Showing 114001 words to 117000 words out of 171073 words

Chapter 39 - KASAITAR SO Completed Book by Nana Haleema.doc

13 Oct 2025

7832

ta dake shi.

Mik'ewa tsaye yayi yace, "ina son maman ki precious ina sonta, zan bata hak'uri indai hakan zai saka ki soni ki kuma zauna dani, zan d'urkusa na bata hak'uri koda zata yanka ni da wuk'a amma ki daina cewa na rabu dake bazan iya ba zan iya mutuwa precious" ya fad'a yana had'e hannayen sa duka biyun jikin sa har rawa yake dan sosai yake jin zazza6i yana k'okari rufe shi.

Kallon sa tayi kafin tace, "On your own nake so ka bata hak'uri bawai sabida ni ba, koda ina sonka indai baka son Mamana zan iya rabuwa dakai balle ma bana son ka ba kuma zan soka ba" bata jira taji me zaice ba ta fice a guje daga falon.

Dafe kai yayi ya zauna akan kujerar wani irin zafi yana ratsa ko wanne jikin sa, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine abinda yake furtawa zuciyar sa na masa zugi sosai, ji yake kamar ana saka wuk'a ana yankar zuciyar sa sabida yadda yake ji tana yi masa zafi ga jikin sa yayi bala'in zafi lokaci d'aya, wayar sace tayi k'ara har zai k'yale sai kuma ya danna kawai ya saka ta a speaker ba tare da yayi magana ba daga can b'angaren Daddy yace, "Zaid ance malaysia na neman ka akan sabon sample d'in da kuka tura kace baza ka ba ko? To yanzu nan ka shirya na siya maka ticket oh ready nasan kana da visa dan haka yanzu ka shirya kaje ai kwana biyu zakayi jirgin ka k'arfe shida zai tashi yanzu kuma kaga 5:30, kar kace min A'a ka shirya kawai ka tafi" bai jira mai zaice ba ya yanke wayar kawai.

Dukan kansa yayi da duka hannun sa yana jin wani irin kuka na tawo masa amma ya danne ya mik'e dak'yar ya shiga d'aki ya d'auki trolley ya fara zuba kaya ba tare da yasan abinda yake zubawa ba, kulle jakar yayi ya d'auki jakar tare da passports d'in kansa na juyawa ya fito daga d'akin nasa, k'asan yake sakkowa amma gani yake steps din nayi masa nisa haka yake kulle ido ya bud'e har ya sakko ya fara jiyo muryar Mummy sama-sama a gidan.

Mummy da tazo sake duba shi itace ta kula da sakkowar sa da kuma yanayin da yake ciki ta k'araso tace, "Zaid lafiya kake kuwa?". Rungume ta yayi yana sauke ajiyar zuciya jikin sa na bala'in rawa kamar an jona masa shocking kar kar kar har ita motsawa take yi, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Zaid lafiya?" Ta fad'a tana bubbuga bayan sa jin yadda zafin jikin sa yake shiga jikin ta.

Saukar abu mai d'umi Mummy taji a bayan ta hakan ya tabbatar mata da kuka yake, "Subahanallahi Zaid kuka? Me ya faru? Ka sanar dani dan Allah" Ta fad'a tana k'okarin d'ago shi amma ta kasa sabida ya rik'e ta gamm kamar zai b'alla ta, "Mummy mutuwa zanyi, tace bata sona wai sai na sake ta Mummy in babu ita zan mutu" ya fad'a a rarrabe sabida yanayin da yake ciki, "yi kukan sosai Zaid zaka ji dad'i, kayi kuka sosai zaka daina jin azabar sosa" ta fad'a murya a sanyaye tausayin sa yana sake kama ta lokaci d'aya itama hawayen ya cika mata ido, inda tana da iko ya za'ayi ta bar gudan jinin y'ar uwar ta yana shan wahala haka.

Kukan kuwa yake sosai mara sauti hawaye na zuba kamar an kunna famfo, babu k'akkauwa, itama Mummy kukan ta fara sabida tausayin sa bata san lokacin da ta fara kukan ba, Anty Amina ce ta fito ta same su a haka tace, "Subahanallahi Mummy lafiya?". Jin maganar Anty Amina ya saka ya saki Mummy zuwa lokacin ya fara gani biyu-biyu, kawai gani sukayi ya zube a k'asa yana fad'in, "Tace baza ta soni ba bana sonki, I'm sorry for anythings? pls forgive me" ya fad'a lokacin ya fara tari ga hawaye dake sauka a idon sa.

