda yake hayayyak'o mata.

Kasa magana tayi sai kukan da take yi a hankali tana jin yadda zuciyar ta take mata zafi sosai, katse ta ya sake yi da fad'in, "Na sha fad'a miki Amina munafuka ce ba'a cikin mu take ba wayo take mana tana jin sirrin mu tana zuwa tana wargatsa komai, ki duba lokacin da aka bawa Zaid guda meyasa bata juye gubar ba ta zuba kad'an,? Kafin gubar abubuwa nawa muka bata ta bashi amma kullum magana d'aya baya cin abincin ta, naji komai da kunne na lokacin da suke tattauwa da Abubakar bata tab'a zuba masa komai ba mu ta mayar shashashai tana amfani damu tana jin sirrin mu tana zuwa ta wargaza, gashi nan muji muna gani y'ar ta ta auri Zaid har ya kaisu ga abinda muke gudu duka sanadin sakacin ki na banza da wofi."

Cikin kuka tace, "Nayi tunanin hakan na kuma jima da sanin Amina ba a cikin mu take ba shiyasa na ajjiye ta a gefe na d'auki Eman, to wallahi basu isa ba dukkan su ran Eman bazai tafi a banza ba, sai na d'auki fansa wallahi" ta fad'a cikin d'aga murya kad'an tana kallon sa, kallan waje yayi yaga babu wanda yake zuwa wajan ya dawo da kallon sa gare ta yace, "yauwa abinda nake so naji kenan daga bakin ki kar mutuwar Eman ta saka ki saduda, lokaci? mutuwar Eman ne yayi ko bata wannan hanyar ba sai ta mutu dan haka yanzu muka fara, tunda abin bazai yu ba zamu fara musu zagon k'asa na farko sa mun raba Amina da Abubakar, na biyu mun raba Zaid da yarinyar sannan komai namu zai yi dai-dai yadda muke so, ina fad'a miki yanzu ne da mu fara shiri da wuri". Share hawayen ta tayi cikin gamsuwa da maganar sa tace, "wannan a rbuce yake" ta fad'a tana sake goge idon ta.

"Shikena muje yanzu zuwa gobe komai zai fara tafiya yadda muke so" ya fad'a yana fita itama ta biyo bayan sa.

Zaid da yakee tsaye yaji komai ya koma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, kenan daman su suka zuba musu abinda ya gusar musu da hankali? Haba no wonder mana lokaci d'aya suka birkice shida Ibteesam d'in, amma ame aka basu suka sha, mik'ewa yayi ya koma d'akin dan ji yayi yama daina jin yunwar, kofin da Ibteesam ta shigo dashi ya gani ya d'auka amma babu d'igon lemon ko kad'an a ciki hasalima kofin ya bushe, ajjiye shi yayi ya juya yana kallon ta yana tuna duk abinda ya faru a cikin kansa.

Tabbas itace ta fara ciwon ciki sannan shi daga nan ta fara shigewa jikin sa tana shafa masa jiki shima kuma bai san lokacin da ya biye mata ba, zafi zafi suke komai dukka su biyun, ajiyar zuciya ya sauke ya sake kallon Ibteesam d'in tausayin ta yana sake bin jikin sa yana jin amon sautin k'arar da tayi kamar a lokacin tayi, runtse ido yayi tsigar jikin sa ta tashi ya bud'e idon ya kalle ta yana jin new feeling na sake ratsa shi, a lokacin idon ta fara bud'e tana kallon d'akin mayar da ido tayi ta lumshe kafin ta kuma bud'ewa tana kallon d'akin, a hankali ta fara motsawa zata mik'e zaune bayan ta ya rik'e ta furta, "oushhh" ta fad'a bayan ta mik'e zaunen tana dafe kanta.

Ta jima a haka kafin ta d'ago kai ta kalli d'akin tana sauke numfashi, a hankali ya tako inda yake ya zube guiwowin sa a k'asa ya rik'e hannun ta yana kallon idon ta, itama idon ta na cikin nasa kafin ta saukar da idon ta k'asa tana numfashia hankali, baice komai ba ya mik'e ya kama hannun ta duka biyun ya mik'ar da ita tsaye, "oushh zafi" ta fad'a komawa ta zauna tana runtse ido sabida azabar da taji tana shiga cikin jikin ta, baice komai ba sai fuskar sa da ta nuna yanayin tausayi ya sake mik'ar da ita ta sake komawa ta zauna sai kawai ta fashe da kuka, tagumi yayi daga tsayen kawai yana kallon ta cikin rashin sanin abinda zaice mata, ya san dole tayi kuka dan ba k'aramar wahala tasha ba duk da shima yasha amma yasan bai kama k'afar ta ba tunda ita har da d'inki, ajiyar zuciya yayi tare da lumshe idon yana jin yadda kukan ta yake ratsa jikin sa zuciyar sa ta fara bugawa da sauri dan ji yake kukan ta tafiya har cikin zuciyar sa hankalin sa ya kuma tashi ya sunkuya dak'yar ya d'auke ta cak sai cikin bathroom.