Jikin Anty Amina yayi bala'in sanyi hankali ta ya tashi a lokacin Daddy ya fito yana fad'in, "wai Zaid bai sakko ya tafi ba saura....." maganar ta mak'ale ganin sa a zube a kan guiwowin sa yana kuka, "Innalillahi, lafiya?" Daddy ya fad'a yana k'arasowa wajan.

Mik'ewa tsaye yayi Daddy ya zuba masa ido ganin yadda yake kuka duk sai abin ya d'aure masa kai dan bai san abinda ya saka shi kukan ba, tarin sane yayi gaba kansa yayi bala'in sarawa falon ya fara juya masa yayi saurin rik'e table din dining, tarin ne yayi k'arfi sosai hankalin su ya tashi suka yo kansa dai-dai lokacin da wani gudan jini ya fad'o daga bakin sa ya sulale a wajan ya zube kamar gawa babu alamun numfashi a tare dashi.


Ina tunanin fa wannan update d'in na yau da gobe ne >??=ض?
@&?=ض?
@&?


*yarinyar nan tana wahalar mana da Zaid wallah.*>?y?>?y?

*?ASAITAR SO!*

*64_65*

Not edited>?'?




Hankali su Daddy ba k'aramin tashi yayi ba sai safa da marwa suke a k'ofar d'akin da aka kwantar da Zaid ana jiran fitowar Dr's d'in da suke ciki a kansa, kuka sosai Mummy take haka ita kanta Anty Aminan kuka take sosai dan sun tsorota da yanayin Zaid d'in tunda a gaban su komai ya faru, sunfi mintina talatin a wajan kafin Dr ya fito yana zare handgloves yana sharce gumin goshin sa, Daddy ya matso kusa dashi yace, "Dr ya jikin sa?". Ajiyar zuciya yayi yace, "Kaine mahaifin sa?". Daddy ya d'aga kai alamun eh, ajiyar zuciya Dr yayi yace, "I'm sorry to say yana cikin bad condition wanda babu abinda yake buk'ata a tare daku sai addu'a dan yanzu haka ma an wuce dashi ICU sabida yanayin jikin nasa dole sai an killace shi a inda babu hayaniya". Baya Daddy yayi kamar zai fad'i Dr yayi saurin rik'o shi yana fad'in, "ka kwantar da hankalin ka zai samu lafiya insha Allah." A lokacin Dr Auwal ya iso da saurin ya rik'e Daddy ya zaunar dashi kafin ya wuce ICU d'in.

Hankalin Daddy ya tashi haka su Mummy ma suna ji ana kiran sallah amma sun kasa barin wajan suje suyi sallah har sai da Dr Auwal ya dawo ya kalle su jikin sa mutuk'ar sanyaye yace, "Alhaji kamar nace a daina barin sa cikin damuwa sabida ciwon zuciyar sa ko?". Sai Anty Amina ce ta iya amsa da, "Eh haka ne likita." "To gaskiya damuwar da ya shiga yau tafi ta ko yaushe, na farko ciwon nan nasa wanda ya jima bai tashi ba ya tashi sannan ga condition na heart attack a tak'aice babu abinda yake buk'ata sai addu'ar ku dan yanzu yana ICU" Dr ya fad'a da damuwa yana kallon su.

Shiru Daddy yayi yana lumshe ido Mummy da Mama kuwa kuka suka sake fashewa dashi, Dr Auwal ya kalli Daddy yace, "Alhaji hak'uri za'ayi kaga kaima ba cikakkiyar lafiya ce da kai ba addu'a kawai yakr buk'ata a yanzu insha Allah zai samu lafiya."

Babu wanda ya amsawa Dr Auwal sabida dukkan su ba'a hayyacin su suke ba ko tunanin halin da Zaid d'inyake ciki yake yi, ganin hakan ya saka Dr ya samu nurse suka shiga dasu Mummy cikin wani d'aki da aka tana mai kyau shi kuma ya shiga da Daddy office d'in sa dan yana buk'atar hutu.

Mummy ta kalli Anty Amina da take kuka tace, "Ina ita Babyn take?". Sai da ta shayar da hawayen nata sannan tace, "Tazo ta same ni bayan la'asar tana so taje gidan Umman ta sai nace taje ta tambaye ta had'a masa tea ta kai masa, ba jimawa ta dawo tace min yace taje nayi mamaki sosai sabida nasan babu yadda za'ayi ya k'yale ta ta tafi ita kad'ai duk abinda yake yi zai katse shi ya kaita amma haka nayi shiru jin tace shine yace d'in ta tafi, yanzu haka tana can gidan."

Mummy tayi shiru bata ce komai ba dan bata da abinda zata ce a akan hakan.

A can gidan Umma kuwa tun zuwan Ibteesam ake ta farin ciki ita kanta Umman taji dad'in ganin ta sai nan ake da ita, suna zaune da Umma suna hira Umma take cewa, "Ibteesam amma dai yanzu kin amince da Zaid matsayin mijin ki ko?". Shiru tayi kamar mai tunani kafin tace, "Wallahi Umma ni har yanzu bazan ce ga abinda nake ji a kansa ba" ta fad'a tana wasa da gefen mayafin ta. "Kamar ya kenan?" Umma ta tambaya. Ajiyar zuciyar tayi tace, "Umma ni wallahi ban san me nake ji a kan sa ba har yanzu" ta fad'a kamar tayi kuka.

"Kina son sa kenan?" Umma ta jefo mata tambayar tana kallon ta, a raunane tace, "ban sani ba nima kawai dai nasan bana jin haushin sa kamar a da". Umma tayi murmushi tace, "Yanzu in aka ajjiye miki Khalid aka ajjiye miki Zaid wanne zaki d'auka?". Shiru tayi tana tunani dan ita wallahi ta manta da wani Khalid ma a rayuwar ta sai da Umma tayi maganar sa yanzu ta tuna, tana jin Zaid a jikin ta sosai dashi take kwana dashi take tashi a zuciyar ta, tana farkawa daga bacci shi take fara tunawa haka fuskar sa ce take fara fad'o mata a rai musamman daga lokacin da suka zama d'aya shi da ita, tana jin nishad'i da farin ciki a duk lokacin da yazo kusa da ita mak'urar jin dad'i kuwa taji yana fad'a mata kalmar ina sonki hakan yana faranta mata sama da komai a duniya, Umma da taga tayi nisa a tunani tace, "Kinyi shiru." Sai da ta sauke numfashi sannan tace, "Gaskiya Umma ni na manta da wata halitta ma a duniya Khalid". Umma tace, "kenan Zaid zaki d'auka?". D'aga kai tayi alamun eh.

Umma tace, "kina son sa Ibteesam". Kamar zatayi kuka tace, "Na sani Umma, amma abinda yake yiwa Mama shine yake b'ata min rai naji bazan iya zama dashi ba at all, baya ganin girman ta ko kad'an harara ce take had'a su wannan dalilin yasa nake jin haushin sa." Umma tace, "Eh hake ne baza kiji dad'i ba ko kad'an da mahaifiya ba abar wasa bace duk da na gari bazai ga ana wulaqanta iyayen sa yayi shiru ba, amma ba kince masa sai ya bata hak'uri ba?". D'aga kai tayi alamun eh tace, "na fad'a masa Umma amma kin san halin sa ba komai ake saka shi yayi ba sai yaga dama." Umma ta gyara zama sosai ta fuskance ta tace, "yana son ki Ibteesam babu abinda bazaiyi a kan ya same ki ba, Ibteesam samun miji a yanzu kamar Zaid yana matuk'ar wahala a duniya, sabida samu soyayya ta gaskiya irin wacce Zaid yake miki tayi wahala a wannan zamanin, Zaid yana sonki Ibteesam kema kuma kina son sa, ya rasa mahaifiyar sa a lokacin da yake matuk'ar buk'atar ta ya rasa mai rarrashin sa ya bashi shawara duk da mahaifin sa na k'okari a kansa amma ba kamar uwa ba Ibteesam, uwa ta wuce duk tunanin ki, uwa tana d'auke matsayin uba da kuma y'an uwa duka ita d'aya sabida duk abinda uba zaiwa d'an sa uwa zata iya, duk abinda d'an uwa zai yiwa d'an uwan sa uwa zata iya, in ka rasa mahaifiya ka rasa wani babban jego daga cikin rayuwar ka Ibteesam, ga mak'iyi da suka sako shi a gaba shi da mahaifin nasa ta ko wanne b'angare sun saka shi a tsakiya, samun ki shine kad'ai kwanciyar hankalin sa a yanzu matuk'ar ya rasa ki kuma rayuwar sa na cikin hatsari kasancewar sa mutum mai zafin gaske wanda kuma yayi zurfi a soyayyar ki, ki amince dashi matsayin mijin ki Ibteesam sabida yanzu keda shi kun zama d'aya ya sanki kin sanshi rabuwar ku a yanzu kin dawo bazawara farashin ki ya karye duk da k'arancin shekarun ki, kiso Zaid Ibteesam domin yana sonki zai kula dake fiye da ko wanne d'a namiji, domin samun wanda yake son ka yafi samun wanda kake so" Umma ta k'arasa fad'a tana rik'e hannun Ibteesam d'in.