A gefen jacuzzi ya ajjiye ta ta zauna ya kunna water heater ya had'a mata ruwan zafi ya kalle ta kawai ya fita daga band'akin, yana tsaye k'ofar band'akin yana jiran fitowar ta duk ta jima sosai kafin yaji takun ta tana niyar fitowa, k'ofar ya bud'e mata yaga yadda take takawa tana runtse ido sai shima ya runtse idon yana kawar da kansa gefe, sake d'auko ta yayi ya dawo da ita cikin d'akin ya ajjiye ta a gefen gado, kama k'ugu yayi yana tunanin abinda zai bata ta saka gashi lokacin sallah yana wucewa, sai kawai ya bud'e wardrobe d'in sa ya d'auko jallabiyar sa mai k'aramin hannu kalar maroon ya mik'o mata, kallon sa tayi kafin ta mayar da idon ta k'asa ta mik'a hannu ta karb'a ya koma gefe yana kallon ta, ba tare da ta mik'e ba ko ta saka wani abu ba kawai ta zura doguwar rigar sannan ta mik'e dak'yar ta zare towel d'in ta koma ta zauna tana hakki.

K'aramin mayafin ta ya d'auko ya mik'o nata tare da fad'in, "La'asar, magrib and i'sha" ya fad'a dan ya jiyo kiran sallar i'sha yana kallon ta kamar ya had'd'iye ta.

Dak'yar aka samu akayi sallolin nan kafin ta mayar da kanta ta kifa akan guiwowin ta tana cigaba da kuka, a gaban ta ya zauna ya tankwashe k'afa yana kallon ta tare da yin tagumi, shifa baya son yaji tana kuka ko kad'an, "Precioussss! Ya furta kamar wanda yake kuka ya kira sunan mutum, bata d'ago ba ba kuma ta amsa ba sai kuka da take yi, dafe kai yayi kamar zaiyi kukak shima yace, "Precious pls stop crying" ya fad'a yana dafe goshi yana jin zafi sosai a ransa, dan ji yake kamar ana masa ruwan abu mai zafi a zuciyar sa.

"Are you hungry right?" Ya fad'a yana matsowa sosai jikin ta ya zube hannun sa a kan guiwar ta yana k'okarin d'ago fuskar ta, ture hannun sa tayi daga jikin ta tana cigaba da kukan ta, "Oh Allah Precious ya kike so nayi ne,? I know am hurted u but kin sani ba'a son raina hakan ya faru ba, I'm sorry, I'm sorry pls" ya Fad'a yana mik'ewa a kan guiwowin sa yana rik'o hannyen ta, k'okarin kwacewa take ya rik'e ta sosai ta sake fashewa da kukan ba tare da ya kalle ta ba, jawo ta yayi ya rungume ta tsam a k'irjin sa yana jin yadda take kukan na ratsa cikin zuciyar sa, mayafin kanta ya zame yana shafa kitson kanta yana fad'in, "I'm sorry precious, I'm sorry" abinda yake fad'a kenan yana runtse ido yana jin yadda kukan ta yake shiga zuciyar sa sosai, bugun da zuciyar sa take yi shi kawai take saurara tana cigaba da kukan ta.

K'arar wayar sa yaji daga can gefe ya sake ta ya k'arasa wajan wayar yana dubawa yaga sunan Daddy kamar bazai d'auka ba sai kuma ya d'auka tare da sakawa a kunne, "Zaid ya jikin naku?". Cikin yanayin damuwa yace, "Daddy she's still crying". "Ka rarrashe ta kaji Zaid, yanzu ka tashi ka karb'i abinci kuci". Da to ya amsa ya kashe wayar ya mik'e dak'yar ya bud'e k'ofar ya fita ya tarar da Zahra tsaye da tray d'in abinci a hannun ta,? kamar ana hankad'a haka yake tafiya ya karb'i tray d'in kamar zai subuce a hannun sa tace, "Sannu ya Zaid" ta fad'a cikin tausayi dan gani tayi ya koma wani iri kamar bashi ba.