Shiru Ibteesam tayi maganar Umma na shiga jikin ta har Umma ta kai k'arshe sannan tace, "Haka ne Umma, insha Allah zanyi k'okarin ganin komai ya daidaita" ta fad'a tana saukar da idon ta k'asa.

"Yauwa ke kefa, kinga yanzu sai a saka lokacin biki ayi biki ki tare a gidan mijin ki ko?" Ta fad'a cikin zolaya tana kallon ta, rufe fuskar ra tayi da mayafi tana murmushi, Umma tace, "yanzu ma zan fara gyara ki duk da angon ya riga ya....." da sauri ta katse Umma da fad'in, "Umma kunya nake ji" ta fad'a tana sake rufe fuskar ta, murmushi Umma tayi sosai tace, "Allah yanzu zan fara gyara ki dan nasan bikin ba wani d'aukar lokaci zaiyi ba." Ibteesam tace, "Umma wai Khalid na zuwa kuwa?". Umma tace, "yana zuwa mana." Tace, "to Umma me yake yi kuma?". Umman tace, "ranar da Zaid yazo kuka fita ai fitar ku kenan babu jimawa Khalid d'in yazo shine Abban ku ya sanar dashi kina da aure yayi miki fatan alkhairi duk da baiji dad'i ba yanayin sa ya nuna, ya kira ki ma take har sau biyu yayi miki fatan alkhairi baki d'auka ba cikin ikon Allah sai Allah ya canja masa da yayar ki." Ibteesam cikin mamaki tace, "Yaya ta kuma? Wacce kenan?".

Umma tace, "Asiya mana, kin san ai ba k'aramin tsorata tayi da Zaid ba da yazo yayi wannan abin a gidan nan sai da tayi jinyar fuskar ta fa dan kumbura tayi sosai, daga ranar kuma sai ta zubar da makaman yak'in ta akan Zaid shi kuma Khalid a lokacin yace ita yake so dan har manya ma sun shiga maganar kud'i za'a kawo". Jimm Ibteesam tayi kafin tace, "Allah ya sanya alkhairi." Umma ta amsa da amin kafin ta mik'e ta shiga d'aki.

Ibteesam kuwa duniyar tunani ta shiga haka kawai jikin ta yake bata there is something wrong amma ta rasa gane ko meye, ajiyar zuciya tayi tana tunanin halin da ta saka shi a ciki kafin tawowar ta gidan duk sai taji ya bata tausayi lokaci daya hankalin ta yayi kansa kawai shi take so ta gani, wayar ta ta d'auko for the first time ta kira shi amma shiru ba'a d'auka ba ta sake kira nan ma ba'a yi picking call d'in ba sai duk ta tsinci kanta cikin tashin hankali, haka ta daure ta mik'e tabi bayan Umma jikin ta sanyaye matuk'a.