A gaban ta ya ajjiye tray d'in ya bud'e abincin duka, jellop d'in pasta ce wacce taji kayan lambu sai khamshi take yi, d'aya flasks d'in kuma farfesun naman rago ne mai ruwa sosai sai tea da kuma kayan had'a tea d'in, tea d'in ya had'a mata mai kauri ya k'arasa gaban ta yace, "Precious badan ni ba ki daina wannan kukan pls, karb'i kisha tea" ya fad'a yana kai kofin bakin ta.

Tana jin yunwa hakan ya saka ta karb'i kofin a hannun sa tana sha a hankali, yamutsa fuska tayi tana jin tea d'in yana d'aci-d'aci a haka ta daure ta sha kad'an ta ajjiye kamar jira yake ya sake mik'o mata plate d'in abincin, ba laifi ta d'an ci kad'an dan tayi loosing appetite ba wani dad'in sa take ji ba, ajjiye plate d'in tayi ta mayar da kanta jikin gadon tana sauke numfashi a hankali.

Yadda tayi shima yayi ya ya rik'e hannun ta d'aya yana kallon candilier d'in da ta haske d'akin ta bada kalar jah, sai yaji baya jin yunwar burin sa bai wuce yaga tana walwala ba amma gashi ko magana tak'i masa hakan ya saka shi yaji komai ya fita a kansa.

"Talk to me precious, bazan iya jure fushin nan naki ba" ya fad'a yana murza hannun ta, bata ce komai ba sai abinda ya faru da yake dawo mata kwakwalwar ta daki-daki, tun daga lokacin da ta sha lemon shima yasha da yadda suka fara watsar da sutturar jikin su har lokacin da ta suma, runtse ido tayi tsigar jikin ta ta tashi ta kawar da kai gefe can k'asan mak'oshi tace, "Mummy, Mama, Umma" abinda tace kenan in badan yana jikin ta ba da bazai ji ba.

"Kiyi hak'uri precious duk abinda ya faru bada sani ba bane yadda kikayi loosing control haka nima nayi, ban san ta yaya hakan ta kasance ba" ya fad'a kamar zai mata kuka. Bata amsa ba ta sake maimaita abinda ta fad'a a d'azu, wayar sa ya jawo ya kira layin Mummy amma bata d'auka ba, numfashi ya fesar dan shi bashi da number Anty Amina balle ya kira ta, cikin kuka sosai ta sake maimaita abinda ta fad'a duk sai ya rud'e ya kira layin Daddy, "Daddy where is she?". Daga can b'angaren Daddy yace, "Who?". "Your wife" ya fad'a murya a k'asa, Daddy yace, "Oh bama tare ka mata waya". Dafe kai yayi kad'an kafin yace, "her number". Daddy yace, "okay i will send it to u" yana fad'ar haka ya kashe wayar shi kuma ya tsurawa wayar ido yana jiran shigowar sak'on Daddy.

Ba jimawa sak'on ya shigo ya zubawa wayar ido yana kallon number a zuciyar sa yana ta daunting d'in kiran nata, kallon Ibteesam d'in yayi yaga har lokacin kukan take bai san lokacin da ya danna kiran wayar tata ba, bugu biyu ta d'auka tare da sallama, shiru yayi ya kasa amsa mata sai saliva da ya had'd'iye yana lumshe ido, daga can b'angaren ta kuma cewa, "Hello". Dak'yar ya iya furta, "ammm she want to see u". Daga can b'angaren Anty Amina tayi shiru tana so ta d'auki murya amma maganar ta canja mata hakan ya saka tace, "Wacece? Wake magana?".

Runtse ido yayi sabida gagamurin takaicin da ya tokare masa mak'oshi, a rayuwar sa ya tsani ya kira waya ace waye baya k'aunar hakan yanzu ransa zai b'aci, niyar katse kiran yake amma sai ya kalli Ibteesam sai yaji bazai iya ba sai ya sake cewa, "I'm Zaid" ya fad'a yana cije bakin sa. Murmushi Anty Amina tayi tace, "au Zaid ina jinka." Mamaki ya sake kamashi kenan tana nufin sai ya kuma maimaitawa, shiru yayi kawai bai magana ba itama kuma bata ce masa komai ba, "kaga Zaid in baka da abin cewa zan kashe waya ta" ta fad'a cikin d'an fad'a kad'an.

Tabbas badan Ibteesam da take son magana da ita ba babu abinda zai hana bai dura mata ashariya ba amma hakan ya daure ya kuma cewa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login