********

Da mamaki Hajiya Luba take kallon Hajiya Batula tace, "Yanzu Batula bazaki hak'ura haka ba? Akan wannan abin fa kika rasa Eman amma hakan bazai saka kiyi hankali ba?". Tsaki tayi tace, "Kinga ni in zaki raka ni ki raka ni kawai bikin magaji ai baya hana na magajiya, dan na rasa Eman ai lokacin tane yayi ki bata hanyar sab'anin magani ba zata mutu kuma ke kina tunanin zan bar ran ya ta ya tafi a banza ne ba tare da na d'auki fansa ba? Inaa ai bazai yu ba wallahi, zaki raka ni ko baza ki raka ni ba?" Ta fad'a yana kallon Luba.

Luba ta tab'e baki tana mamkin bak'ar zuciyar kawar tata tace, "Nikam bazan je ba miji na yana nan amma zan miki kwantace sai kuje keda mijin naki tunda dabi'ar ku d'aya." Batula tace, "Eh anji kome zakice kice, a wanne gari yake?". Luba tace, "a katsina, kuma wai yanzu a lokacin nan da ake garkuwa da mutane zaki iya zuwa katsina?" Ta fad'a tana rik'e baki tana kallon Hajiya Batula.

"Me zai haka mu zuwa? Ke wajan biyan buk'ata rai ba'a bakin komai yake ba" ta fad'a tana gyara zama. Girgiza kai Luba tayi tace, "Ahh lallai kinyi nisa baza kiji kira ba a yanzu, shikenan zanje na dubo miki address d'in in na koma dan rubutawa nayia takarda ban tab'a zuwa ba nima sai na turo miki". Hajiya Batula tace, "Yauwa gwara ki turo min da wuri gobe mu ko jibi mu d'auki hanya". Hira suka shiga da yi kafin Hajiya Luba? ta tafi.

Kamar yadda ta fad'a tana komawa ta turo mata da address d'in wajan cikin murya Hajiya Batula ta duba tana murmushin mugunta.

*******

Bayan sallar i'sha Ibteesam tana ta kiran layin drivern gidan Anty Amina bata samu ba sai ta kira Anty Aminan dan ta sanar da ita itama shiru batayi picking ba, sake kira tayi a kira na uku ta d'auka Ibteesam tayi sallama tare da fad'in, "Mama daman zan dawo ne kuma ina ta kiran wanda ya kawo ni baya d'aukar wayar." Daga can b'angaren Anty Amina tace, "Gashi nan na saka shi yazo ya d'auko ki ya kaiki gida". To kawai Ibteesam tace tana so ta tantance yanayin maganar maman tata dan ji tayi kamar ba ita ba.

Tana nan zaune driver ya zo ya kira ta sukayi sallama dasu Umma ta tafi, koda suka isa gidan shiru taji babu kowa ta duba amma bata ga Mama ba, mai aikin Maman ta gani tace, "Yauwa ina Mama ne?". Tace, "Ai suna asibiti tun d'azu." Da mamaki Ibteesam tace, "Asibiti kuma? Waye babu lafiya?". Tace, "Zaid ne" ta fad'a tana komawa kitchen da sauri dan ta d'ora mai a kan wuta.

Dammm gaban Ibteesam ya yanke ya fad'i hankalin ya tashi tayi saurin zama a kan kujera tare da dafe kai, bata san adadin mintinan da ta d'auka ba maganar Anty Amina ta jiyo ta saka ta mik'e da sauri tana kallon ta, yanayin da taga fuskar ta ya saka hankalin ta ya kuma tashi bata kalle ta ba ta wuce d'aki da sauri Ibteesam tabi bayan ta kamar zata kifa. A tsaye ta same ta tana cire hijjabin jikin ta tace, "Sannu da zuwa Mama". Fuska a d'aure ta amsa da yauwa ba tare da ta kalle ta ba ta shiga band'aki.

Alwala tayi ta fito ta tayar da sallah i'sha har ta idar Ibteesam na tsaye a wajan hankalin ta a tashe, kallon ta tayi tace, "Lafiya kika yi min tsaye a ka haka?". Zama tayi a kan carpet tace, "Mama wai bashi da lafiya?" Ta tambaya murya a sanyaye tana kallon mahaifiyar tata. "Shiwa?" Anty Amina ta tambaye ta itama tana kallon ta, k'asa tayi da kanta a hankali tace, "Yaya Zaid."

K'aramin tsaki tayi tace, "au kin damu da ki san bashi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login